2015/03/28

MAS'ALOLI MASU ALAQA DA QUR'ANI DA TAFSIRINSA, DA TARJAMARSA

GABATAR DA TARJAMAR MA'ANONIN ALQUR'ANI MAI GIRMA


SHIMFIXA
Alqur'ani mai girma maganar Allah ne maxaukaki da ya sauqar da shi (alqur'ani), da harrufansa da ma'anoninsa, zuwa ga manzonsa annabi Muhammadu (s.a.w) don ya zama rahama ga talikai, yana bushara, yana gargaxi, yana kuma qira zuwa ga Allah, da izininSa, kuma fitila ne mai haskakawa.
A NAN GA BAYANI TAQAITACCE, AKAN ALQUR'ANI MAI DARAJA, DA KUMA SAQON DA YA QUNSA:
GAMAMMEN BAYANI KAN ALQUR'ANI MAI GIRMA

NA FARKO: BAYANI KAN ALQUR'ANI MAI GIRMA, DA AMBATO SUNAYENSA, DA SIFFOFINSA:
Alqur'ani mai girma zance ne na Allah maxaukaki da ya saukar da shi ga manzonsa annabi Muhammadu (s.a.w), wanda kuma aka yi masa wahayinsa da lafazinsa da ma'anoninsa, sannan aka rubuce shi a jikin takardu, riwayarsa kuma aka  karvo ta ta hanyoyin mutane dayawa (mutawaatir), ana kuma yin bauta (a samu lada) da yin karatunsa.
            Kuma lallai Allah mabuwayi da xaukaka shine da kansa ya sanya ma wahayin da ya saukar da shi ga manzonsa annabi Muhammadu (s.a.w) suna: Alqur'ani (ma'ana: littafi abun karantawa); Allah ta'alah yana cewa:
(إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ تَنْزِيلاً) [الإنسان: 23].
Ma'ana: "Lallai mune muka sassauqar da alqur'ani akanka sas-sauqarwa" [Insaan: 23]. Kuma ya sanya masa wannan sunan ne (alqur'ani) saboda yana daga sha'anin wannan littafin ayi ta karanta shi (qira'a) da tilawa, kada a qaurace masa.
Kuma Allah ya sanya masa suna; al-kitaab (ma'ana: Alqur'ani abun rubutawa); Allah ta'alah yana cewa:
(إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ) [النساء: 105].
Ma'ana: "Lallai mune muka sauqar maka da wannan littafin da gaskiya" [Nisa'i: 105]. Saboda yana daga cikin sha'anin alqur'ani a rubuta shi, kada ayi ko-oho da shi (ko manta shi).
            Kuma lallai Allah ta'alah ya siffanta wannan alqur'ani da siffofi dayawa; Daga cikinsu; ya siffanta shi da; siffar littafi mai rarrabewa, da tunatarwa, shiriya, haske, waraka, littafi mai hikima, wa'azi, da wassun waxannan daga cikin siffofinsa da suke nuni kan: Girman alqur'ani, da kasantuwar saqon da ke xauke da shi cikakke.
            Ita kuma kalmar "mus-hafi" an ciro ta ne daga takardun da aka rubuta alqur'ani mai girma akansu. Kuma wannan kalma (ta, mus-hafi) sahabban annabi ne (s.a.w) suka qira alqur'ani da ita, don tayi nuni kan littafin da aka rubuta alqur'ani mai girma a takardunsa.
            Kuma lallai alqur'ani mai girma wahayi ne daga Allah ta'alah, wanda mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauqar da shi a zuciyar annabi Muhammadu (s.a.w), Allah maxaukaki yana cewa:
(وَإِنَّهُ لَتَنْزِيلُ رَبِّ الْعالَمِينَ، نَزَلَ بِهِ الرُّوحُ الْأَمِينُ، عَلى قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ الْمُنْذِرِينَ، بِلِسانٍ عَرَبِيٍّ مُبِينٍ) [الشعراء: 192-195].
Ma'ana: "Kuma lallai shi, saukakke ne daga Ubangijin talikai, wanda mala'ika -Jibrilu- amintacce ya sauqar da shi, a zuciyarka domin ka kasance daga cikin masu gargaxi. Da harshen larabci mabayyani" [Shu'ara'i: 192-195].       
Kuma lallai annabi Muhammadu (s.a.w) ba shi ne farkon fari a wannan lamarin ba; saboda dukkan 'yan'uwansa manzanni (a.s) mala'ika Jibrilu (a.s) ya kasance yana sauqar musu da wahayi daga Allah ta'alah. Kuma lallai Allah (s.w.t) ya kasance ya kan zavi wanda ya nufa don ya bashi wannan amanar mai girma, Allah yana cewa:
(اللَّهُ يَصْطَفِي مِنَ الْمَلائِكَةِ رُسُلاً وَمِنَ النَّاسِ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ بَصِيرٌ) [الحج: 75].
Ma'ana: "Lallai Allah yana zaven manzanni daga cikin mala'iku, haka kuma daga cikin mutane. Lallai Allah mai ji ne mai gani" [Hajji: 75].
Kuma Allah shine ya san wanda zai dace da matsayin manzanci, daga wanda ba zai dace da shi ba, saboda dukkan halittu shi ya samar da su, Allah yana cewa:
(وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشاءُ وَيَخْتارُ) [القصص: 68].
Ma'ana: "Kuma Ubangijinka yana halittar abinda ya nufa, ya kuma yi zavi" [Qasas: 68].

NA BIYU: SAUQAR ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Aqur'ani ya fara sauka ga manzon Allah (s.a.w) a ranar litinin, goma sha bakwai ga watan ramadhan (17/ Ramadhan) a shekarar miladiyyah ta 610, a cikin kogon Hirah, wanda shi kuma xaya ne daga cikin duwatsun garin Makkah mai daraja, a lokacin da mala'ika Jibrilu (a.s) ya sauqar masa da waxannan ayoyin:
(اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ، خَلَقَ الْإِنْسانَ مِنْ عَلَقٍ، اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ، الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ، عَلَّمَ الْإِنْسانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ) [القلم: 1-5].
Ma'ana: "Kayi karatu da sunan Ubangijinka da yayi halitta, Ya halicci mutum daga jini, Ka yi karatu da ubangijinka mai karamci, wanda ya sanar da alqalami, ya sanar da Mutum abinda bai sani ba" [Qalam: 1-5].
            Kuma waxannan ayoyin sune farkon abinda suka fara sauka ga manzon Allah (s.a.w).
Sai Annabi (s.a.w) ya koma wajen matarsa (iyalansa) da waxannan ayoyin zuciyarsa tana karkaxawa saboda kwar-jini, da kuma yadda ya tsorace wa kansa, ya kuma bada dukkan qissar ga: Uwar muminai Khadija 'yar Khuwailid (Allah ya qara yarda a gare ta) yace mata:
«لَقَدْ خَشِيتُ عَلَى نَفْسِي، فقَالَتْ لَهُ: كَلَّا أَبْشِرْ، فَوَ اللهِ، لَا يُخْزِيكَ اللهُ أَبَدًا، إِنَّكَ لَتَصِلُ الرَّحِمَ، وَتَصْدُقُ الْحَدِيثَ، وَتَحْمِلُ الْكَلَّ، وَتَقْرِي الضَّيْفَ، وَتُعِينُ عَلَى نَوَائِبِ الْحَقِّ، وَأخذَتْه إلى وَرَقَةَ بْن نَوْفَلِ وكان من ذوي الرأي والحكمة فقالت له خديجة: أَيْ عَمِّ، اسْمَعْ مِن ابْنِ أَخِيكَ، فلما أخبره رسول الله r خبر ما رآه، قَالَ لَهُ وَرَقَةُ بن نوفل: هَذَا النَّامُوسُ الَّذِي أُنْزِلَ عَلَى مُوسَى، يَا لَيْتَنِي فِيهَا جَذَعًا، يَا لَيْتَنِي أَكُونُ حَيًّا حِينَ يُخْرِجُكَ قَوْمُكَ، قَالَ رَسُولُ اللهِ r: أَوَ مُخْرِجِيَّ هُمْ؟ قَالَ وَرَقَةُ: نَعَمْ لَمْ يَأْتِ رَجُلٌ قَطُّ بِمَا جِئْتَ بِهِ إِلَّا عُودِيَ، وَإِنْ يُدْرِكْنِي يَوْمُكَ أَنْصُرْكَ نَصْرًا مُؤَزَّرًا». وتوفي ورقة بعد هذه المقابلة بوقت قصير.
Ma'ana: "Lallai ni na jiye wa kaina tsoro, Sai tace masa: A'a! kwantar da hankalinka, ina rantsuwa da Allah! Har abada Allah ba zai tozarta ka ba; saboda yadda ka ke sada zumunci, da yin gaskiya cikin zance, kuma kana xaukar nauyin gajiyayye, kana karrama baqo, sannan kana taimako kan abubuwan da suke faruwa da mutane na gaskiya. Sannan ta tafi da shi zuwa ga: Waraqah xan Naufal, wanda kuma xaya ne daga cikin mutane masu ilimi da hikima, Sai Khadija tace masa: Ya kai baffana! Ka saurari xan xan'uwanka! A yayin da Manzon Allah (s.a.w) ya bashi labarin duk abinda ya ga ni, Sai Waraqah xan Naufal yace: Wannan ai shine mala'ikan wahayi([1]) da ke zuwa ga: Annabi Musa. Da dai ace ina cikin qarfina! Da dai ace ina da raina; a lokacin da mutanenka za su fitar da kai? Sai Manzon Allah (s.a.w) yace: Shin fitar da ni za su yi Su xin?", Sai Waraqah yace masa: E, ai babu mutum xaya da ya zo da irin abinda ka zo da shi face anyi adawa ko gaba da shi".
Sai Waraqah bada jimawa ba; bayan wannan ganawar ya rasu.
Kuma alqur'ani mai girma ba dukkansa ne ko gabaxayansa ya sauka ga Manzon Allah (s.a.w) a lokaci xaya ba, savanin yadda littatafan da sauran annabawa (a.s) da suka rigayi annabinmu suka sauka, A'a! Shi alqur'ani ya yi ta sauka ne guntu-guntu a cikin tsawon shekaru ashirin da uku (23), Kuma "sura" cikakkiya tana sauka, ko kuma "ayoyi" daga cikin sura.
Hikimar sauqar da alqur'ani guntu-guntu (da kaxan da kaxan) ([2]) kuma Itace: Tabbatar da zuciyar annabi Muhammadu (s.a.w), da qara qarfafarsa, a duk lokacin da mala'ika ya sake sauqar masa da sabon wahayi, don ya kasance yafi samun qarin qarfin jiki da na hali a lokacin da yake fiskantar quren  da mushirkai da qaryatawarsu ga abinda aka saukar masa, tun a farkon turo shi a matsayin manzo daga Allah, Kuma Allah ta'alah yana cewa:
(وَقالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلا نُزِّلَ عَلَيْهِ الْقُرْآنُ جُمْلَةً واحِدَةً كَذلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤادَكَ وَرَتَّلْناهُ تَرْتِيلاً) [الفرقان: 32].
Ma'ana: "Kafirai suka ce: Me ya hana a sauqar masa da alqur'ani a dunqule? Mun yi haka ne, domin mu tabbatar da zuciyarka da shi, kuma muka karanta maka shi karantawa" [Furqan: 32].
            Haka kuma cikin sassauqar masa da alqur'ani guntu-guntu (ba a dunqule ba) akwai hikima mai girma da take da alaqa da tarbiyya, wacce kuma ita ce: Bin muminai a sannu-sannu wajen koya musu ilimin alqur'ani, da yadda za su yi aiki da hukunce-hukuncen addinin Allah, Sai hakan ya zama ya fi sauqi a gare su wajen sanin addini da fahimtarsa, da kuma fita daga duffan abubuwan da suka kasance a cikinsu na: Jahilci da kafirci da shirka, zuwa ga: Imani da tauhidi da ilimi.

NA UKU: RUBUTA ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Yana daga cikin muhimman hanyoyin kiyaye zantuka da bayanai: a rubuta su, kuma duk maganar da ba a rubuta ta ba to lallai za a iya mantata, Wannan ya sanya tun da alqur'ani mai karamci ya zama ya sauka ne don zama shiriya ga dukkan duniya (na jiya da na yau) har zuwa tashin qiyama: To sai ya zama babu makawa sai an rubuta shi.
Kuma lallai Annabi (s.a.w) ya himmatu kana ya bada  kula ta musamman dangane da rubuta alqur'ani mai girma, a lokacin da ya umurci sashin sahabbansa da suka iya rubutu cewa su riqa rubuta alqur'ani mai girma, ya kuma xauke su a matsayin marubutan wahayi. Wanda kuma yafi shahara da wannan aikin a cikinsu shine: sahabinsa mai suna Zaid xan Sabit Al-ansaariy([3]) (r.a).
Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kasance duk lokacin da wahayi ya sauka a gare shi sai ya haddace shi, Sannan sai ya yi imla'insa ga xaya daga cikin marubuta wahayinsa don ya rubuce shi, Sai yace:
"ضَعُوا هَذِهِ الآيَاتِ فِي السُّورَةِ الَّتِي يُذْكَرُ فِيهَا كَذَا وَكَذَا([4])" فيسمي لهم السورة.
Ma'ana: "Ku sanya waxannan ayoyin a cikin surar da ake ambaton kaza da kaza a cikinta", Sai ya faxa musu sunan "surar". Sannan sai Annabi (s.a.w) ya umurce su da rubuta waxannan ayoyin a cikinta. Kuma lallai ya kasance ya kan umurci dukkan sahabbansa da cewa su riqa koyan dukkan abinda ya sauka na alqur'ani mai daraja, tare da haddace shi. Sai aka rubuce dukkan alqur'ani gabaxayansa a zamaninsa (s.a.w) a jikin takardu (رقاع) ([5]).
            Kuma Mala'ika Jibrilu (a.s) ya kasance yana bitar alqur'ani dukkansa tare da Annabi (s.a.w) a kowace shekara, sau xaya, Amma a shekarar da Annabi (s.a.w) ya rasu sai suka yi bitar alqur'ani har sau biyu, tare da jeranta ayoyinsa da surorinsa, kamar yadda yake a cikin "mus-hafi" da ke hannun musulmai a yau, don qara tabbatar da maganar da Allah ta'alah ya yi:
(إِنَّ عَلَيْنا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ، فَإِذا قَرَأْناهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ) [القيامة: 17-18].
Ma'ana: "Kuma lallai tattara shi da karatunsa akanmu ya ke. Kuma idan muka karanta shi to sai ka bi karatunsa" [Qiyamah: 17-18]. Da faxinsa maxaukaki:
(سَنُقْرِئُكَ فَلا تَنْسى) [الأعلى: 6].
Ma'ana: "Da sannu zamu karantar da kai shi, Ba za ka manta ba" [A'alah: 6].

NA HUXU: TATTARA ALQUR'ANI MAI GIRMA A CIKIN TAKARDU:
            Bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) sai khalifansa shiryayye Abubakar Siddiq (r.a) ya yi umurnin a tattara alqur'ani a cikin takardu da aka tsattsara aka tara su, saboda kada a rasa wani abu na alqur'ani sakamakon rasuwar mahaddatansa, ko kuma lalacewar tsofin takardun da aka rubuta alqur'anin a jikinsu (رقاع) Sai marubucin wahayin Annabi mai suna Zaid xan Sabit (r.a) ya xau alhakin wannan aiki mai girma. Bayan kuma ya gama tsaf, ya yi kuma bitar aikin; don samun tabbacin daidaitonSa shi da abinda ke jikin tsofin takardu (رقاع) da wanda mutane suka haddace a qirazansu, Sai aka ajiye waxannan takardun a gidan Abubakar Siddiq (r.a), har zuwa lokacin da Allah ya masa wafati. Sannan aka ci-gaba da kiyaye su a gidan khalifah na biyu: Umar xan Al-khaxxab (r.a). Shima bayan ya yi wafati sai aka ci-gaba da kiyaye su a xakin matar annabi (s.a.w); Uwar muminai Hafsah yar Umar([6]) (r.a).
            Ana nan ana-nan, a lokacin da musulunci ya yaxu, Sai musulmai suka buqaci "mus-hafai" na alqur'ani da za su riqa yin karatu a cikinsu, Sai wassu sahabbai suka bada shawara ga: Shiryayyen khalifah Usman xan Affan (r.a) da cewa wajibi ne a tattara hankalin mutane akan "mus-hafi" guda xaya da zai zama jagora; wanda musulmai za su yi koyi da shi a cikin karatunsu. Sai Usman ya umurci wassu jama'a daga cikin mahaddatan alqur'ani mai girma, waxanda kuma suka iya rubuta shi da cewa su xau alhakin wannan aikin, shugabansu kuma shine Zaid xan Sabit (r.a), suna masu dogara akan "takardun" da aka rubuta alqur'ani a cikinsu a zamanin Abubakar Siddiq (r.a) sai suka tattara waxannan takardun cikin "mus-hafi" guda xaya. Sannan suka kwafi wassu masu yawa daga gare shi, Sai aka aika guda xaya zuwa ga kowanne birni daga cikin biranan musulmai masu girma, sannan aka umurci musulmai da su kwafi "mus-hafansu" daga gare su.
            Lallai kuma dukkan "mus-hafai" da aka sani a duniyar jiya da ta yau, sawa'un waxanda su ke rubuce ne da rubutu irin na hannu (مخطوطة), ko wanda aka buga da injinan buga littatafai (مطبوعة), tushensu daga waxannan "mus-hafai" da aka yi aikin kwafar su, sannan aka aika su zuwa waxannan biranen ne, Basu banbanta da su ko ta fiskar abinda suka qunsa, ko kuma ta fiskar jeranta surori ko ayoyi ba.
            Kuma har zuwa wannan zamanin namu, musulmai suna himmatuwa da lamarin buga "mus-hafai" (alqur'ani mai girma), tare da amfana da sababbin abubuwan da zamani ya kawo na hanyoyin buga littatafai da adana bayanai, domin su taimaka wajen samun mafi darajar kyautata rubutu ko wasalce shi, wajen yin rubutun alqur'ani da kuma "rasamarsa" da irin rasamar da aka rubuta shi da shi a zamanin shiryayyen khalifah Usman xan Affan (r.a), wanda kuma aka san shi da laqabin: "AR-RASAMU AL-USMANIY".
            Kuma samuwar ma'aikatar buga littafin alqur'ani mai girma ta sarki Fahad, a garin Madinar Annabi ba komai ba ne sai xaya daga cikin dalilai na fili da su ke nuna yadda aka bada muhimmanci ga hidima wa alqur'ani mai girma, da yadda shugabannin masarautar larabawa ta Saudiyya ke damuwa da littafin Allah wajen yi masa hidima, da sauqaqe samunsa ga dukkan musulmai a ko-ina su ke, ta yadda za su same shi a cikin mafi kyan yanayi na tsarin bugu, da yin bango mai qarfi wa takardu da zai kiyaye shi, tare da kula da rubutunsa da kyautata shi.

NA BIYAR: JERANTA "MUS-HAFI" DA KARKASA SHI (JUZU'I-JUZU'I):
Alqur'ani mai girma yana farawa ne da "suratu al-fatihat", yana kuma qarewa da "suratu qul a'uzu bi rabbi an-naas". Gabaxaya kuma ya qunshi "surori" guda xari da goma sha huxu (114).
Kuma jerantawa tsakanin "surori" abu ne da aka samo shi daga Annabi (s.a.w) –TAUQIFIY NE-. Kuma bai dogara ga jerin "surori" a lokutan sauqarsu ba; saboda "surar" da ta fara sauqa ita ce: "suratu al-alaq", Jerinta kuma a cikin alqur'ani "mus-hafi" shi ne: 96. Kuma sahabbai suna sanin yadda jeranta ayoyi a cikin "sura" xaya, da jeranta "sura" bayan "sura" suke ne daga yadda Annabi (s.a.w) ya ke karanta alqur'ani mai girma([7]).
Kuma a yau ana karkasa "mus-hafi" har zuwa kashi talatin "juzu'i 30), kowane juzu'i kuma ana kasa shi ne zuwa "izu biyu", kowani izu kuma ya qunshi "rubu'ai guda huxu". Shi kuma wannan karkasuwar a mafi rinjayensa "ijtihadi" ne na maluma, domin suga sun sauqaqe karatun alqur'ani mai karamci ga musulmai.

NA SHIDA: KOYON KARATUN ALQUR'ANI MAI GIRMA:
Lallai musulmai sun himmatu sosai wajen koyan karatun alqur'ani da haddace shi, da tilawarsa, kamar yadda aka sauqar da shi ga manzon Allah (s.a.w).
Kuma mahaddata alqur'ani daga cikin sahabbai sun tsayu wajen su ga sun karantar da shi ga xalibansu tabi'ai, har suka yi kyakkyawan kiyayewa ga lafazin alqur'ani, suna kuma tsayar da su a wajen kowace aya (suna tambayarsu), har su ka yi kyakkyawan fahimta ga ma'anar ayoyi, suka kuma koyi ilimi da yadda ake aiki da shi gabaxaya.
Daga nan sai mahaddata daga cikin tabi'ai su kuma suka assasa makarantu mabanbanta na koya wa mutane karatun alqur'ani, suna yin riqo da abinda suka koye shi daga malumansu sahabbai; na fiskoki mabanbanta na tilawar alqur'ani, da kiyaye laffuzansa, da qididdige harrufansa, da kalmominsa, da jeranta surorinsa da ayoyinsa, da tajwidinsa, da kyautata salon karanta shi, da sanin saqon cikinsa, ana kuma haddace shi, ana tilawarsa.
Xalibi na koyan dukkan haka daga shehinsa (malaminsa) daga cikin makaranta kuma hafizai, baki-da-baki, da yaren larabci mai fasaha, xanye shatak kamar yadda aka saukar da shi ga Manzonmu (s.a.w) har zuwa wannan ranar.
Kuma lallai alqur'ani mai girma ana karanta shi da "qiraa'oi" masu yawa, waxanda kuma siffofi ne da salo-salo na karanta kalmomin alqur'ani, da harrufansa, da hanyoyin furta su, wanda tabi'ai suka koya daga makaranta kuma mahaddata na daga maluman sahabbai, waxanda su kuma suka koya tare da samun izinin gwanancewa a cikin karatunsa da karantar da shi (ijazah) daga Annabi (s.a.w)
Kuma mafi shahara daga cikin waxannan "qiraa'oi a zamaninmu wannan shi ne: qiraa'ar Asim daga riwayar xalibinsa Hafs xan Sulaiman, da kuma qiraa'ar Nafi'i wacce xalibinsa Usman xan Sa'id da ake masa laqabi da Warsh ya rawaito.
Daga cikinsu kuma akwai: Riwayar Duuriy daga Abiy-amrin Albasariy, da kuma riwayar Qaaluun daga Nafi'i.

NA BAKWAI: YIN FASSARAR ALQUR'ANI MAI GIRMA:
"Fassarar alqur'ani" na nufin: Bayyanar da ma'aoninsa([8]).
Lallai kuma magana bata cika ko cimma gayar da aka yi ta sai idan an gane abinda ta ke nunawa da ma'ananta.
Kuma lallai Allah ta'alah ya kwaxaitar da makarancin alqur'ani mai girma da damuwa da lamarin fahimtar ma'anoninsa, a cikin faxinsa:
(كِتابٌ أَنْزَلْناهُ إِلَيْكَ مُبارَكٌ لِيَدَّبَّرُوا آياتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُولُوا الْأَلْبابِ) [ص: 29].
Ma'ana: "Littafi ne da muka sauqar da shi zuwa gare ka, mai albarka, domin su yi tinani cikin ayoyinsa, kuma domin ma'abota hankula su wa'aztu" [Saad: 29].
Abinda ake nufi da "tadabbur" a cikin ayar shi ne: Qoqarin fahimtarsa.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana bayyana wa sahabbai abinda ya shige musu duhu daga ma'anonin alqur'ani mai girma([9]), Sai dai kasancewar sahabbai gwanaye cikin harshen larabci a wancan zamanin, da yadda alqur'anin ya sauka da harshensu Sai ya wadatar da su ga barin: Yawaita tambayoyi kan ma'anonin ayoyin alqur'ani mai girma.
Kamar yadda buqatun mutane kuma suka yi ta qaruwa kan sanin tafsirin alqur'ani: saboda yau da gobe.
Kuma lallai abinda aka rawaito daga Manzon Allah (s.a.w) na tafsirin wassu ayoyi, haka waxanda aka rawaito na tafsirin sahabbai da xalibansu tabi'ai ga wassu ayoyin shine: Tushen da aka gina ilimin fassara ayoyin alqur'ani akansa, Wanda kuma aka sanya masa suna: "Fassara alqur'ani da abinda aka rawaito na hadisai ko aasaar" (tafsir bil ma'asur); Wannan kuma shine salo ko hanyar da ta fi muhimmanci ga mai neman fahimtar alqur'ani mai girma.
Kuma lallai wannan dukkansa yana bayyana mana yadda sahabbai da tabi'ai suka fahimci alqur'ani mai girma; wato saboda gwanancewarsu a harshen larabci, da kuma saboda zuwan rayuwarsu tare da abubuwan da suka auku, ko yanayi da lokaci da suka hukunta sauqar ayoyin alqur'ani mai girma.

(1)  NAU'UKAN TAFSIRI:
Fiskokin da maluman tafsirin alqur'ani suka rubuta littatafan tafsiri a kansu sun banbanta gwargwadon abubuwa na ilimi mabanbanta da maluman ke basu muhimmanci, Sai littatafa na tafsiri suka bayyana; wanda wassu suke bada qarfi ta vangaren bayanin qarfi da fasahar larabcin alqur'ani, Wassu littatafan kuma sun damu da bayanin hukunce-hukuncen fiqihu, Wassu kuma suna bada muhimmanci kan vangarorin tarihi, ko vangaren hankali, ko halayya da xabi'u, da makamantansu. Kuma maluma sun karkasa littatafan tafsirai da suke hannun al'umma, gwargwadon wannan zuwa kashi biyu:
NA FARKO: Yin tafsirin aya da "riwayoyi, ko ma'asuur", Ma'ana: Fassara ayar alqur'ani da abubuwan da aka rawaito su daga Annabi (s.a.w), ko daga sahabbai, ko daga tabi'ai.
NA BIYU: Fassara aya da "ijtihaadi" ko fahimta (ra'ayi, ba da hadisai ba); Wanda ya ginu akan ginshiqai na ilimi ingantattu.

(2)  HANYAR TAFSIRI MAFI KYAU, DA KUMA QA'IDODINSA:
Fassara aya da abinda aka rawaito na hadisi ko maganganun sahabbai ko tabi'ai shine abin fifitawa a lokacin fassarar ayar alqur'ani mai girma; kasancewar hakan shine abinda aka rawaito daga Annabi (s.a.w) ko daga Sahabbansa, da kuma xalibansu daga cikin tabi'ai. Alhalin kuma su suka fi dukkan mutane ilimi.
Sai dai kuma idan fahimtar wassu ayoyin alqur'ani ya nemi qarin bayanin da ba a same shi ba a cikin "riwaya" to a nan wajibi ne Malamin tafsiri ya kula da qa'idodin da suke tafe:
1-     Bada kula ga abinda ya tabbata ta hanyar tafsiri da "riwaya" na bayanin waxannan ayoyin, da rashin kawo abinda zai warware shi ko qaryata shi.
2-     Dole tafsirin da zai yi ta hanyar fahimtarsa (ijtihadi) ya dace da gamamme ko dunqulallen ma'anar da alqur'ani mai girma ya zo da ita, kuma sunnar Annabi ta bayyanar da ita, saboda baya halatta ga mai tafsiri ya fitar wa mutane wani tafsirin da ke cin karo da ma'anonin alqur'ani da hadisai. Saboda alqur'ani mai girma sashinsa yana fassara sashi ne, kuma babu cin karo a tsakanin ayoyinsa. Itama sunnar Annabi (s.a.w) ta zo ne don yin bayanin abinda aka dunqula bayaninsa a cikin alqur'ani mai girma, tana kuma fassara shi.
3-     Dole ya san ilimi da qa'idodin harshen larabci, wajen sanin ma'anan laffuza, da yadda ake tsara jumloli a cikin harshen, da fiskoki mabanbanta na amfani da su, Wannan kuma saboda alqur'ani mai girma an saukar da shi ne da yaren larabci, kuma dole ne a fahimce shi bisa qa'idodin wannan harshen.
4-     Mayar da ma'anonin ayoyin da ma'anarsu ba a fili take sosai ba (mutashabihai) zuwa ga waxanda ma'anarsu ta ke a fili qarara (muhkamai), wannan kuma saboda alqur'ani sashinsa yana fassara sashi, kuma mafi yawan ayoyin alqur'ani mai karamci "muhkamai" ne, da ma'anoninsu yake a fili. Sai dai kuma a cikinsa akwai ayoyi "mutashabihai" waxanda ma'anoninsu ka iya vuya ga sashin maluma. Sai dai kuma mayar da su zuwa ga ayoyi "muhkamai" na taimakawa kan fahimtar abinda suke nunawa na ma'ana. Allah (s.w.t) yana cewa:
(هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ
فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ وَمَا يَعْلَمُ
تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو
الْأَلْبَابِ) [آل عمران: 7].
Ma'ana: "Allah shine wanda ya saukar maka da wannan littafin; a cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, da wassu masu kama da juna, Amma waxanda akwai karkata a cikin zukatansu Sai suna bin abinda akwai kama da juna daga gare shi, domin neman fitina, da neman yin tawilinsa, Kuma babu wanda ya san fassararsa face Allah. Su kuma tabbatattu cikin ilimi suna cewa: Mun yi imani da shi; dukkansu daga wajen ubangijinmu ne. Babu wanda ya ke tunani ya wa'aztu face ma'abota hankula" [Ali-imraan: 7].
5-     Xaukar tabbatattun abubuwan da binciken ilimi ya tabbatar da su, don haskakawa, a lokacin fassarar ayoyin da suke magana kan halittun Allah (na sarari ko teku ko cikin sammai). Tare da nisantar cusa ra'ayoyin da ba dole su zama sun inganta ba (نظريات علمية) cikin tafsirin alqur'ani mai girma, tsoron kada a cusa ma alqur'ani ma'anonin da baya nuni akansu.
6-     Ya kiyaye yin munanan tawilin da suke nisantar da maganar Allah ta'alah daga abubuwan da shari'arsa mai tsarki ta haqqaqe, sannan qa'idodin harshen larabci basa tare da su, ko don saboda nufin jirkita ma'anonin nassoshi, ko kuma don jahiltar harshen larabci da ma'anoninsa da fiskokin da ake amfani da shi, ko kuma don zaton wassu ma'anoni munana waxanda ake tsarkake maganar Allah ta'alah daga bada irinsu.
   
NA TAKWAS: MU'UJIZAR ALQUR'ANI MAI GIRMA (GAGARA-MISALI):
"Mu'ujizah" a yaren shari'a: Wata sifa ce da tafi qarfin ikon mutum ya zo da  wani abu, na aiki ko ra'ayi ko tsari (sai kuma ya zo da ita).
Kuma lallai "mu'ujizah" sifa ce da take fararuwa ba don komai ba sai don ta yi nuni kan "ayoyi da hujjojin annabawa da manzanni (a.s).
Kuma wannan lafazin "na mu'ujizah" ambatonsa bai zo ba a cikin alqur'ani mai girma, Abin sani kawai, lafazin "aya, da burhaan", da wassun haka ne suka zo a cikinsa.
Shi kuma alqur'ani mai girma maganar Allah ne maxaukaki, a cikinsu kuma akwai cika da kamala ta fiskar ma'anoni, da kyan ayoyi da kalmomi da jumlolin da aka gina shi da su, da suka fi qarfin ace mutum ne ya faxe su, Allah ta'alah yana cewa:
(الر، كِتابٌ أُحْكِمَتْ آياتُهُ ثُمَّ فُصِّلَتْ مِنْ لَدُنْ حَكِيمٍ خَبِيرٍ) [هود: 1].
Ma'ana: "A L R, Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa , sa'annan aka bayyana su daki-daki, daga wajen mai hikima mai bada labari" [Hud: 1]. 
            Kuma lallai mushirkai sun yi iya qoqarinsu wajen sanya shakka kan tushen alqur'ani mai daraja, da hana mutane amfana da shi, ta hanyar qirqiran qarerayi, da tada wassu shubuhohi([10]), Sai Allah (s.w.t) ya saukar da ayoyi waxanda a cikinsu ya ke qure mavarnata; ta hanyar cewa su zo da kwatankwacin wannan alqur'anin, ko da surori goma irinsa, ko da sura xaya; in dai sun kasance masu gaskiya([11]). Sai suka gajiya wajen kawo haka, suka kuma tabbatar cewa lallai alqur'ani duk da kasancewarsa da harshen larabci, sai dai kuma ba za a iya kwaikwayonsa ko zuwa da kwatankwacinsa ba, Allah ta'alah yana cewa:
(أَمْ يَقُولُونَ افْتَراهُ قُلْ فَأْتُوا بِسُورَةٍ مِثْلِهِ وَادْعُوا مَنِ اسْتَطَعْتُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ صادِقِين) [يونس: 38].
Ma'ana: "Ko suna cewa: Shi ya qirqire shi, Ka ce: To sai ku zo da sura guda xaya kwatankwacinsa, ku kirayi waxanda kuka samu dama in kun kasance masu gaskiya" [Yunus: 38].
            Kuma lallai alqur'ani mai karamci ya yi shela a fili; cewa mutane gabaxayansu da aljanu a bayansu sun gaza kan zuwa da kwatankwacin alqur'ani mai girma, koda kuwa sashinsu yana taimaka wa sashi:
(قُلْ لَئِنِ اجْتَمَعَتِ الْإِنْسُ وَالْجِنُّ عَلى أَنْ يَأْتُوا بِمِثْلِ هذَا الْقُرْآنِ لا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِ وَلَوْ كانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا) [الإسراء: 88].
Ma'ana: "Ka ce: Da mutane da aljanu za su haxu akan su zo da kwatankwacin wannan alqur'ani, ba za su zo da kwatankwacinsa ba, koda kuwa sashinsu yana taimakon sashi" [Isra'i: 88].
            Akan haka; Shi alqur'ani mai girma "mu'ujizah" ne; saboda kasancewarsa maganar Allah; wanda maganganun halittu basa kama da shi, Kuma shi aya ne kuma hujja, da kalmominsa da ayoyin cikinsa da yarensa, da abinda ke cikinsa na fiskokin bayanai da balagah (fasaha), da kuma abinda ke cikinsa na labaru da qissoshin gaskiya, da abinda ya qunsa na hukunce-hukunce da shari'oi, da qarfin tasirinsa ga zuciya da jiki, da abinda ya qunsa na tabbatattun abubuwan da ilimi ya zo da su masu qayatarwa.
            Kuma sau dayawa alqur'ani mai girma ya kan ximautar da hankulan masana ilimin xabi'a, da sararin sama (falaki), da waxanda suka shagaltu da neman sanin ilimin rayayyun halittu da likitanci, da wassunsu, a inda alqur'anin ke zance kan tabbatattun abubuwa a ilmance, ko ya yi nuni kan wassu halittun  da suke da alaqa da ilimin da suke aiki a cikinsa, da laffuza na ilimi masu zurfi, waxanda baza a tava iya zaton fitowarsu daga annabin da bai iya rubutu da karatu ba, wanda kuma ya rayu cikin al'ummar da bata iya karatu da rubutu ba, a kuma yankin duniyar da ba su san komai ba dangane da waxannan lamuran, Wanda kuma hakan shine ya zama sababin musuluntar mutane da yawa daga waxannan masanan, hakan kuma ya kasance kuma ya kan kasance saboda masanan sun gane cewa lallai dukkan abinda alqur'ani mai girma ya zo da shi ba zai yiwu ya zama maganar mutum ba, sai dai ya zama maganar mahaliccin duniya da mutane.
Kuma a cikin alqur'ani mai girma akwai ayoyi da yawa da suke nuni kan kaxaitakar Allah ta'alah, da kuma bayanin yadda ya ke kyautata halittunsa, Allah ta'alah yana cewa:
(سَنُرِيهِمْ آياتِنا فِي الْآفاقِ وَفِي أَنْفُسِهِمْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُ الْحَقُّ أَوَلَمْ يَكْفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُ عَلى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ) [فصلت: 53].
Ma'ana: "Da sannu, zamu nuna musu ayoyinmu a sararin sama, da kuma a cikin kayukansu, har sai ta bayyana musu cewa alqur'ani gaskiya ne, Ashe kuma ubangijinka bai isa ya zama halartacce akan kowani abu ba!" [Fussilat: 53].

NA TARA: TARJAMAR MA'ANONIN ALQUR'ANI MAI GIRA:
"Tarjama" itace: Xaukar magana daga wani harshe zuwa wani yaren na daban([12]).
Kuma lallai tarjama bata rabuwa da wahalhalu, saboda tsara laffuza a cikin yare har su bada cikakkiyar magana mai amfani xaya ne daga abubuwan da suke samar da maganar, kuma yana da wahala a kiyaye abinda jerin laffuzan ke nunawa na dukkan ma'anarsa a lokacin da aka so a tarjama wannan maganar zuwa wani yaren na daban([13]).
To idan wannan shine halin tarjama cikin maganganun da mutane ke yi, to lallai tarjama zata yi wahala matuqa a yayin da ake nufin tarjamar alqur'ani mai girma; saboda kasancewar alqur'ani maganan Allah ne, wanda ya sauqar da shi da harshen larabci, kuma alqur'ani an yi wahayinsa daga Allah ta'alah da lafazinsa da ma'anarsa, kuma ba zai yiwu wani mutum ya yi da'awar cewa ya san dukkan ma'anonin alqur'ani gabaxayansa ba, ko kuma yace: Wai shi yana da ikon ya dawo da tsarin laffuzan, ta irin hanyar da maganar take a harshen larabci.
Amma tare da cewa tarjamar alqur'ani mai girma tana da wahalar gaske, sai dai kuma maluman musulmai suna qarfafa tare da bayanin wajabcin ko lalurar a isar da alqur'ani mai girma, da saqon da yake xauke da shi zuwa ga dukkan al'ummai a bayan qasa, ko-yaya kuma harshensu ya ke, Hakan kuma zai tabbata ne kawai ta hanyar yin tarjama([14]).
Kuma tarjamar alqur'ani mai girma zuwa ga yaruka na daban, zai kasance ne ko([15]):
1-     Ta hanyar tarjamar ma'anoninsa, Wannan kuma itace tarjamar da babu tafsiri tare da ita, kuma tana taqaita ne ga yin bayanin abinda laffuzan nassin alqur'ani ke nunawa kawai.
2-     Ko kuma ta hanyar tarjama mai qunshe da tafsiri, wacce za a qarfafe ta da fitar da magana a fili, da buga misalai, Wannan kuma kamar: tafsirin alqur'ani ne da wani yaren na daban wanda ba larabci ba.
Kuma duk yadda tarjamar ma'anonin alqur'ani mai girma ta kai ga yin kyau da zurfi, kuma duk yadda shi mai yin tarjamar ya zama ya gwanance a harshen tarjama guda biyu, ya kuma yi zurfi wajen sanin ma'anonin ayoyin, to lallai wannan tarjamar ba za a kira ta da suna: alqur'ani ba, saboda sababi guda biyu([16]):
NA FARKO: Lallai alqur'ani mai girma maganar Allah ne maxaukaki, wanda aka saukar da shi da harshen larabci, kuma ya kai qololuwa wajen kyautatuwa da bayani. Shi kuma xaukar ma'anonin ayoyin tare da sake dawo da su da wani yaren; wanda ba larabci ba, ya vata sunansa na alqur'ani.
NA BIYU: Ita tarjama tana yin bayanin fahimtar mai yinta ne ga ma'anonin alqur'ani mai girma, don haka, A ta wannan fiskar tana yin kama da tafsiri. Kamar yadda shi kuma tafsirin ba a kiransa ace shi: alqur'ani ne, to haka itama tarjamar ba zai yiwu a kira ta alqur'ani ba.
Kuma domin tarjamar ma'anonin alqur'ani mai girma ta kasance karvavviya dole ne ta cika qa'idodin da maluma suka sanya ga mai nufin bayanin ma'anonin alqur'ani mai girma, tare da kiyaye kada mai tarjamar ya riqi tarjamarsa wani lulluvi da zai watsa ma'anoni ta qarqashinsa da suke karkatar da ma'anonin alqur'ani mai girma, ko kuma masu munana wa alamomin addinin musulmai da abubuwan da suke girmama su, wanda hakan kuma shine ya munana tarjamomi da yawa, waxanda wassu daga cikin "mustashriquna([17])" suka yi, ko kuma na wassu mutanen da suke nasabta kansu zuwa ga musulunci da qarya, alhalin kuma suna xauke da munanan aqidu, da suke qoqarin rushe mas'aloli muhimmai na addinin musulunci mai girma, da sukar aqidarsa ingantacciya, da shari'arsa mai sauqi.
Wannan ne kuma ya sanya ma'aikatar sarki Fahad da take buga "mus-hafi" mai girma, a garin Madinar Annabi, ta xauki alhakin fitar da tarjamomin ma'anonin alqur'ani amintattu, da nufin isar da saqon da alqur'ani mai girma ya qunsa, zuwa ga waxanda basa magana da harshen larabci, da yarukansu na asali.

Godiya kuma ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, Salatin Allah ya qara tabbata ga annabinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya, da waxanda suka bi su da kyautatawa zuwa ranar sakamako.





([1]) Yana nufin: mala'ika Jibrilu (a.s), saboda shine aka wakilta shi da yin wahayi ga annabawa
([2]) A duba/ Littafin tafsirin Xabariy (19/ 10), da Almurshid alwajiz na Abu-Shamah Almaqdasiy (shafi: 28)
([3]) Tafsirin Xabariy (1/28). 
([4]) Sunan Abiy-dawud, (lamba: 786), da Sunan At-tirmiziy (lamban hadisi: 3086), kuma Alhakim ya fitar da shi a cikin littafin Almustadrak (lambar hadisi: 3325), Yace: Wannan hadisi ne ingantacce akan sharaxin Bukhariy da Muslim, amma basu fitar da shi ba   . 
([5]) Sahihu Albukhariy (lambar hadisi: 4592, da 4593)
([6]) Sahihu Albukhariy (lambar hadisi: 4986), da Sunan At-tirmiziy (lambar hadisi: 3103), da Musnad na Imam Ahmad (lambar hadisi: 76)
([7]) Imam Ad-daniy a cikin littafin "almuqni'i" (shafi: 8) ya hakaito maganar daga Imam Malik xan Anas
([8]) A duba/ littafin Alburhaan na Azzarkashiy, (1/ 13)
([9]) Duba/ Tafsirin Xabariy, (1/ 37), da Muqaddimah fiy usul attafsir na Ibnu-taimiyyah (35)
([10]) Duba ayoyi kamar haka: An'aam: (7), An'aam: (25), Anbiya'i: (5), Saba'i: (43), Yasin: (69), Saafaat: (36), Saad: (4), da Xuur (30). 
([11]) Duba ayoyi kamar haka: Baqarah (23), Yunus (38), Hud (13) da Xuur: (34)
([12]) A duba/ Lisanu al-arab na Ibnu-manzur (Kalmar, rajama, da tarjama)
([13]) A duba littafin/ Dilalatu al'alfaaz na Ibrahim Anis (shafi: 171-175), da Fannu at-tarjamah na Muhammadu Awadh Muhammadu (shafi: 19)
([14]) A duba/ Majmu'u fatawa na Ibnu-taimiyyah (4/ 116)
([15]) A duba/ Majmu'u fatawa na Ibnu-taimiyyah (4/ 115, da 542), da littafin/ At-tafsiru walmufassiruna na Muhammadu Husaini Azzahabiy (1/ 23)
([16]) A duba/ Almajmu'u sharshu na Annawawiy (3/ 342)
([17]) Kafiran da suka shigo kasashen musulmai suka san addininsu da al'adunsu don su kawo vatanci a cikinsa.  

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...