2015/02/13

SUNNONIN DARE DA YININ JUMA'A

SUNNONIN DAREN JUMA'A DA YININTA

Bismillahir rahmanir rahiim.
Lallai yin aiki da sunnoni tabbatattu dayawa sun tabbata daga aikin Annabi Muhammad (SAW) ko daga umurninsa, a cikin daren juma'a ko a yininta, Ga muhimmai daga waxannan sunnoni:
1-   Sunnah ne –a yinin juma'a da darenta- a yawaita yin salati ga annabi (SAW) saboda faxinsa (SAW):
"أَكْثِرُوا مِنَ الصَّلاة عَلَيَّ يَوْمَ الْجُمُعَةِ"([1]).
Ma'ana: (Ku yawaita salati a gare ni a ranar juma'a).
2-   A sallar asubar wannan yinin (na juma'a) an sunnata liman ya karanta ''suratus sajadah, da Suratu al-insaan''; Saboda kasancewar annabi (SAW) ya tabbata akan aikata hakan([2]).
A cikin yininta kuma a karanta ''suratu alkahf''; saboda faxinsa (SAW):
"مَنْ قَرَأَ سُورَةَ الْكَهْفِ يَوْمَ الْجُمُعَةِ سَطَع لَهُ نُورٌ من تحت قدمه إلى عنان الـسماء يـضيء به
يوم القيامة، وغُفر له مَا بَيْنَ الْجُمُعَتَيْن"([3]).
Ma'ana: (Duk wanda ya karanta ''suratu alkahf'' a yinin juma'a wani irin haske zai vullo masa daga qarqashin dugaduginsa zuwa sararin sama; wanda kuma zai haskaka masa gaba a ranar tashin kiyama, kuma za a gafarta masa abinda ke tsakanin juma'oi guda biyu).
3-   An sunnata yin sammako zuwa ga sallah, don samun lada mai girma; ya zo a cikin hadisin Abu-hurairah (RA) cewa lallai Manzon Allah (SAW) yace:
"مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ثُمَّ رَاحَ فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَـدَنَةً، وَمَـنْ رَاحَ فِي الـسَّاعَةِ الثَّانِيَةِ
فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَـقَرَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّالِثَةِ فَـكَأَنَّمَا قَرَّبَ كَبْشًا أَقْـرَنَ، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ
الرَّابِعَةِ فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ دَجَاجَـةً، وَمَنْ رَاحَ فِي الـسَّاعَةِ الخـَامِسَةِ فَكَأَنَّـمَا قَرَّبَ بَيْضَةً، فَإِذَا خَرَجَ
الإِمَامُ حَـضَرَتِ الـمَلاَئِكَةُ يَـسْتَمِعُونَ الـذِّكْر"([4]).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi wanka a ranar juma'a irin wankan janaba; sannan ya tafi masallaci –a farkon lokaci- to kamar ya bada sadakar raqumi,Shi kuma wanda ya je a lokaci na biyu to kamar ya yi sadaka da saniya, Wanda kuma ya tafi a lokaci na uku shi kuma kamar ya bada sadakar rago mai qaho ne, Wanda ya tafi a lokaci na huxu to kamar ya bada sadakar kaza, Wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar to kamar ya bada sadakar kwai. Idan limami ya riga ya fito to sai Mala'iku su halarto suna sauraron huxuba). Da kuma saboda faxinsa (SAW):
"مَنْ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ وَغَـسَّلَ، وَبَـكَّرَ وَابْـتَكَرَ، وَدَنَا وَاسْتَمَعَ وَأَنْصَتَ، كَانَ لَهُ بِكُلِّ خُطْوَةٍ
يَخْطُوهَا أَجْرُ سَنَةٍ؛ صِيَامُهَا وَقِيَامُهَا"([5]).
Ma'ana: (Duk wanda yayi wanka a ranar juma'a, ya kuma zama sababin wanka, ya kuma yi sammako zuwa masallaci, ya kusanci limami; ya saurari  huxuba, to duk wani taku da yayi yana da ladan shekara; ladan azumtarta da tsayuwan dararen cikinta).
4-   An sunnata yin wanka a cikin yinin juma'a; saboda hadisin Abu-hurairah (RA) wanda ya gabata, cewa:
"مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ..."([6]).
Ma'ana: (Duk wanda yayi wanka a ranar juma'a irin wankan janaba).
Kuma ya dace mutum ya kwaxaitu wajen aikata wankan juma'a; kada ya barshi, musamman ga mutanen da suke da warin jiki, ko na aiki.
5-   Sunna ne a sanya tirare da yin tsafta, da kuma gusar da abinda ya dace a gusar daga jiki: wato kamar yanke farce da wanin haka.
Lallai kuma shi ''tsafta'' wani abu ne qari akan ''yin wanka''; saboda shi ''tsafta'' ya kan kasance ne ta hanyar yanke duk wani wari da kuma abubuwan da ke jawo shi, kamar gashi da shari'a ta yi umurnin a kawar da shi, da kuma faratu; don haka; an sunnata aske gashin gaba tare da wankan juma'a, haka kuma tuzge gashin hamata, da yanke farce, da rage gashin baki, tare da shafa turare; saboda hadisin Salman (RA) daga annabi (SAW) yace:
"لاَ يَغْتَسِلُ رَجُلٌ يَوْمَ الجُمُعَةِ وَيَتَطَهَّرُ مَا اسْتَطَاعَ مِنْ طُهْرٍ، وَيَدَّهِنُ مِنْ دُهْنِهِ، أَوْ يَمَسُّ مِنْ
طِيبِ بَيْتِه"([7]).
Ma'ana: (Mutum ba zai yi wanka a ranar juma'a ba, ya kuma tsarkaka da abinda ya sawwaqa na daga tsarki, ya kuma shafa mansa, ko kuma ya shafa tiraren gidansa).
Alhafiz Ibnu-hajar yace: «cewa da aka yi:
"مِن طُهْرٍ":
Abinda ake nufi da shi, shine kaiwa maqura wajen tsaftace jiki. Shi kuma jingina wannan tsafta da aka yi akan wankan juma'a: ana xauka daga gare shi cewa: abinda ake nufi da wannan tsaftacewa shine, ta hanyar aske gashin-baki, da farce, da gashin-gaba» ([8]).
6-   Kuma an sunnata ma bawa ya sanya mafi kyan tufarsa; Saboda hadisin Abdullahi xan Umar (RA):
"أَنَّ عُمَرَ بْنَ الخَطَّابِ t رَأَى حُلَّةً سِيَرَاءَ عِنْدَ بَابِ الـمَسْجِدِ، فَـقَالَ: يَا رَسُـولَ اللَّهِ! لَوِ
اشْتَرَيْتَ هَذِهِ، فَلَبِسْتَهَا يَوْمَ الجُمُعَةِ، وَلِلْوَفْدِ؛ إِذَا قَدِمُوا عَلَيْك".
Ma'ana: (Lallai Umar xan Alkhaxxab –RA- ya ga wani gyauto da mayafi mai zane-zane da aka sana'anta shi daga ''alharir'' a bakin kofar masallaci, sai yace: Ya ma'aikin Allah! Da ka sayi ''wannan''; sai ka riqa sanya shi a ranar juma'a, da kuma in baqi sun zo maka).
Imamu Albukhariy ya kafa hujja da wannan hadisi, kan: sanya mafi kyan tufa don tafiya sallar juma'a, a inda yake cewa: ''Babi da ke magana kan sanya mafi kyan abinda ya mallaka''.
Alhafiz Ibnu-hajar yace: «lallai fiskar hujja cikin wannan hadisi ga wannan babin shine: Annabi –SAW- ya tabbatar da Umar -RA- kan asalin yin ado da sanya tufa mai kyau don sallar juma'a» ([9]).
Da kuma saboda faxinsa (SAW):
"مَا عَلَى أَحَدِكُمْ لَوِ اشْتَرَى ثَوْبَيْنِ لِيَوْمِ الْجُمُعَةِ، سِوَى ثَوْبِ مِهْنَتِه"([10]).
Ma'ana: (Lallai xayanku ba laifi akansa; ya sayi riga da wando saboda yinin juma'a, qari akan kayan da yake aikinsa da su).
7-   Wanda ya shiga cikin masallaci a yinin juma'a an sunnata cewa kada ya zauna har sai ya sallaci raka'oi guda biyu; Saboda annabi (SAW) ya yi umurni da cewa a aikata haka. Saidai anso ya taqaita su matuqar ya samu limaminsa yana cikin huxuba([11]).
8-   Kuma an sunnata yawaita yin addu'a, ana kuma neman ya kirdadi ''lokacin amsa ta''; Saboda faxinsa (SAW):
"إنّ فِي الجُمُعَة لسَاعَةٌ، لاَ يُوَافِقُهَا عَبْدٌ مُسْلِمٌ، وَهُوَ قَائِمٌ يُصَلِّي، يَسْأَلُ اللَّهَ تَعَالَى شَيْئًا، إِلا
أَعْطَاهُ إِيَّاهُ"([12]).
Ma'ana: (Lallai a cikin yinin juma'a akwai wata sa'a –lokaci xan taqaitacce- bawa musulmi ba zai dace da shi ba, yana tsaye yana sallah, yana kuma roqon Allah wani abu; face Allah ya biya masa buqata).

     Wannan shine abinda ya sauwaqa a wannan dama, da fatan Allah ya mana jagora kan aiki da sunnonin manzonsa (SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAMA) sau-da-qafa.
24/04/1436H = 13/02/2015M




([1]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1047), da An-nasa'iy (3/91), da Ibnu-majah (lamba: 1085), da Alhaakim (1/278), kuma ya inganta shi, Azzahabiy ya masa muwafaqa, Malam Albaniy ma ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 889)
([2]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 891). 
([3]) Alhakim ya rawaito shi (2/0368), kuma ya inganta shi, Albaniy shima ya inganta shi (Irwa'u algalili, 3/093)
([4]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 881), da Muslim (lamba: 850)
([5]) At-tirmiziy ya rawaito shi (lamba: 496), ya kuma ce hadisi ne hasan, Albaniy ya inganta shi a cikin littafin (Sahihu at-targibi wat-tarhibi, lamba:  690)
([6]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 881), da Muslim (lamba: 850)
([7]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 883). 
([8]) Duba  littafin fat'hu albariy (2/432)
([9]) Duba  littafin fat'hu albariy (2/434)
([10]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1078), da Ibnu-majah (lamba: 1095), Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 898)
([11]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 930)
([12]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 935), da Muslim (lamba: 852).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...