2015/02/12

LIKKAFANIN MUSULMI

TAMBAYA:
Yaya ake sanya likkafani ma gawa?

AMSA:
Likkafani na kasancewa ne da tufar da bata siffanta yanayin jiki (fata), kuma dole ne ya zama mai suturcewa, daga jinsin abinda irin wannan mutum ke sanyawa na tufa; saboda ba za a quntata wa mamaci ba, kamar yadda ba za a cutar da magadansa ba. Kuma sunna itace a yi wa xa namiji likkafani da lufafa guda uku, farare, na daga auduga, za a shumfuxa su akan sashinsu, sai a xora shi akansu a tsaye, sa'annan sai a dawo da vangarensa na sama ta gefen hagu i zuwa gefensa na dama, sa'annan qarshensa kuma ta dama i zuwa vangaren hagu, na biyun shima kamar haka, na ukun shima kamar haka, sa'annan sai a sanya abinda ya qaru a wajen kansa, kana kuma a xaure. Idan abinda ya qarun na da yawa, sai a sake tara shi ta wajen qafa a xaure. Wannan irin qulli shi yafi tamke likkafani; saboda faxin A'ishah (RA):
"كُفِّنَ رَسُولُ اللَّهِ r فِي ثَلاَث أَثْوَابٍ بِيضٍ، سَحُولِيَّةٍ جُدُدٍ يَمَانِيَةٍ، لَيْسَ فِيهَا قَمِيصٌ، وَلا عِمَامَةٌ، أُدْرِجَ فِيهَا إِدْرَاجًا"([1]).
Ma'ana: (An yi likkafani wa manzon Allah –SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA- cikin tufofi guda uku, farare, da aka yi da auduga qirar "sahuul" ta qasar Yemen, sababbi; babu riga a cikinsu balle rawani, an shigar da shi cikinsu shigarwa). Da kuma saboda faxinsa (SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA):
"الْبَسُوا مِنْ ثِيَابِكُمُ الْبَيَاضَ فَإِنَّهَا مِنْ خَيْرِ ثِيَابِكُمْ، وَكَفِّنُوا فِيهَا مَوْتَاكُمْ"([2]).
Ma'ana: (Ku sanya fari daga tufafinku, saboda yana daga cikin mafi alherin tufafinku, kuma ku yi likkafani wa mamatanku da shi).
Ita kuma 'ya mace akan yi mata likkafani da tufofi guda biyar na auduga; gyauto, da khimar, da riga, da kuma lufaya guda biyu.
Qaramin yaro kuma likkafaninsa ya kan kasance cikin tufafi guda xaya, amma ya halatta a masa likkafani da tufa uku.
Qaramar yarinya kuma; ana mata likkafani ne cikin riga da lufaya guda biyu.



([1]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 1264), da Muslim (lamba: 941), karshen hadisin yana wajen Imam Ahmad ne (6/118)
([2]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 3878), da At-tirmiziy (lamba: 1005), da Ibnu-majah (lamba: 1472), lafazin na tirmizi ne, At-tirmiziy yace: hadisi ne hasan sahihi, kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu At-tirmiziy, lamba: 792).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...