UMRAH; Falalarta da hukunce-hukuncenta
(العمرة فضائل وأحكام)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Bege ne wanda baya karewa,
Da haniniyar shauki wanda bata
yankewa,
Saboda zukatan Mutane suna
gaggawar begen zuwa dakin Allah,
Shi kuma ruwan zamzam yana kosar
da mai kishi,
Kuma daga FALALAR ALLAH TA'ALAH
yadda ya sanya igiyar ziyara ta ke sade tsakanin bayinsa da dakinsa, saboda
"العمرة إلى العمرة كفارة لما بينهما، والحج المبرور ليس له جزاء إلا
الجنة".
Ma'ana: "Umrah zuwa umrah su kan kankare
abinda ya auku a tsakaninsu, Shi kuma hajji mabruri bashi da wani sakamako sai
Aljannah".
Ita kuma UMRAH
Yin harama ne
Da 'dawafi
Da sa'ayi tsakanin Safah da Marwah,
Sai aski ko rage gashi.
SIFAR UMRAH kuma shi ne:
Mutum ya yi harama daga MIKATI, sai ya tube kayan da suke jikinsa, ya yi
wanka, ya shafa turare (a jikinsa kawai banda ihrami).
Sai mutum namiji ya sanya kwarjalle da mayafi,
Kuma abinda yafi falala shine su kasance farare,
Ita kuma Mace ta sanya abinda ta so, na tufafi na halal, ba tare da ta
bayyanar da ado ba, in banda nikabi da safar hannu guda biyu, sai kuma ta rika
suturce fikarta ga Maza, ta hanyar sake khimar dinta akan fiskarta.
Kuma zai yi niyyar shiga wannan ibadar ne, bayan sallar farilla, idan
lokacinta ya shiga, ko kuma bayan raka'oin sunnar alwala ko makamancinta.
Kuma wajibi ne ga Mai harama ya rika nisantar mahzuratul ihrami (abubuwan
da haramun ne a aikata su idan aka yi harama), kamar yin jima'i, da amfani da
turare, da yanke gashi, da farautar dabbar tudu, da neman aure, da kulla aure
ga maza da mata, da lullebe kai, da sanya riga da wanduna da safar kafa da
makamantansu ga mazaje.
Kuma yana daga cikin sunnah YIN TALBIYYAH da fadinsa: LABBAIKAL LAHUMMA
UMRAH,
LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL
HAMDA WANNI'IMATA, LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA.
Kuma ba zai gushe ba yana yin Talbiyyar, har isa zuwa garin Makkah, sai
ya yanke yin talbiyyar, sannan ya fara yin dawafi.
Kuma idan ya iso Masallaci mai alfarma, sai ya shige shi yana mai
gabatar da kafarsa ta dama, yana mai cewa:
BISMILLAH, WAS SALATU WAS SALAMU ALA RASULIL LAH, ALLAHUMMAG FIR
ZUNUBIY, WAFTAH LIY ABWABA RAHMATIK,
Sai ya fara yin dawafinsa, cikin tsarki,
Yana mai fara shi daga jikin hajarul aswad, yana mai shafa shi, ko
sumbantarsa, idan har ya samu daman aikata hakan, idan kuma bai samu daman
hakan ba, sai ya yi nuni gare shi, yana mai cewa, (a lokacin fara dawafin):
BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA IYMANAN BIK, WA TASDIYKAN BI
KITABIK, WA WAFA'AN BI AHDIK, WATTIBA'AN LI SUNNATI NABIYYIKA; MUHAMMADIN
sallal Lahu alaihi wa sallama.
Sa'annan sai ya sanya dakin ta hannunsa na hagu, sai ya kewaya shi da
dawafi sau bakwai, yana mai faraway da hajarul aswad, yana mai kare su da shi.
Kuma sunnah ne Namiji ya yi abinda ake kiransa iddiba'i a dawafinsa
gabadayansu, yana mai sanya tsakiyan mayafinsa karkashin kafadarsa ta dama,
Geffan mayafin biyu kuma akan kafadarsa ta hagu.
Sai kuma ya yi sassarfa a kewaye guda uku na farko, ta hanyar yin
tafiyar sauri, tare da kusantar tsakanin taku.
Kuma duk lokacin da ya zo daura da hajarul aswad sai ya sake kabbara.
Idan kuma ya kasance tsakanin RUKUNUL YAMANIY da HAJARUL ASWAD sai ya
rika cewa:
RABBANA ATINA FID DUNYA HASANATAN WA FIL AKHIRATI HASANATAN WA KINA
AZABAN NAAR.
Sai kuma ya marairaice ga Ubangijinsa a cikin sauran dawafinsa da abinda
ya so na zikiri da addu'oi da karatun Alkur'ani, ba tare da ya ware wata addu'a
kebantacciya ga kowane zagaye ba.
Idan y agama dawafinsa (bakwai) sai ya gusar da abinda ya yi na
IDDIBA'I, sai ya lullube kafadarsa.
Sai kuma ya sallah raka'oi guda biyu, a bayan MAKAAMU IBRAHIMA, idan ya
samu damar yin hakan, idan kuma bai samu dam aba, to a kowane wuri ya samu dama
a wannan Masallacin.
Yana mai karantawa –a raka'ar farko-: KUL YA AYYUHAL KAFIRUNA, A ta
biyun kuma ya karanta: KUL HUWAL LAHU AHAD.
Sa'annan sai ya nufi yin SA'AYI tsakanin duwatsun SAFAH da MARWAH, Kuma
idan ya kusanci dutsen Safahsai ya karanta:
"INNAS SAFAH WAL MARWATA MIN SHA'AIRIL
LAH" Abda'u bima bada'al Lahu bihi.
Wannan kuma zai fade shi ne kawai a farkon sa'ayinsa kawai.
Sa'annan sai yah au dutsen SAFAH,
Sai ya fiskanci alkiblah,
Ya daga hannayensa
Yana mai yin kabbara yana gode wa Allah, Sa'annan ya ce:
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL
HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR.
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARAL AHZABA WAHDAH,
WA HAZAMAL AHZABA WAHDAH. Zai maimata wannan zikirin ne har sau uku, sai kuma
ya rika addu'oi da bukatun da yaga dama, a tsakanin kowane zikiri da wanda ke
biye da shi. Amma ba zai yi addu'a ba, bayan fadin zikirin a karo na uku.
Sa'annan sai ya sauka domin tafiya dutsen MARWAH,
Idan ya isa zuwa ga alamomi biyu korra, sai Namiji ya yi gudu a
tsakaninsu gudu mai tsanani. Idan kuma ya wuce alamomin sai ya cigaba da
tafiya, irin tafiyarsa ta al'ada.
Idan kuma ya isa zuwa ga dutsen MARWAH sai ya hau kan dutsen, ya
fiskanci alkiblah, sai kuma ya aikata irin abinda ya aikata lokacin yana kan
dutsen SAFAH.
Sai kuma ya sauka da tudun dutsen MARWAH yana mai tafiya zuwa ga dutsen
SAFAH, Yana mai aikata irin abubuwan da aikata a lokacin tafowarsa daga SAFAH
zuwa MARWAH.
Idan har ya kamala zagaye bakwai, wato daga dutsen SAFAH zuwa MARWAH
zagaye daya kenan, Sannan daga MARWAH zuwa SAFAH wani zagayen na daban. To a
nan, sai ya aske gashin kansa gaba daya, ko ya rage shi, saidai askewan
gabadaya shine yafi falala.
Ita kuma Mace zata rage kamar kan yatsa daga dukkan bangarorin gashin
kanta.
To idan maniyyaci ya aikata haka, umrarsa ta cika, kuma ya warware daga
haramarsa.
Muna rokon Allah Ta'alah ya karbi umrar masu umrah, da sauran ayyukansu.
No comments:
Post a Comment