TSAWATARWA
DAGA ASKE GEMU
(التحذير من حلق اللحية)
Na
Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah
ya yi masa rahama
Tarjamar Abubakar Hamza
Aske gemu haramun ne, saboda saba wa Manzon
Allah ne (S.A.W),
domin Annabi (S.A.W) ya ce: "Ku cika gemu, ku rage gashin baki". Kuma saboda
askwar ficewa ne daga shiriyar Manzanni, zuwa ga shiriyar masu bautar Wuta
(Majusawa) da Mushirkai.
IYAKAR GEMU (LIHYAT) –Kamar yadda masanan
harshen Larabci suka fada- shine: Gashin da ya tsiro a fiska, da muka-mukai
biyu, da kumatu biyu; Ma’anar wannan shine: Duk abinda ya tsira a jikin kumatu
biyu, ko a muka-mukai biyu, da haba, to wannan yana daga cikin gemu (lihyat).
Kuma cire wani abu daga cikin hakan ya shiga cikin sabo, domin Annabi (S.A.W) ya ce:
"Ku cika gemu", "Ku sake gemu",
“Ku tara gemu”, “Ku ajiye gemu”. Wadannan kuma sai suka nuna cewa, lallai bai
halatta a cire wani abu daga jikin gemu ba. Saidai saboda kasancewar sabo
mataki-mataki ne, sai aske gemun gaba dayansa yafi muni, akan yanke wani abu
daga jikinsa, domin askewan yafi girma kuma yafi rage shi nuna sabawar mai
aikata hakan ga Sunnah. Wannan kuma shine gaskiya, kuma ita ce, tafi cancantar
a bi ta.
Kuma ka tambayi kanka: Mai zai hana ni karbar gaskiya, da yin aiki da
ita, domin yardar da Allah tare da neman ladansa? Don haka, kada ka fifita son
rai, da ganin damarka,ko abinda abokai suke so, akan yardar Ubangijinka, Allah
Ta’alah ya ce: "Amma
wanda ya ji tsoron tsayuwa ga UbangijinSa, sai ya hana ransa abinda take so *
To lallai Aljannah ita ce, makoma a gare shi”
[40-41].
Shi kuma rage gashin gemu, ya saba wa abinda Annabi (S.A.W) ya bada umurni a cikinj fadinsa: “Ku tara gemu”, "Ku bar gemu", "Ku sake gemu"; Don haka, Wanda ya so bin umurnin Manzon
Allah (S.A.W) da bin shiriyarsa (S.A.W), to kada ya ciri wani abu daga gemunsa;
domin shiriyar Manzon Allah (S.A.W) ita ce, kada
Mutum ya cire wani abu daga gemunsa. Kuma hakan (wato tara gemu) ita ce
shiriyar Annabawan da suka gabace shi, saboda dukkanmu mun karanta fadin Allah
Ta’alah dangane da Haruna ga annabi Musa: "Ya dan mamata: Kada ka kama min gemuna, ko kaina". Wannan kuma dalili ne akan cewa, lallai
Annabi Haruna yana da gemun da za a iya damkewa. Kuma hakan shine shiriyar
cika-makon annabawa; Muhammadu (S.A.W) domin
gemunsa ya kasance mai tarin yawa, cikakkke. Don haka; Duk wanda ya so ya bi
Annabi cikakken bi, ya kuma bi umurninsa
sau da kafa, to kada ya aske komai daga gemunsa; ta fiskar tsawonsa ko fadinsa.
Wasu Mutane a farkon farin fitowar gemunsu, ya kan
kasance gashi ne a rarrabe, sai Mutum ya ce: zai aske shi, domin gashin su fito
gaba daya a tare. Wannan kuma ba daidai ba ne; saboda Mutum zai iya askewan, ya
zama ya saba umurnin Annabi (S.A.W) da
aikata hakan, sai kuma ya mutu gabanin sake tsirowar gemun. Wajibin shine ya
bar gemun kamar yadda ya kasance,saboda idan gemun y agama girmansa ko
fitowansa, to ya kan taru cikin yanayi mai kyau.
Allah
ne Mai datarwa ([1]).
Your Affiliate Profit Machine is waiting -
ReplyDeleteAnd making money with it is as easy as 1---2---3!
This is how it all works...
STEP 1. Input into the system which affiliate products the system will promote
STEP 2. Add some push button traffic (this LITERALLY takes 2 minutes)
STEP 3. Watch the system grow your list and sell your affiliate products for you!
Are you ready to start making money???
Click here to launch the system