HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 06/SHA'ABAN/1437H
Daidai da 13 /MAY/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
SAVAWA AIYUKA IRIN NA
JAHILIYYA
Shehin Malami wato: Liman Abdulmuhsin
xan Muhammadu Alqasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SAVAWA AIYUKA IRIN NA
JAHILIYYA,
Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan mafi girman ni'imar da aka yi wa Mutane;
wato: Ni'imar Musuluci, yana mai bayyana wajabcin sanin Jahiliyya, ga mai son
ya san haqiqanin musuluci da falalarsa, Sannan ya tattauna kan yadda addini mai
girma (wato: Musulunci) ya sava wa: Aqidun Mushirkai, da na Yahudu da Nasara,
da kuma al'adunsu, Yana mai dogara kan abinda ya zo cikin littafin Allah da
sunnar Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم).
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrace-sharracen kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu
mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa,
kuma ku yi riqo a Musulunci da igiya mai qarfi (amintacciya).
Ya ku Musulmai!
Allah shine Mai yin ni'ima
shi kaxai, kuma ni'imominsa Mabuwayi akan bayinSa ba a iya qidaya su kuma basa
lissafuwa. Kuma mafi girman ni'ima wajen falala, shine ni'imar musulunci, Allah
(تعالى) yana cewa:
"A yau, na kammala
addininku a gare ku, kuma na cika ni'imata a kanku, kuma na yarje muku
musulunci a matsayin addini" [Ma'ida: 3].
Addini cikakke, wanda ya
haxa kyawawan ababe gabaxayansu, kuma Allah ya yarda da shi ga halittanSa, Sai
ya shiryar da wanda ya nufa daga cikinsu zuwa ga wannan addinin, kuma yayi musu
falala da shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Haqiqa Allah ya
yi baiwa ga muminai, a lokacin da ya tayar da wani Manzo a cikinsu daga
kayukansu, yana karanta musu ayoyinSa, yana tsarkake su, kuma yana ilmantar da
su littafi da hikima, kuma lallai sun kasance daga gabani, haqiqa suna cikin
vata bayyananniya"
[Ali-Imran: 164].
Kuma duk wanda bai san JAHILIYYA ba to bai san haqiqanin
MUSULUNCI ba, da kuma falalarsa.
Kuma lallai ana warware
tuqar musulunci; tuqa-tuqa idan ya rayu a musulunci wanda bai san jahiliyya ba.
Kuma haqiqa mutane sun kasance a cikin baqar jahiliyya,
wanda hanyoyi suka shafe a cikinsa, alamomin annabta suka vace, Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Kuma lallai
Allah (gabanin zuwan Manzonsa) yayi dubi ga mutanen duniya, sai ya qi su;
larabawansu da ajamawansu, sai wasu da suka saura daga ma'abuta littafi". Sai Allah ya tayar
da Manzonmu Muhammadu (صلى
الله عليه سلم) da hujjoji, da shiriya. Kuma ya fitar da mutane da wannan
annabin daga duffai zuwa ga haske.
Kuma yana daga MANYAN MANUFOFIN ADDINI: Sava wa
maqiya addini, domin kada mutane su koma zuwa ga jahiliyyarsu; Sai musulunci ya
yi hani kan kamancecceniya (da maqiyan musulunci), ya kuma yi hani kan lamuran
jahiliyya, daga cikin irin nau'ukan ibadodin Ahlul-kitabi da mushirkai, da kuma
al'adodinsu; cikin abinda suka kevanta da su. Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ku riqa
savawa Mushirkai",
Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Allah yayi hani kan bin son zuciyarsu, a inda yace:
"Kuma kada ka bi son
zuciyar waxanda ba su sani ba" [Jasiya: 18].
Kuma kowani abu daga cikin lamuran jahiliyya walaqantacce
ne; saboda Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya sanya shi qarqashin qafarsa ya take, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ku saurara!
Kowani abu daga cikin lamuran jahiliyya an take shi a qarqashin qafata", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma "Daga cikin
mutane mutumin da Allah yafi qi shine: me neman cusa sunnar jahiliyya a cikin
musulunci",
Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma mafi girman varnar da mutanen jahiliyya suke kanta
ita ce: ROQON WANIN ALLAH TARE DA ALLAH, da sanya ababen tarayya a gare shi, a
cikin bautarSa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma suna bautawa
koma bayan Allah abinda ba zai cutar da su, ba kuma ba zai amfanar da sub a,
kuma suna cewa: Waxannan masu cetonmu ne a wurin Allah" [Yunus: 18]. Kuma
suka ce:
"Bama bauta musu
face su kusantar da mu zuwa ga Allah kusantarwa" [Zumar: 3].
Kuma wannan shine mafi
girman abinda Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya sava wa mutanen jahiliyya akansa; Sai y azo musu da
tauhidi, da kuma yin ikhlasin addini ga Allah shi kaxai. Kuma don haka ne,
Mutane suka rarrabu zuwa ga musulmai da kafirai, da mai taimakon addini da kuma
mai yin gaba da shi. Kuma bayin Allah
sune waxanda basa roqon wani abin bautar wanda ba Allah ba, tare da Allah, kuma
basa bauta wa wani idan ba shi ba.
Kuma kawar da kai ko fiska daga abinda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) shine hanyar vata. Kuma idan ganin kyan
varna ya haxu da hakan to lallai tavewa da hasara sun gama cika, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma waxanda suka
yi Imani da varna, kuma suka kafirce wa Allah, to lallai sune waxanda suka yi
hasara"
[Ankabut: 52].
Kuma kyautata zato ga Allah ibada ne, kuma addini. Wanda
kuma ya munana zatonsa ga UbangijinSa to lallai ya bi hanyar jahiliyya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Suna yin zato wa
Allah ba na gaskiya ba; irin zaton jahiliyya" [Ali-Imran: 154].
Kuma yana cikin munana wa
Allah zato:
Yin suka kan hikimarSa, da ilhadi cikin sunayenSa da sifofinSa, da nasabta
naqasa zuwa ga Allah; kamar jingina masa xa, da abokin tarayya, da gajiyawa, ko
wata wahala, saboda Allah ya xaukaka ga barin haka.
Kuma lamari na Allah ne shi
kaxai; saboda shine Ubangiji, kuma a hannunSa linzamin kowani abu yake. Kuma
rataya layu, da zuwa wurin masu sihiri da bokaye da masu duba suka ne ga
addini, kuma yana lalata fixrah, ya raunana hankali, kuma bin hanyar ma'abuta
karkata da vata ne, An ruwaito daga Mu'awiya xan Alhakam As-sulamiy, ya ce: Na
ce: Ya Manzon Allah! Wasu lamura ne da muka kasance muna aikata su a jahiliyya; Mun
kasance muna zuwa wurin bokaye, Sai ya ce: Kada ku je wurin bokaye. Ya ce, Sai na ce: Mun kasance muna canfa
abubuwa? Ya ce: Wannan wani abu ne wanda xayanku ke jinsa a cikin ransa, to
amma kada ya hana ku ci gaba da aikata abin da kuka sa a gaba". Muslim ya ruwaito shi.
Kuma Allah ya umurce mu da
YIN DOGARO KO TAWAKKALI akansa, da kuma fawwala lamura izuwa gare shi. Shi kuma
neman tsarin aljanu baya qara wa mai yinsa face sakwarkwancewa da rauni, Allah
(تعالى) yace:
"Sha'anin, lallai
wasu mazaje daga cikin mutane sun kasance suna neman tsari daga aljanu, sai
suka qara musu tsaurin kai" [jinn: 6].
A cikin musulunci sai Allah
ya bamu canji; da cewa mu riqa neman tsarinSa. Kuma duk wanda ya sauka a wani
masauki sai ya ce:
"أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق"
Ma'ana: "Ina neman
tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta", to babu abinda zai
cutar da shi, har sai ya tashi daga wannan masauqin nasa.
Su waxanda suka mutu sun
tafi zuwa ga abinda suka gabatar, su kuma salihan mutane ana yin addu'a a gare
su, amma ba a roqonsu tare da Allah. Kuma riqan kaburbura masallatai da yin
filasta akansu, da yin gini akansu, da qawata su, da yin ado a gare su, da
roqon ma'abuta cikinsu yana daga cikin sunnar ahlul kitabi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Tsinuwar
Allah ta tabbata akan yahudu da nasara; saboda sun riqi qaburburan annabawansu
masallatai".
Kuma hukunci na Allah ne shi kaxai, kuma kaiwar hukunci
wajibi ne zuwa ga addininSa da shari'arSa. Canza hakan kuma da waninsa fasadi
ne da varna, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin hukuncin
jahiliyya suke nema! Wanene yafi Allah kyan hukunci ga mutane" [Ma'ida: 5].
Shi kuma yin canfi yana raunana azamomi, kuma yana kawo
rauni cikin yaqini ko ya gusar da shi, Maqiya manzanni sun ce wa Manzanninsu:
"Lallai ne mu mun
canfa ku"
[Yasin: ].
Shi kuma musulmi yana yin
Imani da abinda Allah ya hukunta ko ya qaddara, kuma yana son kyakkyawar fata (فأل) a cikin sha'anonisa gabaxaya. Don haka;"Cuta bata
da tasirin yaxuwa da kanta, kuma canfi bashi da tasiri, haka canfin tsuntsun
duji, kuma canfi da watan Safar bashi da tasiri".
Yana daga cikin sunnonin jahiliyya neman shayar da
tsirrai ko mutane da taurari, da kuma rataya zuciya ga motsawan falaki To sai
muslunci ya zo da lalata su, da kuma rataya zukata da Allah shi kaxai; don haka: Duk wanda yace:
an yi mana ruwan sama da falalar Allah da rahamarSa to wannan shine mai yin
Imani da Allah mai kafirce wa taurari. Wanda kuma yace: An yi mana ruwa ne da
tauraro iri kaza ko kaza to wannan ya kafirce wa Allah kuma yayi imani da
taurari.
Kuma duk wanda ya xoxani wani yanki na ilimin taurari to
lallai ya xoxani wani yanki na ilimin sihiri, idan kuma yayi qari sai ya qaru.
Ita kuma albarka ana fatan samunta ne daga wurin Allah
shi kaxai. Kuma lallai nemanta daga bishiyoyi da duwatsu ko rayayyu da matattu,
ko qudurta cewa a cikinsu akwai hakan = waxannan vata ne, da tavewa, kuma akan
haka masu bautar gumaka suka kasance a kai.
Kuma duk wanda ya jingina ni'imomi ba zuwa ga UbangijinSa
ba, to wannan bai san falalarSa ko ya san hanyar godiya a gare shi ba. Kuma
wannan shine hanyar jahilai. Saboda
"Suna sanin ni'imomin Allah, sa'annan sai su musanta su, kuma
mafi yawansu kafirai ne" [Nahl]. Kuma shi Mumini mai godiya ne ga
UbangijinSa, mai kuma faxar ni'imominsa da baki, kuma yana fore falalar da aka
yi masacikin abinda zai yardarm da Allah.
Shi kuma zamani halitta ne da ake hore shi, don haka duk
wanda ya zage shi, ko kuma ya jingina masa wani aiki, to a tare da akwai wata
alama daga cikin alamomin jahiliyya, a inda suke cewa:
"Kuma babu
abinda yake halakar da mu sai zamani" [Jasiya: 24].
Shi qaddara shine ikon Allah. Kuma wajibi ne ga mumini
yayi Imani da qaddara, da sallamawa ga lamarin Allah da qaddararSa. Su kuma
mushirkai suna musanta qaddara, kuma suna sanya qaddara ta zama tana cin karo
da umurni ko shari'a, a inda suke cewa:
"Da Allah ya so da
bamu yi shirka ba, da iyayenmu" [An'am: 148].
Shi kuma qaryata lamarin tayar da mutane bayan mutuwa, ko
yin shakka akansa kafirci ne, daga cikin hanyoyin jahiliyya, a inda suke cewa:
"Kuma mu ba waxanda
za a tayar da su ba ne" [An'am: 29, Mu'uminuna: 37].
Duk kuma wanda ya qaryata ayoyin Allah, ko sashinsu, ko
yayi shakka a cikinsu, to lallai shi mabiyi ne ga mushirkai, a inda suka ce:
"Ba komai ba ne
wannan face tatsuniyar mutanen farko" [An'am: 25].
Shi kuma amintuwa daga makircin Allah, ko xebe tsammani
daga rahamarSa = yana cin karo da Imani, kuma akan haka ma'abuta bautar gumaka
suke. Shi kuma mumini yana tafiya zuwa ga Allah tsakanin tsoro da fata; sai
yayi fatar samun rahamarSa, yana tsoron azabarSa, yana mai raya zuciyarSa da
son UbangijinSa.
Shi kuma Allah shine yake halattawa kuma yake haramtawa,
kuma halittu basu da wani abu na hakan, savanin abinda ahlul-kitabi suke kansa
"Sun riqi malumansu da masu yin bauta a cikinsu ababen bautawa koma
bayan Allah"
[Tauba: ]. Adiyyu yake cewa: Ya ma'aikin Allah! Lallai ne mu bama bauta musu
Sai ya ce: "Shin ba suna haramta muku
abinda Allah ya halatta, sai ku kuma ku halatta ba? Su kuma halatta muku abinda
Allah ya haramta amma sai ku halatta shi? Na ce: Na'am, yace: Hakan
shine bauta musu".
Kuma hujjar Mumini da tushen da yake ciran addininsa sune
littafin Allah da Sunnah, a bisa fahimtar magabatan wannan al'umma na kwarai.
Da kuma qaranta ko qaranta ko nisantar kafa hujja da iyayen farko, wanda hakan
kuma yana cikin hijjojin jahilai, kuma akan haka suke gina addininsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan aka ce musu:
Ku bi abinda Allah ya sauqar, Sai su ce: Na'am za mu bi abinda muka samu
Ubanninmu akansu"
[Baqara: ].
Kuma yawa bata tunkuxe gaskiya, kuma bata sanya varna ta
zama gaskiya. Kuma ruxuwa da yawa yana daga cikin addini ko sunnonin maqiya
addini. Kuma shi mumini baya samun kewa saboda qarancin masu bin gaskiya, kuma
baya ruxuwa da yawan waxanda za su halaka.
Kuma duk wanda ya yi raddin gaskiya saboda ma'abutanta
suna da rauni, ko qaranci, to lallai ya jahilci addini ba, kuma bai bi hanyr
salihan mutane.
Shi kuma ajiye littafin alqur'ani da sunnah, da canza su
da littatafan ma'abuta vata, na daga hanyoyin ahlul-kitabi, alokacin da suka yi
watsi da littafin Allah a bayan bayansu, sai kuma suka bi abubuwa da shexanu
suke karanta musu.
Shi musulunci addine
ne miqaqqe, Allah ya sanya ma'abutansa da su zama al'umma matsakaiciya,
mai adalci, babu guluwi ko gajertawa, kuma babu wuce iyaka kuma babu taqaitawa,
hanya ne miqaqqe, wanda yayi hannun riga da hanyar waxanda aka yi fushi da su
(yahudawa), da kuma hanyar vatattu (Nasara).
Kuma yana daga cikin
hanyoyin nasu: Wuce iyaka, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ina yin
gargaxi a gare ku, kan wuce iyaka a cikin addini, saboda abinda ya halaka
waxanda suka kasance a gabaninku shine wuce iyaka a cikin addini".
Shima cakuxa gaskiya da varna, ko voye gaskiya yana daga
hanyoyinsu, saboda sun riqi addininsu da wargi da wasa, kuma suna bin son
zuciyarsu, suna canza kalmomi daga gurabensu, suna sayen ayoyin Allah da
alkawarinsa, da rantse-rantsensu da kuxaxe kaxan, kuma suna voye abinda Allah
ya saukar na hujjoji da shiriya, kuma suna yin da'awar soyayya, ko tsira ba
tare da sun yi aiki, ko suna da hujja ba, suna masu dogara kan burace-burace na
qarya, da maganganu na varna, kuma suka ce:
"Mu 'ya'yan Allah ne
kuma masoyansa"
[Ma'ida: 18].
Kuma suna yin qoqarinsu
wajen aiki da nau'ukan wayo na bayyane da na voye, kuma suna danganta varnarsu
zuwa ga annabawa, da kuma mutane masu girma
"Kuma idan suka aikata alfasha sai su ce: Mun samu ubanninmu akansu,
kuma Allah ne yayi mana umurni da aikata su" [Ma'ida: 28].
Kuma suna faxan qarya akan
Allah alhalin suna sane.
Ma'abuta jahiliyya daga cikin Ahlul-kitabi da mushirkai
sun fi dukkan mutane son rayuwa ba a cikin Imani ba, suna roqon Allah ya basu
duniya banda lahira, suna yin fankama idan aka yi musu ni'ima, suna masu yanke
qauna a lokacin saukar azaba, suna bautar Allah a karkace, suna yanke abun da
Allah ya yi umurnin a sadar, kuma suna yin varna abayan qasa; basa kawo gyara,
kuma suna son a riqa gode musu akan abinda basu aikata ba. Mai iliminsu baya
amfani da iliminsa, jahilinsu yana yin qarya wa Allah ba tare da ilimi ko sani
ba, kuma yana yin bautar Allah akan vata, suna neman canzar abinda yake qasa da
abinda shi yafi alkhairi, kuma suna tottoshe hanyar Allah, kuma suna sayan
wargin zance domin su vatar da mutane daga bin tafarkin Allah, sun rabe
tsakanin annabawan Allah da manzanninSa, kuma sun kashe kuma suna kasha
waxannan da suke yin umurni a yi adalci daga cikin mutane, kuma sun yi makirci
ga wannan addinin babban makirci, basu san komai ba ga gaskiya sai kafa masa
tsana da gaba, su nkuma dangane da varna masu taimako ne, abokai.
Kuma lallai addini ya zo, da cewa a sava wa abinda suka
kasance akansa, IBNU-ABDILBARR –Allah yayi rahama a gare shi- yace: "Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) yana son savawa Ahlul-kitabi da sauran
dangogin kafirai, kuma ya kasance yana tsorace wa al'ummarsa bin waxannan
mutane, Har suke cewa: Baya son ya bar wani abu daga cikin lamarinmu face
ya sava mana akansa".
Don haka; aka sava musu a WURIN YIN YANKANS, ballantana
cikin aiyuka! Wani Mutum yayi
bakancen zai soke raqumi a buwanah, Sai ya zo wajen Annabi (صلى الله عليه وسلم)Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Shin a
wurin akwai gunki daga cikin gumakan jahiliyya da ake yin bauta a gare su? Sai suka
ce: A'a. Ya sake cewa: "Shin akwai wani idi a wurin daga cikin idinsu?"
Sai suka ce: A'a! Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Ka
cika bakancenka".
A dangane da SALLA, da KUMA KIRAN MUTANE ZUWA GARE TA an
umurce mu da sava musu; Sai aka shar'anta mana yin kiran sallah, aka kuma hana
mu amfani da sharewar yahudawa, da qaraurawar nasara, kuma ya hana yin sallah
bayan asuba, har sai rana ta fudo, da kuma bayan la'asar har sai rana ta faxi;
saboda rana tana fudowa kuma tana faxuwa a tsakanin qahon shexan guda biyu,
kuma alokacin ne kafirai suke yi mata sujjada. Kuma sallarsu a jikin xakin
ka'aba bata kasance ba face Shewa da fito. Kuma yayi hani kan yin sallah tare
da fiskantar duk wani abinda ake bauta masa koma bayan Allah, kamar wuta, koda kuwa
mai yin bautar bai nuface ta ba. Kuma yayi hani kan riqe kwankwaso da اشتمال a
cikin sallah saboda yahudawa suna aikata shi. Kuma yayi hani kan mutum ya zauna
a cikin sallah yana mai dogara akan hannunsa; saboda yin haka yana daga cikin
sifar sallar yahudu da aka yi fushi akansu. Kuma yayi hanin mamu suyi sallah a
tsaye alhalin limami yana zaune, a inda ya ce: "Lallai kun
yi kusa ku aikata irin aikin Farisa da Rum; na tsayuwa akan sarakunansu amma su
suna zaune",
Muslim ya ruwaito.
A lamarin BUNNE MAMATANMU muna da hanyar da ta sava wa
tasu, saboda "Nau'in qabarin lahadu namu ne, shi kuma shaqqu na wassunmu".
A wajen CIYARWA kuma sai umurni y azo cewa mu ciyar da
dukiya ta hanyar fiysabillahi, savanin waxanda suke ciyar da ita, don neman
toshe bin tafarkin Allah "Da sannu zasu ciyar
da ita, sa'annan ta kasance nadama akansu, sa'an nan ayi rinjaye akansu, kuma
waxanda suka kafirta zuwa ga jahanna ake tara su" [Anfal: 36].
A lamarin AZUMI kuma Abinda ya rabe tsakanin azuminmu da
azumin Ahlul-kitabi shine cin sahur, kuma mutane ba za su gushe suna cikin
alkhairi ba, matuqar suna jinkirta yin sahur, suna kuma gaggauta yin buxa baki,
a matsayin savawa ahlul-kitabi. Kuma manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya azumci azumin Ashura (10 ga watan
muharram), a yayin da ya san cewa yahudawa suna azumtarsa sai ya ce:
"Idan har na
kai baxi to zan azumci ranar tara".
Kuma ya sanya lokacin fara
azumi da lokacin ajiye shi, yana da alaqa da ganin jinjirin wata, Shekhul Islam
yana cewa:
"Ba akan hanyar
wasunta ba daga al'ummai, wajen dogara da ilimin lissafi, cikin ibadodinsu da
bukukuwan idinsu".
A lamarin AIKIN HAJJI kuma mutanen jahiliyya sun kasance
basa yin umrah a cikin watannin hajji, sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya zo da lamarin a sava musu, kuma ya ce:
"Umrah ta
shiga cikin hajji".
Kuma sun kasance suna barin
arafah gabanin faxuwar rana, Muzdalifa kuma da hantsi, Sai ya sava musu; ta
hanyar jinkirta wannan, da kuma gabatar da wannan. Kuma a wasu lokutan suna yin
hajji babu tufa; tsirara, sais hi kuma yayi umurnin a suturce al'aura. Da kuma
yin ado wajen tafiya kowace salla, ko masallaci.
Kuma ya kasance suna da ababen yankawa a jahiliyya, sai
ya yi hani akansu, a inda yace:
"Babu
maganar yanka dabbar da aka fara haifa, kuma babu yin yanka don allolin mushirkai".
Kuma yayi hani kan yin
yanka da farce; saboda shine wuqar mutanen Babasha.
A lokacin MUSIBU (da mutuwa) kuma ya umurce mu da yin
haquri da neman lada, ya kuma yi hani daga dukkan abinda zai sava wa haka,
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) yace:
"Baya
cikinmu wanda ya mari kumatu, ko ya yayyaga wuyar riga, ko yake addu'oi irin na
jahiliyya".
Kuma an umurce mu da QAN-QAN-DA-KAI, aka hane mu da GIRMAN
KAI, Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Sifofi huxu
a cikin al'ummata suna cikin lamarin jahiliyya, ba za su bar su ba: Alfahari da
muqamai, da suka cikin danganta, da neman shayarwa da taurari, da yin kuka wa
mamaci".
Kuma yana daga cikin qan-qan-da-kai: Hanin da y azo kan
ci, ko sha, a cikin masakin zinari da azurfa. Da kuma cikin tufa; wanda babu
alfahari a cikin haka ko girman kai; Sai yayi hani kan sanya tufar da aka rine
ta da tsiron usfur, kuma ya ce:
"Lallai
wannan tufafi na kafirai ne, kada ka sanya shi", Muslim ya ruwaito.
Kuma ya yi hani kan izgilanci ga wasu, ko raina su; a
inda Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) yak e cewa mutumin da ya aibanta wani mutum da mahaifiyarsa:
"Lallai kai
mutum ne wanda a tare da kai akwai jahilyya".
Kuma ya ja kunnenmu daga
qabilanci, saboda kasancewarsa sababin da ke haifar da jayayya da rabuwar kai
"A lokacin da waxanda suka kafirta suka sanya ta'assubancin qabilanci
a cikin zukatansu irin ta'assubancin jahiliyya" [Fat-h: 26].
Kuma a lokacin da Mutumin
garin Madina (Ansariy) ya buxi baki ya nemi xauki ko taimakon mutanen Madina,
shima wanda yayi hijira, ya ce: Xaukinku ya waxanda suka yi hijira, Sai Annabi
(صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Shin kira
irin ta jahiliyya za ku yi alhalin ga ni a tsakaninku?".
Idan har za a kira wannan
lamari da suna da'awar jahiliyya tare da cewa sun ambaci sunaye ne na shar'ia
(Ansar, Muhajirun), to yaya kuma idan da wasu sunayen suka ambata (kamar na
qabilanci?!).
Kuma ya umurce mu da mu riqa jin buwaya da mu'amalolinmu
na kasuwanci da wasunsu, saboda abinda ke cikinsu na yin gaskiya, da adalci, da
amana, Kuma yayi hani kan kasuwanci irin na jahiliyya, da tauye mudu da
ma'auni, da samun dukiya ta hanyar wasan caca, kuma ya tsananta a lamarin riba,
ya walaqanta shi ya sanya shi qarqashin qafarsa ya take.
Kuma yana daga cikin
nau'ukan ribar jahiliyya: juya bashi ga
mutumin da ya gagara biyansa, Sai ya ce: Ko dai ka biya da riba, ko ka nemo ka
biya. Kuma suka sanya riba ya zama kamar kasuwanci, har suke cewa: "Ciniki kamar riba
yake"
[Baqara: 275].
Kuma Allah ya halatta mana cin DAXAXAN abubuwa, kuma ya
haramta mana cin kowani MAI DAUXA, Sai su kuma suka kishiyanci haka.
Babu abinda ya fi kyau fiye da halittar Allah. Saidai
kuma yana daga cikin al'adun ahlul-kitabi: Jirkita halittar Allah, suna masu
bin shexan wanda ya yi umurnin a riqa aikata hakan, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi hani kan binsu, a inda ya ce:
"Ku saki
gemu, ku aske gashin-baki". Kuma ya yi umurni da a rina faring emu, amma a nisanci
kalan baqi. Kuma ya barranta daga wanda ya xaure gemunsa, ko ya rataya
tsirkiya, irin na mutanen jahiliyya.
Kuma MACE ta kasance a jahiliyya walaqantacciya ce;
saboda babu wani hijabin da zai suturce ta, ko wani addinin da zai bata kariya,
"Kuma idan aka yi bushara wa xayansu da 'ya mace sai fuskarsa ta wuni
baqa qirin, alhali yana mai cike da baqin ciki" [Nahl: 58].
Kuma sun kasance suna bunne
'ya'ya mata. Daga cikin mas'alolin alkalanci kuma a wurinsu akwai bada gado wa
'ya'ya maza banda mata, da halatta muharramai. Su kuma yahudawa suna qaurace wa
mace a kwanakin hailanta; basa cin abinci da ita. Su kuma nasara suna aikata
komai da ita, Sai musulunci y azo da karrama mace, da suturce ta, sannan ya ce
musu:
"Kuma kada ku yi
fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyyar farko" [Ahzab: 33].
Kuma (musulunci) ya sanya
wa mata haqqoqi, kamar yadda ya xora musu wajibai, kuma mata sune qashin bayan
al'ummai; saboda a cikinsu akwai: Uwa, da Mata, da 'Ya, da 'Yar'uwa. A lamarin gado nan ma sai ya sanya musu wani
rabo yankakke. "Kuma duk wanda ya yi tarbiyyar 'ya'ya mata biyu ko fiye to sun
kasance kariya a gare shi daga shiga wuta".
Kuma jahiliyya ta kasance ta kan NASABTA YARO ga wand aba
Ubansa ba, ko saboda shayarwa, ko ta'adar mayar da yaro xa, ko riskarwa. Yayin
da kiyaye nasaba da dangantaka a cikin musulunci take cikin manyan lamura na
wajibi (ضروريات); Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Yaro na
shumfuxin aure ne, Mazinaci fajiri kuma ya cancanci hana shi mallakar xa".
Kuma SANYA SUNA yana da tasiri ga masu sunayen; Sai aka
umurce mu da mu zavo mafifitan sunaye, aka kuma hane mu, riqon irin abinda
mutanen jahiliyya ke riqo na sunaye, kamar bautarwa zuwa ga wanin Allah (kamar
Abdusshams), ko sunaye masu muni, ko kuma waxanda akwai ma'anan tsarkake kai ko
yabo a cikinsu; Sai Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya canza sunan Asiya zuwa Jamila, Barrah kuma zuwa Zainab,
AbulHakam zuwa Abu-Shuraih, kuma ya ce:
"Sunayen da
Allah yafi sonsu sune: Abdullahi da Abdurrahman".
Mutanen jahiliyya sun riqi BUKUKUWAN IDI kamar yadda suka
so, Amma sai Allah ya canza mana da bikin idin sallar azumi, da na layya.
Yana daga cikin sunnoninsu kasancewar basa UMURNI DA
KYAKKYAWA, KUMA BASA HANA MUMMUNA, idan kuma za su yi to sai manta kayukansu,
Sai wannan al'ummar kuma ta kasance mafi alherin al'ummar da aka fitar don
mutane; tana yin umurni da kyakkyawa, kuma tana hani ga mummuna, kuma jagora ce
ga watanta.
Alama ce ta jahiliyya RARRABUWAR KAI da SAVANI, ta yadda basa
haxuwa akan wani addini, ko akan wata duniya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ku
kasance daga mushirkai * Wato waxanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance
qungiya-qungiya, kowace qungiya tana mai alfahari kawai da abinda keg are ta" [Rum: 31-32].
Shi kuma haxuwar kai qarfi
ne da sabo, wanda musulunci y azo da shi, kuma ya yi hani kan kishiyarsa, Allah
(سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku yi riqo da
igiyar Allah gabxaya kada ku rarraba" [Ali-imran: 103].
Kuma haxuwar mutane akan wani shugaba wanda zai tsayar
musu da lamuran addininsu da duniyarsu, tare da ji da yin biyayya a gare shi ba
a cikin savo ba, sababin samun aminci ne, da wadaci, da qarfi akan maqiya. Kuma
yana da cikin sunnoni jahiliyya: Yin fito-na-fito da shugaba, da vangarewa daga
jama'a, Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce:
"Wanda ya yi
khuruji ga shugaba daidai da taqi xaya sai yam utu to yayi mutuwa irin ta
jahiliyya",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito. Kuma ya ce:
"Wanda ya
vangare wa jama'a daidai da taqi xaya sai yam utu, to yayi mutuwa irin ta
jahiliyya",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma
"Duk wanda yam utu alhalin babu wata bai'a a wuyansa to yam utu mutuwa
irin ta jahiliyya",
Muslim ya ruwaito shi.
Shima JIHADI yana cikin manya-manyan aiyuka, idan aka kyautata niyya ga
Allah "Kuma duk wanda yayi yaqi qarqashi tutar vata wand aba a sani ba,
yana yin fushi ga qabilanci, ko yana kira zuwa ga qabilanci, ko yana taimakon
qabilanci sai aka kasha shi, to an masa kisa irin ta jahiliyya", Muslim ya ruwaito.
"Kuma lallai
Allah ya yarda muku da abubuwa guda uku; ku bauta masa kada ku hada shi da
kowa, ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya kada ku rarraraba, kuma ku yi nasiha
ga wanda ya jivintar masa da lamarinku".
Kuma waxannan ababen guda uku gabaxayansu, sun sava da
ababen da mutanen jahiliyya suke kansu, As-Sheikh Muhammadu xan Abdulwahhab –رحمه الله- ya ce:
"Babu wata
matsala da aka samu a addinin mutane ko a rayuwarsu ta duniya sai da sababin
sakacinsu da waxannan abubuwa guda uku, ko sashinsu".
BAYAN HAKA;
Ya ku Musulmai!
Addininmu addini ne na
kamala da buwaya, yana da rahama cikin abubuwan da ya shar'anta, da adalci
cikin hukunce-hukuncensa, da gaskiya cikin loabarun da ya bayar.
Kuma riqo da shi shine
tushen kowani alkhairi da cin nasara, kuma alheri yana zuwa da wani alherin.
Yayin da bin addinin da ban
a musulunci ba, da aiki da abubuwan jahiliyya su kuma sune tushen kowani
sharri, kuma sababin gogewan alamomin addini. Kuma lallai bin abu yak an haifar
da sonsa. Tarayya kuma da abu a zahiri hanya ce ta qoqarin dacewa da shi a
voye.
Kuma duk wanda ya yi koyi
da wasu mutane to yana daga cikinsu.
Koyi kuma da mutanen
jahiliyya da mushirkai alama ce ta rauni, da raina kai, da raunin yaqini da
Imani.
Kuma wata al'umma ba za ta
qirqiro wata bidi'a ba face an cire kwatankwacin wannan a cikinsu na daga sunna.
Kuma wasu mutane ba za su
raya wata daga cikin sunnonin jahiliyya ba, face sun bar ninkin baninkiyanta na
shiriya,
A'UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Kuma wannan itace
hanyata miqaqqiya sai ku bi ta, kada ku bi qananan hanyoyi sais u vatar da ku
daga tafarkinSa, Da wannan ake muku wasici domin ku samu kariya" [An'am: 153].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA. …
HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Yabo kuma nasa ne
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Mafi alherin wanda ake yin
koyi da shi Shine Annabinmu (صلى
الله عليه وسلم) wanda Allah ya bashi kamala a cikin dukkanin sha'anoninsa,
kuma ya cika masa shari'ar da y azo da ita da addininsa. Kuma Allah ya ymurce
mu da yin koyi da shi a cikin dukkanin zantukansa da aiyukansa da halayensa,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Haqiqa ya kasance a
gare ku abun koyi mai kyau cikin rayuwar Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana
fatan Allah da gidan lahira, kuma ya ambaci Allah dayawa" [Ahzab: 21].
Kuma shaidawa cewa shi annabi ne ba za ta amfani
sahibinta ba matuqar bai lazimta wa kansa yin xa'a a gare shi, da binsa ba.
Kuma Imani yana komawa ne zuwa ga tushe guda biyu: Yin
biyayya wa Manzon Allah cikin abinda yayi umurni. Da kuma gaskata shi cikin
abinda ya labarta.
Kuma duk lokacin da bawa ya zama yafi bin annabi (صلى الله عليه وسلم) to yafi girman tauhidi ga Allah, da
ikhlasin addini a gare shi.
Kuma wanda zai fi samun rabo cikin halittu kuma yafi samun
mafi girman ni'ima, da mafi qololuwar daraja Shine wanda yafi su bin annabi da
dacewa da shi cikin ilimi da aiki.
Kuma dukkan hanyoyi gabaxayansu an rufe su; ba za su kai
halittu ga tudun tsira ba, sai ga wanda ya yi koyi da Manzon Allah sau-da-qafa,
ya kuma bi sunnarsa, ya lazimci hanyarsa da xariqarsa; Saboda hanyoyin samun
alkhairori an buxe masa su.
Don haka wajibi ne ga Duk wanda ya yi nasiha ga kansa,
kuma yake son tsiranta da sa'adarta: Ya san shiriyar Annabi da turbarsa, da
sha'aninsa gwargwadon abinda zai fitar daga shi daga cikin waxanda suka jahilci
annabi, don ya shiga cikin waxanda ake qirga su daga mabiyansa da za su
rabauta.
Sannan ku sani; Lallai
Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa
Sai yace, a cikin mafi kyan
abinda aka saukar:
"Lallai Allah da
Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah! Ka mayar da su izuwa ga addininka,
mayarwa mai kyau.
Ya Allah! Ka sanya qasashensu su zama garurrukan
aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi!
Ya Allah! Ka tabbatar da rundumarmu, Ya Allah! Ka
tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka daidaita jifansu, kuma ka azurta
su da yi don kai (ikhlasi), Ya Ma'abucin girma da Baiwa.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu, kuma ka sanya aikinsa ya
zama cikin yardarka. Kuma ka datar da sauran jagororin Musulmai wajen yin aiki
da littafinka, da hukunta shari'arka, Ya ma'abucin girma da yin baiwa.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya,
ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah! Lallai ne Mu muna roqonka ilimi mai
amfani da kuma aiki mai kyau.
Ya Allah! Lallai kai ne abin bautawa; Babu wani
abin bauta face kai, Kai ne Mawadaci, mu kuma mune Faqirai, Ka saukar mana da
ruwan sama kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka
bamu ruwan sama!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!!
"Ya Ubangijinmu lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan
har baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, za mu kasance daga cikin masu
hasara"
[A'araf: 23].
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku
wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment