2015/04/01

GARIN DADI BA "KUSA" BA

GARIN DADI BA "NESA" BA

Daga kamar shekaru uku da suka wuce a nan masarautar larabawa mai suna "Saudia"  akan sanya ruwan gora ko kwalba (wato, kamar swan water, ko paro) a fridges da suke cikin masallatan unguwanni, a ko-da yaushe, musamman kuma a lokacin zafi.
Lafiya kuma ga dan kasa, da duk wanda kasar ta zaunar da shi a cikinta kyauta ne.
Haka ilimi daga farkonsa har karshe, a cikin yanayi da ake zaton cewa ilimin zai shiga zukata, tare da daukan nauyin mai karatu da bashi wurin zama da scolarship, In kuma dan wata kasar ne a hada masa da ticket da Visa.
 Abinci na gama-gari a gidan kowa: shinkafa da kaza, Naman rago kuma loto-loto.
Ga kuma kungiyoyin da hukuma ta musu rajista don tallafawa ko ta fiskar kayan da za a yi amfani da su a cikin gida; kamar gado da katifa da barguna, da bada kayan shayi da madara da dabino, dana abinci ga wanda ke da bukata, ko don ya gajiya ko tsufa, ko don wani sababin na-daban.
Haka kuma wassu kungiyoyin aikinsu shine saukake lamuran aure da tallafa wa mabukatansa, tare da dauke musu nauyinsa ta kowace fiska (Sai dai kuma kungyoyin suna kukan cewa 'yan kasa suna ganin wai kasha ne hukuma ko kungiya ta yi wa mutum aure, shi yasa suke karanta bada kai don bori ya hau).
Suma kuma wadannan kungiyoyin suna karbar babban gudumawarsu ne daga hukuma, a kowace shekara, da kuma manyan masu hanu da shuni na kasa.
Aminci da jin dadin zama a kasa kuma kada ka tona, saboda Allah ta'alah yayi bayanin cewa Shine ya amintar da su daga tsoro kamar yadda ya ciyar da su daga yunwa, a inda ya umurtarsu da su bauta masa shi kadai
(فَلْيَعْبُدُوا رَبَّ هذَا الْبَيْتِ، الَّذِي أَطْعَمَهُمْ مِنْ جُوعٍ وَآمَنَهُمْ مِنْ خَوْفٍ) [ قريش: 3-4].
Sannan;
          Ga kuma hanyoyi a cikin garurruka masu dadin bi, da na sufuri daga gari zuwa gari; wadanda idan baka fadaka ba, saboda rashin gargadarsu sai kayi barci alhalin kana tuki.
          Da kuma kokari tare da yin aiki tukuru don zamanantar da duk bangarori na rayuwa don saukake ma kowa-da-kowa mu'amalarsa ta bankuna da ofisoshin hukuma da sauransu, ta yadda zai yi ta koda yana cikin gidansa ta hanyar internet, da sauransu ba tare da ya fita ba.

KAI jama'a wannan dadin zai je ko-ina ya mamaye dukkan al'ummai, matukar mutane sun kiyaye sharrudan da Allah ta'alah ya shardanta gabanin moriya da jin dadin duniya da kuma na lahira, Wanda kuma sharrudan sun kimsu cikin YIN IMANI DA ALLAH, DA TAKAWA, DA AIKATA AIYUKA MANAGARTA MASU KYAU, Allah yana cewa:
((ولو أن أهل القرى ءامنوا واتقوا لفتحنا عليهم بركات من السماء والأرض ولكن كذبوا)).
Yana kuma cewa:
((وعد الله الذين ءامنوا منكم وعملوا الصالحات ليستخلفنهم في الأرض كما استخلف الذين من قبلهم وليمكننهم الذين ارتضى لهم وليبدلنهم من بعد خوفهم أمنا يعبدونني لا يشركون بي شيئًا)).
Da kuma fadinsa:
((ومَن يتق الله يجعل له مخرجًا ويرزقه من حيث لا يحتسب، ومن يتوكل على الله فهو حسبه)).
Allah kasa mu cika sharadi, Allah ka tausasa mana. Ya Allah aminci, Amin !!!

Abubakar Hamza
01/04/2015h

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...