2015/03/18

MASALLATAN MADINA DA AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSU DA WADANDA BA A SHAR'ANTA BA (01)






BAYANI KAN ABINDA AKA SHAR'ANTA ZIYARTARSA

DA WANDA BA A SHAR'ANTA ZIYARTARSA BA

DAGA  MASALLATAN MADINA








BABBAN MALAMI
ABDUL'AZIZ BN ABDILLAHI BN BAAZ
(Allah ya yi masa rahama)











Fassarar
Abubakar Hamza


Bismil lahir rahmanir rahim


  FASALI: CIKIN HUKUNCE – HUKUNCEN ZIYARA DA KUMA LADDUBOBINTA:

  Sunna ne ziyartar masallacin annabi (s a w) kafin hajji ne ko bayansa; saboda abin da ya tabbata a cikin ingantattun littatafa biyu (sahihul Bukhari da Muslim) daga Abu hurairata (r a) ya ce: manzon Allah (s a w) ya ce:

 (( صلاةٌ في مسجدي هذا خيرٌ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ ))
 Ma'ana: '' Salla a masallacina wannan yafi alkhari fiye da salla dubu a waninsa;  sai dai masallaci mai alfarma " (wato makkah), ya kuma zo daga Ibnu Umar (r a) lallai annabi (s a w) ya ce:

  (( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ ))

 Ma'ana: '' Salla a masallacina wannan yafi salla dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma ", Muslim ya ruwaito shi. (ya zo daga) Abdullahi bnuz Zubair (r a) ya ce: manzon Allah (s a w) ya ce:

   (( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ، وصلاةٌ في المسجد الحرام أفضل من مائة صلاةٍ في مسجدي هذا ))
 Ma'ana: '' Salla a masallacina wannan yafi salla dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah dari a masallaci na wannan ", Ahmad ne da Ibnu Khuzaimata da Ibnu Hibban su ka fitar da shi. (ya kuma zo) daga Jabir (r a) lallai manzon Allah (s a w) ya ce:

    (( صلاةٌ في مسجدي هذا أفضلُ من ألف صلاةٍ فيما سواه إلا المسجدَ الحرامَ، وصلاةٌ في المسجد الحرام أفضل من مائة ألف صلاةٍ فيما سواه ))
 Ma'ana: '' Salla a masallaci na wannan yafi salla dubu a waninsa falala;  sai dai masallaci mai alfarma, sallah kuma a masallaci mai alfarma ya fi falala fiye da sallah dubu dari a cikin wadda ba shi ba ". Ahmad ne da Ibnu Maajah su ka fitar da shi; hadisai da ke dauke da wannan ma'anan suna da yawa.

  Idan mai ziyara ya isa masallacin; Mustahabbi ne ya fara gabatar da kafansa na dama lokacin shigansa; ya kuma ce:

 (( بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، أعوذ بالله العظيم، وبوجهه الكريم، وسلطانِه القديم، من الشيطان الرجيم، اللهم افتح لي أبواب رحمتك ))
 Ma'ana: " (Ina shiga) da sunan Allah, Karin yabo da sallama ya tabbata ga manzon Allah, Ina neman tsarin Allah mai girma, da fiskarsa mai karimci, da kuma karfin mulkinsa da ya jima (bashi da farko) = daga Shedan wadda aka jefe shi, ya Allah! Ka bude min kofofin rahamarka ", (mutum zai fadi hakan) kamar yadda ya ke fadan hakan wajen shigansa sauran masallatai; domin babu wani zikiri da aka kebe shiga masallacinsa da shi, koma – bayan sauran masallatan.
  Sannan sai ya yi sallah raka'a biyu, ya kuma roki abin da ya so a cikinsu na alkhairin duniya da lahira; Da kuwa zai sallaci raka'o'in biyun a RAUDA MADAUKAKIYA to da hakan shi ya fi; saboda fadinsa (s a w):

 (( ما بين بيتي ومِنبري روضةٌ من رياضِ الجنّة ))
Ma'ana: '' Tsakanin gidana da minbarina wani dausayi ne daga cikin dausayin aljanna ''.
  Sannan bayan sallan sai ya ziyarci kabarin annabi (s a w) da kuma kabari guda biyu na sahabbansa Abubakar da Umar (r a); sai ya tsaya yana mai fiskantar kabarin annabi (s a w) da ladabi da kuma kankan da sauti; sannan ya yi sallama a gare shi (yabo da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) yana mai cewa:

 (( السلام عليكَ ورحمة الله وبركاته ))
 Ma'ana: " Aminci ya kara tabbata a gare ka da rahamar Allah da kuma albarkokinsa "; saboda abin da ke cikin sunan na Abu Dawood da sanadi ingancecce daga Abu Hurairata (r a ) ya ce: manzon Allah (s a w) ya ce:

 (( ما من أحدٍ يُسلِّم عليَّ إلا ردَّ الله عليَّ رُوحي حتى أَرُدَّ عليه السلام ))
 Ma'ana: " Babu wani mutum guda da zai min sallama face Allah ya dawo min da raina don na amsa masa sallaman ".

  Inda mai ziyaran zai ce – a cikin sallaman da zai yi masan - :

  (( السلام عليك يا نبيَّ الله، السلام عليك يا خِيرَة الله مِن خلقه، السلام عليك يا سيِّدَ المرسلين وإمامَ المتقين، أشهد أنَّك قد بلَّغت الرسالةَ، ونَصحتَ الأُمةَ، وجاهدتَ في الله حق جهاده ))
 To da ba laifi; saboda wannan dukansa yana cikin sifofinsa (s a w).

 Ma'anan sallaman shi ne: " Ya annabin Allah! Aminci ya kara tabbata a gare ka, aminci ya kara tabbata akanka ya kai zabebben Allah cikin halittunsa, aminci ya kara tabbata akanka ya shugaban manzanni kuma jagoran masu takawa, na shaida cewa lallai ka isar da manzanci, kuma ka sauke amana, ka yi nasiha wa wannan al'ummar, sannan ka yi jihadi iyaka jihadi don daukaka addinin Allah ".
  Sannan kuma sai ya yi masa salati ya kuma yi masa addu'a saboda abin da ya tabbata a cikin wannan shari'ar na shar'anta gamewa tsakanin salati da sallama a gare shi (s a w) aiki da fadinsa madaukaki:

 ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ الأحزاب: ٥٦
 Ma'ana: " Ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati akansa (neman Karin yabo a gare shi cikin mala'iku) kuma ku masa sallama (neman karin aminci) ",
 Sannan sai ya yi sallama wa Abubakar da Umar (r a) ya kuma yi musu addu'a yana mai neman Karin yarda a gare su. (Abdullahi) Ibnu Umar (r a) ya kasance ya yi idan ya yi sallama wa manzo (s a w) da kuma abokansa biyu baya karawa – a mafi rinjayen lokaci – akan fadinsa:

 (( السلام عليك يا رسول الله، السلام عليك يا أبا بكرٍ، السلام عليك يا أبَتَاه ))
 Ma'ana: " aminci ya kara tabbata akanka ya ma'aikin Allah, aminci ya kara tabbata akanka ya Aba bakrin, aminci ya kara tabbata akanka ya babana! " sannan sai ya juya.
  Wannan ziyarar abin sani kawai an shar'anta ta ne cikin hakkin maza a kebe (kawai), Amma mata kam ba su da daman ziyartan wani abu na kaburbura; kamar yadda ya tabbata daga annabi (s a w) ..

(( لعن زوَّرات القبور مِن النساء، والمتخِذين عليها المساجد، والسُّرُج ))
Ma'ana: " lallai shi ya la'anci masu zuwa ziyartan kabari daga mata, da kuma masu rikansu masallaci (wato: masu yin salla a makabartai) da kuma sa fitillu ".
  Amma nufan madina (wato: tafowa zuwa gare ta daga wani gari) don yin salla a masallacim manzo (s a w) da kuma yin addu'a a cikinsa da makamancin haka na daga abubuwan da aka shar'anta yin su a cikin kowani masallatai = to wannan kam an shar'anta shi ne ga kowa (maza da mata); saboda abin da ya gabata na hadisai.

 An kuma sunnanta wa mai ziyaran da ya rinka sallatan salloli biyar a masallacin manzo (s a w), kuma ya yawaita zikiri da addu'a da sallan nafila a cikinsa yana mai ribatan wannan ganimar; saboda abin da ke cikin haka na lada mai yawa, kuma an so ya yawaita sallan nafila a RAUDHA MADAUKAKIYA saboda abin da ya gabata na inganceccen hadisi kan falalanta; wadda shi ne fadin annabi (s a w):

(( ما بين بيتي ومنبري روضةٌ من رياض الجنة ))
 Amma sallan farilla kam to ya dace ga mai ziyara da waninsa ya wuce ta (wato: ya gabaci raudhar) ya kuma kiyaye sahun farko ta ko yaya ya samu dama, koda kuwa cikin karin da ke ta alkibla ne; saboda abin da ya zo na hadisai ingantattu daga annabi (s a w) na zaburarwa da kwadaitarwa kan sahun farko; kamar fadinsa (s a w):

 (( لو يعلم الناس ما في النداء والصفِّ الأوَّل، ثم لم يجدوا إلا أنْ يستَهِمُوا عليه لاستَهَمُوا ))
 Ma'ana: " Da mutane sun san abin da ke cikin kiran salla (ladanci) da kuma sahun farko (na lada) sannan ba su samu ba sai dai su yi kuri'a akansa da sun yi kuri'ar " (Bukhari da Muslim) sun yi ittifaki akansa, da kuma kamar fadinsa ga sahabbansa:

 (( تقدَّموا فائتموا بي وليأْتمَّ بكم مَنْ بعدَكم، ولا يزال الرَّجُلُ يتأخر عن الصلاة حتى يُؤَخِّرَه الله ))
 Ma'ana: " Ku gabato don ku yi koyi da ni, wadanda su ke bayanku su yi koyi da ku; mutum ba zai gushe ba yana jinkiri ga (zuwa) salla face Allah ya jinkirtar da shi ", Muslim ne ya fitar da shi, Abu Dawood kuma ya fitar daga A'ishatu (r a) da sanadi mai kyau lallai annabi (s a w) ya ce:

 (( لا يزال الرجل يتأخَّر عن الصفِّ المقدَّم حتى يُؤخِّرَه الله في النار ))
 Ma'ana: " Mutum ba zai gushe ba yana jinkiri ga sahu na gaba face Allah ya jinkirtar da shi a cikin wuta ".
Kuma ya tabbata daga gare shi (s a w) lallai shi ya ce ma sahabbansa:

 (( آلا تصُفُّون كما تصُفُّ الملائكةُ عند ربِّها! قالوا: يا رسول الله! وكيف تصُفّ الملائكة عند ربِّها؟ قال يُتمُِّون الصفوفَ الأولى، ويتراصون ))
 Ma'ana: " Shin ba za kuna yin sahu ba kamar yadda mala'iku ke yin sahu a wajen ubangijinsu? Sai su ka ce: Ya ma'aikin Allah! Ta yaya mala'iku ke yi sahu a wajen ubangijinsu? Sai ya ce: suna ciccika sahu –sahun farko kuma suna hadewa sashinsu zuwa sashi a cikin sahu ", Muslim ne ya ruwaito shi.
Hadisai da su ke dauke da wannan ma'anan suna da yawa; kuma (hukuncinsu) ya game masallacinsa (s a w) da waninsa, kafin kara shi da bayan karin.
  Kuma ya inganta daga annabi (s a w) lallai shi ya kasance ya kan kwadaitar da sahabbansa kan: damanta sahu, kuma sananne ne lallai daman sahu a tsohon masallacinsa (kafin kare – kare da bayansa) ya fita daga cikin (kewayen) rauda; hakan sai ya sanar da cewa: damuwa da sahun farko-farko, da kuma dama-daman sahu, shi ne abin gabatarwa (da fifitawa) akan damuwa da raudha madaukakiya (a cikin farilla kawai), kuma lallai kiyaye su, su biyun shi ya fi cancanta fiye da kiyaye yin salla a raudha (a farilla). wannan kuma a bayyane ya ke a fili ga wadda ya yi nazari da tunani kan hadisan da su ka zo a wannan babin. Allah shi ne mai datarwa.

  Baya halatta ga wani mutum ya shafi dakin (da manzon Allah -s a w- ya ke kwance; dakin A'ishatu -r a- ) ko ya sunbance shi, ko ya rinka kewaya shi (dawafi); saboda hakan ba a samo mana shi daga magabaata na kwarai cewa suna yi ba, kai hakan bidi'a ne abun ki, kuma baya halatta ga wani mutum ya roki manzo (s a w) biyan bukata, ko yaye wani bakin ciki, ko warkar da wani maras lafiya ko makamancin haka; saboda hakan dukkansa ba a nemansa sai daga Allah mai tsarki. nemansa kuma daga mamata shirka ne da Allah kuma bautan waninsa ne; shi kuma addinin musulunci ya ginu ne kan ginshikai biyu (tushe biyu):
Na farkonsu: Kar ayi bauta sai ga Allah shi kadai,
Na biyun kuma: Kar ayi bautan sai da abin da manzo (s a w) ya shar'anta; wannan kuma shi ne ma'anan: SHAHADATU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, WA ANNA MUHAMMADAR RASULUL LAH, (ma'ana: shaidawa ba wadda za a bauta masa sai Allah -don shi kadai ya cancanci hakan-, kuma lallai – annabi –Muhammadu- s a w manzon Allah ne), haka kuma baya halatta ga wani mutum (ko aljani) ya nemi ceto daga wajen manzo (s a w); saboda shi (ceton) mallakan Allah mai tsarki ne (shi kadai); don haka ba a nema sai daga wajensa; kamar yadda madaukaki ya ce:

  ﮗﮘ [الزمر: ٤٤]
 Ma'ana: " Ka ce: ceton gaba daya na Allah ne ".
Amma ka samu ka ce:

 (اللهم شفِّع فِيَّ نبيَّك، اللهم شفِّع فِيَّ ملائكتَك وعبادَك المؤمنين، اللهم شفِّع فِيَّ أفراطي ونحو ذلك)
 Ma'ana: " Ya Allah ka karbi ceton annabinka a kaina, ya Allah ka karbi ceton mala'ikunka da bayinka muminai a kaina, ya Allah ka karbi ceton 'ya'yana da su ka rigaye ni (mutuwa) a kaina, da makamantan haka. Amma matattu kam ba a neman komai a wajensu; ceto ne ko waninsa, kuma daidai ne sun kasance annabawa ne ko wassunsu; saboda hakan ba a shar'anta shi ba, kuma saboda macecce aikinsa ya yanke sai wadda shari'a ta toge; ( ya zo) cikin sahihu Muslim daga Abu Hurairata (r a) ya ce:

 (( إذا مات ابنُ آدم انْقَطع عملُه إلا من ثلاثٍ: صدقةٍ جاريةٍ أو علمٍ يُنتفَع به، أو ولدٍ صالحٍ يدعو لَه ))
 Ma'ana: " Idan 'dan Adam ya mutu aikinsa ya yanke sai guda uku: sadaka da ta ke gudana, ko kuma ilimi da ake amfana da shi, ko kuma da na gari da ya ke masa addu'a ". Kuma abin sani kawai ya hallata ne a nemi ceto daga annabi (s a w) a lokacin da ya ke raye da kuma ranar kiyama ne = saboda yana da iko akan hakan; wato yana da ikon isa don ya roki ubangijinsa ga mai neman. amma a (rayuwar) duniya kam to sananne ne hakan ba wai ya kebanta da shi kadai ba ne, kai haka ya game shi da kuma waninsa; domin ya halatta ga musulmi ya ce wa dan'uwansa:

 (( اشفِع لِي إلى ربِّي في كذا وكذا بمعنى: ادع الله لي ))
 Ma'ana: " Ka nema min ceton ubangijina cikin kaza da kaza; ma'ana: ka roka min Allah! ", ya kuma halatta ga wadda aka gaya masa hakan ya roki Allan ya kuma nemi ceton wa 'dan'uwansa; idan wannan abin neman yana daga cikin abin da Allah ya halatta nemansa. Amma ranar (tashin) kiyama wani mutum ba shi da damar ceto har sai bayan Allah mai tsarki ya masa izini; kamar yadda Allah madaukaki ya ce:

[البقرة: ٢٥٥ ]
 Ma'ana: " Babu wadda zai yi ceto a wajensa face da izininsa ". Amma halin mutuwa kam to wannan hali ne kebancecce, baya halatta a riskar da shi (ayi kiyasinsa) da halin mutum kafin mutuwa, ko kuma da halinsa bayan tayar da mutane (daga kabari) da kuma fitar da su; saboda aikin mutum (a wannan lokacin) ya yanke, kuma ya kaura da aikinsa, sai dai abin da shari'a ta toge; kuma neman ceton matattu baya cikin abin da shari'ar ta toge; don haka baya halatta a riskar da shi da haka. Kuma ba makawa lallai annabi (s a w) bayan rasuwarsa yana raye a cikin kabarinsa rayuwa irin ta barzakh; wadda kuma ta fi rayuwar SHAHIDAI cika; sai dai ita (wannan rayuwar) ba irin rayuwarsa ba ne ta kafin rasuwarsa, kuma ba irin rayuwar da zai yi ba ne a yinin kiyama, kai dai! rayuwa ce da ba wadda ya san hakikaninta da yanayinta sai Allah mai tsarki; shi yasa ma fadinsa (a s) ya gabata cikin hadisi madaukaki:

 (( ما من أحدٍ يُسلِّم عليَّ إلا ردَّ اللهُ عليَّ رُوحِي حتى أَرُدَّ عليه السلامَ ))
 Ma'ana: " Babu wani mutum guda da zai min sallama face Allah ya dawo min da raina don na amsa masa sallaman ", sai haka ya nuna cewa shi (manzo s a w) macecce ne, kuma ransa ya rabu da jikinsa, sai dai akan dawo da shi zuwa gare shi lokacin da aka yi masa sallama, su kuma nassoshi (dalilai) da su ke nuni kan rasuwarsa na daga alqur'ani da sunna sanannu ne, kuma al'amari ne da ma'abuta ilimi su ka yi ittafaki akansa sai dai kuma hakan baya hana rayuwarsa ta barzakh, kamar yadda mutuwan shahidai bai hana rayuwarsu ta barzakhun da aka ambata cikin fadinsa madaukaki ba:

  [آل عمران: ١٦٩] Ma'ana: " Kada ku yi zaton wadanda aka kashe su don daukaka kalmar Allah matattu ne, A'a rayayyu ne, a wajen ubangijinsu ake azurta su ".
 Abin sani kawai mun shumfuda Magana ne kan wannan mas'alar saboda bukatan hakan; sakamakon yawa-yawan wadanda su ke kawo shubuha a wannan babin, sannan su kira (mutane) zuwa ga shirka da kuma bautan matattu koma bayan Allah. Muna kuma rokon Allah ga mu da sauran musulmai kubuta (da kariya) daga dukkan abin da ya saba wa shari'arsa (Allah). Allah shi ne mafi sani.

 Amma abinda sashin masu ziyara ke aikatawa na daga sauti a wajen kabarinsa (s a w), da kuma dogon tsayuwa a can to wannan shima ya saba wa abinda aka shar'anta; saboda Allah mai tsarki ya hana al'umma ta daga sauti sama da sautin wannan annabin (s a w) da kuma bayyanar masa magana kamar bayyanawan sashinsu ga sashi, ya kuma kwadaitar da su kan runtse (kankanta) sauti a wajensa cikin fadinsa madaukaki:

 ﭽ ﮠ  ﮡ  ﮢ  ﮣ  ﮤ  ﮥ   ﮦ  ﮧ  ﮨ  ﮩ    ﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ               ﮮ   ﮯ  ﮰ  ﮱ  ﯓ  ﯔ  ﯕ    ﯖ  ﯗ  ﯘ  ﯙ   ﯚ  ﯛ  ﯜ  ﯝ  ﯞ  ﯟ  ﯠ  ﯡ  ﯢ   ﯣ  ﯤﯥ  ﯦ   ﯧ           ﭼ

 Ma'ana: " Ya ku wadanda su ka yi imani kada ku daga sautinku sama da sautin wannan annabin, kuma kada ku bayyana masa magana kamar yadda sashinku ke bayyana wa sashi; sai aikinku ya rushe alhali ku ba ku sani ba *. Lallai wadanda su ke runtse (kankanta) sautinsa a wajen manzon Allah to wadannan sun e wadanda Allah ya jarrabi zucciyarsu don tsoronsa (takawa) suna da wata irin gafara da wani irin lada mai girma ", kuma saboda dogon tsayuwa a wajen kabarinsa (s a w) da kuma yawaita maimaita sallama (a gare shi) zai kai zuwa ga cunkoson da yawaita ihu da kuma daguwan sautuka a wajen kabarinsa (s a w); wannan kuma ya saba wa abin da Allah ya shar'anta shi ga musulmai a cikin wadannan ayoyi da hukuncinsu yak e tabbace (ba a shafe su ba), shi kuwa (s a w) abun girmamawa ne yana raye ko yana mace; don haka baya dacewa ga mumini ya aikata – a wajen kabarinsa – abin da ya saba ma ladabin shari'a.

  Haka kuma abinda wassu masu ziyara da wassunsu su ke yi na kirdadon addu'a a wajen kabarinsa (s a w) yana mai fiskantan kabarin (ya sa shi a gaba a matsayin algibla) ya daga hanunsa yana addu'a; to wannan dukkansa ya saba wa abin da magabata na kwarai ke kansa na daga sahabban manzon Allah (s a w) da wadanda su ka bi su da kyautatawa, A'a haka din na daga cikin bidi'o'i da aka kirkiro; kuma hakika annabi (s a w) ya ce:

 (( عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين المهديين من بعدي تمسكوا بها وعضُّوا عليها بالنواجذ، وإياكم ومحدثات الأمور؛ فإنَّ كلَّ محدثةٍ بدعةٌ، وكلَّ بدعةٍ ضلالةٌ ))
 Ma'ana: " Ina horonku (da riko) da sunnata da kuma sunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa a bayana, ku yi riko da su, kuma ku kama su da fikoki, kuma ina gargadanku kan kirkirarrun al'amura; saboda kowani kirkirarre bidi'a ne, kuma kowani bidi'a bata ne ", Abu Dawu'ud da Nasa'i sun fitar da shi da sanadi mai kyau. Kuma (s a w) ya ce:

 (( من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو ردٌّ ))
 Ma'ana: " Wadda ya kirkiro (wani abu) a cikin wannan al'amarinmu (addininmu) wadda ba ya cikinsa to an mayar masa ", Bukhari da Muslim su ka fitar da shi, a cikin wata riwayar Muslim:

 (( من عمِل عملاً ليس عليه أمرنا فهو ردٌّ ))
 Ma'ana: " Wadda ya aikata wani aiki wadda al'amarinmu (addininmu) ba a kansa ya ke ba to an mayar masa ". Kuma Aliyu bnul Husain (ZAINUL ABIDINA) (r anhuma) ya ga wani mutum na addu'a a wajen kabarin annabi (s a w) sai ya hana shi hakan kuma ya ce: Shin ba zan baka labarin hadisin da na ji shi daga babana (Husain r a) daga kakana (Aliyu bn Abiy Dalib r a) daga manzon Allah (s a w) lallai shi ya ce:

 (( لا تتخذوا قبري عيداً، ولا بيوتكم قبورًا؛ وصلُّوا عليَّ؛ فإنَّ تسليكم يبلغني أينما كنتم ))
 Ma'ana: " Kada ku riki kabarina wajen kai komo, haka kuma (kada ku riki) gidajenku kuma (a matsayin) kaburbura (da ba a salla a cikinsu); kuma ku rinka min salati; saboda sallamarku zai iso ni a duk inda ku ke ", ALHAAFIZ MUHAMMAD BN ABDILWAHID ALMAKDASIY ne ya fitar da shi a cikin littafinsa ALMUKHTARAH.

  Haka kuma abin da wassu masu ziyara su ke yi a wajen yi masa sallaman (s a w) na dora (hanun) dama kan hagu a saman kirji ko kuma kasansa kamar yanayin mai sallah; shi ma wannan yanayin  ba ya halatta (a aikata shi) a wajen yi masa sallama (s a w) haka kuma wajen sallama ga waninsa daga cikin masu mulki da jagorori da wassunsu; saboda kasancewanta yanayi ne na kaskanci da kankan da kai da kuma ibada da bata dacewa sai ga Allah; kamar yadda ALHAFIZ IBNU HAJAR (r l) a cikin ALFAT'HU ya hakaito daga maluma, al'amarin cikin haka a fili kuma a sarari ya ke ga wadda ya yi tunanin matsayin kuma ya zama manufarsa shi ne bin magabata na kwarai, Amma wadda TA'ASSUBANCI da son zuciya da kuma bi irin na makaho (ga wassu maluman bidi'a) tare da munana zato ga masu kira zuwa ga shiriyar magabata na kwarai to al'amarinsa yana ga Allah, muna kuma rokon Allah ga mu da shi = shiriya da datarwa wajen fifita gaskiya akan abin da ke waninsa, lallai shi (Allah) mai tsarki shi ne mafi alkhairin wadda ake roko.

  Haka kuma abinda wassu mutane ke aikata shi na fiskantar wannan kabari madaukaki daga nesa da kuma mommotsa lebba biyu da sallama ko addu'a; duk wannan shi ma na jinsin abin da ke kafinsa na kirkirarrun abubuwa; kuma baya dacewa (halatta) ga wani musulmi ya kirkiri wani abu a cikin addininsa da Allah bai yi izini da shi ba; sannan shi – da wannan aikin nasa – ya fi kusa da yi masa JAFA'I (s a w) JIBINTARSA DA KUMA GARAUTAKA; kuma hakika AL'IMAM MALIK (r l) ya yi inkarin (tsawatar) akan wannan aikin da makamantansa, ya kuma ce:

 (( لن يصلح آخر هذه الأمة إلا ما أصلح أولها ))
 Ma'ana: " Ba abin da zai gyara Karshen wannan al'ummar sai abin da ya gyara farkonta  ", kuma sananne ne lallai shi abin day a gayra farkon wannan al'ummar shi ne tafiyarsu kan turban annabi (s a w) da kuma khalifofinsa shiryayyu, da kuma sahabbansa yardaddu da kuma wadanda su ka bi su da kyautatawa, kuma babu abin da zai gyara karshen wannan al'ummar sai rikonsu da hakan da kuma tafiyarsu akansa. Allah ya datar da musulmai zuwa ga abin da tsiransu da rabautarsu da kuma izzarsu a duniya da lahira ya ke cikinsa; lallai shi mai kyauta ne mai karimci.


FADAKARWA: Ziyaran kabarin annabi (s a w) ba wajibi ko sharadi ne a aikin hajji ba, kamar yadda wassu marasa ilimi da makamantansu (kamar ma'abuta son zuciya) su ke zato, A'a ita dai (ziyarar) mustahabbi ce ga kan wanda ya ziyarci masallacin manzo (s a w) ko kuma ya kasance a kusa da shi (a madina). Amma na nesa da madina ba shi da damar daure sirdinsa (da niko garinsa don tahowa) da nufin ziyarar kabari, sai dai an sunnata masa daura sirdinsa (bulaguro) da nufin ziyartar wannan masallaci mai girman; in ya iso mata kuma (Madina) sai ya ziyarci kabari madaukaki da kuma kabarin sahabbai biyun (Abubakar da Umar – r a – kuma ziyarar kabarinsa (a s) da kabarin abokansa (r a) ya samu shiga ne (a matsayin) mabiyin ziyarar masallacinsa (s a w) (wato: ziyarar masallacinsa shi ne asali,); haka kuma ya kasance ne saboda abin day a tabbata a cikin (littatafa biyu) ingantattu (Bukhari da Muslim) lallai annabi (s a w) ya ce:

 (( لا تُشد الرِّحالُ إلا إلى ثلاثة مساجد؛ المسجدِ الحرام، ومسجدي هذا، والمسجدِ الأقصى ))
 Ma'ana: " Ba'a daura sirdi (a kuma kimtsa tafiya da nufin lada) Sai in zuwa ga masallatai ne guda uku:
1) Masallaci mai alfarma(makkah)
2) Masallacina wannan.
3) da kuma masallaci mai nisa (da ke Kudus) " to da daura sirdi (da shiga mota ko jirgi) da nufin zuwa kabarinsa (a s) ko kabarin waninsa shari'a ne to da ya nuna wa al'umma hakan kuma day a shiryad da su zuwa gare zuwa ga falalansa; saboda shi ne ya fi dukkan mutane yin nasiha (ga mutane), kuma shi ne ya fi su ilimin Allah (da abin da Allah ya ke so) sannan shi ya fi su tsananin tsoronsa, kuma ya isar (da manzanci bai boye ba) isarwa mabayyaniya, ya kuma nuna wa al'ummarsa dukkan alkhairi, sannan ya hane ta daga dukkan sharri; to ta yaya kuma bayan ya yi gargadi kan daura sirda (da bulaguro) in ba ya zuwa wadannan masallaci guda ukun ba!!! Ya kuma ce:

 (( لا تتخذوا قبري عيدا، ولا بيوتكم قبورا؛ وصلوا عليَّ فإنَّ صلاتكم تبلغني حيث كنتم  ))
 Ma'ana: " Kada ku riki kabarina wajen kai komo, haka kuma (kada ku riki) gidajenku kuma (a matsayin) kaburbura (da ba a salla a cikinsu); kuma ku rinka min salati; saboda salatinku zai iso ni a duk inda ku ke ",Shi kuma maganan shari'ancin daura sirdi (yin bulaguro) zuwa ga kabarinsa (s a w) zai kai ya zuwa rikonsa idi (gun kai komo (da ya hana cikin wannan hadisin), da kuma aukuwan abin da annabin (s a w) ya ji tsoron faruwansa na wuce – gona – da – iri da wuce iyaka wajen yabonsa, kamar yadda mafi yawan mutane su ka auka cikin hakan saboda sun kudurta shari'ancin bulaguro don ziyartar kabarinsa (a s).

 Amma abinda ake rawaitowa na hadisai a wannan babin wadanda wadda ya fadi shari'ancin yin bulaguro ya zuwa kabarinsa (a s) su ke kafa hujja da su = to hadisai ne da sanadinsu mai rauni ne, kai na karya ne ma, kamar yadda wadanda ake musu lakabi da ALHUFFAZ (wato: bajamayen maluma a ilimin hadisin manzo – s a w - ) su ka fadakar kan haka; kamar: ADDARAKUDUNIY, da ALBAIHAKIY da ALHAFIZ IBNU HAJAR da WASSUNSU; don haka baya halatta a gwara su da hadisai ingantattu da su ke nuni kan haramcin bulaguron in bag a masallatai ukun ba.

 Ya kai makaranci! Ga wani abu wadannan hadisan karyan (rubabbun hadisai) da ke wannan babin domin ka sansu kuma ka nisanci ruduwa da su:

 Na farko:

(( من حجّ ولم يزرني فقد جَفانِي ))
  Ma'ana: " Duk wanda ya yi aikin hajji, bai kuma ziyarce ni ba; To ya min wauta kuma ya gajarta wajen ban hakkina ''.
 Na biyu:

(( من زارني بعد مماتي فكأنما زارني في حياتِي ))
 Ma'ana: '' Duk wadda ya ziyarce ni bayan mutuwa ta to kamar ya ziyarce ni ne a rayuwa ta ''.
 Na uku:

  (( من زارني وزار أبي إبراهيم في عامٍ واحدٍ ضمِنْت له على الله الجنة ))
 Ma'ana: '' Duk wadda ya ziyarce ni, kuma ya ziyarci Babana Ibrahim a shekara 'daya; To na masa lamunin Aljanna a kan Allah ''.
 Na hudu:

 (( من زار قبري وجبت له شفاعتي ))
Ma'ana: '' Wanda ya ziyarci kabarina cetona ya wajaba (tabbata) masa ''.

 Wadannan hadisan da makamantansu ba wani abu da ya tabbata daga cikinsu daga annabi (s a w); ALHAFIZ IBNU HAJAR ya fada a cikin ATTALKHIIS (Attalkhiis al habiir) – bayan ya ambaci mafi yawan wadannan riwayoyin -: " Hanyoyin wannan hadisin dukkansu masu rauni ne, ALHAFIZUL UKAILIY ya ce: Ba wani abu da ya inganta a wannan babin, SHEKHUL ISLAM IBNU TAIMIYYA (r l) KUMA ya yi yanke cewa wadannan hadisan dukkansu: MAUDU'AI NE (na karya ne), kuma dai (Ibnu Taimiyya) ya ishe ka wajen ilimi da hadda da kuma lege – liken karatu. Kuma da wani abu daga cikinsu ya inganta to da sahabbai (r a) sun riga mutane aiki da shi, da kuma bayanin haka ga al'umma, da kiransu zuwa gare shi; saboda su ne mafi alkhairin mutane bayan annabawa, kuma su su ka fi su (mutane) sanin dokoki da iyakokin Allah da kuma abin da ya shar'anta a bayinsa, kuma su su ka fi yin nasiha ga Allah da kuma halittunsa; to yayin da ba a ciro wani abu daga gare su ba; hakan sai ya yi nuni cewa lallai hakan (nufan kabari da ziyara daga wani gari) ba shari'a ba ne; to kai da wani abu ma ya inganta daga cikinsu (hadisai) to da wajibi ne a dauki hakan da cewa na nuni ne akan ziyara ta shari'a wacce babu bulaguro a cikinta don nufan kabari; don (neman) yin jam'i (hade) tsakanin hadisan. ALLAH SUBHANAHU WA TA'ALA shi ne mafi sani ".


Alhamdu lil lah
07 / 11 / 1429h = 06 / 11 / 2008m.


FASALI: CIKIN MUSTAHABBANCIN ZIYARTAR MASALLACIN QUBA'A DA KUMA (MAKABARTAN) BAQI'I:
Kuma an so ga mutmumin da ya ziyarci Madina ya ziyarci masallacin Quba'a ya kuma yi salla a cikinsa; saboda abin day a zo cikin (littatafa) ingantattu guda biyu (sahihul Bukhari da sahihu Muslim) daga hadisin (Abdullahi) bn Umar (r a); lallai ya ce:

 (( كان النبيُّ r يزور مسجد قباء راكباً وماشياً، ويصلِّي فيه ركعتين ))
 Ma'ana: " Annabi (s a w) ya kasance yak an ziyarci masallacin Quba'a akan abin hawa (a wani lokaci, a wani lokacin kuma) da kafa; sa an nan kuma ya sallaci raka'a biyu a cikinsa ", (ya zo) kuma daga Sahal bn Hunaif (r a) lallai ya ce; Manzon Allah (s a w) ya ce:

 (( من تطهَّر في بيته ثم أتى مسجد قباء فصلَّى فيه صلاةً كان له كأجر عمرةٍ ))
  Ma'ana: " Duk wadda ya tsarkaka (alwala) a gidansa sa an nan ya zo masallacin Quba'a; sai kuma ya sallaci wata salla a cikinsa to yana da kamar ladan umra ".

 Kuma an sunnanta masa ziyartan kabarurrukan Baqi'I, da kabarurrukan wadanda su ka yi shahada (a Uhud) da kabarin Hamza (r a); saboda annabi (s a w) ya kasance yak an ziyarce su ya kuma yi musu addu'a, kuma saboda fadinsa (s a w):

 (( زُورُوا القبورَ؛ فإنها تذكِّرُكُمُ الآخرةَ ))
Ma'ana: " Ku ziyarci kaburbura; domin suna tuna mu ku Lahira " Muslim ne ya ruwaito shi. Kuma annabi (s a w) ya kasance yana ilmantar da sahabbansa idan su ka ziyarci kabarurruka da su ce:

 (( السلام عليكم أهلَ الديار من المؤمنين والمسلمين، وإنَّا إنْ شاء الله بِكُم لاحقون، أسأل اللهَ لنا ولكم العافيةَ ))

Ma'ana: " Aminci ya tabbata a kan ku ya ku ma'abotan wadannan gidaje na mu'uminai da musulmai, Kuma muma – In Allah ya so – Ma su haduwa ne da ku, muna roka mana Allah lafiya (kariya daga azaba …) – mu da ku " Muslim ne ya ruwaito shi daga hadisin Sulaiman bn Buraidata daga Babansa. Haka kuma tirmiziy ya fitar daga (Abdullahi) bn Abbas (r a) ya ce: Annabi (s a w) ya wuce kaburburan Madina; sai ya fiskance su da fiskarsa sa an nan ya ce:

 (( السلام عليكم يا أهل القبور، يغفر الله لنا ولكم، أنتم سلفُنا ونحن بالأثر ))
 Ma'ana: " Aminci ya tabbat a gare ku yak u ma'abuta kaburbura! Allah ya mana gafara mu da ku, ku kuka rigaye mu, mu kuma muna tafe ".

 Daga wadannan hadisan za a san cewa lallai ita ziyara ta shari'a ya zuwa kaburbura = manufarta shi ne: tuna lahira (wadda hakan sababi ne na gyara aiki) da kuma kyautata wa matattu da yi musu addu'a tare da nema musu rahama.
 Amma ziyararsu da su ke yi da nufin roko (n Allah) a wajen Kaburbura, ko kuma tsayuwa a wajen tare da jimawa, ko kuma rokonsu (Mamatan) biyan bukatu, ko warkad da marasa Lafiya, ko kuma rokon Allah da su, ko da matsayinsu, ko makamancin haka; =To (duk) wannan ziyara ce ta bidi'a, abun kuma kyama, Allah bai shar'anta ta ba, haka manzonsa, sannan magabata na kwarai (Allah ya yarda da su) ba su aikata ta ba, Kai ta na cikin HUJUR (yawaita Magana kan abin da bai dace da shari'a ba) da Manzon Allah ya yi hani akai cikin fadinsa:

[ زوروا القبور ولا تقولوا: هُجْراً]
 Ma'ana: " Ku ziyarci kabari, amma kada ku fadi abin da ba daidai ba (kamar abubuwan da su ka gabata).

 Wadannan abubuwan da aka ambata (a baya) Duk kan su sun hadu wajen kasancewarsu bidi'a amma martabobinsu da matsayinsu sun banbanta; saboda sashensu: Bidi'a ne ba shirka ba; kamar rokon Allah mai girma da daukaka wajen kabari, da kuma rokonsa da hakkin mamaci ko matsayinsa … da makamancin haka, Yayin da sashen su kuma suna cikin (nau'in) babban shirka; kamar rokon mamata da kuma neman agajinsa … da makamantan haka.
 Kuma hakika bayanin wannan dalla – dalla ya gabata cikin abin da ya gabata; don haka ka fadaka! Kuma ka kiyaye!! Sannan ka roki ubangijinka datarwa da shiriya zuwa ga gaskiya!!!; domin shi (Allah) mai tsarki shi ne mai datarwa kuma mai shiryarwa, babu wani abun bauta da cancanta waninsa, kuma babu ubangiji sai shi.

  Wannan shine karshen abin da mu ka yi nufin IMLA'INSA (shiftarsa), godiya da yabo sun tabbata ga Allah a farko da karshe.

 Salati da sallama kuma su kara tabbata ga bawansa kuma manzonsa kuma zabebbensa daga cikin halittunsa Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa, da wadda ya bi su da kyautatawa zuwa ranar sakamako.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...