HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 20/SHA'ABAN/1437H
Daidai da 27/Mayu/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
NI'IMOMIN ALLAH AKAN
MUTUM
Shehin Malami wato: Aliyu xan Abdurrahman
Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar
juma'a mai taken: NI'IMOMIN
ALLAH AKAN MUTUM, Wanda kuma ya tattauna a cikinta,
akan mutuwa da kasancewarta maqura ko gaya ga kowace halitta, kuma qarshen
kowani rayayye, yana mai bayyana HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI YA SHIRYA MATA na
kyawawan aiyuka, kuma mafi girma daga cikin hanyoyin shine: TABBATAR DA TAUHIDI
ga Allah ta'alah, kamar yadda ya bayyana sabuban samun kyakkyawan qarshe, da
kuma na mummunan qarshe.
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah Maxaukaki Mai
girma, Masani Mai ikon qudura, Ina yin godiya wa Ubangijina, kuma ina yin yabo
a gare shi, akan ni'imominSa na zahiri da na voye, kuma ina roqonSa dawwamar
godiya akan ni'imominSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, zuwa gare shi makoma ta ke.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonSa, kuma masoyinSa badaxi.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da
albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu Mai albishir da gargaxi, kuma
fitila mai haskakawa, da kuma iyalansa da sahabbansa waxanda suka yi jihadi da
dukiyoyinsu da kuma kayukansu, domin taimakon addinin Allah, har duniya ta haskaka da shiriya da kuma hasken (annabta da
wahayi) .
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa domin ku isa
zuwa ga yardarSa da aljannoninSa, sannan ku tsira daga fushinSa da uqubobinSa.
Bayin Allah!
Lallai Ubangijinku mabuwayi da xaukaka YANA
TUNATAR DA KU DA NI'IMOMINSA, waxanda suke da gamewa, da
kevantattu, domin ku yi godiya a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane, ku tuna ni'imomin Allah a
kanku, Shin akwai wani Mahalicci wanda ba Allah ba, da yake azurta ku daga
sama, da qasa. Babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ta yaya ake juya ku" [Faxir:
3].
Kuma Allah (تعالى) ya
ce:
"Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, da
alkawarinsa wanda ya alkawarta da ku, a lokacin da kuka ce: Mun ji, mun yi
xa'a, kuma ku bi dokokin Allah, lallai Allah Masani ne ga abinda ke cikin
qiraza" [Ma'ida: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya
ce:
"Shin ba ku gani ba ne, cewa lallai Allah ya
hore muku abinda ke cikin sammai da kuma abinda ke cikin qassai, kuma ya
kwararo akanku ni'imominsa, a bayyane da kuma a voye" [Luqman:
20 ].
Kuma
Allah mabuwayi da xaukaka ya bamu labari cewa, lallai ni'imomi gabaxayansu daga
wajenSa suke, domin mu tsayu wajen sauke haqqinSa (تبارك وتعالى) na bauta, da godiya. Sannan mu bayyanar
da kwaxayinmu zuwa gare shi na neman qarin ni'imomi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk abinda ke tattare da ku, na
ni'imomi to daga Allah ne" [Nahl:
53]. Kuma Allah (تعالى) ya
ce:
"Abinda ya same ka na kyakkyawa daga Allah
ne, Wanda kuma ya same ka mummuna to daga kanka ne" [Nisa'i:
79]. Su kyawawa su kan samu mutum da falalar Allah, da rahamarSa, ta kowace
fiska. Munana kuma su kan kasance ne da sababin mutum. Allah kuma shi yake
rubuta su kuma ya qaddara su, Kuma Ubangiji mabuwayi da xaukaka baya zaluntar
wani, ko daidai da kwayar zarra.
Kuma mutane suna sane da dayawa daga cikin
ni'imomi, saidai kuma sun jahilci mafi yawan ni'imomi. Saboda sau dayawa akwai
ni'imomin da Allah ya kwararo maka –ya kwai wannan mutum- ya kuma jiyar da kai
daxi da su, amma kai kuma baka ma ji su ba. Kuma nawa-nawa ne, sharri da musibu
Allah ya ke tunkuxe su daga barinka, alhalin kai baka sani ba, Allah (تعالى) yana cewa a dangane da kiyaye Mutum:
"Yana da Mala'iku masu canjin aiki, a ta
gaba gare shi, da bayansa suna kiyaye shi, da umurnin Allah" [Ra'ad:
11]. Kuma Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma ya hore muku abinda ke cikin sammai da
abinda ke cikin qassai, gabaxayansu daga wurinSa, lallai ne cikin haka akwai
ayoyi ga mutanen da suke yin tunani" [Jasiya: 13].
Kuma
dayawa daga gavvan jikin Mutum suna yin aikin da aka samar da su, don aikatawa, domin
amfanin jikin da tsayawar rayuwarsa, kuma suna yin aikinsu ba tare da mutum ya
yi nufi, ko yayi wani abu a cikin haka ba, Allah (تعالى) ya ce:
"Da kuma a cikin kayukanku, Shin ba za ku
gani ba" [Zariyaat: 21]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma idan za ku qidaya ni'imomin Allah ba
za ku qididdige su ba, Lallai mutum mai yawan zalunci ne mai yawan butulci"
[Ibrahim: 34]. Wanda ba zai iya qididdige ni'imomi ba, to lallai ya jahilci
mafi yawansu.
Kuma
Allah (تعالى) ya yi baiwa da
ni'imomi domin a sanya su cikin xa'a wa Allah, da yin bauta a gare shi, da
qoqarin raya qasa da kawo gyara a cikinta, Allah (تعالى) ya ce:
"Kamar haka, ya ke cike ni'imominSa akanku,
tsammaninku za ku miqa wuya" [Nahl: 81]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Allah shine ya fitar da ku daga cikin
uwayenku; alhalin ba ku san komai ba, sai ya sanya muku ji da gani da zukata,
tsammaninku za ku yi godiya" [Nahl: 78].
SHI KUMA
GODIYA KAN NI'IMOMI YA KAN KASANCE NE DA HAXUWAR WASU LAMURA; (Farko):
Da son wanda ya yi ni'imomin mabuwayi da xaukaka, saboda ni'imomin da ya yi.
(Na biyu): Da kuma qanqan da kai ga Allah (سبحانه),
akan abinda ya kwararo na ni'imomi, (Na uku) Tare da samun yaqini a cikin
zuciya cewa dukkan wata ni'ima da Allah ya yi falala da ita, ko ya kyautata ga
bawa da ita, ta kowace fiska shi bawan bashi da cancantarta ga Allah, (Na huxu)
Da yin yabo ga Ubangiji, da harshe, akan waxannan ni'imomin, (Na biyar) Da
karvar waxannan ni'imomin, da nuna halin buqata da talauci zuwa ga Allah (Na
shida) Da girmama ni'imar (Na bakwai) Da kuma amfani da ni'imomin cikin abinda
Allah (تبارك وتعالى) yake so; saboda
duk wanda yayi amfani da ni'imomin Allah cikin abinda Allah yake so, kuma ya
yarda, sannan ya sanya su suka zama masa taimako wajen tsayar da addini, a
karan kansa, kuma ya bayar da wajibai na farillar da suke kansa, ta hanyar
kyautata wa halittu, da waxannan ni'imomin = to, wanda ya aikata haka, ya yi godiya
wa Allah akan ni'imomi. Wanda kuma yayi amfani da ni'imomin Allah cikin abinda
Allah yake qi, ko ya yi hani, ko kuma ya qi bada haqqoqi na wajibai da suke kansa, a cikin
ni'imomin to lallai ya butulce wa ni'imar.
Kuma (ana so) kada ni'imomi su sanya bawa
girman kai, sai ruxu da ruxi su shige shi, Shexan kuma yayi masa waswasin cewa:
Wai yafi waninsa, saboda waxannan ni'imomin, kuma wai ba a kevance shi da
waxannan ni'imomin ba, sai saboda fifikon da yake da shi akan waxanda ba shi
ba.
Kuma
ana son mutum ya sani cewa lallai Allah yana jarrabar mutane da abubuwan
alkhairi, ko sharri, domin ya san Masu godiya da haquri. Kuma shi imani rabinsa
godiya ne, rabinsa kuma haquri, Allah (تعالى) ya
ce:
"Shin baka ga cewa lallai jirgin ruwa yana gudana
a cikin teku da ni'imar Allah, domin ya nuna muku, daga ayoyinSa, lallai cikin
haka akwai ayoyi ga kowani mai yawan haquri, mai godiya" [Luqman:
31].
A'isha (رضي الله
عنه) ta rubuta wa Mu'awuya (رضي الله
عنه) "Lallai mafi qarancin abinda ke wajaba na mai
ni'ima akan wanda yayi masa ni'imar shine kada ya sanya ni'imar da yayi masa ta
zama hanyar sava masa".
Kuma
bayan matakin GODIYA GA NI'IMOMI akwai matakin YIN GODIYA (wa Allah) KAN
MUSIBU DA SHARRACE-SHARRACE, da yin YABO WA ALLAH AKAN ABABEN QI waxanda suke
samun musulmi: Ma'abuta wannan matsayin sune farkon waxanda za a kira su
don shiga cikin aljanna, saboda kasancewarsu masu godiya (wa Allah) a cikin
kowani yanayi.
Kuma
haqiqa Allah Ubangijinmu mabuwayi da xaukkka ya umurce mu da yin godiya a gare
shi, a inda ya ce:
"Ku ambace ni sai in ambace ku, kuma ku yi
godiya a gare ni, kada ku yi min butulci" [Baqara: 152]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Saidai yana son ya tsarkake ku, kuma ya
cika ni'imarSa akanku tsammaninku za ku yi godiya"
[Ma'ida: 6]. Kuma Allah ya ce:
"Kuma ku yi godiya ga ni'imar Allah, idan
kun kasance a shi kaxai kuke yin bauta" [Nahl: 114].
Kuma Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya ce:
"Ku so Allah saboda abinda yake
ciyar da ku da shi na ni'imominSa", Attirmiziy ya ruwaito shi,
kuma ya inganta shi, daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما).
Mafi
girman godiya shine IMANI DA UBANGIJIN TALIKAI, Kuma shine godewa ni'imar
turo manzancin annabi Muhammadu (صلى الله
عليه وسلم) wanda Allah ya turo shi da manzancin don
ya zama jin qai ga mutane.
Bayan
haka kuma, Sai gode wa (Allah) akan kowace ni'ima, a karan-kanta, (manyansu da
qananansu), tare da cewa babu qarami a cikin ni'imomin Allah.
Kuma
mafi girma daga cikin BUTULCE WA NI'IMOMI shine: KAFIRCE WA QUR'ANI DA SUNNA, Kuma
godiya ga wata ni'ima ba zai yi amfani ba matuqar an kafirce wa Musulunci,
Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma duk wanda ya kafirce wa Imani lallai
aikinsa ya ruguje, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara"
[Ma'ida: 5].
Kuma
lallai haqiqa Allah ya yi alqawari ga masu yin godiya, da cewa zai dawwamar
musu da ni'imomi, kuma zai musu qari, zai sanya musu albarka, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Ubangijinku ya yi shela cewa, idan
kuka gode to lallai zan yi qari a gare ku, kuma idan kuka butulce lallai
azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].
Masu
yin godiya sune masu rabauta, da alkhairin duniya da lahira, Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma Allah zai yi sakayya wa masu godiya"
[Ali-imran: 144]. Kuma Allah (تعالى) ya
ce:
"Wanda ya nufi samun ladan duniya za mu
bashi daga gare ta, Wanda kuma ya nufi samun ladan lahira za mu bashi daga gare
ta, kuma za mu yi sakayya ga masu godiya" [Ali-imran: 145].
Kuma
masu godiya sune masu tsira daga uqubobin duniya da sharrace-sharracenta, da
kuma baqin cikin lahira, Allah (تعالى) ya
ce dangane da Mutanen annabi Lux (عليه
الصلام):
"Lallai ne mu mun tura musu iska mai tsanani
mai turvaya, in banda iyalan annabi Lux, mun tseratar da su, a lokacin sahur *
Ni'ima ce daga wurinmu, kamar haka make yin sakayya ga wanda ya yi godiya" [Qamar:
34-35].
Shi
godiya matsayi ne na annabawa da manzanni, da kuma bayin Allah muminai, Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Nuh (عليه الصلاة والسلام):
"Lallai ne shi ya kasance bawa mai yawan
godiya" [Isra'i: 3]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Lallai ne annabi Ibrahima ya kasance
jagora, mai biyayya ga Allah, miqaqqe daga karkata, kuma be kasance daga cikin
mushirkai ba * Mai godiya ne ga ni'imominsa, ya zave shi, kuma ya shiryar da
shi izuwa ga hanya madaidaiciya" [Nahl: 120-121]. Kuma Allah
(تعالى) ya ce:
"Ya Musa lallai ne ni na zave ka akan
mutane, da baka sakwanni na, da kuma maganata, sai ka riqi abinda na baka, kuma
ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
An ruwaito daga A'isha (رضي الله عنها) ta ce: "Annabi ya
kasance yana yin tsayuwar dare (salla), har qafofinsa suna kumbura, Sai ta ce:
Ya Ma'aikin Allah: Kana yin sallar qiyamullaili har qafofinka suna kumbura?
Alhalin Allah ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubanka, da abinda ya
jinkirta, Sai ya ce: Shin ba zan kasance bawa mai yawan godiya ba",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma
masu godiya sune ma'abuta samun ni'imomin Allah, saboda Allah ya kan kevance su
da abinda baya bayar da shi ga waninsu, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kamar haka, muka jarrabi sashinsu da sashi,
domin su ce: Shin waxannan ne, Allah yayi musu baiwa daga cikinmu? Shin ba
Allah ne mafi sanin masu godiya ba" [An'am: 53].
Kuma
masu godiya sune kevantattun Allah, daga bayinSa, wannan ya sanya suka zamo
'yan kaxan, Allah (تعالى) ya
ce:
"Kuma 'yan kaxan ne daga cikin bayina su ke
yawaita godiya" [Saba'i: 13].
Ya
kai Mai godiya, ka dawwama akan ibadar godiya, da tsayuwa akan addini, domin
duk wanda ya cika alkawari wa Allah to Allah zai cika masa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku cika alqawarina zan cika
alqawarinku, kuma nine kaxai za ku ji tsoro" [Baqara: 40].
Kuma
kada ka bari Shexan ya zamar da kai, ya kai mai godiya, sai ka kasa kaiwa ga
godiya ta wajibi, ko ka canza godiyar zuwa ga kafircewa ni'ima, Sai halaye su
caccanza maka; wato daga hali mai kyau izuwa ga mummuna mai sharri, Allah (تعالى) ya ce:
"Ka tambayi banu-isra'ila, sau dayawa mun
basu aya bayyananniya, kuma duk wanda ya canza ni'imar Allah bayan ta zo masa,
to lallai ne Allah Mai tsananin uquba ne" [Baqara: 211].
Saboda duk wanda ya kasance a hali na dawwamar
da godiya sai Allah ya yi masa qari. Wanda kuma ya juya daga aikata savo, zuwa
ga abinda ke yardar da Allah to sai Allah ya juyar masa da ababen da yake qinsu ko suke munana masa zuwa ga ababen
da bawa yake so. Wanda kuma ya dace da Allah cikin aiyukan kusantarSa (na xa'a),
da nisantar savo, to sai Allah ya jivinci lamuransa gabaxayansu, An ruwaito
daga Anas (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), daga Jibrilu, daga UbangijinSa mabuwayi
da xaukaka, Ya ce:
"Wanda ya walaqanta mini waliyyi, to
lallai ne yayi fito-na-fito da ni, na yaqi. Kuma ban yi taraddadin aikata wani
aikin da nine mai aikata shi ba, kamar taraddadina wajen karvar rayin bawana
mumini da yake qin mutuwa, ni kuma nake qin munana masa, tare da cewa bashi da
makawa daga mutuwa. Kuma lallai akwai daga bayina muminai wanda ke nufan wata
qofa ta bauta, amma sai in toshe masa ita, saboda kar jiji-da-kai ko ruxuwa ya
shige shi, sai hakan ya lalata shi. Kuma bawa na bai kusance ni da wata ibada
ba fiye da aikata abinda na farlanta akansa, kuma bawana ba zai gushe yana yin
nafila ba, face na so shi, Duk kuma wanda na so shi, to sai in zama jinsa da
ganinsa da hannunsa, kuma mai qarfafa a gare shi, ta yadda idan ya roqe ni sai
in amsa masa, idan kuma ya tambaye ni sai in bashi, idan kuma ya nemi nasiha
ta sai nayi masa nasiha. Kuma akwai daga cikin bayina waxanda ba abinda zai
gyara imaninsu sai wadaci, kuma da zan mayar da shi faqiri da hakan ya lalata
shi. Kuma akwai daga cikin bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa idan ba
talauci ba, da kuma zan yalwata masa sai hakan ya lalata shi. Akwai daga bayina
wanda babu abinda zai gyara imaninsa sai cutuka, da kuma zan bashi lafiya to da
hakan ya lalata shi. Kuma akwai daga bayina wanda babu abinda zai gyara
imaninsa sai lafiya, da kuma zan hukunta masa cuta, to da hakan ya lalata shi.
Lallai ne ni ina jujjuya lamarin bayina da sanina ga abinda ke cikin zukatansu,
lallai ne ni Masani ne Mai bada labari", Axxabaraniy ya ruwaito shi.
Kuma sashin laffuzan hadisin suna da abinda ke musu shaida daga cikin hadisan
Sahihul Bukhariy.
Sai
ka kasance, Ya kai bawan Allah, tare da masu godiya wa Allah, waxanda Allah ya ke
kwarara musu alkhairi kwararawa.
Ibnul
Qayyim (رحمه الله) ya ambaci wata
Magana da ake danganta ta ga Allah, cewa Allah ya ce:
"Ma'abuta ambatona sune ma'abuta zama
da ni. Su kuma ma'abuta gode mini sune ma'abuta samun qarina, Su kuma ma'abuta
xa'a a gare ni sune ma'abuta samun karamata, Su kuma ma'abuta sava mini su kuma
ba zan sanya su xebe tsammani daga rahamata ba; idan suka tuba to nine
masoyinsu, idan kuma basu tuba ba to nine likitansu; zan jarrabe su da musibobi
domin in tsarkake su daga aibobi ".
Kuma
lallai ne Allah ya umurce ka da ka kasance tare da waxannan bayin masu rabauta,
Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ga Allah shi kaxai za ka yi bauta,
kuma ka kasance daga masu godiya" [Zumar: 66].
Kuma
haqiqa Allah (تعالى) ya
ambaci wasu ni'imomi kevantattu a cikin littafinSa saboda amfaninsu da kuma
albarkarsu, ga al'umma, har zuwa tashin qiyama.
Kuma
yana daga cikin wasiyyoyin Annabinmu (صلى الله
عليه وسلم) masu amfani, faxinSa:
"Ya kai Mu'az! Lallai ne ni ina
sonka, sai ka riqa faxa bayan kowace sallah: (اللهم أعني على ذكرك وشكر وحسن عبادتك) Ma'ana: Ya Allah! Ka
taimake ni akan ambatonka, da yin godiya a gare ka, da kyautata bauta a gare ka",
Abu-Dawud ya ruwaito shi da Annasa'iy.
Da
yin godiya da yin yabo (wato: Alhamdu, da Shukru) ma'anan sashinsu yana shigar
wa sashi, tare da cewa kowannensu yana kevanta da wasu ma'anoni masu zurfi.
Kuma
lallai Allah –a kowani lokaci- yana da ni'imomi kevantattu, da ni'imomi gamammu
(ga xaukacin bayi). Waxanda wajibi ne a riqa godiya wa Allah akansu, ta hanyar
dawwama kan kulawa da su, da kiyaye su, da nisantar sabbuban gushewansu. Kuma
lallai ba a kiyaye ni'imomi face da yin xa'a wa Allah, da kuma barin aikata
ababen kyama, da kuma bayar da haqqin kowace ni'ima.
Kuma
yana daga cikin ni'imomi: Dukiya, Haqqin kuma da ya ke
cikin dukiya shine bayar da zakka, da kuma ciyarwa na wajibi, da yawaita
ciyarwa na mustahabbi.
Kuma
ita zakka tana kawo qari a cikin dukiya, kuma da zakka albarka tana sauka cikin
dukiya, kuma zakka tana kare dukiya daga lalacewa ko halaka, kuma zakka tana
tunkuxe munana wa ma'abucinta, kuma tana xaga darajarsa a duniya da lahira.
Kuma babu wani alheri ga dukiyar da ba a tsarkake ta da fitar da zakka ko
ciyarwa na wajibi ko mustahabbi ba, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Ka karvi sadakar zakka daga dukiyarSu, kana
mai tsarkake su da ita" [Tauba: 103]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma duk abinda kuka ciyar na wani abu, to
shine zai bada mayewarsa, kuma shine mafi alherin masu azurtawa"
[Saba'i: 39].
Ya zo cikin hadisi:
"Babu wani ma'abucin taskar da baya
bada zakkarta face an misalta dukiyar a ranar qiyama da maciji mai kora yana
cizon kumatunsa, yana cewa: Nine taskarka, Nine dukiyarka",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kuma
zakka haqqi ne na faqiri. Kuma da mawadata za su bayar da zakka, da babu wani
faqiri da zai saura.
Kuma
godiya ga ni'imomi, amfanin hakan ya kan koma ga mai godiyan. Ita kuma gafala
daga godiya cutarwarta za ta kasance ga wanda ya gafala, Allah (تعالى) ya ce:
"Wanda ya yi godiya kawai yana yi godiyan ne
wa kansa, Wanda kuma ya butulce to lallai ne Allah Mawadaci ne Abun godiya"
[Luqman: 12].
Yana
daga TASKAR SUNNA wajen godiya ga ni'imomi: Faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda a lokacin da wayi gari
yace: (اللهم ما أصبح بي من نعمة
أو بأحد من خلقك فمنك وحدك لا شريك لك فلك الحمد ولك الشكر)
Ma'ana: Ya Allah! Duk abinda ya wayi gari tare da ni na ni'ima, ko ga wani daga
cikin halittunka, to daga wajenka ne kai xaya; baka da abokin tarayya, godiya
taka ce,kuma yabo naka ne. To lallai ya aiwatar da godiyar darensa. Wanda
kuma yace: (اللهم ما أمسى بي من نعمة
أو بأحد من خلقك فمنك وحدك لا شريك لك فلك الحمد ولك الشكر)
Ma'ana: Ya Allah! Duk abinda ya yi yammaci tare da ni na ni'ima, ko ga wani
daga cikin halittunka, to daga wajenka ne kai xaya; baka da abokin tarayya,
godiya taka ce,kuma yabo naka ne. To lallai ya aiwatar da godiyar yininsa",
Hadisi ne hasan (mai kyau), Abu-dawud ya ruwaito shi da Ibnu-Hibbana, kuma ya
ingata shi, daga hadisi Abdullahi xan Gannam Albayadhiy.
Da
yin godiya da yin yabo (wato: Alhamdu, da Shukru) ma'anan sashinsu yana shigar
wa sashi, tare da cewa kowannensu yana kevanta da wasu ma'anoni masu zurfi.
Allah (تعالى) ya
ce:
"Kuma ka yi godiya a gare ni, da iyayenka
guda biyu, ya zuwa gare ni makoma ta ke" [Luqman: 14].
Allah
yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku
da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu
da shiriyar shugaban Manzanni, da maganganunsa miqaqqu.
Ina faxar Magana ta wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa;
saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin qai.
HUXUBA TA
BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah wanda ya datar da wanda ya so zuwa ga alkhairori, kuma ya
tavar da wanda ya so da adalcinSa da hikimarSa, sai ya bi sha'awowi, Ina yabon
Ubangijina kuma ina yin godiya a gare shi, ina tuba zuwa gare shi, ina kuma
neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Ubangijin qasa da sammai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, matattarar girma da karamomi.
Ya
Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa ma'abuta yin
xa'a.
Bayan
haka!
Ku
kiyaye dokokin Allah da tsayuwa wajen gode masa, kuma ku ambace shi yadda ya
dace a ambace shi.
Bayin Allah!
Allah (تعالى) yana cewa: "Idan kuka kafirce
to lallai Allah Mawadaci ne ga barinku, baya yarda da kafirci wa bayinsa. Idan
kuma kuka yi godiya yana yarje muku, kuma rai bata xaukar zunubin wata rai,
Sa'annan izuwa ga Ubangijinku makomarku ta ke, sai ya baku labarin abinda kuka
kasance kuke aikatawa, lallai shi Masani ne da abinda ke cikin qiraza"
[Zumar: 7].
Kuma
ku sani lallai bawa duk yadda ya kai ga biyayya wa UbangijinSa, ya ke kuma
kusantarSa da dangogin ibadodi to ba zai tava iya tsayuwa da godiyar
Ubangijinsa, a cikakkiyar fiska ba, Saidai kuma yana isar wa bawa ya tsayu
wajen aikata farillai, ya kuma hanu daga laifukan da aka hana, sannan ya sani
cewa ba don rahamar Allah ba da ya kasance cikin masu hasara, Sai kuma ya
lazimci neman gafara akan gajartawarsa, tare da yawaita roqon Ubangijinsa cewa
ya taimake shi ya datar da shi. Hadisi ya zo daga Ibnu-Abbas (رضي الله عنهما) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana addu'a, cewa:
"Ya Ubangijina! Ka sanya ni na
zama mai yawan godiya a gare ka, mai yawan ambatonka, mai yawan jin tsoronka,
mai yawan yi maka biyayya, mai yawan qanqan da kai a gare ka, mai yin kuka da
mayar da al'amari zuwa gare ka.
Ya
Ubangijina! Ka karvi tubata, kuma ka wanke zunubaina, ka amsa addu'a ta, ka
tabbatar da hujjojina, kuma ka shiryar da zuciyata, ka daidaita harshena, ka
zare dauxar zuciyata", Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma ya ce:
hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan sahih).
Bayin
Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga
wannan annabin, ya ku waxanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da
sallamar amintarwa"
[Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda ya yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai salati
a gare shi guda goma saboda shi".
Sai ku yi
salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi
Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi
Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi
Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi
Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai
gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar
da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya,
Ya Allah! Ka yarda da tabi'ai da waxanda
suka bi su da kyautatawa (bi da bi) har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su,
da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai (sau uku), ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai, Ya Ubangijin
talikai.
Ya
Allah ! ka qasqantar da bidi'a da 'yan bidi'a har zuwa tashin
kiyama.???????????????????????????????????????????
Ya ku bayin Allah!
"Lallai Allah yana yin umurni
da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha
da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.