TSAWATARWA
KAN WAKA DA KAYAN KIDA
(التحذير من الغناء وألات الطرب)
Na
Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah
ya yi masa rahama
Tarjamar Abubakar Hamza
Lallai
sauraron waka haramun ne, abun kyama, kuma yana cikin sabubban rashin zukata da
kaikashewarsu, da kangewa su daga ambaton Allah, da kin yin sallah.
Kuma
hakika mafi yawan ma’aboba ilimi sun fassara fadin Allah Ta’alah: "WA
MINAN NAASI MAN YASHTARIY LAHWAL HADISI".
“Daga cikin Mutane akwai masu sayen
zancen wargi …” zuwa karshen ayar, da cewa shine: Waka.
Kuma Abdullahi dan Mas’ud (R.A) yana
yin rantsuwa cewa lallai: shine: Waka.
Idan kuma ya zama a tare da wakar
akwai kayan wargi, kamar sharewa, da tsinke, da kamman, da ganga, to haramcin
yafi tsanani.
Wasu Malamai sun ambaci cewa, Wakar
da ta hadu da kayan wargi to haramun ne da ijma’i.
Don haka, wajibin shine a kiyaye
aikata hakan.
Kuma hakika ya inganta daga Manzon
Allah (S.A.W) lallai shi ya ce: (S.AW) ya
ce: "Wasu
Mutane za su kasance daga al’ummata, suna neman halatta zina (Alhira) da
alharir (ga Maza), da giya, da kayan kida".
Abun da ake nufi da (Alhira) shine
farji na haram, wato zina.
(Ma’azif) shine: Waka, da kayan
kida.
Ina maka wasiyya da sauran Mutane da
sauraron Iza’atul Kur’anil karim, da shirin: Nurun alad darb, saboda a cikinsu
biyun akwai fa’idodi mkasu girma, kuma sauraronsu aiki ne da zai shagaltar da
kai daga sauraron waka da kayan kade-kade([1]).
No comments:
Post a Comment