2018/08/04

BULAGURO ZUWA GA HAJJI رحلة ملبي











BULAGURO ZUWA HAJJI
(رحلة ملبي)





TANADAR

(زاد)





TARJAMAR

ABUBAKAR HAMZA


         Allah ya umarci annabi Ibrahima (alaihis salam) da cewar ya daga ginin Masallaci mai alfarma, sa'annan ya kira mutane zuwa ga tafiya hajji, sai wannan wurin ya kasance mai albarka, kuma shiriya ga talikai, kuma zuwa gare shi, rayukansu su ke shauki, kuma zukatansu su ke karkata.         
Kuma a shekara ta tara (9) ta hijira ayar da ba a soke hukuncinta ba, ta sauka ga Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama), wanda take wajabta wa mutane hajjin dakin Allah, ga wanda ya samu hanyar zuwa gare shi, Sai hajjin ya kasance farilla daga farillan Musulunci, da rukuni daga cikin rukunnansa, Allah Ta'alah ya  ce:
"ولله على الناس حج البيت من استطاع إليه سبيلا ومن كفر فإن الله غني عن العالمين" [آل عمران: 97].
Ma'ana: (Kuma Allah ya wajabta wa mutane, ziyartar wannan dakin, ga wanda ya samu hanyar tafiya gare shi, kuma duk wanda ya kafirce to lallai ne Allah Mawadaci ne ga barin halittu) [Ali-imraana: 97].
         Don haka,
Ya zama wajibi ga Musulmi, ya yi gaggawan sauke farillar hajji, duk lokacin da ya kasance yana da iko, saboda bai san mai zai kasance tare da shi ba, idan ya jinkirta shi, saboda ya zo cikin hadisi daga Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama) lallai shi ya ce: 
"تعجلو إلى الحج –يعني الفريضة-، فإن أحدكم لا يدري ما يعرض له"، رواه أحمد.
Ma'ana: (ku yi gaggawan yin hajji –yana nufin na farilla- saboda dayanku bai san abinda ka-iya bijiro masa ba), [Ahmad ya ruwaito shi, 1/314, kuma Albaniy ya ce hadisi ne hasan [a cikin littafin Irwa'ul galil, 990].         
Kuma wajibi ne ga wanda ya yi azamar aiwatar da wannan farillar mai girma.
1-   SHIRI A GARE TA, ta hanyar gangariyar tuba.              
2-   DA IKHLASIN niyya ga Allah shi kaxai, sai ya nemi ganin fiskar Allah, da hajjinsa, da kuma gidan lahira.
3-   Sai kuma YA YI QOQARIN SAUKE HAQQOQI, DA BASUKA, DA KAYAN MUTANE DA SU KE HANNUNSA.
4-   Sai kuma ya yi WASIYYA GA IYALANSA DA BIN DOKOKIN ALLAH da taqawa.
5-   Sai kuma ya rubuta wasiyyarsa, idan akwai abinda zai yi wasiyyar da shi, na haqqoqi da wasunsu.
6-   Ya kuma TANADI GUZURI daga dukiya ta halal.
7-   Ya kuma nemi abokan tafiya nagari         
8-   Ya kuma KOYI FIKIHUN HAJJI da SIFAR HAJJI             
9-   YANA MAI YIN GUZURI DA LITTAFAN MA'ABUTA ILIMI da suke magana akan haka.
Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa sallama) ya ce:
"العمرة إلى العمرة كفارة لما بينهما، والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة".
"UMRAH ZUWA UMRAH YANA KANKARE ABINDA YA AUKU TSAKANINSU, SHI KUMA HAJJI GANGARIYA BASHI DA WANI SAKAMAKO FACE ALJANNAH", [Bukhariy da Muslim].

UMRAH; Falalarta da hukunce-hukuncenta العمرة فضائل وأحكام









UMRAH; Falalarta da hukunce-hukuncenta
(العمرة فضائل وأحكام)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Bege ne wanda baya karewa,
Da haniniyar shauki wanda bata yankewa,
Saboda zukatan Mutane suna gaggawar begen zuwa dakin Allah,
Shi kuma ruwan zamzam yana kosar da mai kishi,
Kuma daga FALALAR ALLAH TA'ALAH yadda ya sanya igiyar ziyara ta ke sade tsakanin bayinsa da dakinsa, saboda
"العمرة إلى العمرة كفارة لما بينهما، والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة".
Ma'ana: "Umrah zuwa umrah su kan kankare abinda ya auku a tsakaninsu, Shi kuma hajji mabruri bashi da wani sakamako sai Aljannah".
Ita kuma UMRAH
Yin harama ne
Da 'dawafi
Da sa'ayi tsakanin Safah da Marwah,
Sai aski ko rage gashi.

SIFAR UMRAH kuma shi ne:
Mutum ya yi harama daga MIKATI, sai ya tube kayan da suke jikinsa, ya yi wanka, ya shafa turare (a jikinsa kawai banda ihrami).
Sai mutum namiji ya sanya kwarjalle da mayafi,
Kuma abinda yafi falala shine su kasance farare,
Ita kuma Mace ta sanya abinda ta so, na tufafi na halal, ba tare da ta bayyanar da ado ba, in banda nikabi da safar hannu guda biyu, sai kuma ta rika suturce fikarta ga Maza, ta hanyar sake khimar dinta akan fiskarta.
Kuma zai yi niyyar shiga wannan ibadar ne, bayan sallar farilla, idan lokacinta ya shiga, ko kuma bayan raka'oin sunnar alwala ko makamancinta.
Kuma wajibi ne ga Mai harama ya rika nisantar mahzuratul ihrami (abubuwan da haramun ne a aikata su idan aka yi harama), kamar yin jima'i, da amfani da turare, da yanke gashi, da farautar dabbar tudu, da neman aure, da kulla aure ga maza da mata, da lullebe kai, da sanya riga da wanduna da safar kafa da makamantansu ga mazaje.
Kuma yana daga cikin sunnah YIN TALBIYYAH da fadinsa: LABBAIKAL LAHUMMA UMRAH,
LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL HAMDA WANNI'IMATA, LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA.
Kuma ba zai gushe ba yana yin Talbiyyar, har isa zuwa garin Makkah, sai ya yanke yin talbiyyar, sannan ya fara yin dawafi.
Kuma idan ya iso Masallaci mai alfarma, sai ya shige shi yana mai gabatar da kafarsa ta dama, yana mai cewa:
BISMILLAH, WAS SALATU WAS SALAMU ALA RASULIL LAH, ALLAHUMMAG FIR ZUNUBIY, WAFTAH LIY ABWABA RAHMATIK,
Sai ya fara yin dawafinsa, cikin tsarki,
Yana mai fara shi daga jikin hajarul aswad, yana mai shafa shi, ko sumbantarsa, idan har ya samu daman aikata hakan, idan kuma bai samu daman hakan ba, sai ya yi nuni gare shi, yana mai cewa, (a lokacin fara dawafin):
BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA IYMANAN BIK, WA TASDIYKAN BI KITABIK, WA WAFA'AN BI AHDIK, WATTIBA'AN LI SUNNATI NABIYYIKA; MUHAMMADIN sallal Lahu alaihi wa sallama.
Sa'annan sai ya sanya dakin ta hannunsa na hagu, sai ya kewaya shi da dawafi sau bakwai, yana mai faraway da hajarul aswad, yana mai kare su da shi.
Kuma sunnah ne Namiji ya yi abinda ake kiransa iddiba'i a dawafinsa gabadayansu, yana mai sanya tsakiyan mayafinsa karkashin kafadarsa ta dama, Geffan mayafin biyu kuma akan kafadarsa ta hagu.
Sai kuma ya yi sassarfa a kewaye guda uku na farko, ta hanyar yin tafiyar sauri, tare da kusantar tsakanin taku.
Kuma duk lokacin da ya zo daura da hajarul aswad sai ya sake kabbara.
Idan kuma ya kasance tsakanin RUKUNUL YAMANIY da HAJARUL ASWAD sai ya rika cewa:
RABBANA ATINA FID DUNYA HASANATAN WA FIL AKHIRATI HASANATAN WA KINA AZABAN NAAR.
Sai kuma ya marairaice ga Ubangijinsa a cikin sauran dawafinsa da abinda ya so na zikiri da addu'oi da karatun Alkur'ani, ba tare da ya ware wata addu'a kebantacciya ga kowane zagaye ba.
Idan y agama dawafinsa (bakwai) sai ya gusar da abinda ya yi na IDDIBA'I, sai ya lullube kafadarsa.
Sai kuma ya sallah raka'oi guda biyu, a bayan MAKAAMU IBRAHIMA, idan ya samu damar yin hakan, idan kuma bai samu dam aba, to a kowane wuri ya samu dama a wannan Masallacin.
Yana mai karantawa –a raka'ar farko-: KUL YA AYYUHAL KAFIRUNA, A ta biyun kuma ya karanta: KUL HUWAL LAHU AHAD.

Sa'annan sai ya nufi yin SA'AYI tsakanin duwatsun SAFAH da MARWAH, Kuma idan ya kusanci dutsen Safahsai ya karanta:
"INNAS SAFAH WAL MARWATA MIN SHA'AIRIL LAH" Abda'u bima bada'al Lahu bihi. Wannan kuma zai fade shi ne kawai a farkon sa'ayinsa kawai.
Sa'annan sai yah au dutsen SAFAH,
Sai ya fiskanci alkiblah,
Ya daga hannayensa
Yana mai yin kabbara yana gode wa Allah, Sa'annan ya ce:
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR.
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARAL AHZABA WAHDAH, WA HAZAMAL AHZABA WAHDAH. Zai maimata wannan zikirin ne har sau uku, sai kuma ya rika addu'oi da bukatun da yaga dama, a tsakanin kowane zikiri da wanda ke biye da shi. Amma ba zai yi addu'a ba, bayan fadin zikirin a karo na uku.
Sa'annan sai ya sauka domin tafiya dutsen MARWAH,
Idan ya isa zuwa ga alamomi biyu korra, sai Namiji ya yi gudu a tsakaninsu gudu mai tsanani. Idan kuma ya wuce alamomin sai ya cigaba da tafiya, irin tafiyarsa ta al'ada.
Idan kuma ya isa zuwa ga dutsen MARWAH sai ya hau kan dutsen, ya fiskanci alkiblah, sai kuma ya aikata irin abinda ya aikata lokacin yana kan dutsen SAFAH.
Sai kuma ya sauka da tudun dutsen MARWAH yana mai tafiya zuwa ga dutsen SAFAH, Yana mai aikata irin abubuwan da aikata a lokacin tafowarsa daga SAFAH zuwa MARWAH.
Idan har ya kamala zagaye bakwai, wato daga dutsen SAFAH zuwa MARWAH zagaye daya kenan, Sannan daga MARWAH zuwa SAFAH wani zagayen na daban. To a nan, sai ya aske gashin kansa gaba daya, ko ya rage shi, saidai askewan gabadaya shine yafi falala.
Ita kuma Mace zata rage kamar kan yatsa daga dukkan bangarorin gashin kanta.
To idan maniyyaci ya aikata haka, umrarsa ta cika, kuma ya warware daga haramarsa.

Muna rokon Allah Ta'alah ya karbi umrar masu umrah, da sauran ayyukansu.

ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'DAH خصائص شهر ذي القعدة









ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'DAH
(خصائص شهر ذي القعدة)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Allah ya fifita sashen watanni akan sashe,
"وربك يخلق ما يشاء ويختار".
Ma'ana: "Kuma Ubangijinka yana halitta abinda ya so, sai kuma ya yi zabi".
Kuma yana daga cikin watannin da Allah Ta'alah ya fifita su, WATAN ZULKA'ADAH, wanda kuma shine wata na goma sha daya (11) daga cikin watannin shekarar hijira.
Kuma an sanya masa wannan suna na zul-ka'ada ne, saboda labara a cikin wannan watan su kan zauna su bar yaki, saboda girmama wannan watan, kuma domin su shirya domin yin hajji a watan zul-hijjah.

Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WANNAN WATAN, Shine farkon watanni masu alfarma guda hudu, wadanda Allah Ta'alah yake cewa a kansu:
"إن عدة الشهور عند الله اثنا عشر شهرا في كتاب الله يوم خلق السموات والأرض منها أربعة حرمٌ، ذلك الدين القيم فلا تظلموا فيهن أنفسكم".
"Lallai kidayar watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne, a cikin littafin Allah, tun ranar da ya halitta sammai da kasa, a cikinsu akwai guda hudu masu masu alfarma, wannan shine addinin mikakke, don haka kada ku zalunci kayukanku a cikinsu".   
Kuma larabawa sun kasance suna daukar wadannan watannin (hudu) masu alfarma ne, saboda Mutane su samu aminci, a hanyarsu ta tafiya zuwa ga hajji, Sai musulunci ya zo, ya kara basu alfarma, kuma ya haramta fara yin yaki a cikinsu, kuma yay i hani kan zalunci a cikinsu, domin kara girmama lamarinsu, da kausasa lamarin yin zunubi a cikinsu, duk da cewa, yin zalunci lamari ne da aka yi hani akansa a cikin sauran watannin wadanda ba hudun nan ba.

Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'ADAH, Lallai shi yana daga watannin hajji, wanda niyyar hajji bata kulluwa sai a cikinsu, kamar yadda Allah Ta'alah yake cewa:
"الحج أشهر معلومات فمن فرض فيهن الحج فلا رفث ولا فسوق ولا جدال في الحج".
"Hajji watanni ne sanannu, kuma duk wanda yay i niyyar hajji a cikinsu, to babu kwarkwasa, babu fasikci, kuma babu jayayya a cikin hajji".

Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'ADAH, Lallai Annabi صلى الله عليه وسلم  ya yi umrarsa guda hudu ne, a cikin wannan watan, saboda an ruwaito daga Anas –Allah yakara yarda a gare shi-, "Lallai Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya yi umrah guda hudu, kuma dukkansu a watan zul-ka'adah ne, in banda wanda take tare da hajjinsa".
Nawawiy ya ce:
"Lallai Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- yay i wadannan umran ne gabadayansu a watan zul-ka'adah, saboda falalar wannan watan, kuma domin ya saba wa mutanen jahiliyya cikin haka, domin su sun kasance suna ganin yin umrah a cikin watanni masu alfarma guda hudu, daga cikin mafi girman fajirci".

YI MA KAI HISABI Hudubar Masallacin Annabi SAW ta Alhuzaifiy 21 zulkaadah 1439h daidai 3 August 2018M محاسبة النفس












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
              (صلى الله عليه وسلم)    
JUMA'A, 21/Zulki'ida/1439H
daidai da 03/Ogosdos/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
YI MA KAI HISABI
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YI MA KAI HISABI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ya ke karbar tuban bayinSa, yake yafe munanan ayyuka. Ya yalwaci dukkan komai da jin-kai da ilimi. Kuma cikin falalarSa yake ninninka kyawawan ayyuka, yake daga darajojin ma'abutansu.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Babu abinda ke gagaransa a cikin kassai, ko a cikin sammai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, wanda Allah ya karfafe shi da nasara daga wurinSa da kuma mu'ujizozi.
Ya Allah ka yi dadin salati  da sallama da albarka, ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu gaggawar aikata alkhairori.

Bayan haka:
Ku bi Allah Ta'alah da takawa; ta hanyar kusantarSa da abinda ke yardar da shi, da kuma nisantar abinda ke fusata shi, kuma yake kinsa.
kuma Lallai ne, wanda yayi takawa ya samu babban rabo kuma ya tsira, Wanda kuma ya bi son zuciyarsa, to ya tabe, ya yi hasara.

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Ku sani Lallai ne, samun rabon dan-adam da tsiransa ya rataya ne kan iya fin karfin ransa, da yin hisabi a gare ta, da sa mata ido; cikin dukkan kanana da manyan zantuka da ayyukansa, saboda duk wanda ya yi hisabi ga ransa, kuma ya yi dabaibayi ga zantukansa da ayyukansa, har da irin ababen da suke darsuwa a cikin zuciyarsa, sai ga abinda Allah yake so ya yarda, to lallai ya rabauta rabo mai girma, Allah Ta'alah yana cewa: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaba ga  UbangijinSa, sai ya kange kansa daga son rai * To lallai ne, Aljannah ita ce makomarsa" [Nazi'at: 40-41].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga UbamgijinSa yana da Aljanna guda biyu" [Rahman: 46].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, kuma rai ta yi dubin abinda ta gabatar domin gobe (kiyama), kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne akan abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi takawa, idan waswasi daga Shedan ya shafe su; har suka aikata zunubi, sai su tuna girman Allah, sai su komo cikin basira" [A'araf: 202].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ba sai nayi rantsuwa da Rai mai yawan zargin kanta ba" [Kiyamah: 2].
Maluman tafsiri suka ce: Allah ya yi rantsuwa ne da ran da take zargin kanta akan sakaci, wajen aikata wajibai, take kuma zargin kanta akan aukawa cikin wasu ayyuka na haramun, sai ta yawaita zargin kanta, har zuwa lokacin da lamarinta zai daidaita.
        Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya yi imani da Allah da ranar karshe, to ya fadi alkhairi ko ya yi shiru", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Wannan kuma ba zai kasance ba, sai ta hanyar yin hisabi ga rai.
        Kuma an ruwaito daga Shaddad bn Aus, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya biye wa son zuciyarsa, Sai yake kwallafa buri ga Allah", Hadisi ne hasan.
        Umar bn Alkhaddabi (رضي الله عنه) ya ce: "Ku yi hisabi ga kayukanku, gabanin a muku hisabi, kuma ku auna kayunanku gabanin a dora ku akan sikelin awu, kuma ku yi shiri domin babban hisabi".
        Kuma Maimun bn Mihran ya ce: "Mutum mai takawa, ya fi tsananta hisabi ga kansa, fiye da marowacin abokin gamayyar kasuwanci, ga abokin hadakar kasuwancinsa".
        Kuma Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Lallai ne mumini yana ganin zunubansa, kamar akan kololuwar dutse ne, wanda yake tsoron ya rikito akansa. Shi kuma fajiri yana ganin zunubansa ne, kamar wani kuda, wanda ya hau karan hancinsa, sai ya yi haka da hannunsa, wato ya kore shi da tafin hannunsa", Bukhariy ya ruwaito shi.
        Shi mumini –a har kullum- ya kan yi hisabi ga kansa, yana kuma kula da ransa, domin ya iya daidaituwa akan mafi kyan halaye; sai ya yi hisabi wa kansa akan ayyukansa, yana mujahadar kansa wajen ganin ya aikata ibadodi da da'oi; har ya iya aikata su da cikakken ikhlasi, suna tsaftatattu lafiyayyu daga abinda ka iya shiga cikinsu na bidi'oi, da riya, da jiji-da-kai da ganin aiki, yana neman dacewa ta hanyar aikinsa da ganin fiskar Allah, da samun rabon gidan lahira.
Kuma yana hisabi ga kansa domin ganin ya yi aiki na kwarai, kuma ya aikata shi yana mai dacewa da sunnar Annabi (صلى الله عليه وسلم), tare da lazimtar dawwama kan aikata aiki, ba tare da yin ridda ko dena aikin ba, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma wadannan da suka yi kokari ga neman yardarmu, to lallai za mu shiryar da su ga hanyoyinmu, kuma lallai Allah tabbas yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
        Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya yi jihadi, to lallai yana yin jihadin ne ga kansa, Kuma lallai Allah Wadatacce ne ga barin talikai" [Ankabut: 6].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Mu, mun saukar da littafi zuwa gare ka, da gaskiya, sai ka bauta wa Allah, kana mai tsarkake addini a gare shi * Kuma addini tsarkakakke na Allah ne" [Zumar: 2-3].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce, idan kun kasance kuna son Allah, sai ku bi ni, Sai Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, saboda Allah Mai gafara ne Mai jin kai" [Ali-imraana: 31].
Kuma Sufyanus Sauri ya ce: "Babu abinda na wahala masa wajen gyaransa, wanda yafi wahalar da ni, fiye da niyyata, saboda tana kokarin caccanzawa".
Kuma Fadl bn Ziyad ya ce: "Na tambayi Imam Ahmad kan niyyah, a cikin aiki; Na ce: Yaya niyyar zata kasance? Sai yace: Ya yi ta fama da ransa, idan ya so yin aiki, har ya zama baya nufin mutane da wannan aikin".                                                                                                                                                                                              
Kuma an ruwaito daga Shaddad bn Aus, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Duk wanda ya yi sallah da niyyar riya, to lallai ya yi shirka. Wanda ya yi azumi da niyyar riya, to lallai ya yi shirka. Wanda ya yi sadaka da niyyar riya, to lallai ya yi shirka".
Ahmad a cikin littafin Musnad ya ruwaito shi, da Alhakim, da Dabaraniy a cikin littafin mu'ujamul kabir.
Kuma mutum ya rika hisabi ga ransa akan furucinsa da maganarsa; ta yadda ba zai rika sakan harshensa wajen fadin yasassun maganganu ba, da kuma laffuza na haram. Kuma ya rika tuna cewa, lallai Shi an wakilta Mala'iku biyu suna rubuta dukkan abinda harshensa ke furtawa, da dukkan abinda ya aikata na ayyuka; sai kuma a masa sakayya akan haka, ko a masa ukuba, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma lallai akanku akwai Mala'iku masu kiyayewa, * masu karamci, marubuta * suna sanin duk abinda kuke aikatawa" [Imfidar:10-12].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ba zai furta wata magana ba, face a tattare da shi, akwai mai tsaro, halartacce" [Kaaf: 18].
An ruwaito daga Abdullahi bn Abbas (رضي الله عنهما) lallai ya ce: "Lallai akan rubuta dukkan abinda mutum ya yi magana da shi; na alheri da na sharri; har a rubuta fadinsa cewa; Na ci kaza, na sha, na tafi, na zo, na ga".
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Mutum ya kan fadi ko furta kalma, wanda Allah ya yarda da ita, ba tare da ya kai tunaninsa ba, sai Allah ya daga darajojinsa da ita. Kuma lallai bawa, ka iya fadin wata kalma, wanda take fusata Allah, ba tare da ya kai tunaninsa ba, sai ta gangarar da shi cikin wutar Jahannama" , Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Abdullahi bn Mas'ud ya ce: "Na rantse da Allah wanda babu abin bautawa face shi! A bayan kasa, babu wanda yafi cancantar a tsawaita dabaibayi a gare shi, fiye da harshe".
Kuma Abubakar (رضي الله عنه) ya kasance yana kama harshensa sai ya ce: "Wannan shine ya aukar da ni wuraren halaka".

Kamar yadda ya wajaba ga Musulmi ya rika hisabi ga ransa, yana kuma yakarta, akan ababen da suke darsuwa, da wadanda suke-kaiwa suna komowa a cikin zuciyarsa, da ababen da suke masa waswasi, domin mafarin alheri da sharri; dukkansu daga ababen da suke darsuwa ne a cikin zukata, suna kaiwa-suna komowa;
Don haka, idan musulmi ya iya sanya wa ababen da suke kaiwa suna komowa a cikin zuciyarsa dabaibayi, har ya zama yana farin ciki da abin alkhairin da suke kai-komo, yana natsuwa da su, yana kuma zartar da su cikin aiki, to sai ya tsira; ya kuma rabauta.
Haka idan ya kori waswasin Shedanu, da abinda shedan ke sanya masa, kuma ya nemi tsarin Allah daga waswasinsa, to sai ya tsira daga sharrinsa ya kubuta ya samu salama daga aikata munanan ayyuka da sabo.
Idan kuma ya gafala daga waswasin ransa, ya karbe su –hannu bibbiyu-, to sai su kai shi zuwa ga aikin haramun; Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan wata fizga daga Shedan ta fizge ka, sai ka nemi tsarin Allah, lallai ne shi Mai ji ne Masani" [Fussilat: 36].
Kuma Allah a cikin suratun Naas, ya bada umarnin a rika neman tsarinsa daga wannan makiyin mabayyani (wato Shedan); Abdullahi bn Abbas ya ce: "Lallai Shedan yana lazimtar zuciyar kowane dan-adam, idan ya yi mantuwa ya gafala, sai ya sanya masa waswasi, idan kuma ya ambaci Allah, sai ya buya".
Kuma an ruwaito daga Anas (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Shedan ya kan sanya mummunan hancinsa, akan zuciyar dan-adam; amma idan mutum ya ambaci Allah, to sai shedan ya buya, idan kuma ya manta da Allah, sai ya lankwame zuciyarsa, to wannan shine mai sanya waswasi a boye a cikin kirazan mutane", Abu-Ya'alah Almusily ya ruwaito shi.

Kiyaye aukawa cikin zunubai yana kasancewa, a matakin farko, ta hanyar kididdige waswasin da Shedan ke sanyawa, da kare kai daga fizgar shedanu, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma kada ku kusanci alfasha; abinda ya bayyana daga cikinta, da wanda ya buya, kuma kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta kasha ta, face da hakki, Wannan ne Allah yake muku wasiyya da shi, tsammaninku ku hankalta" [An'aam: 151]. Rashin kusantan alfasha yana kasancewa ne, ta hanyar yin hisabi ga rai, a lokacin faruwan sabubansu.

Don haka, duk wanda ya ke hisabi ga kansa, ya ke yakarta, sai kyawawan ayyukansa su yawaita, munanan ayyukansa su karanta, sai kuma ya fita daga duniya yana abin yabo, a tayar da shi bayan mutuwa yana mai rabauta, sai ya kasance tare da Annabi (عليه الصلاة والسلام) wanda aka turo shi domin ya zama mai bada shaida.
Wanda kuma ya rika biye wa son zuciyarsa, ya juya baya ga Kur'ani, sai yake aikata dukkan abinda ransa ta yi sha'awa, har yake jin dadin ababen sha'awa, yake dulmuya cikin laifukan kaba'irai, ya kuma baiwa Shedan akalar jagorancin zuciyarsa, to sai Shedan ya aukar da shi cikin dukkan zunubi mai girma, sai kuma a dawwamar da shi tare da Shedan cikin azaba mai radadi, Allah Ta'alah yace: "Kuma kada ka  bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu, sai ya bi son zuciyarsa, alhalin al'amarinsa yana a watse" [Kahf: 28].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ke rayar da zukata da wahayin Alkur'ani, yana karbar kyawawan ayyuka, kuma yana yin afuwa ga munanan ayyuka.
Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masanin ababen da suka buya,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai kira zuwa ga aikata alkhairori,

Ya Allah ka yi dadin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa; jagororin shiriya, kuma fitilun haskaka dufu.

Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah, iyakar takawa, saboda tsoron Allah shine mafi alherin tanadi a duniya da lahira,

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai rayayyar zuciya, Itace, wanda kyakkayawan aikinta ke faranta mata, mummunansa kuma ke bakanta mata.
Matacciyar zuciya kuma, itace wanda bata jin radadin aikata zunubi, kuma bata damuwa kan haka, kuma bata yin farin ciki kan aikata kyakkayawan aiki, ko biyayya; kuma bata damuwa da ukobobin da aka rataya ga zunuban; Sai ni'imar lafiyar jiki, da yadda duniya take fiskanto masa, ta rude shi. Har ya rika zaton ni'imar da aka bashi, wata karama ce a gare shi daga Allah, Allah Ta'alah yana cewa: "Shin zato, suke yi, cewa lallai abinda muke karfafarsu da ita na dukiya da 'ya'ya, * muna gaugawan basu alheri ne? Kai dai basu sani ba" [Mu'uminuna: 55-56].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa, "Lallai ana bijirar da fitintinu ga zukata, kamar yadda ake bijiro da tabarma; tsinke-tsinke. Kuma duk zuciyar da ta kyamaci fitina, sai a sanya mata farar alama. Duk kuma zuciyar da ta kwankwadeta, sai a zana mata bakar alama; har zukatan su wayi gari, kamar zuciya guda biyu; zuciya fara kal, kamar falalen dutse; wanda wata fitina ba ta cutar da ita, tsawon dawwamar sammai da kassai. Da zuciyar da tayi baki; launinta ya caccanza, kamar kofin da aka kife shi, wato aka mayar da kansa kasa; wanda bata sanin aiki mai kyau, kuma bata iya kyamatar mummuna, in banda wanda ta  kwankwada na bin son zuciyarta".

Kuma dukkan cutukan zukata, suna sanya zuciyar jinya, ko su kashe ta kurmus gabadaya, matukar mutum bai rika yin hisabi ga zuciyarsa ba.
Kuma yana daga cikin azama da alheri ga mutum, ya rika yin hisabi ga ransa a cikin yini da dare, da sati, da wata, da shekara, domin ya rika gano ta ina Shedan ya kutso masa, sai ya tuba, kuma domin ya iya risko abinda yayi sakaci a cikinsa, da fatan a yaba wa ayyukansa, a kuma datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe.

Shi Mumini; zuciyarsa rayayya ce, mai zurfin basira, Idan aka bashi; sai ya yi godiya, idan kuma ya aikata zunubi, sai ya tuba, idan kuma aka jarrabe da wani ibtila'i, sai ya dangana ya yi hakuri; saboda a cikin zuciyar mumini akwai mai masa wa'azi, da ke farkar da shi daga gafala, mai tsoratar da shi daga aukawa halaka, saboda ya zo cikin wani hadisi cewa:
"Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya zana mana mikakken zane,
sai ya zana wasu zanen ta geffansa,
kuma akan wannan zanen, akwai wani mai yin da'awa,
A samansa kuma akwai mai wa'azi;
SHI WANNAN MIKAKKEN ZANEN, SHINE: HANYAR ALLAH,
MAI YIN KIRA KUMA AKAN WANNAN HANYAR SHINE LITTAFIN ALLAH,
WANDA KUMA YAKE WA'AZA A SAMAN WANNAN HANYAR, SHINE MAI WA'AZI ZUWA GA ALLAH WANDA KE CIKIN ZUCIYAR KOWANE MUMINI,
SU KUMA HANYOYIN DA SUKE TA DAMA DA HAGUN DINSA, SUNE HANYOYIN BATA".

        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...