2015/03/20

LADDUBAN CIN ABINCI A MAHANGAR SHARI'A

LADDUBAN CIN ABINCI A MUSULUNCI 

(آداب الأكل)
Lallai Addinin Allah (musulunci) addini ne mai girma, wanda bai bar wani abu don qarancinsa ba face yayi bayanin "cikakkiyar shiriyar" da musulmai ya kyautu su tafi akanta, lura da wannan, addinin Musulunci ya zo da ladduba masu yawa da kuma tarin amfani dangane da "shiga makewayi da kuma fita daga gare shi". Haka ya sake bayani kan ladduban cin abinci, A kan na qarshen, ga ambaton muhimman "ladduba kan cin abinci", kamar haka: 
1.     Faxin "bismillah" a lokacin fara cin abinci: Wannan kuma saboda hadisin Umar xan Abiy-salamah (RA) yace: Na kasance yaro qarqashin kulawar manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- kuma hanuna ya kasance yana yawo a cikin akwashin abinci, sai yace:
"يَا غُلاَمُ! سَمِّ اللَّهَ، وَكُلْ بِيَمِينِكَ، وَكُلْ مِمَّا يَلِيك. فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْد"([1]).
Ma'ana: (Ya kai yaro! Ka ambaci sunan Allah, ka ci da hanunka na dama, ka kuma ci daga abinda ke gabanka. –Jabir yace:- Daga wannan lokacin ban gushe ba; wannan ne irin cin abincina).
2.     Cin abinci da hannun dama: Wannan kuma sunna ne saboda hadisin da ya gabata.
3.    Mutum ya ci gabansa: Shima wannan sunna ne saboda hadisin da ya gabata. Sai dai idan mutum ya san cewa mutumin da suke cin abinci tare da shi ba zai cutu ko kyamaci yawo da hannu a cikin kwaryar abinci ba, to a nan babu laifi kan ya ci daga ko-ina na kwano; saboda hadisin Anas (RA)  a qissar "telan nan da ya gayyaci manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) i zuwa ga wani abinci" Anas yace:
"فَرَأَيْتُهُ –يعني النبي r- يَتَتَبَّعُ الدُّبَّاءَ مِنْ حَوَالَيِ القَصْعَة"([2]).
Ma'ana: (Sai na ganshi –yana nufin: annabi SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- yana bibiyan kabewa daga geffan kwano). Ko kuma idan mutum ya kasance yana cin abincin ne shi kaxai; babu wani a tare da shi, ko kuma abincin akwai launukan abun ci da dama; a irin wannan halin ya halatta ya ci abincin da ke gaban waninsa; matuqar dai bai cutar da wani da hakan ba.
4.     Faxin "alhamdu lillah" a qarshen abinci: Saboda hadisin Abu-umamah (RA) yace: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya kasance idan aka xage akwashin abinci –bayan kammala cinsa- daga gaba-gare shi sai yace:
"الْحَمْدُ لِلَّهِ حَمْدًا كَثِيرًا طَيِّبًا مُبَارَكًا فِيهِ, غَيْرَ مُوَدَّعٍ, وَلا مُسْتَغْنًى عَنْهُ رَبَّنَا"([3]).
Ma'ana: (Yabo mai yawa daddaxa mai albarka sun tabbata ga Allah, Allah Ubangijinmu ba a barin yi masa xa'a, ko kuma ace an wadata ga barinsa). Da kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"إِنَّ اللهَ لَيَرْضَى عَنِ الْعَبْدِ أَنْ يَأْكُلَ الأَكْلَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا، أَوْ يَشْرَبَ الشَّرْبَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا"([4]).
Ma'ana: (Lallai Allah yana rubuta yardarsa ga bawa, idan ya ci abinci ya gode masa akanta, ko ya sha abun sha ya gode masa akansa).
5.    Cin abinci akan ledar cin abinci (Sufurah): Wannan kuma saboda hadisin Anas xan Malik (RA) yace:
"مَا أَكَلَ نَبِيُّ الله r عَلَى خِوَانٍ، وَلاَ فِي سُكُرُّجَةٍ، وَلاَ خُبِزَ لَهُ مُرَقَّقٌ. قال: فقُلْتُ لِقَتَادَةَ: فعَلاَمَ كانوا
يَأْكُلُونَ؟ قَالَ: عَلَى هذه السُّفَرِ"([5]).
Ma'ana: (Annabin Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- bai tava cin abinci a kan "khiwaan([6])", ko a kan "Sukurrujah([7])" ba, haka kuma ba a tava yi masa al-khubuz mai laushi ba. Yace, sai nace wa Qatadah: To, a kan me suka kasance suke cin abinci? Sai yace: A kan waxannan "sufurori([8]); -ledodin cin abinci").
6.    Makruhi ne cin abinci a kishingixe: Wannan kuma saboda hadisin A'ishah (RA) tace:
"قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، كُلْ -جَعَلَنِي اللَّهُ فِدَاكَ- مُتَّكِئًا؛ فَإِنَّهُ أَهْوَنُ عَلَيْكَ، فَأَصْغَى بِرَأْسِهِ حَتَّى كَـادَ أَنْ
تُصِيبَ جَبْهَتُهُ الأَرْضَ، قَالَ: لا، بَلْ آكُلُ كَمَا يَأْكُلُ الْعَبْدُ، وَأَجْلِسُ كَمَا يَجْلِسُ الْعَبْد"([9]).
Ma'ana: (Nace: ya ma'aikin Allah! Ka ci abinci –Allah ya sanya ni na zamo fansarka- a halin kishingixa; saboda zai fiye maka sauqi, Sai manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA-  ya karkata kansa har sai da goshinsa ya yi kusan tava qasa, sai yace: A'a! zan ci abinci ne kamar yadda bawa ke cin abinci, zan kuma zauna kamar yadda bawa ke zaunawa). Da kuma saboda hadisin Abu-juhaifah (RA) yace: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"إِنِّي لا آكُلُ مُتَّكِئًا"([10]).
Ma'ana: (Lallai ni bana cin abinci a kishingixe).
7.    Mustahabbi ne hanuwa daga aibata abincin da mutum baya son cinsa: Wannan kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA) yace:
"مَا عَابَ رَسُولُ اللَّهِ r طَعَامًا قَطُّ، إِنِ اشْتَهَاهُ أَكَلَهُ، وَإِلا تَرَكَه"([11]).
Ma'ana: (Manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- bai tava aibanta abinci ba; idan ya yi sha'awarsa sai ya ci, in kuma bai yi ba, sai ya bari).
8.    Cin abinci daga geffan masaki, da kuma kasancewar cinsa daga tsakiyar kwarya makruhi ne: Wannan kuma saboda hadisin Ibnu-abbas (RA), daga annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) lallai shi an zo masa da masaki da aka sanya kwavavven alkubuz da nama mai suna (Sarid), Sai yace:
"كُلُوا مِنْ جَوَانِبِهَا، وَلا تَأْكُلُوا مِنْ وَسَطِهَا؛ فَإِنَّ الْبَرَكَةَ تَنْزِلُ فِي وَسَطِهَا"([12]).
Ma'ana: (Ku ci daga geffan masakin, kada ku ci daga tsakiyansa, saboda albarka tana sauka ne a tsakiyarsa).
9.     Cin abinci da yatsu guda uku, da kuma suxe su bayan kammalawa: Wannan kuma saboda hadisin Ka'ab xan Malik (RA) yace:
"كَانَ النَّبِيُّ r يَأْكُلُ بِثَلاثَةِ أَصَابِعَ، وَلا يَمْسَحُ يَدَهُ حَتَّى يَلْعَقَهَا"([13]).
Ma'ana: (Annabi –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya kasance yana cin abinci da 'yan yatsunsa guda uku, baya kuma wanke hannunsa har sai ya suxe su).
10.                        Cinye abin da ya zuba ana tsakiyar cin abinci, ko wanda ya warwatsu: Wannan kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"إِذَا سَقَطَتْ لُقْمَةُ أَحَدِكُمْ فَلْيُمِطْ عَنْهَا الأَذَى وَلْيَأْكُلْهَا، وَلا يَدَعْهَا لِلشَّيْطَان"([14]).
Ma'ana: (Idan lomar xayanku ta faxi to sai ya kaxe mata kura, sannan ya cinye ta, kada ya barta ga shexan).
11. Sude kwaryar da aka ci abinci a cikinta da lashe yatsu: Wannan kuma saboda faxin Anas (RA) a cikin hadisin da ya gabata:
"وَأَمَرَنَا –يعني النبي r- أَنْ نَسْلُتَ الْقَصْعَة"([15]).
Ma'ana: (Kuma ya umurce mu –yana nufin annabi SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- da mu katse kwaryar abinci). Ma'ana: mu suxe ta, mu kuma bibiyi abinda ya rage a cikinta na abinci. A wata riwayar kuma aka ce: Annabi –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya umurce mu da mu suxe 'yan yatsu da kuma akwashi, yace:
"إِنَّكُمْ لا تَدْرُونَ فِي أَيِّه الْبَرَكَة"([16]).
Ma'ana: (Saboda lallai ku ba ku san a ina ne daga cikin abincinku albarkar ta ke ba!).




([1]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5376), da Muslim (lamba: 2022)
([2]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5379)
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5459)
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 2734)
([5]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5386)
([6]) "Khiwaan": Teburi ne da ake cin abinci akansa, Kalmar asalinta ba larabci ba ne.
([7]) "Sukurrujah"; Masaki ne qarami da ake sanya abinci kaxan don a ci a cikinsa. Itama wannan kalma ce ta "farisanci". La'alla abinda ya sanya manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya qi ya ci a cikin "khiwaan" saboda kasancewarta daga al'adan "ajamawa", da ke kasancewa a kan wani hali aiyananne. Kuma la'alla wannan shi ya hana shi ya ci akan teburin "sukurrujah".    
([8]) "Sufrah": Kamar leda ne da ake cin abinci akansa
([9]) Albagawiy a cikin littafin "Sharhus sunnah" ya rawaito shi (11/286-287), da Ahmad a "Zuhdu" (5-6) kuma Shu'aibul Arna'ux ya inganta shi da "wani hadisi mursal da ya ke masa shaida", a cikin (Hashiyar sharhus sunnah)
([10]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5398)
([11]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5409), da Muslim (lamba: 2064)
([12]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 5409), da Muslim (lamba: 2064)
([13]) Ahmad ya rawaito shi (1/270), da At-tirmiziy (lamba: 1805), ya kuma ce: hadisi ne hasan ingantacce. Da Abu-dawud (lamba: 3772), da Ibnu-majah, (lamba: 3277), Albaniy ya inganta shi (Sahihu sunan Ibni-majah, lamba: 2650)
([14]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 2032)
([15]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 2305)
([16]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 2033).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...