2015/02/15

AZUMIN NAFILFILI

AZUMIN NAFILFILI (AZUMIN SUNNAH)

Yana daga cikin hikimar Allah da rahamarsa ga bayinsa: Ya sanya musu "taxawwu'i na nafilfili" a matsayin wani abu da ke kamantacceniya da farilloli; domin ya basu damar qarin lada da kuma qarin aiki ga masu son yin aiki, kuma domin cike abinda ka iya faruwa na givi ko naqasa a cikin farilloli, kuma hadisi ya tabbatar cewa a ranar tashin alqiyamah za a cike givin da aka samu cikin farilloli da nafilfilin bawa. Wannan hadisin da ya nuna cewa nakasa na shiga ma farillai,  kuma lallai nafilfilin ibadodin bawa suna cike wannan givin ya zo ne daga sahabain annabi (SAW) mai suna Abu-hurairah (RA), daga annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA), yace:
"إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ الْـمُسْلِمُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، الصَّـلاةُ الْمَكْتُوبَةُ، فَإِنْ أَتَمَّهَا، وَإِلا قِيلَ: انْظُرُوا هَلْ لَهُ مِنْ تَـطَوُّعٍ؟ فَـإِنْ كَانَ لَهُ تَطَـوُّعٌ أُكْـمِـلَـتِ الْفَـرِيـضَةُ مِنْ تَطَـوُّعِهِ، ثُمَّ يُفْعَلُ بِسَائِرِ الأَعْمَالِ الْمَفْرُوضَةِ مِثْلُ ذَلِكَ" ([1]).
Ma'ana: (Lallai farkon abinda za a fara hisabi wa bawa musulmi a ranar kiyama shine: sallah; idan ya cika ta to, Idan kuma ba haka ba sai a ce: Ku duba shin bawana yana da ''taxawwu'in nafilfili? Idan ya kasance yana da ''taxawwu'i'' sai a cikate farilla daga ''taxawwu'insa''. Sa'annan sai a aikata kwatankwacin haka da sauran aiyuka na ''farilla'').
Lallai kuma yana daga cikin kwanakin da "mustahabbi" ne a azumce su:
1-   Azumtar kwanaki shida (6) a cikin watan shawwal: Wannan kuma saboda hadisin Abiy-ayyub al'ansaariy (RA) yace:
"مَنْ صَامَ رَمَضَانَ، ثُمَّ أَتْبَعَهُ سِتًّا مِنْ شَوَّالٍ، كَانَ كَصِيَامِ الدَّهْر"([2]).
Ma'ana: (Duk wanda ya yi azumin watan ramadhana, sa'annan ya biyar da azumi guda shida -6-, daga watan shawwal, to kamar ya azumci zamani ne -shekara-).
2-   Azumtar yinin arafah ga wanda ba mahajjaci ba: Saboda hadisin Abu-qatadatah (RA):
"صِيَامُ يَوْمِ عَرَفَةَ، أَحْتَسِبُ عَلَى اللهِ أَنْ يُكَفِّرَ السَّنَةَ الَّتِي قَبْلَهُ، وَالسَّنَةَ الَّتِي بَعْدَهُ"([3]).
Ma'ana: (Azumin ranar arafah ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shi, da wacce za ta zo).
Amma bawan da ya ke cikin aikin hajji kam to irin wannan ba a sunnanta masa ya yi azumin yinin arafah ba; saboda annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya sha abin shansa a wannan yinin, alhalin mutane suna kallonsa. kuma lallai yin haka yafi bada karfi ga mahajjaci wajen yin bauta da addu'oi a wannan yinin mai girma.
3-   Azumin yinin ashurah: Saboda an tambayi annabi kan azumtar wannan yinin (10 ga watan al-muharram) sai yace:
"أَحْتَسِبُ عَلَى اللهِ أَنْ يُكَفِّرَ السَّنَةَ الَّتِي قَبْلَهُ"([4]).
Ma'ana: (Ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabace shi).
Kuma mustahabbi ne bawa ya haxa da azumtar yinin da ke gabaninsa, ko wanda ke bayansa; saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"لَئِنْ بَقِيتُ إِلَى قَابِلٍ لأَصُومَنَّ التَّاسِع"([5]).
Ma'ana: (Idan har na kai shekarar baxi to zan azumci ranar tara –ga watan muharram-). Da kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"صُومُوا يَوْمًا قَبْلَهُ أَوْ يَوْمًا بَعْدَه، خَالِفُوا الْيَهُودَ"([6]).
Ma'ana: (Ku azumci yini da ke gabaninsa, ko kuma yinin da ke bayansa; ku sava wa yahudu).
4-   Azumtar ranar litinin da alamis na kowani sati: Saboda hadisin A'ishah (RA) tace:
"كَانَ النبي r يَتَحَرَّى صِيَامَ الاثْنَيْنِ وَالْخَمِيسِ"([7]).
Ma'ana: (Annabi –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya kasance yana qirdadon azumtar ranar litinin da alamis). Da kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"تُعْرَضُ الأَعْمَالُ يَوْمَ الاِثْنَيْنِ وَالخَمِيسِ، فَأُحِبُّ أَنْ يُعْرَضَ عَمَلِي وَأَنَا صَائِم"([8]).
Ma'ana: (Ana bijiro da aiyuka a ranar litinin, da alamis; don haka ina son a bijiro da aikina alhalin ina azumi).
5-    Azumtar kwanaki uku cikin kowani wata: Saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ga Abdullahi xan amru (RA):
"صُمْ مِنَ الشَّهْرِ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ؛ فَإِنَّ الحَسَنَةَ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، وَذَلِكَ مِثْلُ صِيَامِ الدَّهْر"([9]).
Ma'ana: (Ka azumci kwana uku daga kowani wata; saboda aiki mai kyau ana ruvanya ladansa har sau goma; in kayi haka lallai kamar ka azumci shekarar baki xayanta ne). Wani hadisin ya zo daga Abu-hurairah (RA) yace:
"أَوْصَانِي خَلِيلِي r بِثَلاَثٍ : صِيَامِ ثَلاَثَةِ أَيَّامٍ مِنْ كُلِّ شَهْرٍ ، وَرَكْعَتَيِ الضُّحَى ، وَأَنْ أُوتِرَ
قَبْلَ أَنْ أَنَامَ"([10]).
Ma'ana: (Masoyina badaxi –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- ya min wasici da abubuwa guda uku: azumtar kwanaki uku cikin kowani wata, da kuma raka'oi guda biyu na walaha, da kuma cewa na yi witiri gabanin na yi barci).
Kuma mustahabbi ne azumin yini ukun su kasance a kwanakin da hasken wata ke cika a cikinsu, wanda ake kiransu "ayyamul-biydh"; wato: ranar goma sha uku ga wata, da sha huxu, da sha biyar (13-15); saboda hadisin Abu-zarrin (RA), yace: Manzon Allah (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace: 
"مَنْ كَانَ مِنْكُمْ صَائِمًا مِنَ الشَّهْرِ، فَلْيَصُمِ الثَّلاثَ الْبِيضَ"([11]).
Ma'ana: (Duk wanda zai yi azumi daga cikinku a cikin kwanakin wata; to ya azumci ranaku guda uku; waxanda wata a cikinsu ya ke da haske).
6-    Azumtar yini da shan ruwan yinin da ke bayansa: Wannan kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA)
"أَفضلُ الصِّيَامِ صِيَامُ دَاوُدَ u، كَانَ يَصُومُ يَوْمًا، وَيُفْطِرُ يَوْمًا"([12]).
Ma'ana: (Mafificin azumi shine irin azumin annabi Dawud –AS-; ya kasance ya kan azumci yini, ya sha ruwa a wani yinin). Yin haka kuma yana daga cikin mafificin nau'ukan "taxawwu'i".
7-    Azumi cikin watan Allah; al-muharram: Wannan kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA), yace:
"أَفْضَلُ الصَّيَامِ بَعْدَ شَهْرِ رَمَضَانَ شَهْرُ اللَّهِ الْمُحَرَّمُ، وأَفْضَلُ الصَّلاةِ بَعْدَ الفريضة صَلاةُ اللَّيْلِ"([13]).
Ma'ana: (Mafificin azumi bayan na ramadhana shine azumin watan Allah; al-muharram, mafificin sallah kuma bayan ta farilla itace: sallar dare).
8-    Azumtar kwana tara na farkon watan zulhijjah: Waxannan kwanakin suna farawa ne daga ranar xaya ga watan zul-hijjah, su kuma qare ranar tara ga wannan watan; wanda kuma shine ranar arafah, dalili kuma akan wannan azumi shine gamemmun hadisai da su ka yi magana kan falalar aiyuka na kwarai a cikin waxannan kwanakin; kamar faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"مَا مِنْ أَيَّامٍ العَمَلُ الصَّالِحُ فِيهِنَّ أَحَبُّ إِلَى اللهِ مِنْ هَذِهِ الأَيَّامِ العَشْرِ"([14]).
Ma'ana: (Babu wassu kwanaki wanda aiki na-kwarai ya fi soyuwa a cikinsu a wajen Allah fiye da waxannan kwanaki guda goma).
Shi kuma lallai "azumi" na daga cikin "aiyuka na kwarai".




([1]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 684), da An-nasa'iy (lamba: 466, 467), da Ibnu-majah (lamba: 1425). Albagawiy ya ce: hadisi ne hasan (Sharhus sunnah 4/ 159), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu an-nasa'iy, lamba: 451, 453). Lafazin na Ibnu-majah ne.
([2]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 1164)
([3]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 1162)
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 1162), Vangare ne na dogon hadisi
([5]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 1133)
([6]) Ahmad ya rawaito shi (1/241), da Ibnu-khuzaimah (lamba: 2095), a cikin isnadinsa akwai rauni, sai dai ya inganta i zuwa ga Ibnu-abbas (RA) daga faxinsa
([7]) Ahmad ya rawaito shi (5/201), da At-tirmiziy (lamba: 745), ya ce: hadisi ne hasan sahih,  Albaniy shima ya inganta shi (Atta'aliq ala Ibni-khuzaimah, lamba: 2116). 
([8]) At-tirmiziy ya rawaito shi (lamba: 751), da An-nasa'iy (1/322), da Abu-dawud (lamba: 2436), kuma At-tirmiziy yace: hadisi ne hasan, Albaniy kuma ya inganta shi a cikin (Sahihu At-tirmiziy, lamba: 596). 
([9]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1976)
([10]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1981)
([11]) Ahmad ya rawaito shi (5/152), da An-nasa'iy (4/222), lafazin na Ahmad ne, Albaniy kuma yace: hadisi ne hasan, (Sahih sunan An-nasa'iy, lamba: 2277-2281)
([12]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1976)
([13]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 1163)
([14]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 969).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...