HADISAI
ARBA'IN KAN AZUMI
أربعون حديثا تتعلق بالصيام
TATTARAWAR
DA TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم
الله الرحمن الرحيم
والصلاة
والسلام على أشرف المرسلين، وعلى آله وصحبه أجمعين، أما بعد:
فهذه طائفة كبيرة من الآثار
النبوية التي تتعلق بالصيام أو برمضان، والله أسأل القبول والإخلاص، فقد ورد عن
عُمَرَ بْن الْخَطَّابِ رضي الله تعالى عنه قال: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «إِنَّمَا الأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ،
وَإِنَّمَا لكل امْرِئٍ مَا نَوَى، فَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ
وَرَسُولِهِ فَهِجْرَتُهُ إِلَى اللَّهِ وَرَسُولِهِ، وَمَنْ كَانَتْ هِجْرَتُه لدُنْيَا
يُصِيبُهَا، أَوِ امْرَأَةٍ يَنْكِحُهَا فَهِجْرَتُهُ إِلَى مَا هَاجَرَ إِلَيْهِ».
رواه
البخاريّ، ومسلم([1]).
An ruwaito
daga Umar xan Alkhaxxabi (r.a) yace: Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"Dukkan aiyuka su kan inganta tare da niyya, kuma lallai kowane mutum
yana samun sakamakon abinda yayi niyya; Wanda hijirarsa ta kasance saboda Allah
ne da ManzonSa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da Manzonsa. Wanda kuma
hijirarsa ta kasance saboda wata duniya ce da zai same ta, ko saboda wata matar
da zai aure ta, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da yayi hijira dominsa. Bukhariy
[lamba: 1], da Muslim [lamba: 1907] suka ruwaito shi.
الأول:
بيان أنّ صوم رمضان من الخمس التي بني عليها الإسلام
عَنِ عبد الله بْن عمر رضي
الله عنهما، قَالَ: سمعتُ رَسُول اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقول: «بُنِيَ
الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ
مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ،
وَصَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ، وَحَجَّ الْبَيْتِ». رواه
البخاري ومسلم.
NA XAYA: AZUMIN RAMADHANA NA CIKIN GINSHIQAI
BIYAR DA AKA GINA MUSULUNCI AKANSU
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace:
Naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "An gina musulunci akan abubuwa
guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu
manzon Allah, da tsayar da salla, da bada zakka, da yin hajjin wannan xakin, da
azumin watan ramadana".
Bukhariyy [8] da Muslim [16] suka ruwaito shi.
صيام رمضان هو الفرض والتطوع مطلوب
عَنْ طَلْحَة بْن عُبَيْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، قال: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى
رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَإِذَا هُوَ يَسْأَلُهُ عَنِ
الإِسْلاَمِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خَمْسُ صَلَوَاتٍ فِي اليَوْمِ
وَاللَّيْلَةِ»، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهَا؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا أَنْ
تَطَّوَّعَ» فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«وَصِيَامُ شَهْرِ رَمَضَانَ»، قَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُ؟ قَالَ: «لاَ، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ»، قَالَ: وَذَكَرَ لَهُ رَسُولُ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الزَّكَاةَ، ... الحديث متفق عليه([2]).
NA HUXU: AZUMTAR WATAN RAMADHANA
SHINE FARILLA, SAIDAI ANA SON A RIQA YIN AZUMIN NAFILA
An ruwaito daga Xalhah xan
Ubaidullahi (r.a) yace: Wani Mutum ya zo zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) sai ya
tambaye shi kan musulunci, Sai Manzon Allah (s.a.w) yace masa: "Salloli biyar ne
cikin yini da dare, Sai mai tambayar ya ce: Shin akwai wasu a kaina? Sai ya ce:
A'a;
saidai idan za ka yi sallar taxawwu'iy –ta nafila-. Sai Manon Allah
(s.a.w) ya sake cewa: Da azumtar watan ramadhana, Sai mai
tambayar ya ce: Shin akwai wasu aumin a kaina? Sai ya ce: A'a; saidai idan
za ka yi na taxawwu'iy –nafila- . Ya ce: Sai Manzon Allah
(s.a.w) ya ambata masa zakka…. Bukhariy (46, da 2678) da Muslim (11) suka
ruwaito shi .
تكفير السيئات مِن فضل صيام رمضان إلى رمضان
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "الصَّلَـوَاتُ
الْخَمْسُ، وَالْـجُـمُعَةُ إِلَى الْجُـمُـعَةِ، ورمضـان إلى رمضـان: مكفِّرات لِمَا
بَيْنَهُمَا مَا اجْـتـنبَت الْكَبَائِر"([3]).
NA UKU: KANKARE KURA-KURAI NA DAGA CIKIN FALALAR
AZUMTAR RAMADHAN ZUWA RAMADHAN
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) daga Annabi
(s.a.w) ya ce: (Salloli guda biyar, da kuma juma'a zuwa wata juma'ar, da azumin
ramadana zuwa wani ramadan: masu kankare qananan zunuban da su ka kasance a
tsakaninsu ne; matuqar an nisanci manyan-manyan laifuka",
Muslim ya ruwaito shi (233).
غفران الذنوب المتقدمة مِن فضل صيام رمضان إيمانا
واحتسابا
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَنْ قَامَ لَيْلَةَ القَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا
تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْـبِهِ، وَمَـنْ صَامَ رَمَـضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا
غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِه»([4]).
NA HUXU: GAFARTA ZUNUBAN DA SUKA GABATA NA
DAGA CIKIN FALALAR AZUMTAR RAMADHAN CIKIN IKHLASI
An ruwaito daga Abu-hurairah (RA), daga Annabi
(SAW) ya ce: (Wanda ya yi tsayuwar lailatul-kadri, yana mai imani da kuma neman
lada an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa, kuma wadda ya yi azumin
ramadana yana mai imani, da kuma neman lada: an gafarta masa abin da ya gabata
na zunubansa).
DAGA CIKIN SHARUXAN WAJABCIN AZUMI:
إنما تجب الصيام على البالغ العاقل
عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "رُفِعَ
الْقَلَمُ عَنْ ثَلاثَةٍ: عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ، وَعَنِ
الْمَجْنُونِ حَتَّى يفيق، وعَنِ الصَّغِيرِ حَتَّى يَبْلُغَ"([5]).
NA BIYAR: AZUMI YANA WAJABA NE KAWAI
AKAN BALIGI MAI HANKALI
An ruwaito daga Aliyu (r.a), daga Annabi
(s.a.w) lallai shi ya ce: "An xauke alqalami akan mutane guda uku;
Ga mai barci har sai ya tashi, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake, da
qaramin yaro har sai ya balaga).
Ma'ana: (An dage alkalami kan mutum uku),
الطهر من الحيض ودم النفساء من شروط
صحة الصلاة والصوم
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ الخُدْرِيِّ، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ: «أَلَيْسَ
إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ تَصُمْ؟ فَذَلِكَ نُقْصَانُ دِينِهَا»([6]).
TSARKAKA DAGA HAILA DA JININ
NIFASI SUNA CIKIN SHARUXAN INGANCIN SALLAH DA AZUMI
An ruwaito daga Abu-Sa'id Alkhudriy (r.a) ya
ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Shin mace ba ta kasance, idan ta
yi haila ba ta sallah kuma ba ta azumi ba? To wannan na daga tawayar addininta!".
وعَنْ مُعَاذَةَ، قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ فَقُلْتُ: مَا بَالُ
الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ،
وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ. فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ
بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: «كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ
الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ»([7]).
Kuma an ruwaito daga Mu'azatu, tace: Na
tambayi A'isha, Na ce: Me yasa Mace mai haila ta ke biyan azumi, amma bata yin
ramukon sallah? Sai ta ce: Ke daga matattarar khawarijawa; Harura'u, ki ke? Sai
nace: Ni ba daga garin Harura'u nake ba, saidai ina yin tambaya ne kawai, Sai
ta ce: "Hakan ya
kasance ya kan same mu; sai a umurce mu da yin ramukon azumi, amma ba a
umurtarmu da mu rama sallah".
بمَ يدخل شهر رمضان، وبمَ ينتهي؟
عَن ابْن عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ:
سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَصُومُوا، وَإِذَا
رَأَيْتُمُوهُ فَأَفْطِرُوا، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَاقْدُرُوا لَهُ»، متفق عليه([8]).
وفي رواية عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، في آخره: فَإِنْ غُبِّيَ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا
عِدَّةَ شَعْبَانَ ثَلاَثِينَ»([9]).
SHIGAN WATAN
RAMADHANA YANA TABBATA DA GANIN JINJIRIN WATA, KO CIKAN WATAN SHA'ABAN 30, HAKA
KUMA YA KAN FITA DA GANIN JINJIRIN WATAN SHAWWAL, KO CIKAR RAMADHANA 30
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) yace:
Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Idan ku ka ganshi –ma'ana:
jinjirin wata- to sai ku yi azumi, Idan kuma kuka gan shi sai ku ajiye azumi
–bikin sallah-, Idan kuma an yi muku hazo to sai ku qaddaramasa (cikar talatin). Bukhariy
da Muslim suka ruwaito shi. A wata ruwaya, daga hadisin Abu-Hurairah (r.a), ya
ce: "Idan aka yi muku hazo to sai ku cika kirgen sha'aban ya zama yini
talatin.
وعَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما، قَالَ: «تَرَائِى النَّاسُ الْهِلَالَ»
فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنِّي رَأَيْتُهُ فَصَامَهُ، وَأَمَرَ النَّاسَ بِصِيَامِهِ"([10]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (R.A) ya
ce: Mutane sun fita dobiyar wata, Sai na bada Manzon Allah –S.A.W-
labari cewa ni na gan shi, Sai ya azumce shi (ramadhan), ya kuma umurci Mutane
da su azumce shi".
وقت النية في صوم الفرض والتطوع
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ، عَنْ حَفْصَةَ رضي
الله عنهما، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَنْ لَمْ يُبَيِّتِ الصِّيَامَ
قَبْلَ الْفَجْرِ، فَلا صِيَامَ لَه» ([11]).
LOKACIN YIN NIYYA A AZUMIN FARILLA DA NA
NAFILA
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar, daga
Hafsat (r.a), daga Annabi (s.a.w) yace: "Duk wanda bai kwana da niyyar
azumi gabanin ketowar alfijir ba to bashi da azumi".
وعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، قَالَتْ: دَخَلَ
عَلَيَّ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ يَوْمٍ فَقَالَ: «هَلْ عِنْدَكُمْ شَيْءٌ؟» فَقُلْنَا: لَا، قَالَ: «فَإِنِّي إِذَنْ صَائِمٌ». ثُمَّ
أَتَانَا يَوْمًا آخَرَ فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، أُهْدِيَ لَنَا حَيْسٌ
فَقَالَ: «أَرِينِيهِ،
فَلَقَدْ أَصْبَحْتُ صَائِمًا» فَأَكَلَ ([12]).
An ruwaito daga A'ishah (R.A), ta ce: Annabi
–S.A.W- ya shigo kaina, a wani yini, sai ya ce: Shin akwai wani
abu a wajenku? Sai mu ka ce: A'a; babu, Sai ya ce: To na xauki
azumi!". Sa'annan sai y azo wurinmu a wani yini na daban, Sai
muka ce: An kawo mana kyautar Haisa, Sai ya ce: "Nuna min shi,
Haqiqa da na wayi gari ina azumi", Sai ya ci.
الأعذار المبيحة للفطر في رمضان، فمنها:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا: أَنَّ حَمْزَةَ بْنَ عَمْرٍو
الأَسْلَمِيَّ قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَأَصُومُ فِي السَّفَرِ؟ وَكَانَ
كَثِيرَ الصِّيَامِ -، فَقَالَ: «إِنْ شِئْتَ فَصُمْ، وَإِنْ شِئْتَ فَأَفْطِرْ» ([13]).
DAGA CIKIN
UZURORI DA SU KE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI TAFIYA:
An ruwaito daga A'isha (r.a), tace: Lallai
Hamza xan Amru Al-sulamiy, ya ce wa Annabi (s.a.w): Shin zan yi azumi a halin
tafiya? –Kuma ya kasance mutum ne mai yawan yin azumi-, Sai ya ce: "In ka so ka yi
azumi, in kuma ka so sai ka karya".
وعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، حين سُئِلَ عَنْ صَوْمِ رَمَضَانَ
فِي السَّفَرِ؟ قَالَ: «كُنَّا
نُسَافِرُ مَعَ النَّبِيِّ r
فَلَمْ يَعِبِ الصَّائِمُ عَلَى المُفْطِرِ، وَلاَ المُفْطِرُ عَلَى الصَّائِمِ» ([14]).
An ruwaito daga Anas xan Malik (R.A) a lokacin
da aka tambaye shi, akan azumtar ramadhana a halin tafiya, Sai ya ce: "Mun kasance
muna yin tafiya tare da annabi –SAW-; mai azumi bai kasance yana aibanta wa
mutumin da ya karya ba, haka shima wadda ya karyan bai kasance yana aibanta mai
azumi ba).
وعَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: كَانَ
رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَرَأَى زِحَامًا
وَرَجُلًا قَدْ ظُلِّلَ عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا هَذَا؟»، فَقَالُوا: صَائِمٌ،
فَقَالَ: «لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ فِي
السَّفَرِ» ([15]).
An ruwaito daga Jabir xan Abdullahi (r.a), Ya
ce: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani
cunkoso, da wani mutum wanda aka yi masa inuwa, sai ya ce: Menene wannan? Sai aka
ce: Me azumi ne, Sai ya ce: "Baya cikin xa'a wa Allah yin azumi a
halin tafiya", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
DAGA CIKIN
UZURORI DA SU KE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI ZUWAN JININ HAILA (hadisin ya
gabata).
ومن الأعذار أيضا:
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه،،، قَالَ: أَغَارَتْ عَلَيْنَا
خَيْلُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَتَيْتُ الرَّسُولَ
وَهُوَ يَتَغَدَّى فَقَالَ: «ادْنُ فَكُلْ» قُلْتُ: إِنِّي صَائِمٌ، قَالَ:
«اجْلِسْ أُحَدِّثْكَ عَنِ الصِّيَامِ،
إِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ وَضَعَ عَنِ الْمُسَافِرِ شَطْرَ الصَّلَاةِ. وَعَنِ
الْمُسَافِرِ وَالْحَامِلِ وَالْمُرْضِعِ الصَّوْمَ»([16]).
DAGA CIKIN
UZURORI DA SU KE HALATTA KARYA AZUMI, AKWAI CIKI DA SHAYARWA:
An ruwaito daga Anas (R.A) ya ce: Dokunan
yaqin Manzon Allah (S.A.W) sun kawo mana farmaki, Sai n azo wajen Manzon Allah
alhalin yana karyawa, Sai ya ce: "Matso, ka ci";
Sai na ce: Lallai ni ina azumi, sai ya ce: "Ka zauna in
baka hadisi kan azumi, Lallai Allah ya janye wa matafiyi rabin sallah. Da kuma
azumi ga Matafiyi, da Mai ciki, da Mai shayarwa".
في صحيح البخاري معلقا (قبل حديث برقم: 4505): قَالَ الحَسَنُ،
وَإِبْرَاهِيمُ:
«فِي المُرْضِعِ أَوِ الحَامِلِ، إِذَا
خَافَتَا عَلَى أَنْفُسِهِمَا أَوْ وَلَدِهِمَا تُفْطِرَانِ ثُمَّ تَقْضِيَانِ».
"Mai shayarwa da mai ciki idan
har su ka ji tsoron wahala ga kansu, ko ga 'ya'yansu to sai su karya azumi,
kana sai su yi ramuko".
وعن ابن عباس رضي الله عنهما، أنه قال: "وَالْمُرْضِع
والْحُبْلَى إِذَا خَافَتَا عَلَى أَوْلادِهِمَا أَفْطَرَتَا، وَأَطْعَمَتَا"([17]).
Saidai kuma an ruwaito daga Abdullahi xan Abbas
(R.A) cewa: "Mai shayarwa da mai ciki idan har su ka ji tsoron wahala ga
'ya'yansu to za su karya azumi, kana –idan su ka yi ramuko- sai su ciyar".
DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE KARYA AZUMI:
AKWAI CI DA SHA DA GANGAN:
fadinsa (SAW):
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ
نَسِيَ وَهُوَ صَائِمٌ، فَأَكَلَ أَوْ شَرِبَ، فَلْيُتِمَّ صَوْمَهُ، فَإِنَّمَا
أَطْعَمَهُ اللهُ وَسَقَاهُ»([18]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) yace:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Duk wadda ya manta alhali yana azumi
sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; Allah ne ya ciyar da shi, ya kuma
shayar da shi".
DAGA CIKI, AKWAI:
YIN JIMA'I:
عَنِ أبي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: "بَيْنَمَا نَحْنُ
جُلُوسٌ عِنْدَ النَّبِيِّ r، إِذْ جَاءَهُ رَجُلٌ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ هَلَكْتُ.
قَالَ: مَا لَكَ؟ قَالَ: وَقَعْتُ عَلَى امْرَأَتِي وَأَنَا صَائِمٌ،
فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ r: هَلْ
تَجِدُ رَقَبَةً تُعْتِقُهَا؟ قَالَ: لاَ، قَالَ: فَهَلْ
تَسْتَطِيعُ أَنْ تَصُومَ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ، قَالَ: لاَ، فَقَالَ: فَهَلْ تَجِدُ إِطْعَامَ سِتِّينَ
مِسْكِينًا. قَالَ: لاَ،
قَالَ: فَمَكَثَ النَّبِيُّ r، فَبَيْنَا نَحْنُ عَلَى ذَلِكَ أُتِيَ النَّبِيُّ r بِعَرَقٍ فِيهَا تَمْرٌ
-وَالعَرَقُ المِكْتَلُ- قَالَ: أَيْنَ
السَّائِلُ؟ فَقَالَ: أَنَا،
قَالَ: خُذْهَا، فَتَصَدَّقْ بِهِ، فَقَالَ الرَّجُلُ: أَعَلَى
أَفْقَرَ مِنِّي يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ فَوَ اللَّهِ مَا بَيْنَ لاَبَتَيْهَا -يُرِيدُ الحَرَّتَيْنِ- أَهْلُ
بَيْتٍ أَفْقَرُ مِنْ أَهْلِ بَيْتِي، فَضَحِكَ النَّبِيُّ r حَتَّى بَدَتْ أَنْيَابُهُ،
ثُمَّ قَالَ: أَطْعِمْهُ أَهْلَكَ"([19]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (R.A) ya ce: "Wata
rana muna zaune a wajen Annabi –S.A.W- sai wani mutum ya zo masa, ya ce: Na
halaka! Sai ya ce: Me ya same ka? Sai ya ce: Na auka wa matata alhali ina
azumi, Sai Manzon Allah –S.A.W- ya ce: Shin zaka samu baiwa da zaka 'yanta ta? Sai ya
ce: A'a! Sai ya ce: Shin zaka iya azumin wata biyu a jere? Sai ya
ce: A'a! Sai ya ce: Shin kana da damar ciyar da miskinai sittin? Sai ya
ce: A'a!, Sai ya ce: Sai Annabi –S.A.W- ya zauna, muna nan a cikin wannan hali
Sai aka zo wa Annabi –S.A.W- da wani masaki da dabino a cikinsa, Sai ya ce: Ina mai wannan
tambayar? Sai na ce: Ni ne, Sai ya ce: Karvi wannan ka
yi sadaka da shi, Sai mutumin ya ce: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai wanda ya
fi ni talauci? Na rantse da Allah! Tsakanin duwatsu biyu na Madina –unguwar
gabas da ta yamma- babu wasu iyalai da suka fi iyalaina talauci. Sai Annabi –S.A.W-
ya yi dariya har sai da fiqoqinsa su ka bayyana, sa'annan ya ce: Ka je ka ciyar
da shi iyalenka".
DAGA CIKIN HAKA AKWAI: YIN AMAI (KO HARASWA)
DA GANGANCI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ ذَرَعَهُ القَيْءُ فَلَيْسَ عَلَيْهِ قَضَاءٌ، وَمَنْ
اسْتَقَاءَ عَمْدًا فَلْيَقْضِ"([20]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a), lallai
Manzon Allah (s.a.w) ya ce:"Duk wanda amai ya rinjaye shi, to babu
ramuko akansa, wanda kuma ya jawo amai da ganganci to ya rama".
DAGA CIKIN HAKA AKWAI: YIN QAHO:
عَنْ ثَوْبَانَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: "أَفْطَرَ
الْحَاجِمُ وَالْمَحْجُومُ"([21]).
"Mai qahon da wanda aka yi masa
azuminsu ya karye".
DAGA CIKIN HAKA AKWAI: FITAN JININ HAILA DA
NA HAIHUWA (Hadisi akan haka ya gabata).
MUSTAHABBAN AZUMI
(1)
DAGA CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN SAHUR:
عن أَنَس بْن مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ:
قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَسَحَّرُوا فَإِنَّ فِي السَّحُورِ
بَرَكَةً» ([22]).
An ruwaito
daga Anas xan Malik (r.a) yace: Manzon Allah (s.a.w) yace "Ku yi sahur;
saboda akwai albarka a cikin sahuur".
(2)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI JINKIRTA YIN SAHUR:
عَنْ أَنَسٍ، عَنْ
زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، قَالَ:«تَسَحَّرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ r، ثُمَّ قُمْنَا إِلَى
الصَّلاةِ»، قُلْتُ: كَمْ كَانَ قَدْرُ مَا
بَيْنَهُمَا؟ قَالَ: خَمْسِينَ آيَة([23]).
An
ruwaito daga Anas (r.a) daga Zaidu xan Sabit (r.a) yace: Mun yi sahur
tare da manzon Allah –SAW- sa'annan sai mu ka tashi izuwa ga sallah, Sai na
ce: Menene tsakanin sahur da sallan? Sai ya ce: Gwargwadon karanta aya hamsin).
(3)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI GAGGAUTA BUXA-BAKI:
عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: "لاَ
يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ، مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ"([24]).
An ruwaito daga Sahl bn Sa'ad (r.a), cewa
lallai Annabi (s.a.w) ya ce: "Mutane ba za su gushe ba cikin alheri;
matukar suna gaggauta buda-baki".
(4)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN BUXA BAKI DA XANYEN DABINO
عن أَنَس بْن مَالِكٍ رضي الله عنه قال: «كَانَ رَسُولُ اللَّهِ r يُفْطِرُ عَلَى رُطَبَاتٍ
قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ رُطَـبَاتٌ، فَعَلَى تَمَرَاتٍ، فَإِنْ
لَمْ تَكُنْ حَسَا حَسَوَاتٍ مِنْ مَاءٍ»([25]).
An ruwaito
daga Anas xan Malik (R.A), ya ce: Manzon Allah –SAW- ya kasance yana buxa-baki
da dabino "ruxab" gabanin ya yi sallah, in kuma bai samu dabino
"ruxab" ba to sai ya karya da busasshen dabino, in kuma bai samu ba
to sai ya sha ruwa".
(5)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN ADDU'A A LOKACIN BUXA-BAKI, DA KUMA YAYIN
AZUMI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
ثَلاَثَةٌ لاَ تُرَدُّ دَعْوَتُهُمْ: الصَّائِمُ حَتَّى يُفْطِرَ، وَالإِمَامُ
العَادِلُ، وَدَعْوَةُ الْمَظْلُومِ يَرْفَعُهَا اللَّهُ فَوْقَ الغَمَامِ
وَيَفْتَحُ لَهَا أَبْوَابَ السَّمَاءِ وَيَقُولُ الرَّبُّ: وَعِزَّتِي
لأَنْصُرَنَّكِ وَلَوْ بَعْدَ حِينٍ"([26]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mutane uku ba a mayar da addu'oinsu:
mai azumi har sai ya sha ruwa, da shugaba adali, da addu'ar wanda aka zalunta,
Allah yana xaga ta a saman girgije, kuma yana buxe mata qofofin sammai, kuma
Ubangijina yana cewa: Na rantse da buwayata, zan taimake ki, koda bayan wani
lokaci".
(6)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YAWAN YIN SADAKA, DA KUMA TILAWAR ALQUR'ANI, DA
SHAYAR DA MASU AZUMI, DA SAURAN AIYUKAN XA'A:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، قَال: "كَانَ رَسُولُ اللَّهِ r أَجْوَدَ النَّاسِ، وَكَانَ
أَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي رَمَضَانَ حِينَ يَـلْقَاهُ جِـبْرِيلُ، وَكَانَ
يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ مِنْ رَمَضَانَ فَـيُدَارِسُهُ القُرْآنَ،
فَلَـرَسُولُ اللَّهِ r أَجْـوَدُ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ"([27]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (R.A), ya
ce: "Manzon Allah ya kasance shi ne yafi kowa kyauta ta alkhairi, kuma
kyautarsa tafi yawa a watan ramadhana a lokacin da mala'ika jibrilu ke saduwa
da shi, kuma jibrilu ya kasance ya kan haxu da shi a cikin kowani dare; sai ya
yi bitar alqur'ani tare da shi; lallai Manzon Allah –S.A.W- a lokacin da mala'ika
jibrilu ke saduwa da shi yafi iska sakakkiya kyautar alkhairi".
(7)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI: AKWAI QOQARI WAJEN YIN SALLAR DARE:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ: «كَانَ النَّبِيُّ r إِذَا دَخَلَ العَشْرُ شَدَّ مِئْزَرَهُ، وَأَحْيَا لَيْلَهُ،
وَأَيْقَظَ أَهْلَه»([28]).
An ruwaito daga A'ishah (R.A) ta ce: "Annabi –S.A.W-
ya kasance idan waxannan goman su ka shiga ya kan tamke kwarjallensa, ya kuma
raya darensa, ya kuma tayar da iyalensa".
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: "مَنْ قَامَ رَمَضَانَ
إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ"([29]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (R.A), daga
Annabi (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya yi tsayuwar dare a ramadana yana mai
imani da neman lada to an gafarta abin da ya gabata na daga zunubansa".
(8)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI YIN UMRAH:
وعَنْ ابْن عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قال: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِامْرَأَةٍ مِنَ الأَنْصَارِ: «مَا مَنَعَكِ أَنْ تَحُجِّينَ مَعَنَا؟»، قَالَتْ: كَانَ
لَنَا نَاضِحٌ، فَرَكِبَهُ أَبُو فُلاَنٍ وَابْنُهُ، لِزَوْجِهَا وَابْنِهَا،
وَتَرَكَ نَاضِحًا نَنْضَحُ عَلَيْهِ، قَالَ: «فَإِذَا كَانَ رَمَضَانُ اعْتَمِرِي فِيهِ، فَإِنَّ
عُمْرَةً فِي رَمَضَانَ حَجَّةٌ»([30])، وفي رواية: "عُمْرَةً فِي رَمَضَانَ تَعْدِل حَجَّةً".
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce wa wata mata daga cikin Ansaar: "Me ya hana ki
kiyi hajji tare da mu? Sai ta ce: Ya kasance muna da raqumin hawa
da xebu ruwa guda xaya, Sai baban wane ya hau shi; shi da xansa, Tana nufin
mijinta da xanta. Sai kuma ya bar mana raqumi xaya da muke xebo ruwa a kansa.
Sai ya ce: "To, idan watan Ramadhan y azo, sai ki yi umrah a cikinsa; saboda yin
umrah a watan ramadana tana daidai da yin hajji".
(9)
DAGA
CIKIN MUSTAHABBAN AZUMI : AKWAI FAXIN CEWA ''NI MAI AZUMI NE'' GA WANDA YA ZAGE
SHI:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قال:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "قَالَ اللَّهُ: كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ
لَهُ، إِلَّا الصِّيَامَ، فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، وَالصِّيَامُ
جُنَّةٌ، وَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَصْخَبْ،
فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ، فَلْيَقُلْ: إِنِّي امْرُؤٌ صَائِمٌ"([31]).
An ruwaito daga Abu-Hurairah (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w): "Allah ya ce: Dukkan aikin xan adam nasa ne, in
banda azumi, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, kuma azumi
garkuwa ne, kuma idan ranar azumin dayanku ya zo, to kada ya yi batsa cikin
zance da iyali ko jima'i "rafasu", kada kuma ya yi ihu, Idan wani ya
nemi zaginsa ko yin fada da shi to ya ce: Ni Mutum ne mai azumi ne".
MAKRUHAN AZUMI
1- DAGA CIKIN MAKRUHAN AZUMI AKWAI: KAIWA MAQURA LOKACIN
KURKURAN BAKI, DA SHAQA RUWA A HANCI;
في حديث لَقِيطِ
بْنِ صَبْرَةَ رضي الله عنه لما وفدوا علَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، وفيه، قال: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَخْبِرْنِي عَنِ الْوُضُوءِ،
قَالَ: «أَسْبِغِ
الْوُضُوءَ، وَخَلِّلْ بَيْنَ الْأَصَابِعِ، وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا
أَنْ تَكُونَ صَائِمًا» ([32]).
Daga hadisin Laqid xan Sabrah (r.a) a lokacin
da tawagarsu ta zo wajen ManzonAllah (s.a.w), A cikinsa ya ce: Na ce: Ya
Ma'aikin Allah k aba ni labari akan alwala Sai ya ce: "Ka cika alwala,
kuma ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kuma, kai makura wajen shakar ruwa, sai
dai in ka kasance kana azumi".
2- DAGA CIKIN MAKRUHAN AZUMI AKWAI: YIN SUMBA GA WANDA ZATA
MOTSA SHA'AWARSA, KUMA BAYA AMINCE WA KANSA:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ
اللهُ عَنْهَا، قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
«يُقَبِّلُ وَهُوَ صَائِمٌ، وَيُبَاشِرُ
وَهُوَ صَائِمٌ، وَلَكِنَّهُ أَمْلَكُكُمْ لِإِرْبِهِ»([33]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a) ta ce: "Manzon Allah
(s.a.w) ya kasance yana yin sumba, alhalin yana yin azumi, kuma yana runguma,
alhalin yana azumi, saidai ya kasance ya fi ku iya mallakar bukatarsa".
BAYANIN
AZUMI NA "MUSTAHABBI":
(1)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR KWANAKI SHIDA (6) A CIKIN WATAN
SHAWAAL:
عَنْ أَبِي أَيُّوبَ
الْأَنْصَارِيِّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ
صَامَ رَمَضَانَ، ثُمَّ أَتْبَعَهُ سِتًّا مِنْ شَوَّالٍ، كَانَ كَصِيَامِ
الدَّهْر»([34]).
An ruwaito
daga Abu-Ayyub (r.a) lallai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Wanda ya yi
azumin watan ramadana, sa'annan ya biyar da azumi guda shida -6-, daga watan
shawwal, to kamar ya azumci zamani ne -shekara-".
(2)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR YININ ARFAH GA WANDA BA
MAHAJJACI BA:
عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قال، قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "صِيَامُ يَوْمِ عَرَفَةَ، أَحْتَسِبُ عَلَى
اللهِ أَنْ يُكَفِّرَ السَّنَةَ الَّتِي قَبْلَهُ، وَالسَّنَةَ الَّتِي بَعْدَهُ"([35]).
An ruwaito
daga Abu-qatadatah (r.a) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Azumin ranar
arfah ina zaton Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabace shi, da wacce
za ta zo, bayansa".
(3)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI" AKWAI: AZUMIN YININ ASHURA:
عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قال، قَالَ
رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "صِيَامُ يَوْمِ عَاشُورَاء أَحْتَسِبُ عَلَى اللهِ أَنْ يُكَفِّرَ
السَّنَةَ الَّتِي قَبْلَهُ"([36]).
An ruwaito daga Abu-qatadatah (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Kuma azumtar yinin 10 ga watan almuharram
(ashura), Ina fatan Allah zai kankare zunuban shekara da ta gabace shi".
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا، قَالَ: قَالَ
رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَئِنْ بَقِيتُ إِلَى قَابِلٍ لَأَصُومَنَّ
التَّاسِعَ»([37]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (r.a) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Idan har na kai baxi to zan azumci
ranar tara –ga watan muharram-".
عن ابْن عَبَّاسٍ رضي الله عنهما مرفوعا، قال: "صُومُوا يَوْمًا قَبْلَهُ
أَوْ يَوْمًا بَعْدَه، خَالِفُوا الْيَهُودَ"([38]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (r.a)
yace: "Ku azumci yini da ke gabaninsa, ko kuma yinin da ke bayansa; ku saba
wa yahudu".
(4)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR RANAR LITININ DA ALAMIS NA
KOWANI SATI:
عَنْ عَائِشَة رضي الله عنها،
قالت: "كَانَ النبي r يَتَحَرَّى صِيَامَ الاثْنَيْنِ وَالْخَمِيسِ"([39]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a) ta ce: "Annabi –SAW- ya
kasance yana kirdadon azumtar ranar litinin da alamis".
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "تُعْرَضُ الأَعْمَالُ
يَوْمَ الاِثْنَيْنِ وَالخَمِيسِ، فَأُحِبُّ أَنْ يُعْرَضَ عَمَلِي وَأَنَا صَائِم"([40]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a), lallai Manzon
Allah (s.a.w) ya ce: "Ana bijiro da aiyuka a ranakun litinin, da alamis;
don haka ina son a bijiro da aikina alhalin ina azumi".
(5)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR KWANAKI UKU CIKIN KOWANI WATA:
عَنِ عَبْد اللَّهِ بْن عَمْرٍو رضي الله عنه مرفوعا، قَالَ: "صُمْ مِنَ الشَّهْرِ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ؛ فَإِنَّ الحَسَنَةَ بِعَشْرِ
أَمْثَالِهَا، وَذَلِكَ مِثْلُ صِيَامِ الدَّهْر"([41]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Amru (r.a),
dagaManzon Allah (s.a.w) yace: "Ka azumci kwanaki uku daga
kowani wata; saboda aiki mai kyau ana ruvanya ladansa sau goma; idan ka yi, to
kamar ka azumci shekara ne baki-xayanta".
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَال: "أَوْصَانِي خَلِيلِي r
بِثَلاَثٍ: صِيَامِ ثَلاَثَةِ أَيَّامٍ مِنْ كُلِّ شَهْرٍ، وَرَكْعَتَيِ الضُّحَى،
وَأَنْ أُوتِرَ قَبْلَ أَنْ أَنَامَ"([42]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) ya ce:
"Masoyina kuma badaxi –SAW- ya min wasici da abubuwa guda uku:
azumtar kwanaki uku cikin kowani wata, da kuma raka'oi guda biyu na walaha, da
kuma cewa na yi witiri gabanin na yi barci".
عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "مَنْ كَانَ مِنْكُمْ صَائِمًا مِنَ
الشَّهْرِ، فَلْيَصُمِ الثَّلاثَ الْبِيضَ"([43]).
An ruwaito daga Abu-zarrin (r.a), ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Duk wanda zai
yi azumi daga cikinku a cikin kwanakin wata; to ya azumci ranaku guda uku; da
wata a cikinsu ya ke da haske".
(6)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR YINI DA SHAN RUWAN YININ DAKE
BAYANSA:
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرٍو، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "أَفضلُ الصِّيَامِ صِيَامُ دَاوُدَ u، كَانَ يَصُومُ يَوْمًا، وَيُفْطِرُ يَوْمًا"([44]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Amru (r.a) yace:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mafificin azumi
shi ne irin azumin annabi Dawud –A.S-; ya kasance ya kan azumci yini, ya sha
ruwa a wani yini".
(7)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMI CIKIN WATAN ALLAH; ALMUHARRAM:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْضَلُ
الصَّيَامِ بَعْدَ شَهْرِ رَمَضَانَ شَهْرُ اللَّهِ الْمُحَرَّمُ، وأَفْضَلُ
الصَّلاةِ بَعْدَ الفريضة صَلاةُ اللَّيْلِ»([45]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a), ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mafificin azumi
bayan na ramadana shi ne azumin watan Allah; al-muharram, Mafificin sallah kuma
bayan ta farilla ita ce: sallar dare".
(8)
DAGA
CIKIN AZUMI NA "MUSTAHABBI": AZUMTAR KWANAKI TARA NA FARKON WATAN
ZULHIJJAH:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "مَا مِنْ أَيَّامٍ العَمَلُ
الصَّالِحُ فِيهِنَّ أَحَبُّ إِلَى اللهِ مِنْ هَذِهِ الأَيَّامِ العَشْر، فَقَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، وَلاَ الجِهَادُ فِي
سَبِيلِ اللهِ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: وَلاَ الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ، إِلاَّ
رَجُلٌ خَرَجَ بِنَفْسِهِ وَمَالِهِ فَلَمْ يَرْجِعْ مِنْ ذَلِكَ بِشَيْءٍ"([46]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (s.a.w),
yace: Manzon Allah (s.a.w) yace: "Babu wasu kwanaki wanda aiki na-kwarai
ya fi soyuwa a cikinsu a wajen Allah fiye da waxannan kwanaki guda goma. Sai suka ce:
Ya ma'aikin Allah, koda jihadi fiysabilillahi ne? Sai Manzon Allah (s.a.w)
yace: Koda jihadi fiysabillahi ne, Saidai
mutumin da ya fita da kansa, da dukiyarsa, sai bai dawo da komai ba daga
cikinsu".
BAYANIN AZUMI NA "HARAMUN" DA NA
"MAKRUHI":
Makruhi ne a kebe watan
"rajab" da azumi;
Ahmad bn Kharishah bn Al-hurri ya ruwaito; ya
ce:
"رأيت عمر يضرب أكف المترجبين حتى يضعوها فى الطعام؛ ويقول:
كلوا فإنما هو شهر كانت تعظمه الجاهلية"([47]).
"Lallai na ga Umar bn Alkhaddab –RA-
yana bugun hanayen masu azumi a watan "rajab", yana ta aikata haka;
har sai sun sanya su a cikin abinci, kana kuma yana cewa: Ku ci; shi rajab abin
sani kawai; wata ne da mutanen jahiliyya suka kasance suna girmama shi".
1. Makruhi ne keve yinin "juma'a" da azumi:
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لا تَصُومُوا يَوْمَ الْجُمُعَةِ إِلا أَنْ تَصُومُوا يَوْمًا
قَبْلَهُ، أَوْ يَوْمًا بَعْدَهُ"([48]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) yace:
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Kada ku yi azumin yinin juma'a sai dai
in za ku azumci yinin gabaninsa, ko yinin bayansa".
2. Makruhi ne kevance yinin "asabat" da azumi:
عَنْ عَبْد اللهِ بْن بُسْرٍ الْمَازِنِيَّ رضي الله عنه قال: قَالَ
رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لا تَصُومُوا يَوْمَ السَّبْتِ إِلا فِيمَا
افْتُرِضَ عَلَيْكُمْ"([49]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Busr Almaziniy
(r.a) yace: Manzon Allah (s.a.w) yace: "Kada ku yi azumin yinin asabat
sai cikin abin da aka farlanta muku".
وعَنْ جُوَيْرِيَةَ رضي الله عنه، قَالَتْ: دَخَلَ عَلَيَّ رَسُولُ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا صَائِمَةٌ يَوْمَ الْجُمُعَةِ، فَقَالَ: "أَصُمْتِ أَمْسِ؟ قالت:
لا، فَقَالَ: أَتَصُومِينَ غَدًا؟ قالت: لا، فَقَالَ: أَفْطِرِي"([50]).
An ruwaito daga Uwar muminai Juwairiyyah (r.a)
ta ce: Manzon Allah ya shigo wurina alhalin ina azumi a ranar juma'a, Sai ya ce:
"Shin kin yi azumi jiya? Sai ta ce: A'a! sai ya ce: Shin za
ki yi azumin gobe? Sai ta ce: A'a! Sai ya ce: To ki karya".
Al-imamut tirmiziy –RL- yana cewa bayan ya
ambaci hadisin hani da ya gabata:
"وَمَعْنَى الكَرَاهية فِي هَذَا: أَنْ يَخُصَّ الرَّجُلُ
يَوْمَ السَّبْتِ بِصِيَامٍ، لأَنَّ اليَهُودَ يُعَظِّمُون يَوْمَ السَّبْتِ".
"Ma'anar abinda aka nufa da qiyewa na
makruhi a nan: Shi ne Mutum ya kevance yinin asabat da azumi; saboda yahudawa
sun kasance suna girmama yinin asabat".
3. Haramcin azumtar ranar shakka:
An ruwaito daga Ammar (r.a), ya ce: "Wanda ya azumci
ranar da ake shakka to haqiqa ya savawa "baban alkasim –SAW-").
وعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «لاَ يَتَقَدَّمَنَّ أَحَدُكُمْ رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ أَوْ يَوْمَيْنِ،
إِلا أَنْ يَكُونَ رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمَهُ، فَلْيَصُمْ ذَلِكَ اليَوْم"([52]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a), daga
Annabi (s.a.w) ya ce: "Kada xayanku ya rigayi watan ramadana da azumin
yini guda xaya ko yini biyu, saidai ga mutumin da ya kasance yana azumtar
azuminsa, to shi kam ya azumci wannan yinin".
4. Haramun ne azumtar ranakun idi guda biyu:
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: «نَهَى النَّبِيُّ r عَنْ صَوْمِ يَوْمِ الفِطْر وَالنَّحْر"([53]).
An ruwaito daga Abu-sa'id alkudriy (r.a) ya ce:
"Annabi –SAW- ya hana azumtar yinin sallar azumi –karamar sallah-, dana
layyah).
عَنْ أَبِي عُبَيْدٍ مَوْلَى ابْنِ أَزْهَرَ، قَالَ: شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ
عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، فَقَالَ: "هَذَانِ يَوْمَانِ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ r عَنْ صِيَامِهِمَا: يَوْمُ
فِطْرِكُمْ مِنْ صِيَامِكُمْ، وَالـيَوْمُ الآخَرُ تَأْكُلُونَ فِيهِ مِنْ
نُسُكِكُم"([54]).
An ruwaito daga Abu-ubaid; wato: 'yantaccen
bawan Ibu-Azhar, ya ce: Na halarci idi tare da Umar xan Alkhaxxab (r.a) sai ya
ce: "Waxannan yini ne guda biyu da Manzon Allah –S.A.W- ya hana
azumtarsu; yinin da kuka karya azuminku a cikinsa –sallar azumi-. Yini xayan
kuma shi ne: wanda ku ke ci a cikinsa daga layyanku".
5.
Makruhi
ne azumtar kwanakin da ake kiransu: (ayyamut tash-riq)
Wato: ranar goma sha xaya (11), da sha biyu
(12), da kuma sha uku (13), saboda faxinsa (SAW):
عَنْ نُبَيْشَةَ الْهُذَلِيِّ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَيَّامُ التَّشْرِيقِ أَيَّامُ أَكْلٍ وَشُرْبٍ، وَذِكْرٍ لِلَّه U"([55]).
An ruwaito daga Nubaisha Alhuzaliy, ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Kwanakin da ake kiransu kwanakin
"at-tashriq" kwanaki ne na ci da sha, da kuma ambaton Allah mabuwayi
da xaukaka".
وعَنْ
عُقْبَةَ بْن عَامِرٍ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "يَوْمُ عَرَفَةَ، وَيَوْمُ
النَّحْرِ، وَأَيَّامُ التَّشْرِيقِ، عِيدُنَا -أَهْلَ الإِسْلاَمِ-، وَهِيَ
أَيَّامُ أَكْلٍ وَشُرْبٍ"([56]).
An ruwaito daga Uqbah xan Amir (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Yinin arfah, da
yinin layyah, da kwanaki "at-tashriq" idi su ke a wajenmu; mu ma'abuta
musulunci; don haka: su kwanaki ne na ci da sha).
وعَنْ عُرْوَةَ عَنْ عَائِشَةَ، وَعَنْ سَالِمٍ عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ
اللَّهُ عَنْهُمْ، قَالاَ: «لَمْ يُرَخَّصْ فِي أَيَّامِ التَّشْرِيقِ أَنْ يُصَمْنَ، إِلا لِمَنْ لَمْ
يَجِدِ الهَدْي"([57]).
An ruwaito daga Urwat daga A'ishah (r.a), da kuma
ta hanyar Salim daga Abdullahi xan Umar (R.A) sun ce: "Ba a yi
rangwame kan azumtar kwanakin "attashriq" sai ga wadda bai samu
hadaya ba".
I'ITIKAAF:
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، «أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَان يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ حَتَّى تَوَفَّاهُ
اللَّهُ، ثُمَّ اعْتَكَفَ أَزْوَاجُهُ مِنْ بَعْدِهِ»([58]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a) cewa: "Lallai Annabi
–S.A.W- ya kasance yana yin "I'itikaafin" kwanaki goman karshen
ramadana, har Allah ta'alah ya karvi ransa. Sa'annan sai matansa suka yi
i'itikafi a bayansa".
عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، أَنَّ عُمَرَ سَأَلَ النَّبِيَّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: كُنْتُ نَذَرْتُ فِي الجَاهِلِيَّةِ أَنْ أَعْتَكِفَ
لَيْلَةً فِي المَسْجِدِ الحَرَامِ، قَالَ: «فَأَوْفِ بِنَذْرِكَ» ([59]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) cewa
lallai Umar (r.a), ya ce: "Ya manzon Allah! Lallai ni na yi
bakancen zan yi "i'itikaafin" dare guda a masallaci mai alfarma
–makka-, a jahiliyya? Sai ya ce: Ka cika bakancenka".
Daga cikin Abubuwan da aka halatta ga mai i'itikaafi:
عَنْ صَفِيَّةَ بِنْتِ حُيَيٍّ رضي
الله عنها، قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ مُعْتَكِفًا فَأَتَيْتُهُ أَزُورُهُ لَيْلًا، فَحَدَّثْتُهُ ثُمَّ
قُمْتُ فَانْقَلَبْتُ، فَقَامَ مَعِي لِيَقْلِبَنِي، وَكَانَ مَسْكَنُهَا فِي
دَارِ أُسَامَةَ بْنِ زَيْدٍ، فَمَرَّ رَجُلاَنِ مِنَ الأَنْصَارِ، فَلَمَّا
رَأَيَا النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَسْرَعَا، فَقَالَ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَلَى رِسْلِكُمَا إِنَّهَا صَفِيَّةُ بِنْتُ حُيَيٍّ»، فَقَالاَ: سُبْحَانَ اللَّهِ يَا
رَسُولَ اللَّهِ! قَالَ: "إِنَّ الشَّيْطَانَ يَجْرِي مِنَ الإِنْسَانِ مَجْرَى الدَّمِ، وَإِنِّي
خَشِيتُ أَنْ يَقْذِفَ فِي قُلُوبِكُمَا سُوءًا، أَوْ قَالَ: شَيْئًا"([60]).
An ruwaito daga Safiyyah (r.a) ta ce: "Manzon Allah
–SAW- ya kasance yana i'itikafi, sai na zo masa a cikin dare don na ziyarce
shi, kuma na yi masa taxi, sa'annan na tashi zan koma, sai shima ya tashi don
ya raka ni. Kuma wurin zamanta ya kasance a gidan Usamah xan Zaid, Sai wasu
mutane biyu daga cikin ansarawa, Yayin da su biyu suka ga annabi (s.a.w) sai
suka yi sauri, Sai Annabi (s.a.w) ya ce: Ku bi a hankali, Wannan Safiyyah 'yar
Huyay ce, Sai suka ce: Subhanallah, ya ma'aikin Allah! Sai ya ce: Lallai shexan
yana gudana a mutum kamar gudanar jini, kuma lallai na ji tsoron a jefa mummuna
abu ne a cikin zukatanku, ko kuma ya ce: Wani abu".
Daga cikin Abubuwan da su ke bata
"I'itikafi" akwai: Ficewa daga masallaci ba tare da bukata ba (da-gangan);
عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ: وَإِنْ كَانَ رَسُولُ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ «لَيُدْخِلُ عَلَيَّ رَأْسَهُ وَهُوَ فِي المَسْجِدِ،
فَأُرَجِّلُهُ، وكان لاَ
يَدْخُلُ البَيْتَ إِلا لِحَاجَةٍ؛ إِذَا كَانَ مُعْتَكِفًا"([61]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a) ta ce: "Mazon Allah
(s.a.w) ya kasance yana shigo min da kasa, alhalin yana cikin masallaci, sai na
tace masa, kuma ya kasance baya shiga gida sai don bukata, idan ya kasance yana
I'itikaafi).
ZAKKAR FID-DA-KAI, KO SADAKAR
FID-DA-KAI (AL-FIXR):
عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ
شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ
وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ
النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ» ([62]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a), ya
ce: "Manzon Allah –r- ya wajabta
zakkar fid da kai; sa'iy xaya na dabino, ko kuma sa'iy na sha'ir, akan bawa da
xa, namiji da mace, da yaro da babba, daga cikin Musulmai. Kuma ya yi umurni
cewa a fitar da ita gabanin Mutane su fita i zuwa sallar idi".
وعَنْ أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُول اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَيْسَ فِي الْعَبْدِ صَدَقَةٌ إِلا صَدَقَةُ
الْفِطْر»([63]).
An ruwaito daga Abu-hurairah (r.a) ya ce:
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ba a bada wata sadaka akan bawa in
banda sadakatu alfixr".
HIKIMAR WAJABTA ZAKATU ALFIXR:
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما، قَالَ: «فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ،
وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ، فَمَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلَاةِ فَهِيَ زَكَاةٌ
مَقْبُولَةٌ، وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلَاةِ فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنَ
الصَّدَقَاتِ»([64]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (r.a) ya
ce: "Manzon Allah (s.a.w) ya farlanta ''zakatu al-fixr" don ta zama
tsarkaka ga mai azumi daga wargi da batsa, kana ta zama abinci ga miskinai. Duk
mutumin da ya bayar da ita gabanin sallar idi to wannan zakka ce karvavviya,
duk kuma wanda ya bada ita bayan sallah to sadaka ce daga cikin sadakoki".
SALLAR IDI (BIYU):
Wuraren da ake sallatar idi a cikinsu:
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه، قَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَخْرُجُ يَوْمَ الفِطْرِ وَالأَضْحَى إِلَى المُصَلَّى،
فَأَوَّلُ شَيْءٍ يَبْدَأُ بِهِ الصَّلاَةُ، ثُمَّ يَنْصَرِفُ، فَيَقُومُ مُقَابِلَ
النَّاسِ، وَالنَّاسُ جُلُوسٌ عَلَى صُفُوفِهِمْ فَيَعِظُهُمْ، وَيُوصِيهِمْ،
وَيَأْمُرُهُمْ، فَإِنْ كَانَ يُرِيدُ أَنْ يَقْطَعَ بَعْثًا قَطَعَهُ، أَوْ
يَأْمُرَ بِشَيْءٍ أَمَرَ بِهِ، ثُمَّ يَنْصَرِفُ»([65]).
An ruwaito daga Abu-sa'id (r.a) cewa: (Manzon
Allah (s.a.w) ya kasance a idin azumi da na lahiyah ya kan fita zuwa
"wurin sallah", kuma farkon abinda yake faraway da shi shine sallah,
sa'annan sai ya juya, sai ya tsaya yana fiskantar Mutane, alhalin mutane suna
zaune a cikin sahunsu, sai ya yi musu wa'azi, ya musu wasici, ya umurce su ).
وعَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، خَرَجَ رَسُولُ
اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي أَضْحًى أَوْ فِطْرٍ إِلَى المُصَلَّى، ثُمَّ انْصَرَفَ، فَوَعَظَ النَّاسَ، وَأَمَرَهُمْ بِالصَّدَقَةِ،
فَقَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، تَصَدَّقُوا»، فَمَرَّ عَلَى النِّسَاءِ،
فَقَالَ: «يَا مَعْشَرَ النِّسَاءِ، تَصَدَّقْنَ،
فَإِنِّي رَأَيْتُكُنَّ أَكْثَرَ أَهْلِ النَّارِ» فَقُلْنَ: وَبِمَ ذَلِكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟
قَالَ: «تُكْثِرْنَ
اللَّعْنَ، وَتَكْفُرْنَ العَشِيرَ، مَا رَأَيْتُ مِنْ نَاقِصَاتِ عَقْلٍ وَدِينٍ،
أَذْهَبَ لِلُبِّ الرَّجُلِ الحَازِمِ، مِنْ إِحْدَاكُنَّ، يَا مَعْشَرَ
النِّسَاءِ»، ثُمَّ انْصَرَفَ، فَلَمَّا صَارَ إِلَى
مَنْزِلِهِ، جَاءَتْ زَيْنَبُ، امْرَأَةُ ابْنِ مَسْعُودٍ، تَسْتَأْذِنُ عَلَيْهِ،
فَقِيلَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، هَذِهِ زَيْنَبُ، فَقَالَ: «أَيُّ الزَّيَانِبِ؟» فَقِيلَ: امْرَأَةُ ابْنِ مَسْعُودٍ، قَالَ: «نَعَمْ، ائْذَنُوا لَهَا» فَأُذِنَ لَهَا، قَالَتْ: يَا نَبِيَّ اللَّهِ،
إِنَّكَ أَمَرْتَ اليَوْمَ بِالصَّدَقَةِ، وَكَانَ عِنْدِي حُلِيٌّ لِي،
فَأَرَدْتُ أَنْ أَتَصَدَّقَ بِهِ، فَزَعَمَ ابْنُ مَسْعُودٍ: أَنَّهُ وَوَلَدَهُ
أَحَقُّ مَنْ تَصَدَّقْتُ بِهِ عَلَيْهِمْ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «صَدَقَ
ابْنُ مَسْعُودٍ، زَوْجُكِ وَوَلَدُكِ أَحَقُّ مَنْ تَصَدَّقْتِ بِهِ عَلَيْهِمْ»([66]).
An ruwaito daga Abu-sa'id (r.a) cewa: "Manzon
Allah (s.a.w) ya fita a idin azumi da na lahiyah zuwa "wurin sallah",
sa'annan ya juya, sai ya yi wa'azi wa mutane, kuma ya umurce su da yin sadaka,
Ya ce: "Ya ku Mutane ku yi sadaka", Sai ya zo ta wajen mata,
Ya ce: "Ya ku mata ku yi sadaka, saboda naga kune kuka fi yawa daga cikin
ma'abuta shiga wuta", Sai suka ce: Menene ya sabbaba hakan ya ma'aikin
Allah? Sai ya ce: "Kuna yawaita yin la'ana, kuma kuna butulce wa
abokin zama (miji), Ban ga masu tawaya a cikin hankali da addini, wanda suka fi
tafiyar da hankalin namiji mai azama, fiye da xayanku",
Sannan ya juya, da ya tafi gidansa sai Zainab; matar Abdullahi xan Mas'ud ta
je, tana neman izininsa, Sai aka ce, Ya ma'aikin Allah! Ga nan Zainab, Sai ya
ce: Wace daga cikin Zainabobi? Sai aka ce masa: Matar Abdullahi
xan Mas'ud, Ya ce: "Na'am, ku yi izini a gare ta",
Sai aka yi mata izini, Sai ta ce: Ya ma'aikin Allah! Lallai a yau ka yi umurnin
a bada sadaka, kuma ya kasance a wurina akwai kayan adona (na zinari), sai na
yi nufin na bada sadakarsa, Sai Xan Mas'ud ya riya cewa: Wai shi, da 'ya'yansa
sune suka fi cancantar sadakata, Sai Annabi (s.a.w) ya ce: "Xan Mas'ud,
yayi gaskiya; saboda mijinki da 'ya'yanki sune waxanda suka fi cancantar
sadakarki".
YAWAN RAKA'OIN SALLAR IDI
عن عُمَر رضي الله عنه قَالَ: «صَلَاةُ الْأَضْحَى رَكْعَتَانِ، وَصَلَاةُ
الْجُمُعَةِ رَكْعَتَانِ، وَصَلَاةُ الْفِطْرِ رَكْعَتَانِ، وَصَلَاةُ
الْمُسَافِرِ رَكْعَتَانِ تَمَامٌ غَيْرُ قَصْرٍ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّكُمْ،
وَقَدْ خَابَ مَنِ افْتَرَى»([67]).
An ruwaito daga Umar (r.a) ya ce: "Sallar idin layyah
raka'oi biyu ne, sallar juma'a itama raka'oi biyu ne, sallar idin azumi (fixr)
raka'oi biyu ne, sallar matafiyi raka'oi biyu ne, a cike suke, ba qasaru ba,
wannan ya zo a harshen annabinku. Haqiqa wanda yayi qirqira ya tave".
عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنه، قالت: «إنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ كَانَ يُكَبِّرُ فِي الْفِطْرِ وَالْأَضْحَى، فِي الْأُولَى سَبْعَ
تَكْبِيرَاتٍ، وَفِي الثَّانِيَةِ خَمْسًا، سِوَى تَكْبِيرَتَيِ الرُّكُوع»([68]).
An ruwaito daga A'ishah (r.a), lallai Manzon
Allah (s.a.w) ya kasance yana yin Kabbarori a idin azumi dana lahiyah, a
raka'ar farko kabbarori bakwai, a raka'a ta biyu kuma kabbarori biyar; qari
akan kabbarori guda biyu na tafiya zuwa ruku'i).
Yaushe ake yin huxuba?
عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما، قَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، وَأَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، يُصَلُّونَ
العِيدَيْنِ قَبْلَ الخُطْبَةِ» ([69]).
An ruwaito daga Abdullahi xan Umar (r.a) ya ce:
"Manzon Allah (s.a.w) ya kasance, da Abubakar da Umar (Allah ya qara
yarda a gare su) suna yin sallar idin azumi dana lahiya, gabanin yin huxuba".
Daga cikin Sunnonin idi:
عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: «كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ إِذَا كَانَ يَوْمُ عِيدٍ خَالَفَ الطَّرِيقَ»([70]).
An ruwaito daga Jabir (r.a), yace: "Annabi (s.a.w)
ya kasance idan ranar idi ta zo ya kan sava hanya".
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه، قَالَ: «كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لاَ يَغْدُو يَوْمَ الفِطْرِ حَتَّى يَأْكُلَ تَمَرَاتٍ»، وفيه: «وَيَأْكُلُهُنَّ وِتْرًا»([71]).
An ruwaito daga Anas xan Malik (r.a), yace:
"Manzon Allah (s.a.w) ya kasance baya wayan gari ranar idin azumi har
sai ya ci kwayoyin dabino", "kuma yana cinsu
mara (uku, biyar, ko bakwai)".
في صحيح البخاري
4508 –
عَنِ
البَرَاءِ،
سَمِعْتُ
البَرَاءَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: «لَمَّا
نَزَلَ صَوْمُ رَمَضَانَ كَانُوا لاَ يَقْرَبُونَ النِّسَاءَ رَمَضَانَ كُلَّهُ،
وَكَانَ رِجَالٌ يَخُونُونَ أَنْفُسَهُمْ». فَأَنْزَلَ اللَّهُ {عَلِمَ
اللَّهُ أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَخْتَانُونَ
أَنْفُسَكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ وَعَفَا عَنْكُمْ} [البقرة:
187]
في سنن أبي داود
2313 –
عَنِ
ابْنِ عَبَّاسٍ، {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ
كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ} [البقرة: 183]، " فَكَانَ النَّاسُ عَلَى عَهْدِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا صَلَّوُا الْعَتَمَةَ حَرُمَ عَلَيْهِمُ الطَّعَامُ
وَالشَّرَابُ وَالنِّسَاءُ، وَصَامُوا إِلَى الْقَابِلَةِ،
فَاخْتَانَ رَجُلٌ نَفْسَهُ، فَجَامَعَ امْرَأَتَهُ، وَقَدْ صَلَّى الْعِشَاءَ،
وَلَمْ يُفْطِرْ، فَأَرَادَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ أَنْ يَجْعَلَ ذَلِكَ يُسْرًا
لِمَنْ بَقِيَ وَرُخْصَةً وَمَنْفَعَةً، فَقَالَ سُبْحَانَهُ: {عَلِمَ اللَّهُ
أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَخْتَانُونَ أَنْفُسَكُمْ}
[البقرة: 187] الْآيَةَ، وَكَانَ هَذَا مِمَّا نَفَعَ اللَّهُ بِهِ النَّاسَ
وَرَخَّصَ لَهُمْ وَيَسَّرَ.
في
مسند الإمام أحمد جاء التصريح باسم بعض الصحابة الذين وقعوا في النهي، فـ15795 - من طريقه إلى ابْن لَهِيعَةَ، ... إلى كَعْبِ
بْنِ مَالِكٍ، رضي الله عنه، قَالَ: كَانَ النَّاسُ فِي رَمَضَانَ إِذَا صَامَ
الرَّجُلُ، فَأَمْسَى فَنَامَ حَرُمَ عَلَيْهِ الطَّعَامُ، وَالشَّرَابُ،
وَالنِّسَاءُ حَتَّى يُفْطِرَ مِنَ الْغَدِ، فَرَجَعَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ
مِنْ عِنْدِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ذَاتَ لَيْلَةٍ، وَقَدْ
سَهِرَ عِنْدَهُ فَوَجَدَ امْرَأَتَهُ قَدْ نَامَتْ، فَأَرَادَهَا فَقَالَتْ:
إِنِّي قَدْ نِمْتُ، قَالَ: مَا نِمْتِ ثُمَّ وَقَعَ بِهَا، وَصَنَعَ كَعْبُ بْنُ
مَالِكٍ مِثْلَ ذَلِكَ، فَغَدَا عُمَرُ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ فَأَخْبَرَهُ فَأَنْزَلَ اللهُ تَعَالَى: " {عَلِمَ اللهُ
أَنَّكُمْ كُنْتُمْ تَخْتَانُونَ أَنْفُسَكُمْ
فَتَابَ عَلَيْكُمْ وَعَفَا عَنْكُمْ} [البقرة: 187] ".
([25]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba:
2356), da
At-tirmiziy (lamba: 696), kuma ya ce: hasan ne, Albagawiy a cikin littafinsa
(Sharhu assunah, ya fitar da shi, 6/266), ya kuma ce hadisi ne: hasan, Albaniy
kuma ya inganta shi a cikin (Sahihu At-tirmiziy, lamba: lamba: 560), Malam
Al-arna'ux ya ce: isnadinsa mai karfi ne a cikin ''ta'aliqinsa ga littafin:
Sharhu assunnah") .
([26]) At-tirmiziy
ya ruwaito shi (lamba: 2526), kana ya ce: hasan ne, kuma Albaihaqiy ya fitar da
shi (3/345), da waninsu; daga Anas (R.A), daga Annabi (S.A.W) da lafazin:
" ثَلاَثُ دَعَوَاتٍ لاَ تُرَدُّ، دَعْوَةُ
الْوَالِدِ، وَدَعْوَةُ الصَّائِمِ، وَدَعْوَةُ الْمُسَافِر".
Ma'ana: «Adduo'i guda uku ba a raddinsu, addu'ar iyaye, da ta mai azumi, da addu'ar
matafiyi», Kuma Albaniy ya inganta shi a cikin (Silsilatu as-sahihah,
lamba: 1797).
([49]) Abu-dawud
ya ruwaito shi (lamba: 2421), da At-tirmiziy (lamba: 744), da Ibnu-majah
(lamba: 1726), da Alhakim (1/435), kuma At-tirmiziy yace: hadisi ne hasan,
Alhakim kuma ya inganta shi akan sharadin Bukhariy, kana kuma Azzahabiy ya masa
"muwafaqah", Albaniy ma ya inganta shi (Sahihu At-tirmiziy, lamba: 1986).
([51]) Bukhariy ya ambace shi -a cikin sahihinsa a
matsayin hadisi "mu'allaq", amma da "sigar tabbatarwa"-
(Duba: fat-hul baariy, 4/143). A littafin azumi, a babin faxin Annabi (SAW):
idan ku ka ga jinjirin wata to sai ku yi azumi. Amma At-tirmiziy da waninsa sun
ruwaito shi a matsayin "hadisi mausul", ya kuma ce: hadisi ne hasan
sahih, Albaniy ya inganta shi (Sahihu At-tirmiziy, lamba: 553).
No comments:
Post a Comment