GINA MASALLACIN ANNABI MAI GIRMA
DA KUMA QARE-QAREN DA AKA YI MASA
Gina masallatai da raya su, da kuma basu kula ta musamman, na
daga cikin manya-manyan aikyuka, da kuma ibadodin da aka fi kusantar Allah da
su, Allah ta'alah yana cewa:
(وَطَهِّرْ
بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَالْقائِمِينَ وَالرُّكَّعِ السُّجُودِ) [الحج: 26].
Ma'ana: "Kuma ka
tsarkake xakina ga masu xawafi, da masu tsayuwa
da ruku'i da sujjada" [Hajj: 26].
Manzon Allah (SAW) kuma yace:
"مَنْ
بَنَى مَسْجِدًا يَبْتَغِي بِهِ وَجْه اللَّه بَنَى اللَّه لَهُ بيتًا فِي
الْجَنَّة".
Ma'ana: "Duk wanda ya
gina wa Allah masallaci; yana neman ganin fiskar Allah da shi –da ikhlasi- to
lallai Allah zai gina masa wani irin gida a aljannah". Wannan kuma yana
daga cikin hadisai da suka zo ta hanyoyi masu xunbun
yawa (mutawatir).
A abinda ke tafe zamu bada tarihin masallacin annabi, da
kuma qare-qaren da aka yi ta yi a lokuta
mabanbanta, kamar haka:
·
Yayin da
Manzon Allah (SAW) ya iso garin Madina a lokacin da yayi hijira daga garin
Makka sai ya gina masallacinsa mai daraja, a lokacin girmansa kamar mita
talatin (30m) ne ta nan, Ta can kuma kamar mita talatin da biyar (35m).
Sai
kuma a lokacin da adadin musulmai ya qaru,
masallacin kuma yayi musu qunci sai ya qara
girmansa; ta yadda ya wayi gari cewa ya kai mita hamsin (50m) ta nan, da ta can,
Wato ya zama kamar mita dubu biyu da xari biyar (2500)
da lissafin murabba'i.
Kuma
dangane da wannan sai muce Annabi (SAW) da kansa shine farkon wanda ya qara
girman masallacinsa mai daraja.
·
Kuma yayin
da yin qare-qare a masallaci da yalwata shi
ya zama daga cikin sunnonin Annabi (SAW) da shiriyarsa, da kuma kasancewarsa
cikin aiyukan da ladansu ke gwavava To sai
khalifofin Annabi (SAW) da shugabanni a bayansu a zamani mabanbanta suka tsayu
wajen yin wannan aiki; Shiryayyen khalifa Umar xan Alkhaxxab
shima ya yalwata masallacin Annabi (SAW), Sannan sai khalifa shiryayye Usman
shima ya qara faxaxa shi (Allah ya qara
yarda a gare su), Sannan sai Alwalid xan
Abdulmalik a daular Umawiyyawa, Sannan sai khalifa Almahdiy xan
Mansur a daular Abbasiyyawa, Sannan sai sarki (sultan) Qayitbaay,
Sannan sai sarki (sultan) Abdulhamid a daular Usmaniyyah, Haka faxaxawarsa
ta wanzu har lokacin qare-qare mabanbanta na daular
saudiyya ta farko suka zo, wanda Sarki Abdul'aziz yayi, da kuma 'ya'yansa a
bayansa kamar; Sarki Sa'ud, da Sarki Faisal, Sannan sai sarki Khalid (Allah
yayi musu rahama gabaxaya).
·
A yayin da
aka sake samun matsananciyar buqatar a sake sabunta qarin
masallacin, a kuma yalwata shi saboda qaruwar tuttuxowar baqin
Allah; mahajjata da masu umrah, da kuma ziyara ya ninninku To sai sarki Fahd
(Allah ya masa rahama) wanda ya samu laqabin
"mai hidimtawa harami guda biyu" ya tsayu wajen samar da mafi girman qari
da masallacin Annabi mai daraja ya tava samu a tarihinsa, ya kuma zo da kansa don dasa harsashin
wannan aiki a watan safar na shekarar 1405 ta hijirar Manzon Allah (SAW), Bayan
nan kuma; A watan Muharram na shekarar 1406h sai wannan aikin ya fara, aka kuma
kammala shi tsaf, a shekarar hijira 1414h, Sai sarki Fahd ya sake dawowa don ya
sanya bulo na qarshe na wannan aiki mai albarka a ranar Juma'a 04/11/ 1414h,
wanda yayi daidai da 15/ 04/ 1994 na miladiyya.
A
lokacin da aka zo wannan aiki, an samar da filin da shi qarin
ke buqata
ta fiskar tsige mulkin fiye da mita dubu xari (100,000m)
a lissafin murabba'i, daga cikin filaye da gidaddajin da suke makwabtaka da
masallacin annabi mai daraja, aka kuma biya waxanda
suka mulke su haqqoqinsu
cikakku, sai kuma aka shigar da su cikin filin masallaci ko harabarsa.
Shi
wannan qari da aka jingina da tsohon masallaci an yi shi ne a filin da
girmansa ya kai mita dubu tamanin da biyu (82,000) da lissafin murabba'i, wanda
hakan ya sanya sabon qarin ya ninninka filin daxaxxen
masallacin har sau biyar, ta yadda jimillarsu gabaxaya
ya zama ya kai mita dubu casa'in da takwas da xari
biyar (98,500m) da lissafin murabba'i. shi kuma yawan waxanda
a da can suke sallah a cikin kwaryar masallacin ya qaru
daga mutane dubu ashirin da takwas zuwa abinda yayi kusa da masallata dubu xari
biyu da hamsin, dukkansu suna sallah a cikin kwaryar masallacin, da kuma saman
masallacin, bayan an tanade shi don haka, da shumfuxe
shi da tayils xin bulo mai sanyi. Shi kuma faxin
saman ya kai mita dubu sittin da bakwai (67,000m) na lissafin murabba'i. Sai
dai kuma idan dukkanin harabar da take kewaye da masallacin ta cika, aka samu qaruwar
mahajjata da masu sallah da masu ziyara To a nan masallacin da dukkanin
farfajiyarsa a lokacin cunkoso ya kan xauki
yawan kimanin masallata miliyan xaya.
Wannan
qarin
da aka yi mai girma wa masallacin annabi mai daraja ya ginu ne akan filoli guda
dubu biyu da xari xaya da saba'in da huxu
(2174) waxanda aka qawata su gabaxayansu da ………..
(Zamu qarisa)
·
A zamanin
sarki Abdullahi ………….
Jaxakallahukhairan
ReplyDelete