2015/03/14

SHARUDAN "LA ILAHA ILLAL LAHU" (شروط لا إله إلا الله)

SHARUDAN "LA ILAHA ILLAL LAHU" 

DA BAYANIN HATSARIN JAHILTARTA([1])
Tambaya: An lura cewa da dama daga cikin waxanda ake lissafa su cikin "al-umma musulmai" sun jahilci ma'anar "LA ILAHA ILLAL LAHU"; Sai hakan ya haifar da aukawarsu cikin aiyuka ko zantukan da su ke warware wannan kalmar, ko kuma su tauye ta; Akan haka; Menene ma'anar: La ilaha illal lahu? Me kuma ta ke hukuntawa? Sa'annan menene sharruxanta?
Amsa: Ba shakka lallai ita wannan kalma; ta La ilaha illal lahu ita ce ginshiqin wannan addinin (musulunci), kuma ita ce rukunin farko daga cikin rukunnansa, tare da SHAHADATU ANNA MUHAMMADAN RASULUL LAHI, kamar yadda hakan ya zo cikin hadisi ingantacce daga annabi (saw) lallai ya ce:
«بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ، شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Ma'ana: "An gina musulunci akan ginshiqai guda biyar; Shaidawa babu abun bauta da cancanta sai Allah, kuma annabi Muammadu bawan Allah ne kuma manzonsa, da tsayar da sallah, da bada zakka, da aikin hajji, da azumin watan ramadana"([2]). Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi, daga hadisin Abdullahi xan Umar.
Kuma ya zo a cikin littafin Sahihul Bukhariy da Sahihu Muslim daga hadisin Abdullahi xan Abbas (ra) a lokacin da Annabi ya aiki Mu'azu xan Jabal (ra) yankin Yemen, sai ya ce da shi:
«إِنَّكَ تَأْتِي قَوْمًا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ، فَادْعُهُمْ إِلَى أَن يشهدوا أن لا إِلَهَ إِلا اللهُ وَأَنِّي رَسُولُ اللهِ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لِذَلِكَ فَأَعْلِمْهُمْ أَنَّ اللهَ افْتَرَضَ عَلَيْهِمْ خَمْسَ صَلَوَاتٍ فِي اليَوْم وَاللَّيْلَة، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لِذَلِكَ فَأَعْلِمْهُمْ أَنَّ اللهَ افْتَرَضَ عَلَيْهِمْ صَدَقَةً تُؤْخَذُ مِنْ أَغْنِيَائِهِمْ فَتُرَدُّ فِي فُقَرَائِهِمْ».
Ma'ana: "Lallai kai zaka je wa mutanen yahudawa; to sai ka kira su zuwa ga shaidawa babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma lallai Ni manzon Allah ne, idan har su ka yi maka da'a akan haka; to sai ka sanar da su cewa lallai Allah ya farlanta musu yin salloli guda biyar a cikin yini da dare, idan su ka yi maka biyayya akan haka sai ka sanar da su cewa lallai Allah ya farlanta musu zakka daga dukiyarsu; wacce za a karve ta daga mawadatansu, a kuma mayar da ita zuwa ga faqiransu"([3]). Kuma hadisai da su ke magana akan wannan mas'alah suna da yawa.
            Ma'anar "shahadatu an la ilaha illal lahu" shi ne: Babu abun bauta da gaskiya sai Allah; don haka, wannan kalmar tana kore cancantar bauta ga wanin Allah ta'alah, tana kuma tabbatar da ita ga Allah shi kaxai, kamar yadda Allah ta'alah ya ke faxa a cikin suratul hajji:
              الحج: ٦٢
Ma'ana: "Haka kuma ya kasance ne saboda bautar Allah ita ce gaskiya, kuma lallai abin da su ke yi musu bauta koma bayansa su ne varna, kuma lallai Allah shi ne maxaukaki mai girma", [hajji: 62].                 Har ila yau, Allah maxaukakin sarki ya faxa a cikin suratul muminuna:
   ﯲﯳ                 المؤمنون: ١١٧
Ma'ana: "Duk wanda ya kirayi wani abun bauta na daban tare da Allah, bashi da hujja akan haka; to lallai hisabinsa yana wajen ubangijinsa, kuma yadda sha'anin ya ke kafirai basa rabauta",                     [Muminuna: 117]. Kuma Allah mabuwayi da xaukaka ya faxa a cikin suratul baqarah:
         ﯿ                                               البقرة: ١٦٣
Ma'ana: "Kuma abun bautanku abun bauta ne guda xaya, babu abun bauta na gaskiya face shi, mai rahama mai jin kai",             [Baqarah: 163]. Har ila yau Allah ya sake faxa a cikin suratul bayyinah:
                                البينة: ٥
Ma'ana: "Kuma ba a umurce su ba face da su yi bauta ma Allah; suna masu tsantsance addini a gare shi, suna masu karkata daga shirka zuwa tauhidi", [Bayyinah: 5]. Ayoyin alqur'ani da su ke magana akan wannan mas'ala suna da yawa.
            Ita kuma wannan kalma mai girma bata amfani ga mutumin da ya faxe ta; ta kuma fitar da shi daga da'irar shirka face ya san ma'anarta, ya kuma gaskata ta, tare da yin aikinsa da abin da ta ke hukuntawa.
            Saboda "Munafiqai" sun kasance suna faxarta, tare da cewa suna cikin quryar wuta; saboda basu yi imani da ita ba, haka kuma basu yi aiki tare da ikhlasi da abin da kalmar ke hukuntawa ba.
            Haka suma yahudawa suna faxar wannan kalma, tare da cewa suna cikin waxanda suka fi kowa kafirci; saboda suma basu yi aiki da abin da ta ke hukuntawa ba.
            To haka suma masu bautar kaburbura da waliyyai daga cikin kafiran wannan al'ummar, sun kasance suna faxar wannan kalma, alhalin suna masu sava mata da zantukansu ko aiyukansu da aqidarsu, don haka; wannan kalmar ba zata amfanar da su ba, sa'annan faxarta ba zai sa su zamto daga cikin musulmai ba; saboda kasancewar sun warware ta da zantuttukansu da aiyukansu da kuma aqidunsu.
            Kuma lallai wassu maluma sun ambaci sharruxar "la ilaha illal lahu" guda takwas, su ka tara su a cikin baitin waqe guda biyu:
علمٌ، يقينٌ، وإخلاص، وصدقك، مع

محبة، وانقياد، والــــــــقــبول لـــــــــــــهــا
وزيد ثامنها: الكفران مــــنك بــمـــــــــــــــــــــــا

سوى الإله من الأشياء قد ألـها
Ma'ana: "ilimi, yaqini, da ikhlasi, da gaskatawarka, tare da soyayya, da mika wuya, da karbar kalmar la ilaha illal lahu.
An qara na takwas dinsu wanda shi ne: kafircewanka da dukkan wani abu da aka bauta masa koma bayan Allah.
            Waxannan baitoci guda biyu, sun qunshi dukkan sharruxan la ilaha illal lahu guda takwas;
Na farko: Sanin ma'anarta; wanda ke kishiyantar jahiltar haka; kuma ya riga ya gabata cewa: ma'anarta shi ne: Babu abun bauta da cancanta in banda Allah; don haka; Dukkanin abubuwan da mutane ke bauta musu –in banda Allah- barna ne.
           Na biyu: Samun yaqini akanta; wanda ke kishiyantar shakka, saboda dole ne a hakkin wanda ya faxi wannan kalmar ya zamto ya samu yaqinin cewa Allah (swt) shi kaxai ne abun bauta da gaskiya.
      Na uku: Ikhlasi; Wannan kuma shi ne bawa ya tsarkake niyyarsa ga ubangijinsa Allah mabuwayi da daukaka (ma'ana: ya zama Allah tsantsa kawai ya ke nufa), wajen aikata dukkan ayyuka, kasancewar da bawa zai aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah; kamar annabi, ko waliyyi, ko sarki, ko gunki, ko aljani, ko makamancin haka To ya zama mutumin da ya yi shirka ma Allah, kuma ya warware wannan sharaxi; wanda shi ne sharaxin tsarkake addini ga barin shirka (ikhlasi).
            Na hudu: Gaskiya; Wannan kuma ma'anarta shi ne: Mutum ya faxi kalmar alhalin yana mai gaskata abin da ta kunsa na ma'anah; ta yadda zuciyarsa za ta zama ta dace da abin da harshensa ya furta; saboda da mutum zai faxe ta da harshe kawai, sai kuma zuciyarsa ta zamto bata yi imani da ma'ananta ba To a nan ba za ta amfane shi ba; sai ya kasance kafiri -tare da haka-; kamar sauran munafikai.
        Na biyar: Soyayya; Ma'anar wannan kuma shi ne ya zamto yana son Allah mabuwayi da daukaka; saboda da bawa zai faxi wannan kalmar alhalin kuma baya son Allah To ya zama kafirin da bai riga ya shiga cikin musulunci ba, kamar sauran munafikai. Kuma yana daga cikin dalilan haka faxinsa maxaukakin sarki:
                                   آل عمران: ٣١
Ma'ana: "Ka ce: In har kun kasance kuna son Allah To ku bini; Allah zai so ku" [Aa-li imrana: 31], da faxinsa (swt):
ﭿ      ﮇﮈ     البقرة: ١٦٥
Ma'ana: "Akwai daga cikin mutane waxanda su ke riqon wanin Allah a matsayin kishiyoyi a gare shi; suna sonsu kamar son Allah, Sai dai kuma waxanda su ka yi imani sun fi tsananin so ga Allah",                         [Baqarah: 165], Ayoyin alqur'ani da su ke magana a kan wannan suna da yawa. 
           Na shida: Mika wuya ga abin da kalmar ta nuna na ma'ana; Ma'anan haka kuma shi ne: Bawa ya bauta ma Allah shi kaxai, ya kuma miqa wuya ga shari'arsa, yana mai imani da ita, da kuma qudurta cewa ita din nan gaskiya ce, kasancewar da zai faxi wannan kalmar sai kuma ya zama baya bauta ma Allah shi kadai, bai kuma miqa wuya ga shari'arsa ba, hasali ma ya mata girman kai To, da bai zama musulmi ba; sai ya zama kamar Iblis (shexan) da makamantansa na daga (bayi masu girman kai ga Allah).
         Na bakwai: Karvar abin da kalmar ta yi nuni, Ma'anar haka shi ne: Ya karvi abin da ta nuna na tsarkake bauta da kuma yinta ga Allah ta'alah shi kaxai, da barin yin bauta ga waninsa, a nan sai bawa ya yarda da hakan, kana kuma ya yi ta aiki da shi.
        Na takwas: Kafirce ma duk abin da ake bauta masa koma bayan Allah; Ma'anar haka kuma shi ne: Mutum ya kubuta yana kuma mai yin bara'a daga bautar wanin Allah, tare da qudurta cewa yin hakan barna ne, kamar yadda Allah (swt) ya ke cewa:
ﰕﰖ       البقرة: ٢٥٦
Ma'ana: "Duk wanda ya kafirce ma dagutu, ya kuma yi imani da Allah, To haqiqa ya yi riqo da igiya mai qarfi; wacce bata tsinkewa, Kuma Allah mai ji ne mai ilimi", [Baqarah: 256], Kuma ya tabbata manzon Allah (saw) ya ce:
"مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَكَفَرَ بِمَا يُعْبَدُ مَنْ دُونِ اللهِ، حَرُمَ مَالُهُ، وَدَمُهُ، وَحِسَابُهُ عَلَى اللهِ"
Ma'ana: "Duk mutumin da ya ce: Ba wani mai cancantar bauta sai Allah, ya kuma kafirce ma duk abubuwan da ake bauta musu koma bayan Allah To dukiyarsa da jininsa sun haramta, Hisabinsa kuma yana ga Allah"([4]). A wata riwayar kuma annabi (saw) cewa ya yi:
"مَنْ وَحَّدَ اللهَ تَعَالَى، وَكَفَرَ بِمَا يُعْبَدُ مِنْ دُونِهِ، حَرُمَ مَالُهُ وَدَمُهُ، وَحِسَابُهُ عَلَى اللهِ"
Ma'ana: "Duk wanda ya yi tauhidin Allah (kaxaita shi cikin bauta), ya kuma kafirce ma duk abubuwan da ake bauta musu koma bayan Allah To dukiyarsa da jininsa sun haramta, Hisabinsa kuma yana ga Allah", Muslim ya rawaito shi a cikin sahihinsa([5]).
            Don haka; wajibi ne ga dukkan musulmai su tabbatar da wannan kalmar, suna masu lura da waxannan sharruxan, Kuma duk lokacin da aka samu wani mutum ya san ma'anarta ya kuma tsayu akansa ta fiskar aiki To wannan musulmi ne gangariya; wanda jininsa da dukiyarsa suka haramta, Kai koda bai san bayani na dalla dalla kan waxannan sharruxan ba, saboda manufa a nan ita ce a san gaskiya a kuma yi aiki da ita, koda kuwa musulmi bai san wannan bayani daki-daki ba.
            Shi kuma "Xagutu" shi ne: Duk wani abin da ake yi masa bauta koma bayan Allah, alhali ya yarda da haka, kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka ya ke cewa:
ﰕﰖ       البقرة: ٢٥٦
Ma'ana: "Duk wanda ya kafirce ma xagutu, ya kuma yi imani da Allah, To haqiqa ya yi riqo da igiya mai qarfi; wacce bata tsinkewa, Kuma Allah mai ji ne masani", [Bakarah: 256], kuma har ila yau Allah subhanahu yana cewa:
           النحل: ٣٦
Ma'ana: "Kuma haqiqa mun tayar da manzo a cikin kowace al'umma, da cewa ku bauta ma Allah, ku kuma nisanci xagutu",                    [Nahl: 36].
Duk waxanda basu yarda da ayi musu bauta ba daga cikin waxanda aka yi musu bauta; kamar annabawa da salihan bayi da mala'iku To wadannan ba xagutu ba ne, Xagutun a nan shi ne shedanin da ya kirayi mutane zuwa ga bauta wa salihan bayi, ya kuma qawata hakan ga mutane. Allah ya kare mu da dukkan musulmai daga dukkan bala'i.
            Amma dangane da banbancin da ke tsakanin aiyukan da su ke warware wa mutum wannan kalma ta LA ILAHA ILLAL LAHU gabaxayanta, da waxanda ke tauye cikarta na wajibi To shi ne: Duk wani aiki ko zance ko quduri na zuci da ke aukar da ma'abocinsa cikin babbar shirka to lallai wannan na warware ita wannan kalmar gabaxaya, haka kuma yana cin karo da ita, Wannan kuma kamar: roqon matattu, da mala'iku, da gumaka, da bishiyoyi, da duwatsu, da taurari, da makamantan haka, da yi musu yanka, ko yin bakance a gare su, ko kuma yi musu sujjada, da makamancin haka. Waxannan dukkaninsu suna warware tauhidi, kuma suna cin karo da LA ILAHA ILLAL LAHU, suna kuma vata ta.
Yana kuma daga cikin haka: Halatta wani abin da Allah ya riga ya haramta; na abubuwan da aka riga aka sansu a addini, ko kuma aka yi ijma'i akan haramcinsu, kamar zina, da shan giya, da cutar da iyaye, da riba, da makamancin haka.
Yana kuma daga cikin haka: Musanta abin da Allah ya wajabta; na abubuwan wajibi na zantuka da aiyuka; da aka riga aka sansu a addini, ko kuma aka yi ijma'i kan wajabcinsu, kamar wajabcin salloli guda biyar, da zakka, da azumin ramadana, da biyayya ma iyaye, da kuma furta kalmar shahada guda biyu, da makamancin haka.
Amma dangane da zantuka da aiyuka ko kudurce-kudurcen da su ke raunata tauhidi da imani, su ke kuma cin karo da "cikarsa na wajibi" To lallai suna da yawa, Daga cikinsu kuma akwai: qaramar shirka, kamar riya, da rantsuwa da wanin Allah, da fadin: "Allah ya so wane ma ya so", ko kuma "Wannan daga Allah ne, tare da wane", da makamantan haka.
Haka kuma gabadayan sabon Allah suna raunata tauhidi da imani, suna kuma cin karo da "cikarsu na wajibi",
Don haka, wajibi ne nisantar duk wani abinda zai warware tauhidi da imani, ko ya rage musu ladansu.
Shi kuma "imani" a wurin Ahlus-sunnah: Zantuka ne da aiyuka, yana karuwa ta hanyar aikata xa'a, yana kuma raguwa idan aka yi sabo, Dalilai kuma akan haka suna da yawa, ma'abuta ilimi sun bayyana su a cikin littafan "aqidah", da kuma na "tafsiri" da na "hadisi"; saboda haka duk wanda ya nufe su zai same su, walhamdu lillahi.
Yana daga cikin haka: Faxin Allah ta'alah:
ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ التوبة: ١٢٤
Ma'ana: "Kuma idan aka saukar da wata sura, akwai daga cikinsu mai cewa: Wanene daga cikinku ta kara masa imani? Amma waxanda su ke da imani sai ta qara musu imani alhalin suna cikin bushara", [Taubah: 124]. Da kuma faxinsa Subhanahu:
ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ         الأنفال: ٢
Ma'ana: "Lallai muminai su ne waxanda idan aka ambaci Allah sai zukatansu su raurawa don tsoro, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa sai su qara musu imani, kuma ga Allah ubangijinsu ne kaxai su ke tawakkali", [Anfaal: 2]. Da faxinsa (swt):
ﯿ                         مريم: ٧٦
Ma'ana: "Kuma Allah yana kara ma waxanda su ka shiryu shiriya", [Maryam: 76].



([1]) MAJMU'U FATAWA IBNU-BAAZ, (1/229-234), TARAWAR: PROF. AD-DAYYAAR, DA AHMAD BN BAAZ, DA KUMA MAJMU'U FATAWA WA MAKAALAAT MUTANAWI'AH, NA IBNU BAAZ, TARAWAR: DR. AS-SHUWAI'IR, (7/ 56-62).
([2]) Buhariy ya rawaito shi (lamba: 8), da Muslim (lamba: 16).
([3]) Buhariy ya rawaito shi (lamba: 1395), da Muslim (lamba: 19).
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 23), daga Abu-malik al-ashja'iy, daga babansa.
([5]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 23), daga Abu-malik al-ashja'iy, daga babansa.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...