2015/03/20

LADDUBAN SHIGA MAKEWAYI A MUSULUNCI

SHIGA MAKEWAYI DA LADDUBANSA A MUSULUNCI

 (آداب قضاء الحاجة في الإسلام)
Lallai Addinin Allah (musulunci) addini ne mai girma, wanda bai bar wani abu don qarancinsa ba face yayi bayanin "cikakkiyar shiriyar" da musulmai ya kyautu su tafi akanta, lura da wannan, addinin Musulunci ya zo da ladduba masu yawa da kuma tarin amfani dangane da "shiga makewayi da kuma fita",Ga ambaton muhimman "ladduba kewayawa", kamar haka:
Na xaya: Fiskantar alqibla da juya mata baya lokacin biyan buqata:
Ba ya halatta a fiskanci alqibla ko a juya mata baya a lokacin biyan buqata ba, a cikin saharar da ba wani abu da ya zame wa bawa shamaki (a filin Allah); saboda hadisin Abu ayyuba al-ansaariy (RA), Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"إِذَا أَتَيْتُمُ الغَائِطَ فَلاَ تَسْتَقْبِلُوا القِبْلَةَ، وَلاَ تَسْتَدْبِرُوهَا وَلَكِنْ شَرِّقُوا أَوْ غَرِّبُوا. قَالَ أَبُو أَيُّوبَ t: فَقَدِمْنَا الشَّأْمَ فَوَجَدْنَا مَرَاحِيضَ قد بُنِيَتْ نحو الكعبة فَنَنْحَرِفُ عنها، وَنَسْتَغْفِرُ اللَّهَ" ([1]).
Ma'ana: (Idan ku ka zo wajen biyan buqata; to kada ku fiskanci alqibla kuma kada ku bata baya, Saidai ana umurtarku da ku kalli gabas ko yamma([2])'', Abu ayyuba –Allah ya qara masa yarda- yace: Sai muka zo qasar Shaam, muka kuma samu wassu shadda –na biyan buqata- an gina su ta fiskar ka'abah; Sai mu karkace mu qi fiskantarta –ka'abah-, Sai kuma mu nemi gafarar Allah).
Amma idan mutum ya kasance zai biya buqatarsa ne a ginannen wuri, ko kuma ya zama a tsakaninsa da alqibla akwai wani abun da ke suturce shi (shamaki) to ba laifi kan haka; saboda hadisin Abdullahi xan Umar (RA), cewa lallai shi:
"أنه رَأَيْ النَّبِيَّ r يبولُ في بيته مُسْتَقْبِلَ الشَّامِ مُسْتَدْبِرَ الْكَعْبَة"([3]).
Ma'ana: (Lallai shi Abdullahi ya ga annbi -SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- yana fitsari a gidansa, yana mai fiskantar "Shaam", ya juya baya ga alqiblah). Kuma saboda hadisin Marwan Al-asfar, yace:
"أَنَاخَ ابْن عُمَرَ رضي الله عنهما بعيرَهُ مُسْتَقْبِلَ الْقِبْلَةِ، ثُمَّ جَلَسَ يَبُولُ إِلَيْه، فَقُلْتُ: أَبَا عَبْدِ الرَّحْمَنِ، أَلَيْسَ قَدْ نُهِيَ عَنْ هَذَا؟ قَالَ: بَلَى، إِنَّمَا نُهِيَ عَنْ ذَلِكَ فِي الْفَضَاءِ، فَإِذَا كَانَ بَيْنَكَ وَبَيْنَ الْقِبْلَةِ شَيْءٌ يَسْتُرُكَ فَلا بَأْسَ"([4]).
Ma'ana: (Abdullahi xan Umar ya gurfanar da rakuminsa ta fiskar alqibla, sa'annan sai ya zauna yana fiskantarsa da fitsari, Sai nace masa: Ya baban Abdurrahman! Shin ba a yi hani akan haka ba? Sai ya ce: E; ai an yi hani ne akan hakan a fili wartal; amma idan akwai wani abu a tsakaninka da tsakanin alqibla dake suturce ka To babu laifi).
Amma mafificin abu shine barin fiskantar alqiblah ko juya mata baya har ma a wurare ginannu. Wallahu a'alam.

Na uku: Abubuwan da aka sunnata aikata su ga mai shiga makewayi:
An sunnata ga mai shiga makewayi faxin:
"بسم الله، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْخُبْثِ وَالْخَبَائِثِ".
(Bismillahi, Allahumma inni a'uzu bika minal khubusi wal khaba'is).
Ma'ana: (Da sunan Allah, Ya Allah; Ina neman tsarinka daga shexanu maza da shexanu mata).
A yayin kammalawa da fita kuma sai yace:
(غُفرانك).
(Gufraanaka). Ma'ana: (Ya Allah ina neman gafararka).
Ya kuma gabatar da kafarsa ta hagu a wajen shiga, ta dama kuma a wajen fita, Sa'annan kada ya yaye al'aurarsa har sai ya yi kusa da qasa.
Idan kuma ya kasance a filin Allah ne (wurin da ba wani shamaki) to mustahabbi ne ya tafi nesa ya kuma sa sutura ta yadda ba za a ganshi ba; Dalilai kan haka kuma sune:
-         Hadisin Jabir (RA) ya ce: Ma'ana:
"خَرَجْنَا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ r فِي سَفَرٍ، وَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ r لا يَأْتِي الْبَرَازَ حَتَّى يَتَغَيَّبَ فَلا يُرَى" ([5]).
(Mun fita tare da manzon Allah -SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- a wata tafiya, Manzon Allah -SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya kasance ba ya zuwa ba-haya face ya fake ta yadda ba za a iya ganinsa ba).
-         Da kuma hadisin Aliyu (RA), yace: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"سِتْرُ مَا بَيْنَ الْجِنِّ وَعَوْرَاتِ بَنِي آدَمَ إِذَا دَخَلَ الْخلاء أَنْ يَقُولَ: بِسْمِ اللَّه" ([6]).
Ma'ana: (Abin da ke suturce tsakanin aljanu da al'aurar 'yan-adam idan su ka shiga makewayi shine mutum ya ce: Bismillahi).
-         Da hadisin Anas (RA) yace: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya kasance idan zai shiga makewayi sai yace:
"اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْخُبْثِ وَالْخَبَائِثِ" ([7]).
(Allahumma inni a'uzu bika minal khubusi wal khaba'isi). Ma'ana: (Ya Allah lallai Ina neman tsarinka daga shexanu maza da shexanu mata).
-         Da kuma hadisin A'ishah (RA), tace: Annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) idan ya fita daga makewayi sai yace:
"غُفرانك" ([8]).
(Gufraanaka) Ma'ana: (Ya Allah; Neman gafararka). Da hadisin Abdullahi xan Umar (RA) yace:
"أَنَّ النَّبِيَّ r كَانَ إِذَا أَرَادَ حَاجَةً لا يَرْفَعُ ثَوْبَهُ حَتَّى يَدْنُوَ مِنَ الأَرْضِ" ([9]).
Ma'ana: (Lallai annabi -SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya kasance idan ya yi nufin biyan bukata baya daga tufansa har sai ya kusanci kasa).

Na huxu: abubuwan da suka haramta wanda yayi nufin biyan buqata ya aikata su:
-         Haramun ne yin fitsari a cikin ruwan dake tsaye (baya gudana); saboda hadisin jabir (RA), daga annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"نَهَى عَنِ الْبَوْل فِي الْمَاءِ الرَّاكِدِ" ([10]).
(Annabi ya yi hani kan fitsari a cikin ruwa da ke tsaye –wanda baya gudana-).
-         Haka Bawa ba zai riqi azzakarinsa da damansa ba alhalin yana fitsari, haka kuma ba zai yi tsarki da shi (daman) ba; saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"إِذَا بَالَ أَحَدُكُمْ فَلاَ يَأخذنَّ ذَكَرَهُ بِيَمِينِهِ، وَلاَ يَسْتَنْجِي بِيَمِينِه" ([11]).
Ma'ana: (Idan xayanku ya zo yin fitsari to kada ya riqi azzakarinsa da damansa, kuma kada yayi "istinja'i" da hanun damansa).
-         Kuma yana haramta ga bawa yayi fitsari ko bayan-gari a kan hanya ko a inuwa ko a gama-garin wuraren hutawa da shakatawa, ko qarqashin bishiya mai 'ya'ya, ko a magudanan ruwa; saboda abun da Mu'azu (RA) ya rawaito, cewa: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"اتَّقُوا الْمَلاعِنَ الثَّلاثَ: الْبَرَازَ فِي الْمَوَارِدِ، وَقَارِعَةِ الطَّرِيق، وَالظِّلِّ" ([12]).
Ma'ana: (Ku kiyayi wuraren tsinuwa guda uku; Yin kashi a mashayan mutane, da tsakiyar hanya, da inuwa). Kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA), lallai annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"اتَّقُوا اللاَّعِنَيْنِ، قَالُوا: وَمَا اللاَّعِنَانِ؟ يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: الَّذِي يَتَخَلَّى فِي طَرِيقِ النَّاسِ أَوْ فِي ظِلِّهِم" ([13]).
Ma'ana: (Ku kiyayi wuraren tsinuwa guda biyu; wanda ke biyan buqata –kashi- a kan hanyar mutane, ko a inuwarsu).
Kuma ya haramta ga bawa yayi istijmari da kashin dabbobi ko da kashi, ko da abinci da ake girmamawa; saboda hadisin Jabir (RA):
"نَهَى النبي r أَنْ يُتَمَسَّحَ بِعَظْمٍ، أَوْ بِبَعْر" ([14]).
Ma'ana: (Annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya hana a yi tsarki da qashi, ko da kashin dabbobi).
Kuma bawa ba zai biya buqatarsa a tsakanin kaburburan musulmai ba saboda; Annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"مَا أُبَالِي أَوَسْطَ الْقُبُورِ قَضَيْتُ حَاجَتِي، أَوْ وَسْطَ السُّوق" ([15]).
Ma'ana: (Bai dame ni ba a tsakanin kaburbura na biya buqatata ko a cikin jama'a; a tsakiyar kasuwa –wajen muni([16])-).

Na biyar: abubuwan da aikata su "makruhi" ne ga mai biyan buqata:
Makruhi ne –a lokacin biyan buqata- a fiskanci wurin da iska ke tashi da kadawa matukar babu abinda ya shamakance; saboda kada fitsarin ya dawo izuwa ga mai yinsa. Haka kuma yin magana lokacin fitsari makruhi ne; saboda wata rana wani mutum ya shige alhalin annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yana yin fitsari, sai ya masa sallama, amma annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) bai amsa masa ba ([17]) .
Kuma an karhanta bawa ya yi fitsari a cikin rami ko makamancinsa; saboda hadisin Qatadah wanda ya samo shi daga Abdullahi xan Sarjis (RA), cewa:
"أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ  r نَهَى أَنْ يُبَالَ فِي الْجُحْرِ، قَالُوا لِقَتَادَةَ: مَا يُكْرَهُ مِنَ الْبَوْلِ فِي الْجُحْرِ؟ قَالَ: كَانَ يُقَالُ: إِنَّهَا مَسَاكِنُ الْجِنِّ" ([18]).
Ma'ana: (Lallai masnzon Allah -SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya yi hani kan yin fitsari a cikin rami, Sai suka ce wa Qatadah: Me yasa a ka yi hani kan fitsari a cikin rami? Sai yace: An kasance ana cewa, Ramuka wuraren zaman aljanu ne –gidajensu-). Kuma saboda mutum ba zai samu amincin cewa ba wata dabba a cikinsa ba; tsoron kar ya cutar da ita. ko kuma ya zama wurin zaman aljanun ne; sai ya cutar da su.
Kuma makruhi ne bawa ya shiga makewayi da abinda akwai ambaton Allah a jikinsa; sai dai in da buqatan hakan; saboda annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya kasance
"كَانَ إِذَا دَخَلَ الْخَلاءَ وَضَعَ خَاتَمَهُ" ([19]).
Ma'ana: (Ya kasance idan zai shiga makewayi sai ya cire zobensa).
Amma matuqar akwai bukatuwa ko larura to nan kam ba komai; wato kamar buqatar a shiga da kuxi makewayi waxanda kuma akwai sunan Allah a jikinsu; saboda in bawa ya barsu a wajen banxakin haqiqa ya bijirar da su ne ga sata, ko kuma mantuwa.
Amma shiga da alqur'ani banxaki hukuncinsa haramun ne; saboda alqur'ani maganan Allah ne, kuma mafificin zance, kuma lallai cikin shiga da shi makewayi akwai nau'i na wulaqanta shi. Saidai idan mutum ya ji tsoron aukuwar wata varnar da tafi barnar shiga da shi din; To!



([1]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba:  144), da Muslim (lamba:  264)
([2]) Wannan hukuncin yana aiki ne ga wanda alqiblarsa ba gabas ko yamma take fiskanta ba
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba:  148), da Muslim (lamba:  266)
([4]) Abudawud ya rawaito shi (lamba:  11), da kuma Addaraqudniy (lamba:  158), da Alhaakim (1/154), kuma Addaraqudniy ya inganta shi, da Alhaakim, Azzahabiy kuma ya masa muwafaqa, Ibnu-hajar ya ce: hadisi ne mai qyau, tare da Al-hazimiy, da Albaniy (ka duba littafin Irwaul galil, lamba:  61). 
([5]) Abudawud ya rawaito shi (lamba:  2), da Ibnu-majah (lamba: 335), kuma wannan lafazinsa ne, sanadin hadisin ingantacce ne (Ka duba Sahihu Ibnu-majah (1/ 60)
([6]) Ibnu-majah ya rawaito shi, (lamba: 297), da At-tirmiziy (lamba: 606), kuma Ahmad Shakir a hashiyar littafin tirmiziy yace: hadisi ne mai kyau "hasan", Albaniy kuma ya ce: ingantacce ne "sahihi" (Sahihul jami'is sagir, lamba: 3611)
([7]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba:  142), da Muslim (lamba:  375)
([8]) Abudawud ya rawaito shi (lamba: 17), da At-tirmiziy (lamba: 7), ya kuma ce: haidisi ne "hasan garib", Albaniy kuma yace: "hasan" (Sahihul jami'is sagir, lamba: 4707)
([9]) Abudawud ya rawaito shi (lamba: 14), da At-tirmiziy (lamba: 14), Albaniy kuma yace: ingantacce ne "sahihi" (Sahihul jami'is sagir, lamba: 4652)
([10]) Muslim ya rawaito shi (lamba:  281), Bukhariy kuma ya rawaito makamancinsa (lamba:  239)
([11]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba:  154), lafazin kuma nasa ne, da Muslim (lamba:  267)
([12]) Abudawud ya rawaito shi (lamba: 26), da Ibnu-majah, (lamba: 328), kuma isnadinsa hasan ne, (Ka duba, Irwa'ul galil, 1/ 100)
([13]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 269)
([14]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 263)
([15]) Ibnu-majah ya rawaito shi (lamba: 1567), Albaniy ya inganta shi a cikin littafin irwa'ul galil (1/ 102)
([16]) Wannan magana da annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya faxa wajen kamanta biyan buqata a tsakanin kaburburan musulmai da biyan buqata a cikin kasuwa; jama'a, kwatance ne wajen daidaita su wajen muni (ka duba: hashiyar da As-sindiy yayi wa sunan na Ibnu-majah, 1/474). 
([17]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 370)
([18]) Abudawud ya rawaito shi (lamba: 26) da An-nasa'iy (lamba: 34), Ibnu-hajar a cikin littafinsa attalkhisu al'habir ya hakaito inganta shi daga Ibnu khuzaimah, da Ibnus sakan. Sheikh Ibnu Usaimin yace: Mafi qarancin halayen wannan hadisin shine ya zama hadisi hasan (As-sharhul mumti'i, 1/ 95-96)
([19]) Abudawud ya rawaito shi (lamba: 29) da At-tirmiziy (lamba: 1746), da An-nasa'iy (lamba:  5228), da Ibnu-majah (lamba:  303), Abu-dawud bayan ya rawaito shi yace: wannan hadisi ne munkari. At-tirmiziy kuma yace: Wannan hadisi ne hasan garib. Albaniy ma ya raunana shi.
Tare da cewa wannan hadisin mai rauni ne, kuma baya halatta a kafa hujja da shi a wannan mas'alar, Saidai mafificin abu shine kada bawa ya shiga makewayi da wani abun da akwai sunan Allah a jikinsa, ba tare da larura ba; saboda girmama sunansa maxaukakin sarki, da kuma girmama shi.  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...