GABATAR DA TARJAMAR MA'ANONIN ALQUR'ANI MAI GIRMA
SHIMFIXA
Alqur'ani
mai girma maganar Allah ne maxaukaki da ya sauqar
da shi (alqur'ani), da harrufansa da
ma'anoninsa, zuwa ga manzonsa annabi Muhammadu (s.a.w) don ya zama rahama ga
talikai, yana bushara, yana gargaxi, yana kuma qira
zuwa ga Allah, da izininSa, kuma fitila ne mai haskakawa.
A
NAN GA BAYANI TAQAITACCE, AKAN ALQUR'ANI
MAI DARAJA, DA KUMA SAQON DA YA QUNSA:
GAMAMMEN BAYANI KAN ALQUR'ANI
MAI GIRMA
NA FARKO: BAYANI KAN ALQUR'ANI MAI GIRMA, DA AMBATO
SUNAYENSA, DA SIFFOFINSA:
Alqur'ani
mai girma zance ne na Allah maxaukaki da ya saukar da
shi ga manzonsa annabi Muhammadu (s.a.w), wanda kuma aka yi masa wahayinsa da
lafazinsa da ma'anoninsa, sannan aka rubuce shi a jikin takardu, riwayarsa kuma
aka karvo ta ta
hanyoyin mutane dayawa (mutawaatir), ana kuma yin bauta (a samu lada) da yin
karatunsa.
Kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka
shine da kansa ya sanya ma wahayin da ya saukar da shi ga manzonsa annabi
Muhammadu (s.a.w) suna: Alqur'ani (ma'ana:
littafi abun karantawa); Allah ta'alah yana cewa:
(إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ
تَنْزِيلاً) [الإنسان:
23].
Ma'ana:
"Lallai mune muka sassauqar da alqur'ani
akanka sas-sauqarwa" [Insaan: 23]. Kuma ya
sanya masa wannan sunan ne (alqur'ani) saboda yana
daga sha'anin wannan littafin ayi ta karanta shi (qira'a)
da tilawa, kada a qaurace masa.
Kuma
Allah ya sanya masa suna; al-kitaab (ma'ana: Alqur'ani abun rubutawa);
Allah ta'alah yana cewa:
(إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ)
[النساء: 105].
Ma'ana:
"Lallai mune muka sauqar maka da wannan littafin da gaskiya" [Nisa'i: 105].
Saboda yana daga cikin sha'anin alqur'ani
a rubuta shi, kada ayi ko-oho da shi (ko manta shi).
Kuma lallai Allah ta'alah ya
siffanta wannan alqur'ani da siffofi dayawa; Daga
cikinsu; ya siffanta shi da; siffar littafi
mai rarrabewa, da tunatarwa, shiriya, haske, waraka, littafi mai hikima, wa'azi,
da wassun waxannan daga cikin siffofinsa da
suke nuni kan: Girman alqur'ani, da kasantuwar saqon
da ke xauke da shi cikakke.
Ita kuma kalmar "mus-hafi" an ciro ta ne daga
takardun da aka rubuta alqur'ani mai girma akansu. Kuma
wannan kalma (ta, mus-hafi) sahabban annabi ne (s.a.w) suka qira
alqur'ani da ita, don tayi nuni kan littafin da aka rubuta alqur'ani
mai girma a takardunsa.
Kuma lallai alqur'ani
mai girma wahayi ne daga Allah ta'alah, wanda mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauqar
da shi a zuciyar annabi Muhammadu (s.a.w), Allah maxaukaki
yana cewa:
(وَإِنَّهُ
لَتَنْزِيلُ رَبِّ الْعالَمِينَ، نَزَلَ بِهِ الرُّوحُ الْأَمِينُ، عَلى قَلْبِكَ
لِتَكُونَ مِنَ الْمُنْذِرِينَ، بِلِسانٍ عَرَبِيٍّ مُبِينٍ) [الشعراء: 192-195].
Ma'ana:
"Kuma lallai shi, saukakke ne daga Ubangijin talikai, wanda mala'ika
-Jibrilu- amintacce ya sauqar da shi, a zuciyarka domin ka kasance daga cikin masu gargaxi.
Da harshen larabci mabayyani" [Shu'ara'i: 192-195].
Kuma
lallai annabi Muhammadu (s.a.w) ba shi ne farkon fari a wannan lamarin ba;
saboda dukkan 'yan'uwansa manzanni (a.s) mala'ika Jibrilu (a.s) ya kasance yana
sauqar
musu da wahayi daga Allah ta'alah. Kuma lallai Allah (s.w.t) ya kasance ya kan zavi
wanda ya nufa don ya bashi wannan amanar mai girma, Allah yana cewa:
(اللَّهُ يَصْطَفِي مِنَ الْمَلائِكَةِ رُسُلاً
وَمِنَ النَّاسِ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ) [الحج: 75].
Ma'ana:
"Lallai Allah yana zaven manzanni daga cikin mala'iku, haka kuma daga cikin mutane.
Lallai Allah mai ji ne mai gani" [Hajji: 75].
Kuma
Allah shine ya san wanda zai dace da matsayin manzanci, daga wanda ba zai dace
da shi ba, saboda dukkan halittu shi ya samar da su, Allah yana cewa:
(وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشاءُ وَيَخْتارُ) [القصص: 68].
Ma'ana:
"Kuma Ubangijinka yana halittar abinda ya nufa, ya kuma yi zavi"
[Qasas:
68].
NA BIYU: SAUQAR ALQUR'ANI
MAI GIRMA:
Aqur'ani
ya fara sauka ga manzon Allah (s.a.w) a ranar litinin, goma sha bakwai ga watan
ramadhan (17/ Ramadhan) a shekarar miladiyyah ta 610, a cikin kogon Hirah,
wanda shi kuma xaya ne daga cikin duwatsun garin Makkah mai daraja, a lokacin da
mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauqar masa da waxannan
ayoyin:
(اقْرَأْ
بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ، خَلَقَ الْإِنْسانَ مِنْ عَلَقٍ، اقْرَأْ
وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ، الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ، عَلَّمَ الْإِنْسانَ مَا
لَمْ يَعْلَمْ) [القلم: 1-5].
Ma'ana:
"Kayi karatu da sunan Ubangijinka da yayi halitta, Ya halicci mutum daga
jini, Ka yi karatu da ubangijinka mai karamci, wanda ya sanar da alqalami,
ya sanar da Mutum abinda bai sani ba" [Qalam:
1-5].
Kuma waxannan
ayoyin sune farkon abinda suka fara sauka ga manzon Allah (s.a.w).
Sai
Annabi (s.a.w) ya koma wajen matarsa (iyalansa) da waxannan
ayoyin zuciyarsa tana karkaxawa saboda kwar-jini, da kuma
yadda ya tsorace wa kansa, ya kuma bada dukkan qissar
ga: Uwar muminai Khadija 'yar Khuwailid (Allah ya qara
yarda a gare ta) yace mata:
«لَقَدْ خَشِيتُ عَلَى نَفْسِي، فقَالَتْ لَهُ: كَلَّا أَبْشِرْ،
فَوَ اللهِ، لَا يُخْزِيكَ اللهُ أَبَدًا، إِنَّكَ لَتَصِلُ الرَّحِمَ، وَتَصْدُقُ
الْحَدِيثَ، وَتَحْمِلُ الْكَلَّ، وَتَقْرِي الضَّيْفَ، وَتُعِينُ عَلَى نَوَائِبِ
الْحَقِّ، وَأخذَتْه إلى وَرَقَةَ بْن نَوْفَلِ وكان من ذوي الرأي والحكمة
فقالت له خديجة: أَيْ عَمِّ، اسْمَعْ مِن ابْنِ أَخِيكَ، فلما أخبره رسول الله r خبر ما رآه، قَالَ
لَهُ وَرَقَةُ بن نوفل: هَذَا النَّامُوسُ الَّذِي أُنْزِلَ عَلَى مُوسَى، يَا
لَيْتَنِي فِيهَا جَذَعًا، يَا لَيْتَنِي أَكُونُ حَيًّا حِينَ يُخْرِجُكَ
قَوْمُكَ، قَالَ رَسُولُ اللهِ r: أَوَ
مُخْرِجِيَّ هُمْ؟ قَالَ وَرَقَةُ: نَعَمْ لَمْ يَأْتِ رَجُلٌ قَطُّ بِمَا جِئْتَ
بِهِ إِلَّا عُودِيَ، وَإِنْ يُدْرِكْنِي يَوْمُكَ أَنْصُرْكَ نَصْرًا مُؤَزَّرًا». وتوفي ورقة بعد هذه المقابلة بوقت قصير.
Ma'ana:
"Lallai ni na jiye wa kaina tsoro, Sai tace masa: A'a! kwantar da hankalinka,
ina rantsuwa da Allah! Har abada Allah ba zai tozarta ka ba; saboda yadda ka ke
sada zumunci, da yin gaskiya cikin zance, kuma kana xaukar
nauyin gajiyayye, kana karrama baqo, sannan kana
taimako kan abubuwan da suke faruwa da mutane na gaskiya. Sannan ta tafi da shi
zuwa ga: Waraqah xan Naufal, wanda kuma xaya ne daga
cikin mutane masu ilimi da hikima, Sai Khadija tace masa: Ya kai baffana! Ka
saurari xan xan'uwanka! A yayin da
Manzon Allah (s.a.w) ya bashi labarin duk abinda ya ga ni, Sai Waraqah
xan
Naufal yace: Wannan ai shine mala'ikan wahayi([1]) da ke zuwa ga: Annabi Musa. Da dai ace
ina cikin qarfina! Da dai ace ina da raina; a lokacin da mutanenka za su fitar
da kai? Sai Manzon Allah (s.a.w) yace: Shin fitar da ni za su yi Su xin?",
Sai Waraqah
yace masa: E, ai babu mutum xaya da ya zo da irin
abinda ka zo da shi face anyi adawa ko gaba da shi".
Sai
Waraqah
bada jimawa ba; bayan wannan ganawar ya rasu.
Kuma
alqur'ani
mai girma ba dukkansa ne ko gabaxayansa ya sauka ga
Manzon Allah (s.a.w) a lokaci xaya ba, savanin
yadda littatafan da sauran annabawa (a.s) da suka rigayi annabinmu suka sauka,
A'a! Shi alqur'ani ya yi ta sauka ne
guntu-guntu a cikin tsawon shekaru ashirin da uku (23), Kuma "sura"
cikakkiya tana sauka, ko kuma "ayoyi" daga cikin sura.
Hikimar
sauqar
da alqur'ani
guntu-guntu (da kaxan da kaxan) ([2]) kuma Itace:
Tabbatar da zuciyar annabi Muhammadu (s.a.w), da qara qarfafarsa,
a duk lokacin da mala'ika ya sake sauqar
masa da sabon wahayi, don ya kasance yafi samun qarin qarfin
jiki da na hali a lokacin da yake fiskantar quren da mushirkai da qaryatawarsu
ga abinda aka saukar masa, tun a farkon turo shi a matsayin manzo daga Allah,
Kuma Allah ta'alah yana cewa:
(وَقالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلا نُزِّلَ عَلَيْهِ
الْقُرْآنُ جُمْلَةً واحِدَةً كَذلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤادَكَ وَرَتَّلْناهُ
تَرْتِيلاً) [الفرقان: 32].
Ma'ana:
"Kafirai suka ce: Me ya hana a sauqar
masa da alqur'ani a dunqule?
Mun yi haka ne, domin mu tabbatar da zuciyarka da shi, kuma muka karanta maka
shi karantawa" [Furqan: 32].
Haka kuma cikin sassauqar
masa da alqur'ani guntu-guntu (ba a dunqule
ba) akwai hikima mai girma da take da alaqa
da tarbiyya, wacce kuma ita ce: Bin muminai a sannu-sannu wajen koya musu
ilimin alqur'ani, da yadda za su yi aiki da hukunce-hukuncen
addinin Allah, Sai hakan ya zama ya fi sauqi
a gare su wajen sanin addini da fahimtarsa, da kuma fita daga duffan abubuwan
da suka kasance a cikinsu na: Jahilci da kafirci da shirka, zuwa ga: Imani da
tauhidi da ilimi.
NA UKU: RUBUTA ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Yana
daga cikin muhimman hanyoyin kiyaye zantuka da bayanai: a rubuta su, kuma duk
maganar da ba a rubuta ta ba to lallai za a iya mantata, Wannan ya sanya tun da
alqur'ani
mai karamci ya zama ya sauka ne don zama shiriya ga dukkan duniya (na jiya da
na yau) har zuwa tashin qiyama: To sai ya zama babu makawa sai an rubuta shi.
Kuma
lallai Annabi (s.a.w) ya himmatu kana ya bada
kula ta musamman dangane da rubuta alqur'ani
mai girma, a lokacin da ya umurci sashin sahabbansa da suka iya rubutu cewa su riqa rubuta
alqur'ani mai girma, ya kuma xauke
su a matsayin marubutan wahayi. Wanda kuma yafi shahara da wannan aikin a
cikinsu shine: sahabinsa mai suna Zaid xan Sabit
Al-ansaariy([3]) (r.a).
Kuma
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance duk lokacin da wahayi ya sauka a gare shi sai
ya haddace shi, Sannan sai ya yi imla'insa ga xaya
daga cikin marubuta wahayinsa don ya rubuce shi, Sai yace:
"ضَعُوا هَذِهِ الآيَاتِ فِي
السُّورَةِ الَّتِي يُذْكَرُ فِيهَا كَذَا وَكَذَا([4])" فيسمي لهم السورة.
Ma'ana:
"Ku sanya waxannan ayoyin a cikin surar da ake
ambaton kaza da kaza a cikinta", Sai ya faxa
musu sunan "surar". Sannan sai Annabi (s.a.w) ya umurce su da rubuta waxannan
ayoyin a cikinta. Kuma lallai ya kasance ya kan umurci dukkan sahabbansa da
cewa su riqa koyan dukkan abinda ya sauka na alqur'ani
mai daraja, tare da haddace shi. Sai aka rubuce dukkan alqur'ani
gabaxayansa a zamaninsa (s.a.w) a jikin takardu (رقاع) ([5]).
Kuma Mala'ika Jibrilu (a.s) ya
kasance yana bitar alqur'ani dukkansa tare da Annabi
(s.a.w) a kowace shekara, sau xaya, Amma a shekarar
da Annabi (s.a.w) ya rasu sai suka yi bitar alqur'ani
har sau biyu, tare da jeranta ayoyinsa da surorinsa, kamar yadda yake a cikin
"mus-hafi" da ke hannun musulmai a yau, don qara
tabbatar da maganar da Allah ta'alah ya yi:
(إِنَّ عَلَيْنا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ، فَإِذا
قَرَأْناهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ) [القيامة: 17-18].
Ma'ana:
"Kuma lallai tattara shi da karatunsa akanmu ya ke. Kuma idan muka karanta
shi to sai ka bi karatunsa" [Qiyamah:
17-18]. Da faxinsa maxaukaki:
(سَنُقْرِئُكَ فَلا تَنْسى) [الأعلى: 6].
Ma'ana:
"Da sannu zamu karantar da kai shi, Ba za ka manta ba" [A'alah: 6].
NA HUXU: TATTARA ALQUR'ANI MAI GIRMA A CIKIN TAKARDU:
Bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w)
sai khalifansa shiryayye Abubakar Siddiq
(r.a) ya yi umurnin a tattara alqur'ani a cikin takardu
da aka tsattsara aka tara su, saboda kada a rasa wani abu na alqur'ani
sakamakon rasuwar mahaddatansa, ko kuma lalacewar tsofin takardun da aka rubuta
alqur'anin
a jikinsu (رقاع) Sai marubucin wahayin Annabi mai suna
Zaid xan Sabit (r.a) ya xau alhakin
wannan aiki mai girma. Bayan kuma ya gama tsaf, ya yi kuma bitar aikin; don
samun tabbacin daidaitonSa shi da abinda ke jikin tsofin takardu (رقاع)
da wanda mutane suka haddace a qirazansu, Sai aka ajiye waxannan
takardun a gidan Abubakar Siddiq (r.a), har zuwa
lokacin da Allah ya masa wafati. Sannan aka ci-gaba da kiyaye su a gidan
khalifah na biyu: Umar xan Al-khaxxab (r.a). Shima
bayan ya yi wafati sai aka ci-gaba da kiyaye su a xakin
matar annabi (s.a.w); Uwar muminai Hafsah yar Umar([6]) (r.a).
Ana nan ana-nan, a lokacin da
musulunci ya yaxu, Sai musulmai suka buqaci
"mus-hafai" na alqur'ani da za su riqa
yin karatu a cikinsu, Sai wassu sahabbai suka bada shawara ga: Shiryayyen
khalifah Usman xan Affan (r.a) da cewa wajibi ne a tattara hankalin mutane akan
"mus-hafi" guda xaya da zai zama
jagora; wanda musulmai za su yi koyi da shi a cikin karatunsu. Sai Usman ya
umurci wassu jama'a daga cikin mahaddatan alqur'ani
mai girma, waxanda kuma suka iya rubuta shi da cewa su xau
alhakin wannan aikin, shugabansu kuma shine Zaid xan
Sabit (r.a), suna masu dogara akan "takardun" da aka rubuta alqur'ani
a cikinsu a zamanin Abubakar Siddiq (r.a) sai suka
tattara waxannan takardun cikin
"mus-hafi" guda xaya. Sannan suka
kwafi wassu masu yawa daga gare shi, Sai aka aika guda xaya
zuwa ga kowanne birni daga cikin biranan musulmai masu girma, sannan aka umurci
musulmai da su kwafi "mus-hafansu" daga gare su.
Lallai kuma dukkan
"mus-hafai" da aka sani a duniyar jiya da ta yau, sawa'un waxanda
su ke rubuce ne da rubutu irin na hannu (مخطوطة), ko wanda aka buga da injinan buga littatafai (مطبوعة), tushensu daga waxannan
"mus-hafai" da aka yi aikin kwafar su, sannan aka aika su zuwa waxannan
biranen ne, Basu banbanta da su ko ta fiskar abinda suka qunsa,
ko kuma ta fiskar jeranta surori ko ayoyi ba.
Kuma har zuwa wannan zamanin namu,
musulmai suna himmatuwa da lamarin buga "mus-hafai" (alqur'ani
mai girma), tare da amfana da sababbin abubuwan da zamani ya kawo na hanyoyin
buga littatafai da adana bayanai, domin su taimaka wajen samun mafi darajar
kyautata rubutu ko wasalce shi, wajen yin rubutun alqur'ani
da kuma "rasamarsa" da irin rasamar da aka rubuta shi da shi a
zamanin shiryayyen khalifah Usman xan Affan
(r.a), wanda kuma aka san shi da laqabin:
"AR-RASAMU AL-USMANIY".
Kuma samuwar ma'aikatar buga
littafin alqur'ani mai girma ta sarki Fahad, a
garin Madinar Annabi ba komai ba ne sai xaya daga
cikin dalilai na fili da su ke nuna yadda aka bada muhimmanci ga hidima wa alqur'ani
mai girma, da yadda shugabannin masarautar larabawa ta Saudiyya ke damuwa da
littafin Allah wajen yi masa hidima, da sauqaqe
samunsa ga dukkan musulmai a ko-ina su ke, ta yadda za su same shi a cikin mafi
kyan yanayi na tsarin bugu, da yin bango mai qarfi
wa takardu da zai kiyaye shi, tare da kula da rubutunsa da kyautata shi.
NA BIYAR: JERANTA "MUS-HAFI" DA KARKASA
SHI (JUZU'I-JUZU'I):
Alqur'ani
mai girma yana farawa ne da "suratu al-fatihat", yana kuma qarewa
da "suratu qul a'uzu bi rabbi an-naas". Gabaxaya
kuma ya qunshi "surori" guda xari da goma
sha huxu
(114).
Kuma
jerantawa tsakanin "surori" abu ne da aka samo shi daga Annabi
(s.a.w) –TAUQIFIY NE-. Kuma bai dogara ga
jerin "surori" a lokutan sauqarsu
ba; saboda "surar" da ta fara sauqa
ita ce: "suratu al-alaq", Jerinta kuma a cikin alqur'ani
"mus-hafi" shi ne: 96. Kuma sahabbai suna sanin yadda jeranta ayoyi a
cikin "sura" xaya, da jeranta "sura" bayan "sura" suke ne
daga yadda Annabi (s.a.w) ya ke karanta alqur'ani
mai girma([7]).
Kuma
a yau ana karkasa "mus-hafi" har zuwa kashi talatin "juzu'i 30),
kowane juzu'i kuma ana kasa shi ne zuwa "izu biyu", kowani izu kuma
ya qunshi
"rubu'ai guda huxu". Shi kuma wannan karkasuwar a mafi rinjayensa
"ijtihadi" ne na maluma, domin suga sun sauqaqe
karatun alqur'ani mai karamci ga musulmai.
NA SHIDA: KOYON KARATUN ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Lallai
musulmai sun himmatu sosai wajen koyan karatun alqur'ani
da haddace shi, da tilawarsa, kamar yadda aka sauqar
da shi ga manzon Allah (s.a.w).
Kuma
mahaddata alqur'ani daga cikin sahabbai sun
tsayu wajen su ga sun karantar da shi ga xalibansu
tabi'ai, har suka yi kyakkyawan kiyayewa ga lafazin alqur'ani,
suna kuma tsayar da su a wajen kowace aya (suna tambayarsu), har su ka yi kyakkyawan
fahimta ga ma'anar ayoyi, suka kuma koyi ilimi da yadda ake aiki da shi gabaxaya.
Daga
nan sai mahaddata daga cikin tabi'ai su kuma suka assasa makarantu mabanbanta
na koya wa mutane karatun alqur'ani, suna yin riqo
da abinda suka koye shi daga malumansu sahabbai; na fiskoki mabanbanta na
tilawar alqur'ani, da kiyaye laffuzansa, da qididdige
harrufansa, da kalmominsa, da jeranta surorinsa da ayoyinsa, da tajwidinsa, da
kyautata salon karanta shi, da sanin saqon
cikinsa, ana kuma haddace shi, ana tilawarsa.
Xalibi
na koyan dukkan haka daga shehinsa (malaminsa) daga cikin makaranta kuma hafizai,
baki-da-baki, da yaren larabci mai fasaha, xanye
shatak kamar yadda aka saukar da shi ga Manzonmu (s.a.w) har zuwa wannan ranar.
Kuma
lallai alqur'ani mai girma ana karanta shi da
"qiraa'oi" masu yawa, waxanda
kuma siffofi ne da salo-salo na karanta kalmomin alqur'ani,
da harrufansa, da hanyoyin furta su, wanda tabi'ai suka koya daga makaranta
kuma mahaddata na daga maluman sahabbai, waxanda
su kuma suka koya tare da samun izinin gwanancewa a cikin karatunsa da karantar
da shi (ijazah) daga Annabi (s.a.w)
Kuma
mafi shahara daga cikin waxannan "qiraa'oi a zamaninmu
wannan shi ne: qiraa'ar Asim daga riwayar xalibinsa
Hafs xan Sulaiman, da kuma qiraa'ar
Nafi'i wacce xalibinsa Usman xan
Sa'id da ake masa laqabi da Warsh ya rawaito.
Daga
cikinsu kuma akwai: Riwayar Duuriy daga Abiy-amrin Albasariy, da kuma riwayar Qaaluun
daga Nafi'i.
NA BAKWAI: YIN FASSARAR ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Lallai
kuma magana bata cika ko cimma gayar da aka yi ta sai idan an gane abinda ta ke
nunawa da ma'ananta.
Kuma
lallai Allah ta'alah ya kwaxaitar da makarancin alqur'ani
mai girma da damuwa da lamarin fahimtar ma'anoninsa, a cikin faxinsa:
(كِتابٌ أَنْزَلْناهُ إِلَيْكَ مُبارَكٌ
لِيَدَّبَّرُوا آياتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُولُوا الْأَلْبابِ) [ص: 29].
Ma'ana:
"Littafi ne da muka sauqar da shi zuwa gare ka, mai albarka, domin su yi tinani cikin
ayoyinsa, kuma domin ma'abota hankula su wa'aztu" [Saad: 29].
Abinda
ake nufi da "tadabbur" a cikin ayar shi ne: Qoqarin
fahimtarsa.
Manzon
Allah (s.a.w) ya kasance yana bayyana wa sahabbai abinda ya shige musu duhu
daga ma'anonin alqur'ani mai girma([9]), Sai dai kasancewar sahabbai gwanaye
cikin harshen larabci a wancan zamanin, da yadda alqur'anin
ya sauka da harshensu Sai ya wadatar da su ga barin: Yawaita tambayoyi kan
ma'anonin ayoyin alqur'ani mai girma.
Kamar
yadda buqatun mutane kuma suka yi ta qaruwa
kan sanin tafsirin alqur'ani: saboda yau da gobe.
Kuma
lallai abinda aka rawaito daga Manzon Allah (s.a.w) na tafsirin wassu ayoyi,
haka waxanda aka rawaito na tafsirin sahabbai da xalibansu
tabi'ai ga wassu ayoyin shine: Tushen da aka gina ilimin fassara ayoyin alqur'ani
akansa, Wanda kuma aka sanya masa suna: "Fassara alqur'ani
da abinda aka rawaito na hadisai ko aasaar" (tafsir bil ma'asur); Wannan
kuma shine salo ko hanyar da ta fi muhimmanci ga mai neman fahimtar alqur'ani
mai girma.
Kuma
lallai wannan dukkansa yana bayyana mana yadda sahabbai da tabi'ai suka fahimci
alqur'ani
mai girma; wato saboda gwanancewarsu a harshen larabci, da kuma saboda zuwan
rayuwarsu tare da abubuwan da suka auku, ko yanayi da lokaci da suka hukunta sauqar
ayoyin alqur'ani mai girma.
(1)
NAU'UKAN TAFSIRI:
Fiskokin da maluman tafsirin alqur'ani
suka rubuta littatafan tafsiri a kansu sun banbanta gwargwadon abubuwa na ilimi
mabanbanta da maluman ke basu muhimmanci, Sai littatafa na tafsiri suka
bayyana; wanda wassu suke bada qarfi ta vangaren
bayanin qarfi da fasahar larabcin alqur'ani,
Wassu littatafan kuma sun damu da bayanin hukunce-hukuncen fiqihu,
Wassu kuma suna bada muhimmanci kan vangarorin
tarihi, ko vangaren hankali, ko halayya da xabi'u,
da makamantansu. Kuma maluma sun karkasa littatafan tafsirai da suke hannun
al'umma, gwargwadon wannan zuwa kashi biyu:
NA FARKO: Yin tafsirin
aya da "riwayoyi, ko ma'asuur", Ma'ana: Fassara ayar alqur'ani
da abubuwan da aka rawaito su daga Annabi (s.a.w), ko daga sahabbai, ko daga
tabi'ai.
NA BIYU: Fassara aya da
"ijtihaadi" ko fahimta (ra'ayi, ba da hadisai ba); Wanda ya ginu akan
ginshiqai
na ilimi ingantattu.
(2)
HANYAR TAFSIRI MAFI KYAU, DA KUMA QA'IDODINSA:
Fassara aya da abinda aka rawaito na hadisi ko maganganun
sahabbai ko tabi'ai shine abin fifitawa a lokacin fassarar ayar alqur'ani
mai girma; kasancewar hakan shine abinda aka rawaito daga Annabi (s.a.w) ko
daga Sahabbansa, da kuma xalibansu daga cikin tabi'ai. Alhalin
kuma su suka fi dukkan mutane ilimi.
Sai dai kuma idan fahimtar wassu ayoyin alqur'ani
ya nemi qarin bayanin da ba a same shi ba a cikin "riwaya" to a
nan wajibi ne Malamin tafsiri ya kula da qa'idodin
da suke tafe:
1-
Bada kula
ga abinda ya tabbata ta hanyar tafsiri da "riwaya" na bayanin waxannan
ayoyin, da rashin kawo abinda zai warware shi ko qaryata
shi.
2-
Dole
tafsirin da zai yi ta hanyar fahimtarsa (ijtihadi) ya dace da gamamme ko dunqulallen
ma'anar da alqur'ani mai girma ya zo da ita, kuma
sunnar Annabi ta bayyanar da ita, saboda baya halatta ga mai tafsiri ya fitar
wa mutane wani tafsirin da ke cin karo da ma'anonin alqur'ani
da hadisai. Saboda alqur'ani mai girma sashinsa yana
fassara sashi ne, kuma babu cin karo a tsakanin ayoyinsa. Itama sunnar Annabi
(s.a.w) ta zo ne don yin bayanin abinda aka dunqula
bayaninsa a cikin alqur'ani mai girma, tana kuma fassara
shi.
3-
Dole ya
san ilimi da qa'idodin harshen larabci, wajen sanin
ma'anan laffuza, da yadda ake tsara jumloli a cikin harshen, da fiskoki
mabanbanta na amfani da su, Wannan kuma saboda alqur'ani
mai girma an saukar da shi ne da yaren larabci, kuma dole ne a fahimce shi bisa
qa'idodin
wannan harshen.
4-
Mayar da
ma'anonin ayoyin da ma'anarsu ba a fili take sosai ba (mutashabihai) zuwa ga waxanda
ma'anarsu ta ke a fili qarara (muhkamai), wannan kuma saboda alqur'ani
sashinsa yana fassara sashi, kuma mafi yawan ayoyin alqur'ani
mai karamci "muhkamai" ne, da ma'anoninsu yake a fili. Sai dai kuma a
cikinsa akwai ayoyi "mutashabihai" waxanda
ma'anoninsu ka iya vuya ga sashin maluma. Sai dai kuma mayar da su zuwa ga ayoyi
"muhkamai" na taimakawa kan fahimtar abinda suke nunawa na ma'ana.
Allah (s.w.t) yana cewa:
(هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ
آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ
فَأَمَّا
الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ
الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ وَمَا يَعْلَمُ
تَأْوِيلَهُ
إِلَّا اللَّهُ وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ
عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو
الْأَلْبَابِ)
[آل عمران: 7].
Ma'ana: "Allah shine wanda ya saukar maka da wannan
littafin; a cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, da wassu masu kama da juna, Amma waxanda
akwai karkata a cikin zukatansu Sai suna bin abinda akwai kama da juna daga
gare shi, domin neman fitina, da neman yin tawilinsa, Kuma babu wanda ya san
fassararsa face Allah. Su kuma tabbatattu cikin ilimi suna cewa: Mun yi imani
da shi; dukkansu daga wajen ubangijinmu ne. Babu wanda ya ke tunani ya wa'aztu
face ma'abota hankula" [Ali-imraan: 7].
5-
Xaukar
tabbatattun abubuwan da binciken ilimi ya tabbatar da su, don haskakawa, a
lokacin fassarar ayoyin da suke magana kan halittun Allah (na sarari ko teku ko
cikin sammai). Tare da nisantar cusa ra'ayoyin da ba dole su zama sun inganta
ba (نظريات علمية) cikin tafsirin alqur'ani
mai girma, tsoron kada a cusa ma alqur'ani
ma'anonin da baya nuni akansu.
6-
Ya kiyaye
yin munanan tawilin da suke nisantar da maganar Allah ta'alah daga abubuwan da
shari'arsa mai tsarki ta haqqaqe, sannan qa'idodin harshen larabci
basa tare da su, ko don saboda nufin jirkita ma'anonin nassoshi, ko kuma don
jahiltar harshen larabci da ma'anoninsa da fiskokin da ake amfani da shi, ko
kuma don zaton wassu ma'anoni munana waxanda
ake tsarkake maganar Allah ta'alah daga bada irinsu.
NA TAKWAS: MU'UJIZAR ALQUR'ANI MAI GIRMA (GAGARA-MISALI):
"Mu'ujizah"
a yaren shari'a: Wata sifa ce da tafi qarfin
ikon mutum ya zo da wani abu, na aiki ko
ra'ayi ko tsari (sai kuma ya zo da ita).
Kuma
lallai "mu'ujizah" sifa ce da take fararuwa ba don komai ba sai don ta
yi nuni kan "ayoyi da hujjojin annabawa da manzanni (a.s).
Kuma
wannan lafazin "na mu'ujizah" ambatonsa bai zo ba a cikin alqur'ani
mai girma, Abin sani kawai, lafazin "aya, da burhaan", da wassun haka
ne suka zo a cikinsa.
Shi
kuma alqur'ani mai girma maganar Allah ne maxaukaki,
a cikinsu kuma akwai cika da kamala ta fiskar ma'anoni, da kyan ayoyi da
kalmomi da jumlolin da aka gina shi da su, da suka fi qarfin
ace mutum ne ya faxe su, Allah ta'alah yana cewa:
(الر، كِتابٌ أُحْكِمَتْ آياتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ
مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ) [هود: 1].
Ma'ana:
"A L R, Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa , sa'annan aka bayyana su
daki-daki, daga wajen mai hikima mai bada labari" [Hud: 1].
Kuma lallai mushirkai sun yi iya qoqarinsu
wajen sanya shakka kan tushen alqur'ani mai daraja, da
hana mutane amfana da shi, ta hanyar qirqiran qarerayi,
da tada wassu shubuhohi([10]), Sai Allah (s.w.t) ya saukar da ayoyi waxanda
a cikinsu ya ke qure mavarnata; ta hanyar cewa su zo da
kwatankwacin wannan alqur'anin, ko da surori goma irinsa,
ko da sura xaya; in dai sun kasance masu gaskiya([11]). Sai suka gajiya wajen kawo haka, suka
kuma tabbatar cewa lallai alqur'ani duk da
kasancewarsa da harshen larabci, sai dai kuma ba za a iya kwaikwayonsa ko zuwa
da kwatankwacinsa ba, Allah ta'alah yana cewa:
(أَمْ يَقُولُونَ افْتَراهُ قُلْ فَأْتُوا بِسُورَةٍ
مِثْلِهِ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ
صادِقِين) [يونس: 38].
Ma'ana:
"Ko suna cewa: Shi ya qirqire shi, Ka ce: To
sai ku zo da sura guda xaya kwatankwacinsa, ku kirayi waxanda
kuka samu dama in kun kasance masu gaskiya" [Yunus: 38].
Kuma lallai alqur'ani
mai karamci ya yi shela a fili; cewa mutane gabaxayansu
da aljanu a bayansu sun gaza kan zuwa da kwatankwacin alqur'ani
mai girma, koda kuwa sashinsu yana taimaka wa sashi:
(قُلْ لَئِنِ اجْتَمَعَتِ الْإِنْسُ وَالْجِنُّ عَلى
أَنْ يَأْتُوا بِمِثْلِ هذَا الْقُرْآنِ لا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِ وَلَوْ كانَ
بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا) [الإسراء: 88].
Ma'ana:
"Ka ce: Da mutane da aljanu za su haxu akan su
zo da kwatankwacin wannan alqur'ani, ba za su zo da
kwatankwacinsa ba, koda kuwa sashinsu yana taimakon sashi" [Isra'i: 88].
Akan haka; Shi alqur'ani
mai girma "mu'ujizah" ne; saboda kasancewarsa maganar Allah; wanda
maganganun halittu basa kama da shi, Kuma shi aya ne kuma hujja, da kalmominsa
da ayoyin cikinsa da yarensa, da abinda ke cikinsa na fiskokin bayanai da
balagah (fasaha), da kuma abinda ke cikinsa na labaru da qissoshin
gaskiya, da abinda ya qunsa na hukunce-hukunce da shari'oi, da qarfin
tasirinsa ga zuciya da jiki, da abinda ya qunsa
na tabbatattun abubuwan da ilimi ya zo da su masu qayatarwa.
Kuma sau dayawa alqur'ani
mai girma ya kan ximautar da hankulan masana ilimin xabi'a,
da sararin sama (falaki), da waxanda suka shagaltu da
neman sanin ilimin rayayyun halittu da likitanci, da wassunsu, a inda alqur'anin
ke zance kan tabbatattun abubuwa a ilmance, ko ya yi nuni kan wassu
halittun da suke da alaqa
da ilimin da suke aiki a cikinsa, da laffuza na ilimi masu zurfi, waxanda
baza a tava iya zaton fitowarsu daga annabin da bai iya rubutu da karatu
ba, wanda kuma ya rayu cikin al'ummar da bata iya karatu da rubutu ba, a kuma
yankin duniyar da ba su san komai ba dangane da waxannan
lamuran, Wanda kuma hakan shine ya zama sababin musuluntar mutane da yawa daga waxannan
masanan, hakan kuma ya kasance kuma ya kan kasance saboda masanan sun gane cewa
lallai dukkan abinda alqur'ani mai girma ya zo da shi ba
zai yiwu ya zama maganar mutum ba, sai dai ya zama maganar mahaliccin duniya da
mutane.
Kuma
a cikin alqur'ani mai girma akwai ayoyi da
yawa da suke nuni kan kaxaitakar Allah ta'alah, da kuma
bayanin yadda ya ke kyautata halittunsa, Allah ta'alah yana cewa:
(سَنُرِيهِمْ آياتِنا فِي الْآفاقِ وَفِي
أَنْفُسِهِمْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ الْحَقُّ أَوَلَمْ يَكْفِ
بِرَبِّكَ أَنَّهُ عَلى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ) [فصلت: 53].
Ma'ana:
"Da sannu, zamu nuna musu ayoyinmu a sararin sama, da kuma a cikin
kayukansu, har sai ta bayyana musu cewa alqur'ani
gaskiya ne, Ashe kuma ubangijinka bai isa ya zama halartacce akan kowani abu
ba!" [Fussilat: 53].
NA TARA: TARJAMAR MA'ANONIN ALQUR'ANI MAI GIRA:
Kuma
lallai tarjama bata rabuwa da wahalhalu, saboda tsara laffuza a cikin yare har
su bada cikakkiyar magana mai amfani xaya ne daga
abubuwan da suke samar da maganar, kuma yana da wahala a kiyaye abinda jerin
laffuzan ke nunawa na dukkan ma'anarsa a lokacin da aka so a tarjama wannan
maganar zuwa wani yaren na daban([13]).
To
idan wannan shine halin tarjama cikin maganganun da mutane ke yi, to lallai
tarjama zata yi wahala matuqa a yayin da ake nufin tarjamar alqur'ani
mai girma; saboda kasancewar alqur'ani maganan Allah ne, wanda ya sauqar
da shi da harshen larabci, kuma alqur'ani
an yi wahayinsa daga Allah ta'alah da lafazinsa da ma'anarsa, kuma ba zai yiwu
wani mutum ya yi da'awar cewa ya san dukkan ma'anonin alqur'ani
gabaxayansa ba, ko kuma yace: Wai shi yana da ikon ya dawo da tsarin
laffuzan, ta irin hanyar da maganar take a harshen larabci.
Amma
tare da cewa tarjamar alqur'ani mai girma tana da wahalar
gaske, sai dai kuma maluman musulmai suna qarfafa
tare da bayanin wajabcin ko lalurar a isar da alqur'ani
mai girma, da saqon da yake xauke da shi zuwa ga
dukkan al'ummai a bayan qasa, ko-yaya kuma harshensu ya ke, Hakan kuma zai tabbata ne
kawai ta hanyar yin tarjama([14]).
1-
Ta hanyar
tarjamar ma'anoninsa, Wannan kuma itace tarjamar da babu tafsiri tare da ita,
kuma tana taqaita ne ga yin bayanin abinda laffuzan nassin alqur'ani
ke nunawa kawai.
2-
Ko kuma ta
hanyar tarjama mai qunshe da tafsiri, wacce za a qarfafe
ta da fitar da magana a fili, da buga misalai, Wannan kuma kamar: tafsirin alqur'ani
ne da wani yaren na daban wanda ba larabci ba.
Kuma
duk yadda tarjamar ma'anonin alqur'ani mai girma ta kai
ga yin kyau da zurfi, kuma duk yadda shi mai yin tarjamar ya zama ya gwanance a
harshen tarjama guda biyu, ya kuma yi zurfi wajen sanin ma'anonin ayoyin, to
lallai wannan tarjamar ba za a kira ta da suna: alqur'ani
ba, saboda sababi guda biyu([16]):
NA FARKO: Lallai
alqur'ani
mai girma maganar Allah ne maxaukaki, wanda aka
saukar da shi da harshen larabci, kuma ya kai qololuwa
wajen kyautatuwa da bayani. Shi kuma xaukar
ma'anonin ayoyin tare da sake dawo da su da wani yaren; wanda ba larabci ba, ya
vata
sunansa na alqur'ani.
NA BIYU: Ita
tarjama tana yin bayanin fahimtar mai yinta ne ga ma'anonin alqur'ani
mai girma, don haka, A ta wannan fiskar tana yin kama da tafsiri. Kamar yadda
shi kuma tafsirin ba a kiransa ace shi: alqur'ani
ne, to haka itama tarjamar ba zai yiwu a kira ta alqur'ani
ba.
Kuma
domin tarjamar ma'anonin alqur'ani mai girma ta kasance karvavviya
dole ne ta cika qa'idodin da maluma suka sanya ga mai
nufin bayanin ma'anonin alqur'ani mai girma, tare da kiyaye
kada mai tarjamar ya riqi tarjamarsa wani lulluvi
da zai watsa ma'anoni ta qarqashinsa da suke karkatar da
ma'anonin alqur'ani mai girma, ko kuma masu
munana wa alamomin addinin musulmai da abubuwan da suke girmama su, wanda hakan
kuma shine ya munana tarjamomi da yawa, waxanda
wassu daga cikin "mustashriquna([17])" suka yi,
ko kuma na wassu mutanen da suke nasabta kansu zuwa ga musulunci da qarya,
alhalin kuma suna xauke da munanan aqidu, da suke qoqarin
rushe mas'aloli muhimmai na addinin musulunci mai girma, da sukar aqidarsa
ingantacciya, da shari'arsa mai sauqi.
Wannan
ne kuma ya sanya ma'aikatar sarki Fahad da take buga "mus-hafi" mai
girma, a garin Madinar Annabi, ta xauki
alhakin fitar da tarjamomin ma'anonin alqur'ani
amintattu, da nufin isar da saqon da alqur'ani
mai girma ya qunsa, zuwa ga waxanda basa magana da
harshen larabci, da yarukansu na asali.
Godiya
kuma ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, Salatin Allah ya qara
tabbata ga annabinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya,
da waxanda
suka bi su da kyautatawa zuwa ranar sakamako.
No comments:
Post a Comment