FALALAR SALLAR JAM'I DA HUKUNCINTA
Bismillahir rahmanir rahim!
Tambaya:
Menene hukuncin yin sallah a cikin "jam'i" (sunna
ne ko wajiba), menene kuma falalarta?
Amsa:
Gabatarwa:
Lallai yin sallar jam'i
a masallatai abu ne mai girma da Musulunci ya zo da shi, saboda shi da kuma aiwatar
da kiran sallah suna nuni kan samuwar
Musulunci a gari, kuma dukkan musulmai sun yi ''ittifaqi''
cewa yin salloli biyar a masallatai na daga cikin manya-manyan fiskoki na xa'a
ma Allahu ta'alah; kuma sananne ne cewa Allah ya shar'anta ma wannan
al'ummar haxuwa a cikin wassu lokuta sanannu; daga cikinsu akwai:
lokutan salloli guda biyar, da sallar juma'a, da idin azumi dana laiya, da
sallar kisfewar rana ko wata. Kuma mafi girman haxuwa
da musulmai ke yi, wanda kuma ya fi muhimmanci, shine: haxuwa
a filin arafah a hajji; Kuma an shar'anta waxannan
tarukan a Musulunci; saboda maslahohin musulmai; saboda a cikin waxannan
tarurrukan akwai: saduwa a tsakaninsu, da qoqarin
sanin sashinsu ga halayya ko matsalolin da 'yan'uwansu suke ciki, tare da
banbancin al'ummansu da kabilunsu; kamar yadda Allah maxaukaki
ya ke cewa:
{يَا أَيُّهَا
النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا
وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ}
[الحجرات: 13].
Ma'ana: (Ya ku mutane lallai
mune muka halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku a matsayin
al'ummomi da qabilu domin ku san juna, lallai mafi karamarku a wajen Allah shine
wanda ya fi ku taqawa) [Hujuraat: 13].
Amma dangane
da falalar sallar jam'i kuma: To haqiqa
annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya kwaxaitar
akan sallar jam'i, ya kuma bayyana falalarta, da girman ladanta; a inda ya ke
cewa:
Ma'ana: (Sallar jam'i ta fi
falala akan sallar mutum shi kaxai, da daraja
ashirin da bakwai). Annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya sake cewa:
"صَلاَةُ الرَّجُلِ فِي الْجَمَاعَةِ تُضَعَّفُ عَلَى
صَلاَتِهِ فِي بَـيْتِهِ وَفِي سُوقِهِ خَمْسًا وَعِشْرِينَ ضِـعْفًا؛ وَذَلِكَ أَنَّهُ
إِذَا تَـوَضَّأَ
فَأَحْسَنَ الْـوُضُوءَ، ثُمَّ خَرَجَ إِلَى الْـمَسْجِدِ لاَ يُـخْرِجُهُ إِلاَّ الـصَّـلاَةُ:
لَمْ يَخْطُ خَطْوَةً إِلاَّ رُفِعَتْ
لَهُ بِهَا دَرَجَةٌ،
وَحُطَّ عَنْهُ بِهَا خَطِيئَةٌ، فَإِذَا صَلَّى لَمْ تَزَلِ الْـمَلاَئِكَـةُ تُصَلِّي
عَلَيْهِ مَا دَامَ فِي مُصَلاَّه..." ([2]).
Ma'ana: (Sallar mutum a cikin
jama'a ana nin-ninkata a kan sallarsa a gidansa, da kuma a wajen kasuwancinsa:
ninki ashirin da biyar; saboda idan bawa ya yi alwala, ya kuma kyautata alwala,
kana ya fita i zuwa masallaci; ba abinda ya fitar da shi sai ita sallar: Ba zai
taka wani taku ba; face an xaga darajarsa da
ita, a kuma kankare masa kura-kurensa da ita, Idan kuma ya yi sallah: To
mala'iku ba za su gushe ba suna yi masa addu'a, matuqar
bai gushe ba a wurin sallarsa… -har qarshen
hadisin).
Amma
dangane da hukuncin yin sallah a "jama'a" kuma:
Lallai sallar jam'i ''wajibi'' ce a salloli biyar, kuma
"alqur'ani" da ''sunna'' sun yi
nuni akan wajabcinta, Dalili daga alqur'ani
shi ne faxin Allah maxaukakin sarki:
{وَإِذَا
كُنْتَ فِيهِمْ فَأَقَمْتَ لَهُمُ الصَّلَاةَ فَلْتَقُمْ طَائِفَةٌ مِنْهُمْ
مَعَكَ} [النساء: 102].
Ma'ana: (Idan ka kasance a
cikinsu sai ka tsayar musu da sallah: to sai wani vangare
daga cikinsu su tsaya tare da kai) [Nisa'i: 102].
Qa'idar musulunci tana
nuna cewa: asali ga umurnin Allah shi ne "wajabci", kuma idan yin sallah
a cikin jam'i ya zamto wajibi a hali na tsoro; (lokacin yaqi):
To in ana cikin aminci; babu yaqi lamarin wajabcin
sallar jam'i yafi zama wajibi.
Amma dalilai kuma daga "hadisai" sune: Na farko: Hadisin
Abu-hurairah (RA), ya ce, annabi (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) yace:
"أَثْقَلَ الصَّلاةِ عَلَى الْـمُنَافِقِينَ صَلاةُ
الْعِشَاءِ وَصَلاةُ الْفَجْرِ ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِيهِمَا لأَتَـوْهُـمَا وَلَوْ
حَبْوًا، ولَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِالصَّلاةِ فَـتُقَامَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلا
يُصَلِّي بِالـنَّاسِ، ثُمَّ أَنْـطَـلِقَ مَعِي بِرِجَالٍ مَعَهُمْ حُزُمُ من حَطَب
إِلَى قَوْمٍ لا يشهدون الصَّلاة، فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ بِالنَّار" ([3]).
Ma'ana: (Sallar da ta fi
nauyi akan munafikai sune sallar ishah data asubah, da matune sun san abinda ke
cikinsu na lada da sun zo musu koda kuwa da ja-gindi, kuma haqiqa
na yi niyyar na yi umurni a tsayar da sallah, kana kuma na umurci wani ya jagoranci
mutane sallah, sa'annan na tafi –tare da wassu mazaje, a tare da su akwai
dami-damin itace- zuwa ga mutanen da basa halartar sallar jam'i; don na qona
gidajensu akansu).
Wannan hadisin na nuna cewa
sallah a cikin jam'i wajibi ne; saboda kasancewar annabi (SALLALLAHU ALAIHI
WASALLAMA) da farkon fari: ya
siffanta waxanda su ke qin halartarta da cewa su "munafiqai"
ne, saboda mutumin da ya qaurace ma abinda shi ke
"sunnah" ba za a qirga shi a matsayin
"munafiqi" ba; sai wannan ya yi
nuni cewa waxannan mutanen sun kauracewa "abu"
na ''wajibi''. Na biyu: Annabi
(SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) ya yi nufin yin horo ga waxanda
basa halartar sallar jam'i; sananne ne kuma shi "uquba
–horo-'' ba ya kasancewa sai in an bar abu na wajibi, kuma abinda ya hana annabi
(saw) zartar da wannan "uqubar" shine
kasancewar ba wanda ke uquba da wuta sai Allah -mabuwayi da xaukaka-.
Wassu maluma kuma suka ce:
dalilin hanuwarsa kan qone su shine abinda ke cikin waxannan
gidajen; na mata da zurriya waxanda sallar jama'a ba
wajibi ba ce akansu.
** Yana cikin dalilai da suke
nuna wajabcin sallar jam'i: Qissar sahabin nan
makaho wanda bashi da jagora; wato: Abdullahi bn Ummi maktum (ra) a lokacin da
ya nemi izinin Annabi (saw) kan ya riqa yin sallah
a gidansa; saboda kasancewarsa makaho, wanda kuma gidansa ke nesa da masallaci,
Sai annabi (saw) ya masa rangwame, yayin da ya juya zai tafi sai ya kira shi,
ya ce da shi:
Ma'ana: "Shin in an yi
kiran sallah kana ji? Sai ya ce: E, Sai ya ce: To ka amsa".
A wata riwayah kuma:
Ma'ana: "Ban sama maka
wani rangwame ba".
*** Da kuma saboda abinda ya
zo da isnadi hasan, daga Abdullahi dan Abbas (ra) lallai annabi (saw) ya ce:
Ma'ana: (Duk wanda ya ji
kiran sallah sai kuma bai amsa ba, to ba shi da sallah; sai dai in yana da
uzuri).
**** Ya zo kuma a cikin
littafin "sahihu Muslim" daga Abdullahi xan
Mas'ud (ra) ya ce:
«مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَلْقَى
اللهَ غَدًا مُسْلِمًا، فَلْيُحَافِظْ عَلَى هَؤُلَاءِ الصَّلَوَاتِ حَيْثُ
يُنَادَى بِهِنَّ، فَإِنَّ اللهَ شَرَعَ لِنَبِيِّكُمْ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ سُنَنَ الْهُدَى، وَإِنَّهُنَّ مَنْ سُنَنَ الْهُدَى، وَلَوْ أَنَّكُمْ
صَلَّيْتُمْ فِي بُيُوتِكُمْ كَمَا يُصَلِّي هَذَا الْمُتَخَلِّفُ فِي بَيْتِهِ،
لَتَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ، وَلَوْ تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ
لَضَلَلْتُمْ، وَمَا مِنْ رَجُلٍ يَتَطَهَّرُ فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ، ثُمَّ
يَعْمِدُ إِلَى مَسْجِدٍ مِنْ هَذِهِ الْمَسَاجِدِ، إِلَّا كَتَبَ اللهُ لَهُ
بِكُلِّ خَطْوَةٍ يَخْطُوهَا حَسَنَةً، وَيَرْفَعُهُ بِهَا دَرَجَةً، وَيَحُطُّ
عَنْهُ بِهَا سَيِّئَةً، وَلَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا يَتَخَلَّفُ عَنْهَا إِلَّا
مُنَافِقٌ مَعْلُومُ النِّفَاقِ، وَلَقَدْ كَانَ الرَّجُلُ يُؤْتَى بِهِ يُهَادَى
بَيْنَ الرَّجُلَيْنِ حَتَّى يُقَامَ فِي الصَّفِّ»([7]).
Ma'ana: "Duk wanda zai faranta
masa rai cewa ya haxu da Allah a gobe kiyama, yana musulmi to ya kiyaye waxannan
sallolin a lokacin da ake kiranSu, saboda lallai Allah ya shar'anta ma
annabinsa (saw) hanyoyin shiriya, kuma lallai waxannan
sallolin suna daga hanyoyin shiriya, kuma da dukkanku za ku yi sallah a cikin
gidaddajinku kamar yadda wannan mai qin zuwa
masallaci ke sallah a cikin gidansa da kun bar sunnar annabinku, da kuma za ku
bar sunnar annabinku da kun vace. Kuma babu wani
mutum da zai yi tsarki sai ya kyautata tsarkinsa, sannan sai ya nufi wani
masallaci daga cikin masallatai face Allah ta'alah ya rubuta masa da kowani
taku da ya yi tattaki lada mai kyau, ya kuma xaga
darajarsa da ita, ya kuma kankare masa mummuna da ita. Kuma na ganmu (a zamanin
sahabbai) babu wanda ke qin halartar jam'i face munafikin da ya sanu da munafurcinsa.
Kuma haqiqa mutum ya kasance ana daddafe da shi (saboda rashin lafiya) a
tsakanin mutum biyu, har a tsayar da shi a cikin sahu".
Dangane da munafikai kuma
dama Allah ta'alah ya siffatasu da cewa:
{وَإِذَا قَامُوا إِلَى
الصَّلاةِ قَامُوا كُسَالَى يُرَاءُونَ النَّاسَ} [النِّسَاء: 142]،
Ma'ana: "Basa zuwa
sallah face suna kasalallu" [Nisa'i: 142].
Ya kuma sake cewa:
{وَلا
يَأْتُونَ الصَّلاةَ إِلا وَهُمْ كُسَالَى ...} [التَّوْبَة: 54]
Ma'ana: "Kuma basa zuwa
sallah face suna cikin kasala" [Taubah: 54].
Kuma lallai ita "sallar jama'a" a masallaci wajibi
ce akan maza; banda mata da kuma yaran da basu riga suka balaga ba; Wannan kuma
saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) dangane da mata:
Ma'ana: (Kuma dakunansu shi
ya fiye musu alkhairi).
Amma kuma babu laifi idan
mata suka halarci "sallar jam'i" a masallatai, tare da lulluvi,
da kiyaye kai, da kuma amintuwa daga fitina da fitinuwa, kuma baya dacewa ga
mijinta ya hana ta; idan ta nemi izininsa don zuwa ga masallaci.
Duk kuma mutumin da ya bar yin sallah a cikin jam'i; ya je ya
yi sallarsa shi kaxai ba tare da uzuri ba: to sallarsa ta inganta, sai dai kuma ya
aikata savo; sakamakon barin "wajibi".
A dunkule: Kula da salloli
guda biyar a cikin jam'i kamar yadda Allah ya yi umurni da haka a cikin
littafinsa, da kuma a harshen manzonsa (saw) wajibi ne akan Mutane.
Amma abun da mutane da dama
ke aikatawa a yau, Na yin salloli a cikin gidaje, da kuma kyale masallatai, to
wannan kuskure ne da ya sava ma dalilan shari'a da ambatonsu ya gabata, kuma wajibi ne su hanu daga aikata haka, tare
da umurtarsu da kiyaye salloli, a cikin masallatai.
Allah ne masani!
Abubakar Hamza
15/04/1436h daidai 04/02/2015
&&&&
No comments:
Post a Comment