2018/08/30

SAUDIYA BATA SHIGAR DA SIYASA CIKIN AYYUKAN HAJJI (لم يسجل على المملكة تسييسها لفريضة الحج)









SAUDIYA BATA SHIGAR DA SIYASA CIKIN AYYUKAN HAJJI
(لم يسجل على المملكة تسييسها لفريضة الحج)









Ministan wakafai da shiryatarwa na kasar Yamen
Dr. Ahmad Adiyah






Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


SIYASANTAR DA HAJJI
MA'AIKATA
Bayani ga 'yan jaridu
SASHEN SADARWA
BA A SAMU SAUDIYA TANA SHIGAR DA SIYASA CIKIN AYYUKAN HAJJI BA KO SAU DAYA
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
10/ Zul-hijjah/1439h
RANA
Ministan wakafai da shiryatarwa na kasar Yamen
MASU MAGANA
SAMUN FALALAR HIDIMAR BAYIN ALLAH, BA TARE DA SUN SANYA SIYASA CIKI BA
SAKON AIKIN

Ministan wakafai da shiryatarwa na kasar Yamen;
BA A SAMU SAUDIYA TANA SHIGAR DA SIYASA CIKIN FARILLAR HAJJI BA  

Ministan wakafai da shiryatarwa na kasar Yamen; Dr. Ahmad Adiyah ya bayyana cewa, ba a taba samun masarautar larabawa ta Saudiya tana shigar da siyasa ko sau daya a cikin lamarin farillar hajjin dakin Allah mai alfarma ba, musamman tare da kasashen da take da matsaya ko sabani na siyasa ba. 
Kuma Wazirin Yaman ya ce: "Lallai tarihin siyasar kasar Saudiya na wannan zamani da muke ciki, yana bada shaida cewa, lallai Saudiya koda tana cikin matsanancin yanayi na siyasa tare da wasu kasashe, to lallai bata taba hana Mahajjata sauke ayyukansu na hajji ba, wannan kuma haka ya ke tun zamanin wanda ya assasa masarautar, wato sarki Abdul'aziz bn Abdurrahman, Allah ya dadada makwancinsa".
Da Ministan Ahmad Adiyah yake tabo matsalar kasar Yaman, sai ya kawo hujjar cewa SAudia ta bada bisar hajji ga mahajjata fiye da dubu 10, wadanda suke zaune a yankunan da suke hannun wadanda suka kifar da gwamnati, kamar garin San'a'a, da Sa'ida, da Imrana, da wasunsu, ya ce wannan kuma dalili ne mai matukar karfi kan yadda hukumar masarautar Saudia take kwadayin kada ta siyasantar da aikin hajji, kuma domin ta baiwa Musulmin da ke kwadayin sauke ibadarsa cikin sauki da jin dadi, koda kuwa yaya akidarsa ta ke.

Ya karfafa maganarsa na cewa lallai masarautar Saudiya bata taba hana wani mutum wanda yay i nufin ziyartar Ka'aba ba, ko-yaya kuwa matsayarsa ta siyasa ta ke, ko mafiskantarsa ta akida, yana mai kara cewa: Saidai matsayar masarautar Saudiya matsaya ce tabbatacciya, kan haninta mai tsanani na a juyar da da ibadar hajji ta zamo minbarorin siyasa, wadanda akidu da kungiyoyi da bangarori da mazhabobi za su yi ta cin-karo da juna.

Kuma Wazirin wakafai da shiryatarwa na Yaman; Dr. Ahmad Adiyah ya karfafa cewa lallai lamarin hajji lokaci ne na addini mai tarin kwarjini, ga duniyar Musulunci, yana da sharrudansa da wajibansa. Kuma biliyoyin mutane suke bibiyan ababen da suke aukuwa a cikinsa; don haka abu ne na dabi'a kasar Saudiya ta shelanta -cikin azama- cewa, tana kin a juya shi ya zama wuri ko filin yada ajendodi na siyasa, kuma lallai Saudiya za ta tsaya kai-da-fata wajen yakan kowane aiki ko dabi'ar da zata sabbaba tashin-tashina, ko ta sanya amincin Mahajjata cikin garari.

Kuma, a nan ya yi nuni kan gudumawa mai girma wanda masarautar Saudiya, karkashin jagorancin Mai hidimar harami madaukaka guda biyu; sarki Salman bn Abdul'aziz Alu-sa'ud –Allah ya kiyaye shi- da mai girma mai jirna gado ma'abucin darajar saurauta yarima Muhammadu bn Salman bn Abdul'aziz, na'ibin shugaban majalisar wazirai, kuma ministan tsaro, (Allah ya kiyaye su). Kuma dukkan hukumomi ma'abuta alaka da hajji, daga cikinsu kuma akwai ministirin hajji da umrah wanda ita ce kamar window ga duniyar Musulunci ta ke saukake hanyar saukake ayyukan ziyartar dakin Allah mai alfarma.

Kuma ya ce: "Duk da cewa wannan shine hajji karo na uku bayan halin yaki, wanda 'yan shi'ar Huthi suka janyo a kasar Yaman, sai kuma taron hadin guiwa wadanda suke karfafa a bar gwamnati halastacciya, karkashin jagorancin masarautar Saudiya, saidai Saudiyyar bata shigar kuma ba za ta shigar da siyasa a lamarin hajji ba, kuma hakan shine tarihinta a tsawon samuwar gwamnatinsu, a'a, sai ma abinda ministirin hajji da umrah a kasar Saudiya ta yi na gabatar da dukkan rangwame ga hukumar hajji ta kasar jamhuriyyar Yaman. Kuma sadarwa yana ci-gaba tsakanin shugaban hukumar hajji, da kuma mai girma na'ibinsa, wadanda duk lokacin da wasu abubuwa masu wahala suka fiskance mu, suna kasancewa masu gaggawan warware mana su, tare da ayyuka masu girma wanda suke wuyansu". 

Kuma ya bayyana cewa lallai, lallai kasar Saudiya a duk lokacin da take fito-na-fito da lamarin siyasantar da hajji, to lallai ita da hakan, tana tsayuwar daka domin hana shigo da tashin-tashinar da ke cikin wannan kasar ko wancan, ko daga tutar wannan kasar ko waccar, a lokacin hajji. Wannan kuma saboda hakan zai munana wa alamomin addini madaukaki, kari a kan cewa hakan zai taba aminci ko zaman lafiyar Mahajjata. Kuma a watan Yuliyo wanda ya gabata, kungiyar kasashen larabawa ta shelanta karfafawanta ga kokarin masarautar larabawa ta SAudiyya, kan rashin siyasantar da lamarin hajji, domin hakan, "layi ne ja, wanda baya halatta a ketare shi".

## Labarin ya kare##

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...