2015/02/17

NAFILFILIN SALLOLI

SALLOLIN NAFILFILI (01)

Bismillahir rahmanir rahim!
Wassalatu wassalamu ala ashrafil anbiya'i wa imamil mursalina, Bayan haka:
Lallai dangane da "kan maganar" dake gabanmu mai taken: "Sallolin nafilfilili" akwai ressan du suka kamata mu tava kamar haka:

NA FARKO: Falalar yin ''taxawwu'i'' da nafilfilin salloli:
Taxawwu'in sallah na daga cikin mafifitan xa'a da Allah ta'alah ya shar'anta bayan ''jihadi fisabilillahi'' da ''neman ilimi''; wannan kuma saboda Annabi (SAW) ya dawwama wajen kusantar Ubangijinsa da nafilfilin salloli; kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA), yace: Manzon Allah (SAW) yace:
"إِنَّ اللَّهَ تعالى قَالَ: مَنْ عَادَى لِي وَلِيًّا فَقَدْ آذَنْتُهُ بِالْحَرْبِ، وَمَا تَقَرَّبَ إِلَـيَّ عَـبْدِي بِشَـيْءٍ  أَحَبَّ إِلَيَّ مِمَّا افْتَرَضْتُ عَلَيْهِ، وَمَا يَزَالُ عَبْدِي يَـتَقَرَّبُ إِلَـيَّ بِالنَّوَافِـلِ حَتَّى أُحِـبَّهُ، فَإِذَا أَحْبَبْتُهُ كُنْتُ سَمْعَهُ الَّذِي يَسْمَعُ بِهِ، وَبَصَرَهُ الَّذِي يُبْصِرُ بِهِ، وَيَدَهُ الَّتِي يَبْطُشُ بِهَا، وَرِجْلَهُ الَّتِي يَمْشِي بِهَا، وَإِنْ سَأَلَنِي لأُعْطِيَنَّهُ، وَلَئِنِ اسْتَعَاذَنِي لأُعِيذَنَّهُ"([1]).
Ma'ana: (Lallai Allah ta'alah yace: Wanda ya yi adawa da masoyina –waliyyin Allah- to haqiqa ina masa shelar yaqi. Bawana baya kusantata da wani abu da ya fi soyuwa a gare ni fiye da abinda na farlanta akansa, kuma bawana ba zai gushe ba yana kusantata da nafilfili face na so shi; Idan kuma naso shi zan kasance "jinsa" da yake ji da shi, da "ganinsa" da yake gani da shi, da "hannunsa" da yake damqa da shi, da "qafarsa" da yake tafiya da ita, kuma wallahi  in ya roqe ni zan bashi, in kuma ya nemi tsarina zan tsare shi).

NA BIYU: Hikimar shar'anta sallolin nafila:
Haqiqa Allah -subhanahu- ya shar'anta yin nafilar taxawwu'i don ta zama rahama ga bayinsa; ya sanya wa jinsin kowace ibada ta farilla nafilfili daga wannan jinsin; domin mumini ya qara xaukaka cikin darajoji idan ya aikata ''taxawwu'i'', kuma domin nafilfilin su kammala farilloli, tare da cike givin da za a samu a cikinSu, a ranar qiyama; wannan kuma ya kasance ne saboda lallai farilloli nakasa na shiga musu, kamar yadda bayanin hakan ya zo cikin hadisin Abuhurairah (RA), daga annabi (SAW), yace:
"إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ الْـمُسْلِمُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، الصَّـلاةُ الْمَكْتُوبَةُ، فَإِنْ أَتَمَّهَا، وَإِلا قِيلَ: انْظُرُوا هَلْ لَهُ مِنْ تَـطَوُّعٍ ؟ فَـإِنْ كَانَ لَهُ تَطَـوُّعٌ أُكْـمِـلَـتِ الْفَـرِيـضَةُ مِنْ تَطَـوُّعِهِ ، ثُمَّ يُفْعَلُ بِسَائِرِ الأَعْمَالِ الْمَفْرُوضَةِ مِثْلُ ذَلِكَ" ([2]).
Ma'ana: (Lallai farkon abinda za a fara hisabi wa bawa musulmi a ranar qiyama shine: sallah; idan ya cika ta, to, Idan kuma ba haka ba, Sai ace: Ku duba shin bawana yana da ''taxawwu'i''? Idan ya kasance yana da ''taxawwu'i'' sai a cikate farilla daga ''taxawwu'insa''. Sa'annan sai a aikata kwatankwacin haka da sauran aiyuka na ''farilla'').

NA UKU: Karkasuwar sallolin "nafila":
Sallar "taxawwu'i" ta kasu zuwa nau'i biyu:
Nau'in farko: Nafilfilin da suke da lokatu ayyanannu, kuma ana kiransu da sunan ''nafilfili masu qaidi'', Su kuma waxannan daga cikinsu akwai waxanda suke biye da sallolin farilla, kamar ''sunnoni ratibai'', akwai kuma waxanda basa biye da farilloli; kamar sallar ''wutiri, walaha, da kuma kisfewar rana ko kuma na wata''.
Nau'i na biyu: Sune nafilfilin da ba a iyakance musu lokuta qayyadaddu ba.
Shi nau'i na farko nau'uka ne mabanbanta; wanda kuma sashinsu yafi sashi qarfin muhimmanci; amma dai wanda ya fi muhimmanci daga cikinsu shi ne: ''sallar kisfewar rana ko na wata'', sa'annan sai ''witiri'', da sallar roqon ruwa, da sallar ''tarawihi''.
Lallai shi nau'i na biyu an shar'anta shi ne a cikin dare gabaxayansa, da kuma yini; in banda lokutan hani, sai dai kuma ''sallar dare'' tafi falala akan ''sallar rana''.
Faxaxan bayanai za su zo –da iznin Allah- akan waxannan nau'ukan xaya bayan xaya a cikin abinda ke tafe.

NA HUXU: Sallolin "nafilfili" da aka sunnanta yinsu a cikin jam'i:
An sunnanta sallar jam'i ga ''tarawihi'', da ''sallar roqon ruwa'', da kuma ''sallar kisfewar rana ko wata''.

NA BIYAR: Adadin sallolin "rawaatib":
Abinda ake kira ''rawaatib'' -jam'in "ratiba"- shi ne: abu ''dawwamamme, na yau-da-kullum, kuma su ''sallolin rawaatib'' su suke bin sallolin ''farilla''.
Fa'idar waxannan ''rawaatib'' shine: Suna cike tawayar da take kasancewa a cikin ''sallar farilla'', kamar yadda bayanin hakan ya gabata.
Adadin ''rawaatib'' raka'oi goma ne, kuma sune ambatonsu ya zo a cikin hadisin Abdullahi xan Umar (RA), cewa:
"حَفِظْتُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ r رَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْمَغْرِبِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْعِشَاءِ، وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الْغَدَاة كَانَتْ سَاعَةً لا أدْخُلُ عَلَى النَّبِيِّ r فِيهَا، فحَدَّثَتْنِي حَفْصَةُ رضي الله عنها أَنَّهُ كَانَ إِذَا طَلَعَ الْفَجْرُ وأَذَّنَ الْمُؤَذِّنُ صَلَّى رَكْعَتَيْن" ([3]).
Ma'ana: (Na haddace daga manzon Allah –SAW- cewa ya kan yi raka'oi biyu kafin azahar, raka'oi biyu bayan azahar, da raka'oi biyu bayan magrib, da raka'oi biyu bayan isha'i, da kuma raka'oi biyu kafin sallar asuba; wannan lokacin lokaci ne da bana shiga wa annabi –SAW- a cikinsa; Amma matarsa Hafsah -RA- ta ban labari cewa: idan alfijir ya keto, kana mai kiran sallah ya yi kira; Annabi ya kan sallaci raka'oi guda biyu).
Kuma yana da qyau musulmi ya kiyaye aiwatar da "raka'oi guda goma sha biyu''; wannan kuma saboda faxin annabi (SAW):
"مَا مِنْ عَبْدٍ مُسْلِمٍ يُصَلِّي لِلَّهِ تعالى كُلَّ يَوْمٍ ثِنْتَيْ عَشْرَةَ رَكْعَةً، إِلا بَنَى اللهُ لَهُ بَيْتًا -أَوْ إِلا بُنِيَ لَهُ بَيْتٌ- فِي الْجَنَّةِ" ([4]).
Ma'ana: (Babu wani bawa musulmi da zai yi sallah ga Allah ta'alah raka'oi guda goma sha biyu a cikin kowani yini; face Allah ya gina masa gida –ko kuma an gina masa gida- a cikin aljanna).
Waxannan raka'oi guda goma sha biyun (12) sune guda goman da ambatonsu ya gabata, sai dai za a yi raka'oi huxu ne kafin sallar azahar; saboda Attirmiziy ya rawaito qarin a cikin hadisin uwar muminai Ummu-habibah da ya gabata, wannan qarin kuma shine:
"أَرْبَعًا قَبْلَ الظُّهْرِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَهَا، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ الْمَغْرِبِ، وَرَكْعَتَيْنِ بَعْدَ العِشَاءِ، وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ صَلاَةِ الْفَجْرِ" ([5]).
Ma'ana: (raka'oi huxu kafin yin sallar azahar, da raka'oi biyu bayan magriba, da raka'oi biyu bayan isha'i, da raka'oi biyu kafin sallar asubah). Da kuma saboda abinda ya tabbata a cikin sahihu Albukhariy na daga hadisin A'ishah (RA), lallai ta ce:
"كَانَ النَّبِيُّ r لا يَدَعُ أَرْبَعًا قَبْلَ الظُّهْر" ([6]).
(Annabi (SAW) ya kasance ba ya barin aiwatar da raka'oi huxu gabanin azahar).
Kuma mafi muhimmanci daga cikin ''rawaatib'' sune abinda ake kiransu: raka'oi biyu da ake yi bayan fudowar alfijir (raka'ataa alfajr); wannan kuma saboda saboda faxinsa (SAW):
"رَكْعَتَا الفَجْرِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا" ([7]).
Ma'ana: (''Raka'oi biyu da ake yi bayan fudowar alfijir'' sun fi duniya da abinda ke cikinta alkhairi). Da kuma saboda faxin A'ishah (RA) dangane da waxannan rakao'in guda biyu:
"وَلَمْ يَكُنْ يَدَعْهُمَا أَبَدًا" ([8]).
Ma'ana: (Manzon Allah –SAW- bai kasance yana barin aiwatar dasu ba har abada).

NA SHIDA: Sallar "sallar witiri" da hukunce-hukuncen da suke rataye da ita:
Hukuncin yin sallar witiri: Yin sallar ''witiri'' sunna ne mai qarfi; wacce annabi (SAW) ya kwaxaitar akan yinta; yace:
"إِنَّ اللَّهَ وِتْرٌ يُحِبُّ الوِتْرَ" ([9]).
Ma'ana: (Lallai Allah ''witri ne'' yana kuma son abu ''wutiri''). A wani wurin kuma Manzon Allah (SAW) yace:
"يَا أَهْلَ القُرْآن أَوْتِرُوا؛ فإِنَّ اللَّهَ وِتْرٌ يُحِبُّ الوِتْرَ" ([10]).
Ma'ana: (Ya ku ma'abota alqur'ani ku yi witiri; saboda lallai Allah ''witiri ne'' kuma yana son abu ''witiri'').
Lokacin yin sallar "witiri": Shine lokacin dake tsakanin sallar ''ishah'' da sallar ''asubah'' da "ijma'in" maluma; saboda aikin manzon Allah (SAW) ya nuna haka, da kuma saboda faxinsa:
"إِنَّ اللَّهَ أَمَدَّكُمْ بِصَلاَةٍ هِيَ خَيْرٌ لَكُمْ مِنْ حُمْرِ النَّعَمِ؛ صلاة الْوِتْرُ، مَا بَيْنَ صلاة الْعِشَاءِ إِلَى طُلُوعِ الْفَجْرِ" ([11]).
Ma'ana: (Lallai Allah ya qarfafe ku da wata sallah; wacce ta fi muku alkhairi fiye da jajayen raquma; Itace sallar wutiri; tsakanin sallar ishah zuwa fudowar alfijir); Don haka; idan alfijir ya fudo babu wutiri; wannan kuma saboda faxinsa (SAW):
"صَلاةُ اللَّيْلِ مَثْنَى مَثْنَى فَإِذَا خَشِيَ أَحَدُكُمُ الصُّبْحَ صَلَّى رَكْعَةً وَاحِدَةً تُوتِرُ لَهُ مَا قَدْ صَلَّى" ([12]).
Ma'ana: (Sallar dare raka'oi bibbiyu ne; Idan xayanku ya ji tsoron asubah: sai ya sallaci raka'a guda xaya; wacce za ta zame masa witiri ga abinda ya sallata). Wannan kuma dalili ne kan fitan lokacin witiri da ketowar alfijir.
Alhafiz Ibnu-hajar ya ce:
«وَأَصْرَحُ مِنْهُ –يعني في الدلالة- مَا رَوَاهُ أَبُو دَاوُدَ وَالنَّسَائِيُّ، وَصَحَّحَهُ أَبُو عَوَانَةَ وَغَيْرُهُ ... أَن ابن عُمَرَ كَانَ يَقُولُ: مَنْ صَلَّى مِنَ اللَّيْلِ فَلْيَجْعَلْ آخِرَ صَلاتِهِ وِتْرًا فَإِنَّ رَسُولِ اللَّهِ r كَانَ يَأْمُرُ بِذَلِكَ؛ فَإِذَا كَانَ الْفَجْرُ فَقَدْ ذَهَبَ كُلُّ صَلاةِ اللَّيْل وَالْوتر»([13]).
Ma'ana: «Dalilin da ya fi fitowa fili: Shine abun da Abu-dawud ya rawaito, da An-nasa'iy, kuma Abu-awanah da waninsa suka inganta shi, … Lallai Abdullahi xan Umar –RA- ya kasance yana cewa: Duk wanda ya yi sallah da daddare, to ya sanya sallarsa ta karshe ta zama ''witiri''; saboda manzon Allah –SAW- ya kasance yana umurni da yin haka, idan alfijir ya keto to haqiqa xaukacin sallar dare ta tafi, haka kuma wutiri».
Kuma sallatar ''witiri'' a qarshen dare shi ya fi falala akan sallatarta a farkon dare, sai dai mustahabbi ne a gaggauta yinta a farkon dare ga wanda ya yi zaton ba zai iya tashi a qarshen dare ba, haka kuma mustahabbi ne a jinkirta ''wutirin'' ga wanda ya yi zaton zai tashi a qarshen dare; wannan kuma saboda abinda Jabir (RA) ya rawaito cewa lallai manzon Allah (SAW) ya ce:
"مَنْ خَافَ أَنْ لا يَقُومَ مِنْ آخِرِ اللَّيْلِ فَلْيُوتِرْ أَوَّلَهُ، وَمَنْ طَمِعَ أَنْ يَقُومَ آخِرَهُ فَلْيُوتِرْ آخِرَ اللَّيْلِ، فَإِنَّ صَلاةَ آخِرِ اللَّيْلِ مَشْهُودَةٌ، وَذَلِكَ أَفْضَلُ" ([14]).
Ma'ana: (Duk wanda ya ji tsoron ba zai tashi ba a qarshen dare, to ya yi witirinsa a farkonsa, wanda kuma ya yi kwaxayin zai tashi a qarshensa to ya yi witirinsa a qarshen daren; saboda sallar qarshen dare mala'iku suna halartarta; wannan kuma shine ke da fifiko).

Siffar ''witiri'' da adadin raka'ointa:
Mafi qarancin wutiri shi ne raka'a xaya; wannan kuma saboda hadisin Abdullahi xan Umar da Ibnu Abbas (RA), daga manzon Allah (SAW):
"الْوَتْرُ رَكْعَةٌ مِنْ آخِرِ اللَّيْلِ" ([15]).
Ma'ana: (Witiri raka'a xaya ne a qarshen dare). Da kuma saboda hadisin Abdullahi xan Umar (RA) wanda ambatonsa ya gabata –a kusa- cewa:
"صَلَّى رَكْعَةً وَاحِدَةً تُوتِرُ لَهُ مَا قَدْ صَلَّى" ([16]).
Ma'ana: (.. Sai ya sallaci raka'a guda xaya; wacce za ta zame masa witri ga dukkan abinda ya sallata).
Amma ya halatta a yi witri da ''raka'oi uku''; saboda hadisin A'ishah (RA), cewa lallai Annabi (SAW) ya kasance:
"يُصَلِّي أَرْبَعًا، فَلاَ تَسْأَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ. ثُمَّ يُصَلِّي أَرْبَعًا، فَلاَ تَسْأَلْ عَنْ حُسْنِهِنَّ وَطُولِهِنَّ. ثُمَّ يُصَلِّي ثَلاَثًا" ([17]).
Ma'ana: (yana sallatar raka'oi huxu; kada ka yi tambaya dangane da qyansu da tsawonsu, sa'annan sai ya sallaci raka'oi guda huxu; kada ka tambaya dangane da kyansu da tsawonsu, sa'annan sai ya sallaci raka'oi guda uku).
Ya halatta a rabe tsakanin waxannan raka'oin uku (na wutiri) ta hanyar yin sallama a tsakaninsu; wannan kuma saboda Abdullahi xan Umar (RA) ya kasance:
"يُسَلِّمُ منْ ركْعَتَيْنِ حَتَّى يَأْمُرَ بِبَعْضِ حَاجَتِه" ([18]).
Ma'ana: (Ya kasance yana yin sallama bayan yin raka'oi biyu; domin ya yi umurni kan wassu buqatunsa).
Kuma ya halatta a yi ''wutiri da raka'oi uku'' a jere da ''tahiya xaya'' da ''sallama xaya''; wannan kuma saboda hadisin A'ishah (RA), tace:
"كَانَ النبي r يُوتِرُ بِثَلاثٍ لا يَقْعُدُ إِلا فِي آخِرِهِنَّ" ([19]).
Ma'ana: (Annabi -SAW- ya kasance yana yin witiri da ''raka'oi guda uku'' baya zama sai a qarshensu).
Sai dai kuma ba a sallatar witrin raka'oi uku da tahiya biyu da sallama guda; domin kada ya yi kamantacceniya da sallar ''magrib'', wannan kuma saboda Annabi (SAW) ya hana aikata hakan([20]).
Kuma ya ''halatta'' a yi ''witiri'' da ''raka'oi bakwai, ko da biyar''; wanda kuma mai sallan ba zai zauna ba sai a qarshensu; wannan kuma saboda hadisin A'ishah (RA), ta ce:
"كَانَ رَسُولُ اللهِ r يُصَلِّي مِنَ اللَّيْلِ ثَلاثَ عَشْرَةَ رَكْعَةً، يُوتِرُ مِنْ ذَلِكَ بِخَمْسٍ، لا يَجْلِسُ فِي شَيْءٍ إِلا فِي آخِرِهَا" ([21]).
Ma'ana: (Annabi -SAW- ya kasance yana yin sallar dare; raka'oi goma sha uku; yana yin ''witiri'' da raka'oi biyar; baya zama a cikin wani abu daga cikinsu sai a qarshensu). Da kuma saboda hadisin Ummu-salamah (RA), ta ce:
"كَانَ رَسُولُ اللَّهِ r يُوتِرُ بِسَبْعٍ أَوْ بِخَمْسٍ، لا يَفْصِلُ بَيْنَهُنَّ بِتَسْلِيمٍ وَلا كَلام" ([22]).
Ma'ana: (Annabi -SAW- ya kasance yana yin ''witiri'' da raka'oi bakwai ko biyar, baya rabe tsakaninsu da sallama ko da magana).

A nan zan dakata, sai a wani kashin (kashi2) don ci gaba da bayani mai faxi akan wassu nau'ukan daga cikin nau'ukan nafilfili tare da bayanin hukunce-hukuncensu. Wallahu aalam!




([1]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 6502). 
([2]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 684), da An-nasa'iy (lamba: 466, 467), da Ibnu-majah (lamba: 1425). Albagawiy ya ce: hadisi ne hasan (Sharhus sunnah 4/ 159), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu an-nasa'iy, lamba: 451, 453). Lafazin na Ibnu-majah ne.
([3]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1180, 1181), da Muslim (lamba: 729)
([4]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 728), daga hadisin Ummu-habibata (RA)
([5]) At-tirmiziy ya rawaito shi (lamba: 415), ya ce: hadisi ne hasan sahihu, kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu sunan At-tirmiziy, lamba: 833, 839). 
([6]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1182). 
([7]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 725). 
([8]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1159). 
([9]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 6410), da Muslim (lamba:  2677)
([10]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1416), kuma Albaniy ya inganta shi (Ta'aliqi ala ibnu-khuzaimata,  lamba: 1067). 
([11]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1418), da At-tirmiziy (lamba:  452), da Alhakim (1/ 306) kuma inganta shi, Azzahabiy ya yi masa muwafaqa, Albaniy kuma ya ce: ingantacce ne in banda faxinsa: (ta fiye muku alkhairi akan jajayen raquma), Duba: Sahihu At-tirmiziy,  lamba: 373). 
([12]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 990). 
([13]) Littafin Fat-hul bariy (2/ 557)
([14]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 755). 
([15]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 752, 753). 
([16]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 990). 
([17]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 738). 
([18]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 991). 
([19]) An-nasa'iy ya rawaito shi (lamba: 1698, 3/234), da Alhakim (1/304), da Albaihakiy (3/28, kuma lafazin nasa ne), Alhakim ya inganta shi, ya ce yana kan sharaxin Bukhari da Muslim, kuma Az-zahabiy ya masa "muwafaqa", An-nawawiy ya ce: An-nasa'iy ya rawaito shi da sanadi mai kyau, da Albaihaqiy da sanadi ingantacce (''Almajmu'u'', 4/17-18). 
([20]) Ad-daraqudniy ya rawaito shi (2/24-25), da Al-hakim (1/304), da Albaihaqiy (3/31), Ad-daraqudniy dangane da maruwaitansa yace: maruwaitansa dukkansu amintattu ne. Kuma Al-hakim ya inganta shi, akan sharaxin Bukhariy da Muslim, kuma Azzahabiy ya "wafaqa" masa, Ibnu-hajar a cikin ''Fat-hul bariy'' (2/558), ya ce: Isnadinsa yana kan sharaxin Bukhariy da Muslim . 
([21]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 737). 
([22]) Ibnu-majah ya rawaito shi (lamba: 1192), Albaniy ya inganta shi, (Sahihu sunani Ibni-majah, lamba: 980).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...