2015/03/18

MASALLATAN DA AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSU DA WADANDA BA A SHAR'ANTA BA A GARIN MADINA (02)






BAYANI KAN ABINDA AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSA DA WANDA BA A SHAR'ANTA ZIYARTARSA BA
DAGA MASALLATAN MADINA








BABBAN MALAMI
ABDUL AZIZ BN ABDILLAHI BN BAAZ
(Allah ya rahamshe shi)











Fassaran
Abubakar Hamza


Bismillahir rahmanir rahim

 FATAWA MAI LAMBA (19729) (DA AKA AMSA TA a ranar 27 /06/1418h.

  Yabo da godiya sun tabbata ga Allah shi kadai, sannan yabo da salati su kara tabbata ga wadda babu annabi a bayansa, kuma bayan haka:

 Hakika "LAJANA TA DIN-DIN-DIN DON BINCIKEN ILIMI DA FATAWA" ta tsinkaya (ta ga) tambayar da aka yi wa mai girma mai yin fatawa na gabadaya (MUFTIL AAM) daga mai neman fatawa (da ya yi nuni zuwa ga sunansa da) م. ا. ع  wadda kuma aka karkato shi ya zuwa ga wannan lajanar daga AL'AMANATUL AMATU (babban ofishi) na HAI'ATU KIBARIL ULAMA'A da lamba (1873) a ranar 30 /03/ 1418h.
Wannan shine lafazin tambayar:
((Ina fata daga gare ku masu girma da amin kyautar amsan tambaya da ke tafe:
Na farko: MENENE HUKUNCIN SHARI'AR MUSULUNCI CIKIN WADDA YA ZO MADINA MAI HASKE; DOMIN YAYI SALLA A MASALLACIN ANNABI MADAUKAKI, SANNAN SAI YA TAFI ZUWA GA MASALLACIN QUBA'A, DA MASALLACIN KIBLATAIN, DA MASSALACIN (DA AKE MASA LAKABI DA MASALLACIN) JUMA'A, DA KUMA MASALLATAN GURABEN SALLA (MUSALLA); (KAMAR) MASALLACIN GIRGIJE (GAMAMAH), DA MASALLACIN (ABUBAKAR) ASSIDIQ, DA MASALLACIN ALIYU – R A -, DA WASSUNSU NA MASALLATAN TARIHI, BAYAN KUMA YA SHIGA CIKINSU SAI YAYI RAKA'OI BIYU NA GAISUWAR MASALLACI; SHIN HAKAN YA HALATTA MASA KO A'A?!
Na biyu: BAYAN MAI ZIAYARA YAYI SALLA A MASALLACIN ANNABI MAI DARAJA SHIN YANA HALATTA A GARE SHI YA MORI DAMARSA DON TAFIYARSA YA ZUWA GA MASALLATAN TARIHI A MADINAR ANNABI DA NIYYAR LEKE DA KUMA TUNANI CIKIN TARIHIN MAGABATA NA KWARAI, TARE DA KUMA KARATU NA AIKACE (PRACTICAL) KAN ABUBUWAN DA YA KARANTA SU A LITTAFAN TAFSIRI DA HADISI DA TARIHI WADANDA SUKA FISKANCI YAKUKKUKA DA KUMA MAZAUNAR (GIDAJEN) KABILUN ANSAAR?!
INA FATAN AMFANARWA !!)).

BAYAN ita wannan LAJANAR ta nazarci tambayoyin sai ta amsa da abinda ke tafe:
Lallai amsa wadannan tambayoyin guda biyu na hukunta yin bayani cikin dalla–dallan kan abinda ke biye:

 Na farko:


FASALI: CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARA DA KUMA LADDUBOBINTA:
Sunna ne ziyartar masallacin annabi (saw) kafin hajji ko bayansa; saboda abin da ya tabbata a cikin ingantattun littatafa biyu (sahihul Bukhari da Muslim) daga Abu-hurairah (r a) ya ce: manzon Allah (s a w):
(( صلاةٌ في مسجدي هذا خيرٌ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ ))
 Ma'ana: "Yin sallah a masallacina wannan yafi alkhari fiye da salla dubu a waninsa;  sai dai masallaci mai alfarma" (wato makkah). Ya kuma zo daga Abdullahi bn Umar (r a) lallai annabi (s a w) ya ce:
(( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ ))
 Ma'ana: "Yin sallah a masallacina wannan yafi salla dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma ", Muslim ya ruwaito shi. (ya zo daga) Abdullahi bn Az-zubair (r a) ya ce: manzon Allah (s a w) ya ce:
(( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ، وصلاةٌ في المسجد الحرام أفضل من مائة صلاةٍ في مسجدي هذا ))
 Ma'ana: '' Yin Sallah a masallacina wannan yafi salla dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah dari a masallacina wannan ", Ahmad ne da Ibnu Khuzaimah da Ibn-Hibban su ka fitar da shi. (ya kuma zo) daga Jabir (r a) lallai manzon Allah (s a w) ya ce:
(( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ، وصلاةٌ في المسجد الحرام أفضل من مائة ألف صلاةٍ فيما سواه ))
 Ma'ana: ''Yin sallah a masallacina wannan yafi sallah dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah dubu dari a cikin wadda ba shi ba ", Ahmad ne da Ibnu Maajah su ka fitar da shi. Kuma hadisai da ke dauke da wannan ma'anar suna da yawa.
Idan mai ziyara ya isa wannan masallacin mustahabbi ne ya fara gabatar da kafarsa ta hagu lokacin shigarsa; ya kuma ce:
(( بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانه القديم، من الشيطان الرجيم، اللهم افتح لي أبواب رحمتك ))
 Ma'ana: " (Ina shiga) da sunan Allah, Karin yabo da sallama ya tabbata ga manzon Allah, Ina neman tsarin Allah mai girma, da fiskarsa mai karimci, da kuma karfin mulkinsa da ya jima = daga Shedan wadda aka jefe shi. Ya Allah! Ka bude min kofofin rahamarka". Kamar yadda zai rika fadar hakan wajen shigarsa sauran masallatai; domin babu wani zikiri da aka kebe shiga masallacinsa da shi, koma – bayan sauran masallatan. Sannan sai ya yi sallah raka'a biyu, ya kuma roki abin da ya so a cikinsu na alkhairin duniya da lahira; da zai sallace su (raka'o'i biyun) a RAUDA MADAUKAKIYA to da hakan shi ya fi; saboda fadinsa (s a w):
(( ما بين بيتي ومنبري روضةٌ من رياض الجنة ))
Ma'ana: "Tsakanin gidana da minbarina wani dausayi ne daga cikin dausayin aljanna". Sannan bayan ya idar da sallah sai ya ziyarci gabarin annabi (s a w) da kuma kabari guda biyu na sahabbansa Abubakar da Umar (r a); sai ya tsaya yana mai fiskantar (gaban) kabarin annabi (s a w) da ladabi da kuma Kankan-da-sauti; sannan ya yi sallama a gare shi (yabo da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yana mai cewa:
(( السلام عليك ورحمة الله وبركاته ))
 Ma'ana: "Aminci ya kara tabbata a gare ka da rahamar Allah da kuma albarkokinsa"; saboda abin da ke cikin sunan na Abu-dawu'ud da sanadi ingantacce daga Abu-hurairah (r a ) ya ce: manzon Allah (s a w) ya ce:
(( ما من أحدٍ يُسلِّم عليَّ إلا ردَّ الله عليَّ روحي حتى أردَّ عليه السلام ))
 Ma'ana: "Babu wani da zai min sallama face Allah ya dawo min da raina don na amsa masa sallamar", da mai ziyaran zai ce – a cikin sallamansa -:
(( السلام عليك يا نبيَّ الله، السلام عليك يا خيرة الله من خلقه، السلام عليك يا سيِّد المرسلين وإمام المتقين، أشهد أنَّك قد بلَّغت الرسالة، ونصحت الأمة، وجاهدت في الله حق جهاده ))
 To da ba laifi; saboda wannan dukansa yana cikin sifofinsa (s a w),
 Ma'anan sallamar ita ce: "Ya annabin Allah! Aminci ya kara tabbata a gare ka, aminci ya kara tabbata akanka ya kai zababben Allah cikin halittunsa, aminci ya kara tabbata akanka, ya shugaban manzanni kuma jagoran masu takawa, na shaida cewa lallai ka isar da manzanci, kuma ka sauke amana, ka yi nasiha wa wannan al'ummar, sannan ka yi jihadi iyaka jihadi don daukaka addinin Allah". Sannan kuma sai ya yi masa salati ya kuma yi masa addu'a saboda abin da ya tabbata a cikin wannan shari'ar na shar'anta gamewa tsakanin salati da sallama a gare shi (s a w) yana mai aiki da fadinsa madaukaki:
 ﭽ ﭹ  ﭺ   ﭻ  ﭼ  ﭽ  ﭾ  ﭿ  ﮀ  ﭼ
 Ma'ana: "Lallai Allah da mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabi, Ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati akansa, kuma ku nema masa karin aminci".
Sannan sai ya yi sallama wa Abubakar da Umar (r a) ya kuma yi musu addu'a yana mai neman karin yarda a gare su. (Abdullahi) bn Umar (r a) ya kasance idan zai yi sallama wa manzo (s a w) da kuma abokansa guda biyu baya karawa –a mafi rinjayen lokaci– akan fadinsa:
(( السلام عليك يا رسول الله، السلام عليك يا أبا بكرٍ، السلام عليك يا أبتاه ))
 Ma'ana: "aminci ya kara tabbata akanka ya ma'aikin Allah, aminci ya kara tabbata akanka ya Aba-bakrin, aminci ya kara tabbata akanka ya babana!".
Sannan sai ya juya.
Ita kuma wannan ziyarar abin sani kawai an shar'anta ta ne ga mazaje kawai. Amma su kuma mata to lallai basu da daman ziyartar wani abu na kaburbura; kamar yadda ya tabbata daga annabi (s a w) cewa lallai Shi ya la'anci masu zuwa ziyartar kabari daga mata, da kuma masu rikansu masallaci da kuma sanya musu fitillu",
Amma nufan madina don yin sallah a masallacin manzo (s a w) da kuma yin addu'a a cikinsa da makamancin haka na daga abubuwan da aka shar'anta yin su a cikin kowani masallatai = to wannan kam an shar'anta shi ne ga kowa (mazaje da mata); saboda abin da ya gabata na hadisai.
An kuma sunnanta wa mai ziyaran da ya rinka sallatan sallolinsa guda biyar a masallacin manzo (s a w), kuma ya yawaita zikiri da addu'a da sallar nafila a cikinsa yana mai ribatan wannan garabasar (ganima); saboda abin da ke cikin haka na lada mai yawa, kuma an so ya yawaita sallar nafila a RAUDHA MADAUKAKIYA saboda abin da ya gabata na ingantaccen hadisi kan falalanta; wadda shi ne fadin annabi (s a w):
(( ما بين بيتي ومنبري روضةٌ من رياض الجنة ))
            Amma su kuma sallolin farilla kam to ya dace ga mai ziyara da waninsa ya wuce ta (ma'ana: ya gabaci raudha mai alfarma) ya kuma kiyaye sahun farko ta ko-yaya ya samu iko, koda kuwa cikin karin da ke ta algibla ne saboda abin da ya zo na hadisai ingantattu daga annabi (s a w) na zaburarwa da kwadaitarwa kan sahun farko; kamar fadinsa (s a w):
(( لو يعلم الناس ما في النداء والصف الأول ثم لم يجدوا إلا أنْ يستهموا عليه لاستهموا )).
 Ma'ana: " Da mutane sun san abin da ke cikin kiran salla (ladanci) da kuma sahun farko (na lada) sannan basu samu ba sai kawai su yi kuri'a akansa da sun yi kuri'ar " (Bukhari da Muslim) sun yi ittifaki akansa. Da kuma kamar fadinsa ga sahabbansa:
(( تقدَّموا فائتموا بي وليأْتمَّ بكم مَنْ بعدكم، ولا يزال الرجل يتأخر عن الصلاة حتى يُؤخره الله )).
 Ma'ana: " Ku gabato don ku yi koyi da ni, wadanda su ke bayanku su kuma su yi koyi da ku; mutum ba zai gushe yana jinkiri ga (zuwa) sallah ba face Allah ya jinkirtar da shi ", Muslim ne ya fitar da shi. Abu Dawu'ud kuma ya fitar daga A'ishah (r a) da isnadi mai kyau (hasan) lallai annabi (s a w) ya ce:
(( لا يزال الرجل يتأخر عن الصفِّ المقدَّم حتى يُؤخِّره الله في النار ))
 Ma'ana: "Mutum ba zai gushe yana jinkiri ga sahu na gaba ba face Allah ya jinkirtar da shi a cikin wuta". Kuma ya tabbata daga gare shi (s a w) lallai ya ce ma sahabbansa:
(( آلا تصفون كما تصف الملائكة عند ربِّها! قالوا: يا رسول الله! وكيف تصف الملائكة عند ربِّها؟ قال يُتمون الصفوف الأولى، ويتراصون )).
 Ma'ana: "Shin ba za kuna yin sahu kamar yadda mala'iku ke yin sahu a wajen ubangijinsu ba? Sai su ka ce: Ya ma'aikin Allah! Ta yaya mala'iku ke yin sahu a wajen ubangijinsu? Sai ya ce: suna ciccika sahu-sahun farko kuma suna hadewa; sashinsu zuwa sashi a cikin sahu", Muslim ne ya rawaito shi. Hadisai da su ke dauke da irin wannan ma'anar suna da yawa. Kuma lallai (hukuncinsu) ya game masallacinsa (s a w) da kuma waninsa, gabanin a yi kari a jikinsa da bayan karin. Kuma ya inganta daga annabi (s a w) lallai ya kasance ya kan kwadaitar da sahabbansa kan: dama–daman sahu–sahu. Kuma sananne ne lallai bangaren daman sahu a tsohon masallacin annabi (gabanin kare–kare da bayan haka) ya fita daga cikin (kewayen) raudha; Sai aka sani da haka cewa: damuwa da sahu–sahu na farko–farko, da kuma dama–daman sahu shi ne abin gabatarwa (da fifitawa) akan damuwa da raudha madaukakiya (a cikin farilla kawai), kuma lallai kiyaye su su biyun shi ya fi cancanta fiye da kiyaye yin sallar farilla a raudha, Wannan kuma a bayyane ya ke, a fili sarai ga wanda ya yi tunani kan hadisan da su ka zo a wannan babin. Allah shi ne mai datarwa.
Baya halatta ga wani mutum ya shafi dakin (da manzon Allah - s a w - ya ke kwance; ma'ana: dakin A'ishatu –r a-) ko ya sunbance shi, ko ya rinka kewaya shi (dawafi); saboda hakan ba a ciro mana shi daga magabata na kwarai ba, kai hakan bidi'a ne kuma abun ki.
Haka kuma baya halatta ga wani mutum ya roki manzo (s a w) biyan wata bukata, ko yaye wani bakin ciki, ko warkar da wani maras lafiya ko makamancin haka, saboda hakan dukkansa ba a nemansa sai daga Allah mai tsarki, nemansa kuma daga mamata hada Allah ne da waninsa (shirka), kuma bautan waninsa; Shi kuma addinin musulunci ya ginu ne kan abubuwa guda biyu (na ginshikai da tushe):
Na farkonsu: Kar ayi bauta sai ga Allah shi kadai,
Na biyun kuma: Kar ayi bautar sai da abin da manzo Allah (s a w) ya shar'anta; Wannan kuma shi ne ma'anar: SHAHADATU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, WA ANNA MUHAMMADAR RASULUL LAHI, (ma'ana: shaidawa ba wadda za a bauta masa sai Allah -don shi kadai ya cancanci hakan-, kuma lallai –annabi– Muhammadu –s a w- manzon Allah ne).
Haka kuma baya halatta ga wani mutum (ko aljani) ya nemi ceto daga wajen manzo (s a w); saboda shi (ceton) mallakin Allah mai tsarki ne (shi kadai); don haka ba a nema sai daga wajensa; kamar yadda madaukakin sarki Allah ya ke cewa:
 ﭽ ﮔ  ﮕ  ﮖ  ﮗﮘ    ﮡ  ﭼ
Ma'ana: "Ka ce: ceton gaba daya na Allah ne", Sai ka ce:
(( اللهم شفِّع فيَّ نبيَّك، اللهم شفِّع فيَّ ملائكتَك وعبادك المؤمنين، اللهم شفِّع فيَّ أفراطي ونحو ذلك ))
Ma'ana: "Ya Allah ka karbi ceton annabinka a kaina, ya Allah ka karbi ceton mala'ikunka da bayinka muminai a kaina, ya Allah ka karbi ceton 'ya'yana da su ka rigaye ni mutuwa a kaina da makamantan haka.
Amma matattu kam ba a neman komai a wajensu; ceto ne ko waninsa, kuma daidai ne sun kasance annabawa ne ko wassunsu; saboda hakan ba a shar'anta shi ba, kuma saboda matacce aikinsa ya yanke sai wadda shari'a ta toge; saboda ( ya zo) cikin sahihu Muslim daga Abu Hurairata (r a) ya ce:
(( إذا مات ابنُ آدم انقطع عملُه إلا من ثلاثٍ: صدقةٍ جاريةٍ أو علمٍ يُنتفَع به، أو ولدٍ صالحٍ يدعو له ))
Ma'ana: " Idan 'dan Adam ya mutu aikinsa ya yanke sai guda uku: sadaka da ta ke gudana, ko kuma ilimi da ake amfana da shi, ko kuma da nagari da ya ke yi masa addu'a".
Kuma abin sani kawai ya hallata ne a nemi ceto daga annabi (s a w) a lokacin da ya ke raye da kuma ranar kiyama = saboda yana da iko akan hakan; kasancewar yana da iko ya isa ga Allah don ya roki ubangijinsa ga mai neman, amma a cikin (rayuwarsa) ta duniya to sananne ne hakan ba wai ya kebanta da shi ne kadai ba, kai hakan ya game shi da kuma waninsa; domin ya halatta ga musulmi ya ce wa dan'uwansa:
(( اشفع لي إلى ربِّي في كذا وكذا بمعنى: ادع الله لي ))
Ma'ana: "Ka nema min ceton ubangijina cikin kaza da kaza; ma'ana: ka roka min Allah!", ya kuma halatta ga wadda aka gaya masa hakan ya roki Allan yana mai neman ceto ga 'dan'uwansa; idan wannan abin neman yana daga cikin abubuwan da Allah ya halatta nemansa.
Amma ranar (tashin) kiyama wani mutum ba shi da damar wata ceto har sai bayan Allah mai tsarki ya yi masa izini; kamar yadda Allah madaukaki ya ke cewa:
 ﭽ ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ   ﯠﯡ  ﯾ  ﭼ
Ma'ana: "Babu wadda zai yi ceto a wajensa face da izininsa".
Amma halin mutuwa kam to wannan hali ne kebantacce, baya halatta a riskar da shi (ayi kiyasinsa) da halin mutum gabanin mutuwa, ko kuma da halinsa bayan tayar da mutane (daga kabari) da kuma fitar da su; saboda aikin mutum (a wannan lokacin) ya yanke, kuma ya kaura da aikinsa, sai dai abin da shari'a ta toge; kuma neman ceton matattu baya cikin abin da shari'ar ta toge; don haka; baya halatta a riskar da shi da haka.
Kuma ba makawa lallai annabi (s a w) bayan rasuwarsa yana raye a cikin kabarinsa rayuwa irin ta barzakhu; wanda kuma ta fi rayuwar SHAHIDAI cika; sai dai ita (wannan rayuwar) ba irin rayuwarsa ba ne ta kafin rasuwarsa, kuma ba irin rayuwar da zai yi ba ne a yinin kiyama, kai dai rayuwa ce da ba wanda ya san hakikaninta da yanayinta sai Allah mai tsarki; shi yasa ma fadinsa (a s) ya gabata cikin hadisi madaukaki:
(( ما من أحدٍ يُسلِّم عليَّ إلا ردَّ الله عليَّ روحي حتى أردَّ عليه السلام ))
Ma'ana: "Babu wani mutum guda da zai min sallama face Allah ya dawo min da raina don na amsa masa sallaman".
Sai haka ya nuna cewa shi (manzo s a w) matacce ne, kuma ransa ya rabu da jikinsa, sai dai akan dawo da shi zuwa gare shi lokacin da aka yi masa sallama.
Su kuma nassoshi (dalilai) da su ke nuni kan rasuwarsa na daga alqur'ani da sunnarsa sanannu ne, kuma al'amari ne da ma'abuta ilimi su ka yi ittafaki akansa.
Sai dai kuma hakan baya hana rayuwarsa ta barzakhu, kamar yadda mutuwan shahidai bai hana rayuwarsu ta barzakhun da aka ambata cikin fadinsa madaukaki ba:
ﭽ ﮔ  ﮕ  ﮖ  ﮗ  ﮘ    ﮙ  ﮚ  ﮛﮜ  ﮝ  ﮞ  ﮟ  ﮠ  ﮡ  ﮢ  ﭼ
 Ma'ana: "Kada ku yi zaton wadanda aka kashe su don daukaka kalmar Allah matattu ne, A'a rayayyu ne, a wajen ubangijinsu ake azurta su".
Abin sani kawai mun shumfuda Magana ne kan wannan mas'alar muka kuma fadada shi, saboda bukata tana hukunta hakan; saboda samuwar masu kawo shubuha a wannan babin da yawa, wadanda su ke kiran (mutane) zuwa ga shirka da kuma bautar matattu koma bayan Allah. Muna kuma rokon Allah ga mu da sauran musulmai kubutuwa (da kariya) daga dukkan abin da ya saba wa shari'arsa (Allah). Allah shi ne mafi sani.
Amma abin da sashin masu ziyara ke aikatawa na daga sauti a wajen kabarinsa (s a w), da kuma dogon tsayuwa a can to wannan shima abu ne da ya saba wa abin da aka shar'anta; saboda Allah mai tsarki ya hana al'umma ta daga sauti sama da sautin wannan annabin (s a w) da kuma bayyanar masa magana kamar bayyanawan sashinsu ga sashi, ya kuma kwadaitar da su kan kankanta sauti a wajensa cikin fadinsa madaukaki:
 ﭽ ﮠ  ﮡ  ﮢ  ﮣ  ﮤ  ﮥ   ﮦ  ﮧ  ﮨ  ﮩ    ﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ               ﮮ   ﮯ  ﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ    ﯖ  ﯗ  ﯘ  ﯙ   ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ  ﯠ  ﯡ  ﯢ   ﯣ  ﯤﯥ  ﯦ   ﯧ           ﭼ
Ma'ana: "Ya ku wadanda su ka yi imani kada ku daga sautinku sama da sautin wannan annabin, kuma kada ku bayyana masa magana kamar yadda sashinku ke bayyana wa sashi; sai aikinku ya rushe alhali ku ba ku sani ba * Lallai wadanda su ke kankanta sautinsu a wajen manzon Allah to wadannan su ne wadanda Allah ya jarrabi zuciyarsu don tsoronsa (takawa) suna da wata irin gafara da wani irin lada mai girma".
Kuma saboda dogon tsayuwa a wajen kabarinsa (s a w) da kuma yawaita maimaita sallama (a gare shi) zai kai zuwa ga cunkoso da yawaita ihu da kuma daguwan sautuka a wajen kabarinsa (s a w); wannan kuma ya saba wa abin da Allah ya shar'anta shi ga musulmai a cikin wadannan ayoyi da hukuncinsu ya ke tabbace (ba a shafe su ba), shi kuwa (s a w) abun girmamawa ne yana raye ko yana mace; don haka baya dacewa ga mumini ya aikata –a wajen kabarinsa– abin da ya saba ma ladabin shari'a.
Haka kuma abin da wassu masu ziyara da wassunsu su ke yi na kirdadon addu'a a wajen kabarinsa (s a w) yana mai fiskantar kabarin (ya sa shi a gaba a matsayin algibla) ya daga hanunsa yana addu'a; to wannan dukkansa ya saba wa abin da magabata na kwarai ke kansa na daga sahabban manzon Allah (s a w) da wadanda su ka bi su da kyautatawa, A'a haka din na daga cikin bidi'o'i da aka kirkiro; kuma hakika annabi (s a w) ya ce:
(( عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين من بعدي تمسكوا بها وعضُّوا عليها بالنواجذ، وإياكم ومحدثات الأمور؛ فإنَّ كلَّ محدثةٍ بدعةٌ، وكلَّ بدعةٍ ضلالةٌ ))
Ma'ana: "Ina horonku (da riko) da sunnata da kuma sunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa a bayana, ku yi riko da su, kuma ku kama su da fikoki, kuma ina gargadanku kan kirkirarrun al'amura; saboda kowani kirkirarre bidi'a ne, kuma kowace bidi'a bata ne", Abu Dawu'ud da Nasa'i sun fitar da shi da isnadi mai kyau (hasan). Kuma (s a w) ya ce:
(( من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو ردٌّ ))
Ma'ana: "Wanda ya kirkiro (wani abu) a cikin al'amarinmu (addininmu) wannan wanda ba ya cikinsa to an mayar masa", Bukhariy da Muslim su ka fitar da shi, a cikin wata riwayar Muslim:
(( من عمِل عملاً ليس عليه أمرنا فهو ردٌّ ))
Ma'ana: "Wanda ya aikata wani aiki wanda al'amarinmu (addininmu) ba a kansa ya ke ba to an mayar masa".
Kuma Aliyu bnul Husain (ZAINUL ABIDINA) (r anhuma) ya ga wani mutum na addu'a a wajen kabarin annabi (s a w) sai ya hana shi hakan kuma ya ce: Shin ba zan baka labarin hadisin da na ji shi daga babana (Husain r a) daga kakana (Aliyu bn Abiy Dalib r a) daga manzon Allah (s a w) lallai shi ya ce:
(( لا تتخذوا قبري عيداً، ولا بيوتكم قبوراً؛ وصلُّوا عليَّ؛ فإنَّ تسليكم يبلغني أينما كنتم ))
Ma'ana: "Kada ku riki kabarina wajen kai-komo, haka kuma (kada ku riki) gidajenku kuma (a matsayin) kaburbura (da ba a salla a cikinsu); kuma ku rinka yi min salati; saboda sallamarku zai iso ni a duk inda ku ke", AL-HAAFIZ MUHAMMAD BN ABDILWAHID ALMAKDASIY ne ya fitar da shi a cikin littafinsa ALMUKHTARAH.
Haka kuma abinda wassu masu ziyara su ke yi a wajen yi masa sallaman (s a w) na dora (hanun) dama kan hagu a saman kirji ko kasansa kamar yanayin mai sallah; shima wannan yanayin  ba ya halatta (a aikata shi) a wajen yi masa sallama (s a w) haka kuma wajen sallama ga waninsa daga cikin masu mulki da jagorori da wassunsu; saboda kasancewanta yanayi ne na kaskanci da Kankan-da-kai da kuma ibada da bata dacewa sai ga Allah; kamar yadda ALHAFIZ IBNU HAJAR (r l) a cikin AL-FAT'HU ya hakaito daga maluma. Al'amarin wannan a fili (a sarari) ya ke ga wanda ya yi tunanin matsayin, kuma ya zama manufarsa ita ce bin magabata na kwarai, Amma shi kuma wanda TA'ASSUBANCI da son zuciya da kuma bi-irin-na-makaho (ga wassu maluman bidi'a) tare da munana zato ga masu kira zuwa ga shiriyar magabata na-kwarai to al'amarinsa yana ga Allah. Muna kuma rokon Allah ga mu da shi = shiriya da datarwa wajen fifita gaskiya akan abin da ke waninsa, lallai shi (Allah) shi ne mafi alkhairin wanda ake roko.
Haka kuma abinda wassu mutane ke aikata shi na fiskantar wannan kabari madaukaki daga nesa da kuma mommotsa lebba biyu da sallama ko addu'a; duk wannan shi ma na jinsin abin da ke kafinsa na kirkirarrun abubuwa; kuma baya dacewa (halatta) ga wani musulmi ya kirkiri wani abu a cikin addininsa da Allah bai yi izini da shi ba; sannan shi –da wannan aikin nasa– ya fi kusa da yi masa JAFA'I (s a w) AKAN JIBINTARSA.
Kuma hakika IMAM MALIK (r l) ya tsawatar akan wannan aikin da makamantansa, a inda ya ke cewa:
(( لن يصلح آخر هذه الأمة إلا ما أصلح أولها ))
Ma'ana: "Babu abin da zai gyara Karshen wannan al'ummar sai abin da ya gyara farkonta".
Kuma sananne ne cewa lallai abinda ya gyara farkon wannan al'ummar shine tafiyarsu kan turbar annabi (s a w) da kuma khalifofinsa shiryayyu, da kuma sahabbansa yardaddu da wadanda su ka bi su da kyautatawa, kuma babu abin da zai gyara karshen wannan al'ummar sai rikonsu da hakan, da kuma tafiyarsu akansa. Allah ya datar da musulmai zuwa ga abin da tsiransu da rabautarsu da izzarsu a duniya da lahira ya ke cikinsa; lallai shi mai kyauta ne mai karimci.


FADAKARWA:
Ziyarar kabarin annabi (s a w) ba wajibi ko sharadi ne a aikin hajji ba, kamar yadda wassu marasa ilimi da makamantansu (na ma'abuta son zuciya) su ke zato, A'a ita dai (ziyarar) mustahabbi ce kan wanda ya ziyarci masallacin manzo (s a w) ko kuma ya kasance a kusa da shi (a madina). Amma na nesa da madina ba shi da damar daure sirdinsa (da niko garinsa don tafiwa) da nufin ziyarar kabari, Sai dai an sunnata masa daura sirdinsa (bulaguro) da nufin ziyartar wannan masallaci mai girma; in ya iso garin Madina kuma sai ya ziyarci kabarin annabi madaukaki da kuma na sahabbansa guda biyu (Abubakar da Umar – r a – kuma ziyarar kabarinsa (a s) da kabarin abokansa (r a) ya samu shiga ne (a matsayin) mabiyi ga ziyarar masallacinsa (s a w) (wato: ziyarar masallacinsa shi ne asali); haka kuma ya kasance ne saboda abin da ya tabbata a cikin (littatafa biyu) ingantattu (Bukhari da Muslim) lallai annabi (s a w) ya ce:
(( لا تُشد الرِّحالُ إلا إلى ثلاثة مساجد؛ المسجدِ الحرام، ومسجدي هذا، والمسجدِ الأقصى ))
Ma'ana: "Ba'a daura sirdi (a kuma kimtsa tafiya da nufin lada) Sai in zuwa ga masallatai ne guda uku:
1) Masallaci mai alfarma (makkah).
2) Masallacina wannan.
3) da kuma masallaci mai nisa (da ke Kudus)".
To da daura sirdi (da shiga mota ko jirgi) da nufin zuwa kabarinsa (a s) ko kabarin waninsa shari'a ne = to da ya nuna wa al'umma hakan, kuma da ya shiryad da su zuwa ga falalansa; saboda shi ne ya fi dukkan mutane yin nasiha (ga mutane), kuma shi ne ya fi su sanin Allah (da kuma sanin abin da Allah ke so) sannan shi ya fi su tsananin tsoronsa, kuma ya isar (da manzanci bai boye komai ba) isarwa mabayyaniya, ya kuma nuna wa al'ummarsa dukkan alkhairi, sannan ya hane su daga dukkan sharri; Don haka Ta yaya bayan ya yi gargadi kan daura sirda (da bulaguro) in ba ya zuwa wadannan masallatai guda ukun ba!!! Ya kuma ce:
(( لا تتخذوا قبري عيدا، ولا بيوتكم قبورا؛ وصلوا عليَّ فإنَّ صلاتكم تبلغني حيث كنتم  ))
Ma'ana: "Kada ku riki kabarina wajen kai-komo, haka kuma (kada ku riki) gidajenku (a matsayin) kaburbura (da ba a salla a cikinsu); kuma ku rinka yi min salati; saboda salatinku zai iso ni a duk inda ku ke".
Shi kuma maganan shari'ancin daura sirdi (da yin bulaguro) zuwa ga kabarinsa (s a w) zai kai izuwa ga rikonsa idi (wurin kai-komo, da ya hana cikin wannan hadisin), da kuma aukuwan abin da annabin (s a w) ya ji tsoron faruwansa na wuce gona da–iri, da wuce iyaka wajen yabonsa, kamar yadda mafi yawan mutane su ka auka cikin hakan; saboda kudurta shari'ancin bulaguro don ziyartar kabarinsa (a s).
Amma abin da ake ruwaitowa na hadisai a wannan babin wanda su wadanda ke ganin shari'ancin yin bulaguro ya zuwa kabarinsa (a s) su ke kafa hujja da su = To lallai hadisai ne da isnadinsu ke da rauni, kai maganganu ne ma na karya, kamar yadda wadanda ake musu lakabi da ALHUFFAZ (wato: bajamayen maluma a ilimin hadisin manzo – s a w - ) su ka fadakar kan haka; kamar: AD-DARAKUDUNIY, da ALBAIHAKIY da ALHAFIZ IBNU HAJAR da WASSUNSU; saboda haka; baya halatta a gwara su da hadisai ingantattu da su ke nuni kan haramcin bulaguron in ba dai  ga masallatai ukun nan ba.
Ya kai makaranci! Ga wassu daga cikin wadannan hadisan na karya, da ake ambatowa a wannan babin; domin ka sansu kuma ka nisanci ruduwa da su:
Na farko:
(( من حجّ ولم يزرني فقد جَفانِي ))
Ma'ana: "Duk wanda ya yi aikin hajji, sai bai ziyarce ni ba; To lallai ya min wauta, ya kuma gajarta wajen bada hakkina''.
Na biyu:
 )) من زارني بعد مماتي فكأنما زارني في حياتِي ))
Ma'ana: "Duk wanda ya ziyarce ni bayan mutuwata to kamar ya ziyarce ni ne a rayuwa ta".
Na uku:
(( من زارني وزار أبي إبراهيم في عامٍ واحدٍ ضمِنْت له على الله الجنة ))
Ma'ana: "Duk wanda ya ziyarce ni, kuma ya ziyarci Babana annabi Ibrahim a shekara 'daya; To na masa lamunin Aljanna a kan Allah".
Na hudu:
(( من زار قبري وجبت له شفاعتي ))
Ma'ana: '' Wanda ya ziyarci kabarina to cetona ya wajaba (tabbata) masa".
                     Wadannan hadisan da makamantansu ba wani abu da ya tabbata daga cikinsu daga annabi (s a w);
ALHAFIZ IBNU HAJAR ya fada a cikin littafinsa ATTALKHIIS (Attalkhiis al habiir) –bayan ya ambaci mafi yawan wadannan riwayoyin-: "Hanyoyin wadannan hadisan dukkansu suna da rauni, AL-HAFIZUL UKAILIY ya ce: Babu wani abu da ya inganta a wannan babin.
SHEKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA (r l) KUMA ya yi yanke cewa wadannan hadisan dukkansu: MAUDU'AI NE (wato na karya), Shi kuma wannan malami (Ibnu Taimiyya) ya ishe ka wajen sani (ilimi), da hadda da kuma lege-liken karatu.
                     Kuma da wani abu daga cikinsu ya inganta to da sahabbai (r a) sun riga mutane aiki da shi, da kuma bayanin haka ga al'umma, tare da kiransu zuwa ga aiki da shi; saboda su ne mafi alkhairin mutane bayan annabawa, kuma sune su ka fi su (mutane) sanin dokoki da iyakokin Allah, da kuma abin da ya shar'anta a bayinsa, kuma sune su ka fi yin nasiha ga Allah da kuma halittunsa; to yayin da ba a ciro wani abu daga gare su ba; hakan sai ya yi nuni cewa lallai hakan (nufan kabari da ziyara daga wani gari) ba wani abu ne da shari'a ta san da shi ba.
                     To kai! da wani abu ma ya inganta daga cikinsu (hadisai) to da wajibi ne a dauki hakan da cewa na nuni ne akan ziyara ta shari'a; wacce kuma babu bulaguro a cikinta don nufan kabari; saboda (neman) yin jam'i (hade) tsakanin hadisan. ALLAH SUBHANAHU WA TA'ALA shi ne mafi sani".


Alhamdu lillah
07 / 11 / 1429h = 06 / 11 / 2008m.


MUSTAHABBANCIN ZIYARTAR MASALLACIN QUBA'A
DA (MAKABARTAR) BAQI'I:
Kuma an so ga mutmumin da ya ziyarci Madina ya ziyarci masallacin Quba'a ya kuma yi sallah a cikinsa; saboda abin da ya zo cikin (littatafa) ingantattu guda biyu (sahihul Bukhari da sahihu Muslim) daga hadisin (Abdullahi) bn Umar (r a); lallai ya ce:
(( كان النبيُّ r يزور مسجد قباء راكبًا وماشيًا، ويصلِّي فيه ركعتين ))
Ma'ana: "Annabi (s a w) ya kasance ya kan ziyarci masallacin Quba'a akan abin hawa (a wani lokaci, a wani lokacin kuma) da kafa; sa'annan ya sallaci raka'a biyu a cikinsa". (Ya zo) kuma daga Sahal bn Hunaif (r a) lallai ya ce; Manzon Allah (s a w) ya ce:
 (( من تطهَّر في بيته ثم أتى مسجد قباء فصلَّى فيه صلاةً كان له كأجر عمرةٍ ))
Ma'ana: "Duk wanda ya tsarkaka (alwala) a gidansa sa'annan ya zo masallacin Quba'a; sai kuma ya sallaci wata sallah a cikinsa to yana da kamar ladan umrah".
Kuma an sunnanta masa ziyartar kaburburan Baqi'i, da kabarurrukan wadanda su ka yi shahada (a yakin Uhud) da kabarin Hamza (r a); saboda annabi (s a w) ya kasance ya kan ziyarce su ya kuma yi musu addu'a, kuma saboda fadinsa (s a w):
(( زُورُوا القبورَ؛ فإنها تذكِّرُكُمُ الآخرةَ ))
Ma'ana: "Ku ziyarci kaburbura; domin suna tuna mu ku Lahira " Muslim ne ya ruwaito shi. Kuma annabi (s a w) ya kasance yana ilmantar da sahabbansa idan su ka ziyarci kaburburbura da su ce:
(( السلام عليكم أهلَ الديار من المؤمنين والمسلمين، وإنَّا إنْ شاء الله بِكُم لاحقون، أسأل اللهَ لنا ولكم العافيةَ ))
Ma'ana: "Aminci ya tabbata a kanku ya ku ma'abotan wadannan gidaje na mu'uminai da musulmai, Kuma muma –In sha' Allahu– Ma su haduwa ne da ku, muna roka mana Allah lafiya; mu da ku" Muslim ne ya rawaito shi daga hadisin Sulaiman bn Buraidah daga Babansa.
Haka kuma tirmiziy ya fitar daga (Abdullahi) bn Abbas (r a) ya ce: Annabi (s a w) ya wuce kaburburan Madina; sai ya fiskance su da fiskarsa sa'annan ya ce:
(( السلام عليكم يا أهل القبور، يغفر الله لنا ولكم، أنتم سلفُنا ونحن بالأثر ))
Ma'ana: "Aminci ya tabbata gare ku ya ku ma'abuta kaburbura! Allah ya mana gafara mu da ku, ku marigaya ne a gare mu, mu kuma muna tafe".
                     Daga wadannan hadisan za a san cewa lallai ita ziyara ta shari'a ya zuwa kaburbura = manufarta su ne: tuna lahira (wadda hakan sababi ne na gyara aiki). Da kuma kyautata wa matattu da yi musu addu'a tare da nema musu rahama.
Amma ziyarar wassu da su ke yi da nufin roko (n Allah) a wajen Kaburbura, ko kuma tsayuwa a wajen tare da jimawa, ko kuma rokonsu (Mamatan) biyan bukatu, ko warkad da marasa lafiya, ko kuma rokon Allah da su, ko da matsayinsu, ko makamancin haka; =To (duk) wadannan ziyarori ne na bidi'a, abun kuma kyama, Allah bai shar'anta su ba, haka manzonsa, sannan magabata na kwarai (Allah ya yarda da su) ba su aikata su ba, Kai suna cikin HUJUR (yawaita Magana kan abin da bai dace da shari'a ba) wanda Manzon Allah ya yi hani akai a cikin fadinsa:
[ زوروا القبور ولا تقولوا: هُجْراً]
Ma'ana: "Ku ziyarci kabari, amma kada ku fadi abin da ba daidai ba (kamar abubuwan da su ka gabata).
Wadannan abubuwan da aka ambata (a baya) Duk kansu sun hadu wajen kasancewarsu bidi'a amma martabobinsu da matsayinsu sun banbanta; saboda sashensu: Bidi'a ne; ba shirka ba; kamar rokon Allah mai girma da daukaka wajen kabari, da kuma rokonsa da hakkin mamaci ko matsayinsa … da makamancin haka, Yayin da sashensu kuma suna cikin (nau'in) babban shirka; kamar rokon mamata da kuma neman agajinsu … da makamantan haka.
Kuma hakika bayanin wannan dalla–dalla ya gabata cikin abin da ya gabata; don haka ka fadaka! Kuma ka kiyaye!! Sannan ka roki ubangijinka datarwa da shiriya zuwa ga gaskiya!!!; domin shi (Allah) shi ne mai datarwa kuma mai shiryarwa. Babu wani abun bauta da cancanta waninsa, kuma babu ubangiji sai shi.
Wannan shi ne karshen abin da mu ka yi nufin shiftarsa (IMLA'INSA), godiya da yabo sun tabbata ga Allah a farko da karshe.

Salati da sallama kuma su kara tabbata ga bawansa kuma manzonsa kana kuma zababbensa daga halittunsa Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa, da wanda duk ya bi su da kyautatawa zuwa ranar sakamako.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...