TAMBAYA:
Yaya siffar wankan gawa ta ke?
AMSA:
Siffar wankan gawa:
Ita ce/ Mutanen zasu xora gawar da
za su wanke ta akan gadon yin wankan, sa'annan sai su suturce mata al'aura, kana
su tove
mata tufafi, suna masu voye al'aurar nasa/nata ga idanu; a cikin xaki
ne ko a makamancin haka.
Sa'annan sai su xaga
kan mataccen har zuwa kusa da yanayin zama, daga nan sai mai yin wankan ya
biyar da hannunsa ta kan cikin mamacin yana matsa cikin a hankali a hankali, sai
ya tsaftace masa mafitar fitsari da kashi, ya kuma yi masa tsarki; ta hanyar
wanke abinda ke jikin mafitan guda biyu; na najasa; bayan ya xaure
hannunsa da tsumma.
Sa'annan sai ya yi niyyar yi
masa wanka, ya yi bismillah, ya masa alwala; irinta mai sallah, in banda kurkuran
baki da kuma shaqa masa ruwa a hanci; waxanda
shafa akan bakin da kuma hancin na iya isarwa.
Sa'annan sai ya wanke masa
kansa da gemunsa da ruwa da kuma gaba-ruwa, ko kuma sabulu, ko wanin haka.
Sa'annan sai ya wanke masa vangaren
dama na jikinsa.
Sa'annan kuma sai vangaren
hagu.
Daga nan sai ya kammala wanke
masa sauran jikinsa.
Mustahabbi ne mai yin wankan ya
naxa
wata tsumma a hannunsa a lokacin da ya ke yi masa wankan.
Abu na wajibi shine wankewa mamaci
kowace gava sau xaya, matuqar dai gavar ta wanku sumul. Kuma an so (mustahabbi ne) koda ta wankun ya
qara
wanketa har sau uku.
Kamar yadda kuma mustahabbi
ne ya sanya ''kafur'' a wanka na qarshe.
Sa'annan ya tsantsamar da jikin
mataccen.
Tare kuma da gusar masa da
dukkan abubuwan da aka shar'anta gusar da su; na faratu da gashi.
Mace kuma a yi mata yawo a
gashin kanta, sa'annan a jefa su ta bayanta.
Idan har wanka wa mamaci bai
yiwu ba saboda rashin ruwa, ko kuma sashin jikinsa akwai qunar
wuta ko makamancin haka to a nan za a yi masa taimama ne da qasa.
Kuma mustahabbi ne ga wanda
ya yi wanka wa mamaci shima ya yi wanka.
WALLAHU A'ALAM!
No comments:
Post a Comment