2015/02/19

SALLAR JUMA'A DA WASSU DAGA CIKIN HUKUNCE-HUKUNCENTA (صلاة الجمعة وأحكامها)

SALLAR JUMA'A:

Bismillahir rahmanir rahim.
Wassalatu wassalamu ala rasulillah, Bayan haka:
A nan –da izinin Allah- zamu gabatar da bayanai ne akan "sallar juma'a" da wassu daga cikin hukunce-hukuncenta, kamar haka:

NA XAYA: Hukuncin yin sallar juma'a da dalilinsa:
Zuwa sallar juma'a farilla ce akan mazaje; saboda faxin Allah maxaukaki:
{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلاَةِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ ، فَاسْعَوْا إِلَى ذِكْرِ اللهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ}  [الجمعة: ٩]
Ma'ana: (Ya ku waxanda suka yi imani idan aka kira sallah a ranar juma'a to ku tafi zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar kasuwanci) [Jumu'a: 9]. Da kuma saboda faxinsa (SAW):
"رَوَاحُ الْجُمُعَةِ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُحْتَلِم"([1]).
Ma'ana: (Tafiya sallar juma'a wajibi ne akan kowani baligi). Da kuma saboda faxinsa (SAW):
"لَيَنْتَهِيَنَّ أَقْوَامٌ عَنْ وَدْعِهِمُ الْجُمُعَاتِ، أَوْ لَيَخْتِمَنَّ اللهُ عَلَى قُـلُوبِهِمْ، ثُمَّ لَـيُكوننَّ مِنَ الـغَـافِلِين"([2]).
Ma'ana: (Wassu mutane su hanu kan barin halartar juma'o'i, ko kuma Allah ya yi rufi akan zukatansu, sa'annan su kasance daga cikin gafalallu rafkanannu). Annawawiy yana cewa:
"فيه: أنّ الجمعة فرضُ عَين"([3]).
Ma'ana: (A cikin wannan hadisin akwai bayani dake nuna cewa lallai sallar juma'a wajibi ce ga kowani mutum). Da kuma saboda hadisi mai zuwa bayan xan lokaci kaxan, wanda a cikinsa aka ce:
"الْجُمُعَةُ حَقٌّ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُسْلِم..."([4]).
Ma'ana: (Juma'a haqqi ne na wajibi akan kowani musulmi…).

NA BIYU: Ga wa juma'a take wajaba?
"Juma'a" tana wajaba ga kowani musulmi, namiji, xa, baligi, mai hankali, wanda ke da ikon halartarta, mazaunin gida; Bata kuma wajaba ga: Bawa, ko mace, ko yaro, ko mahaukaci, ko maras lafiya, ko matafiyi; wannan kuma saboda faxinsa (SAW):
"الْجُمُعَةُ حَقٌّ وَاجِبٌ عَلَى كُلِّ مُسْلِم فِي جَمَاعَةٍ إِلا أَرْبَعَةً: عَبْدٌ مَمْلُوكٌ، أَوِ امْرَأَةٌ، أَوْ صَبِيٌّ، أَوْ مَرِيضٌ"([5]).
Ma'ana: ("Juma'a" haqqi ne na wajibi akan kowani musulmi, ya yi ta a cikin jama'a, sai mutum huxu: Bawa da ake mulkarsa, ko mace, ko yaro, ko maras lafiya).
Matafiyi kuma juma'a bata zama wajibi akansa saboda annabi (SAW) bai kasance yana sallatarta ba a halin tafiye-tafiyensa ba, kuma yinin ARAFAH –a zamaninsa- ya dace da ranar JUMA'A, amma tare da haka sai ya sallaci AZAHAR, ya kuma haxa ta da LA'ASAR.
Amma matafiyin da ya sauka a garin da ake tsayar da juma'a to mafificin lamari akansa shine ya sallace ta tare da 'yan'uwansa musulmai.
Kuma idan da bawa ko mace ko yaro ko maras lafiya ko matafiyi suka halarci sallar juma'a to sallarsu ta inganta, kuma ta isar musu; ba sai sun yi sallar azahar ba.

NA UKU: Lokacin sallar juma'a:
Lokacin yinta shine lokacin yin sallar azahar; daga bayan rana ta yi "zawali" zuwa inuwar kowani abu ta zama kamar tsawonsa; wannan kuma saboda hadisin Anas xan Malik (RA) lallai annabi (SAW) ya kasance yana yin sallar juma'a a lokacin da rana take karkacewa([6]). Wannan kuma shine abinda aka rawaito daga sahabban annabi (SAW) daga aikinsu([7]). Don haka; duk wanda ya riski raka'a xaya kafin lokacinta ya fita to haqiqa ya riski juma'a, in kuma ba haka ba sai ya sallaci azahar; saboda faxinsa (SAW):
"مَنْ أَدْرَكَ رَكْعَةً من الصلاة فَقَدْ أَدْرَكَ الصَّلاة" ([8]).
Ma'ana: (Duk wanda ya riski raka'a xaya daga sallah to haqiqa ya riski wannan sallar).

NA HUXU: Menene ya haramta a ranar juma'a?
          Haramun ne "mamu" ya yi magana alhalin limami yana huxuba; saboda faxinsa (SAW):
 "مَنْ تَكَلَّمَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَالإِمَامُ يَخْطُبُ فَهُوَ كَالْحِمَارِ يَحْمِلُ أَسْفَارًا"([9]).
Ma'ana: (Duk wadda ya yi magana a ranar juma'a alhalin limami yana huxuba to kamar jaki ne da ke xauke da laftun littatafa). Da kuma saboda faxinsa (SAW):
"إِذَا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ: أَنْصِتْ، وَالإِمَامُ يَخْطُبُ فَقَدْ لَغَوْتَ"([10]).
Ma'ana: (Idan kace wa sahibinka: Yi shiru, alhalin limami yana huxuba to lallai ka yi wargi). ''Lagawu'' shine: magana na barna yasashshe.
Kuma haramun ne mutum ya tsallake wuyan mutane a lokacin huxuba; wannan kuma saboda faxinsa (SAW) ga mutumin da ya ganshi yana qetare wuyan mutane:
 "اجْلِسْ فَقَدْ آذَيْت"([11]).
Ma'ana: (Ka zauna saboda ka cutar). Lallai kuma cikin wannan aikin akwai cutar da masu sallah, tare da shagaltar dasu ko hana su sauraron huxuba.
Amma shi kuma limami ba laifi ya tsallake wuyan mamu idan ba zai iya zuwa wajen minbari ba har sai ya aikata hakan.
Kuma ''makruhi'' ne a raba tsakanin mutum biyu; wannan kuma saboda faxinsa (SAW):
"مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ ... ثُمَّ رَاح فَلَمْ يُفَرِّقْ بَيْنَ اثْنَيْنِ فَصَلَّى مَا كُتبَ اللَّهُ لَه... غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ الأُخْرَى"([12]).
Ma'ana: (Wanda ya yi wanka a ranar juma'a, … sa'annan ya tafi sallah, bai rabe tsakanin mutane biyu ba, ya kuma sallaci abinda aka qaddara masa… an gafarta masa abinda ke tsakaninsa da juma'a ta daban –ta gaba-).

NA BIYAR: Da me ake riskar sallar juma'a?
          Ana riskar sallar juma'a ne da riskar raka'a guda xaya tare da limami; saboda ya zo daga Abu-hurairah (RA), daga annabi (SAW) yace:
"مَنْ أَدْرَكَ مِنَ الْجُمُعَةِ رَكْعَةً فَقَدْ أَدْرَكَ الصَّلاة"([13]).
Ma'ana: (Duk wanda ya riski raka'a guda daga juma'a to haqiqa ya riski wannan sallar).
Amma idan ya riski abinda ke qasa da raka'a to a nan sai ya sallaci azahar.

NA SHIDA: Shin juma'a tana da wata nafila?
          Juma'a bata da wata sunna ta nafila da ake sallatarta a gabaninta, sai dai wanda ya sallaci gamammiyar nafila gabanin shigan lokacinta babu laifi ga hakan; saboda kwadaitarwan annabi (SAW) kan hakan, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Salman (RA) da ambatonsa ya gabata anan kusa da ke cewa: (Wanda yayi wanka a ranar juma'a, … sa'annan ya tafi sallar juma'a, bai rabe tsakanin mutane biyu ba, ya kuma sallaci abinda aka qaddara masa). Da kuma saboda sahabbai (RA) sun aikata hakan, Sannan kuma ''sallar nafila'' tana da girman falala.
Sai dai kuma ba za a yi "inkari" ga mutum ba idan har bai yi sallar nafila gabanin sallar juma'a ba; wannan kuma saboda ''sunna ratiba'' ta kan kasance ne, bayan yin sallar juma'a; raka'oi biyu, ko huxu, ko shida; saboda annabi (SAW) ya aikata hakan, kuma ya yi umurni da cewa a aikata shi; Ya zo cewa:
"كَان يُصَلِي بَعْدَ الْجُمُعَةِ رَكْعَتَيْنِ"([14]).
Ma'ana: (Annabi ya kasance yana sallatar raka'oi biyu bayan ya yi juma'a), An samu kuma  cewa annabi (SAW) yace:
"إِذَا صَلَّى أَحَدُكُمُ الْجُمُعَةَ فَلْيُصَلِّ بَعْدَهَا أَرْبَعَ رَكَعَاتٍ"([15]).
Ma'ana: (Idan Xayanku ya sallaci juma'a to ya sallaci raka'oi huxu a bayanta), a wata riwayah kuma:
"مَنْ كَانَ مِنْكُمْ مُصَلِّيًا بَعْدَ الْجُمُعَةِ فَلْيُصَلِّ أَرْبَعًا"([16]).
Ma'ana: (Duk wanda zai yi sallah daga cikinku bayan juma'a to ya sallaci raka'oi huxu).
Amma dangane da raka'oi shida kuma: To saboda ya zo daga Abdullahi xan Umar (RA) cewa lallai shi idan ya kasance a garin Makka sai ya sallaci sallar juma'a, to ya kan zakuxa gaba sai ya sallaci raka'oi biyu, Sannan ya qara zakuxawa gaba ya sallaci raka'oi huxu, idan kuma a garin Madina ya sallaci juma'ar; to sai ya koma gidansa ya sallaci raka'oi guda biyu bayanta, ba zai yi sallah a masallaci ba, sai aka masa magana, sai ya ce:
"كَانَ رَسُولُ اللهِ r يَفْعلُ ذَلِك"([17]).
Ma'ana: (Manzon Allah –SAW- ya kasance yana aikata haka).
          Daga abinda ya gabata sai ya bayyana cewa: lallai mafi qarancin ''sunna ratiba ta bayan juma'a'' shine: raka'oi biyu, mafi yawanta kuma shine: shida.
Wassu malamai kuma suna ganin cewa: in za a yi ''sunna ratiba'' ranar juma'a a masallaci  to sai a sallace ta raka'oi huxu, in kuma a gida za a sallace ta sai a yi raka'oi biyu([18]). Da wannan sai ya zama ana sallatanta akan halaye daban-daban.

NA BAKWAI: Ta yaya ake yin sallar juma'a?
          Sallar juma'a raka'oi ne guda biyu, ana bayyana karatu a cikinsu; saboda annabi (SAW) ya kasance yana aikata haka, aikinsa kuma wani yanki ne na sunnarsa, kuma malamai sun yi "ijma'i" akan haka. Kuma sunna ne limami ya karanta ''suratu aljumu'at" a raka'ar farko bayan ya karanta ''fatihah'', a ta biyun kuma ''suratu almunafiqun([19])'', ko kuma ya karanta ''suratu al'aalah'' a raka'ar farko, a raka'a ta biyun kuma ''suratu algashiyah([20])''; saboda annabi (SAW) ya aikata haka.

Wannan shine abinda ya sauwaqa na bayanai akan sallar juma'a, da wassu daga cikin hukunce-hukuncenta, da fatan Allah ya fahimtar da mu addininsa, amin!




([1]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1371, 3/89), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu aljami'i, lamba:  3521). 
([2]) Muslim ya rawaito su (lamba: 865). 
([3]) Sharhin Annawawiy ga sahihu Muslim (6/152). 
([4]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1054), Albaniy ya inganta shi (Irwa'u algalil, lamba:  592).
([5]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1054), Albaniy ya inganta shi (Irwa'u algalil, lamba:  592).
([6])  Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 904).
([7]) Ka yi dubi cikin littafin (Fat'hu albariy, 2/450). 
([8]) Abu-dawud ya rawaito shi, (lamba: 875), da Ibnu-majah (lamba:  468), kuma Albaniy ya inganta shi a cikin (Irwa'u algalil,  lamba:  496). 
([9]) Ahmad ya rawaito shi (10230), Alhafiz Ibnu-hajar a cikin Bulugu almaram yace: ''isnadinsa bashi da laifi'' (Subulu assalam, 2/101-102, hadisi mai lamba: 421)
([10]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 394), da Muslim (lamba: 851), ka duba littafin (Irwa'ul galil, 3/84)
([11]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1118), da An-nasa'iy (3/103), da Alhakim (1/288) kuma ya inganta shi, Azzahabiy ya masa muwafaqa, kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 910)
([12]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 910). 
([13]) Ibnu-majah ya rawaito shi (lamba: 1121), kuma Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah, lamba: 927, 928)
([14]) Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 937), da Muslim (lamba: 882)
([15]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 881)
([16]) Muslim ya rawaito shi (lamba: 881). 
([17]) Abu-dawud ya rawaito shi (lamba: 1130)
([18]) Duba littafin (zadu alma'ad, 1/440)
([19]) Muslim ya rawaito shi (lamba:  877)
([20])Muslim ya rawaito shi (lamba: 878).  

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...