2019/11/28

TSAWATARWA DAGA DAUKAN FOTO (التحذير من التصوير)


TSAWATARWA DAGA DAUKAN FOTO
(التحذير من التصوير)
Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz
Allah ya yi masa rahama

Tarjamar Abubakar Hamza
Yabo naAllah ne shi kadai.
Salati da sallama su kara tabbata ga wanda babu Annabi a bayansa, Bayan haka:
Hakika hadisai masu yawa sun zo daga Annabi (S.A.W) a cikin littatafan Sihah da Masanid da Sunan, masu nuni akan haramcin daukar foton dukkan abu mai rai; dan adam ne ko waninsa, wasu kumaakan lamarin keta labulen da a jikinsa akwai fotuna, da umurni kan shafe fotuna, da tsinuwa ga masudaukar foto,  da bayyana cewa sune Mutanen da suka fi samun tsananin azaba a ranar kiyama.
Kuma lallai zan Ambato maka wasu daga cikin hadisai ingantattu,wadanda suka zo a wannan babin, kuma sai na bayyana menene daidai a wannan mas’alar,idan Allah ya so.  
Ya zo cikin Sahihul Bukhariy da Muslim, daga Abu-Hurairah (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "Babu wanda yafi girman zalunci, kamar wanda ya tafi yana yin halitta, kamar halitta ta, sai su halicci kwayar zarrah, ko kwayar hatsi, ko alkama", Lafazin na Muslim ne.
Kuma a cikin Bukhariy da Muslim daga Ibnu-Mas’ud (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai Mutanen da suka fi tsananin azaba a ranar kiyama sune masu daukar foto".
Kuma ya zo a cikin Bukhariy da Muslim daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: Manzon Allah (S.AW) ya ce: "Lallai wadanda suke sana’anta wadannan fotunan za a musu azaba ranar kiyama, sai a ce musu: ku rayar da abinda kuka halitta", Lafazin na Bukhariy ne.
Kuma Bukhariy ya ya ruwaito a cikin Sahihinsa daga Abu-Juhaifah (R.A) lallai Annabi (S.AW) ya yi hani kan cin kudin jini, da kudin kare, da dukiyar karuwanci. Kuma ya la’anci mai cin riba, da wanda ya bayar da ita, da mai canza halitta, da wanda ta nemi a canza mata, da mai yin foto".
Kuma an ruwaito daga Ibnu-Abbas (R.A) ya ce: Na ji Manzon Allah (S.AW) yana cewa: "Wanda ya dauki wani foto a Duniya, za a tursasa masa ya busamasa rai, kuma ba zai iya ba", Bukhariy da Muslim.
Kuma Muslim ya fitar da hadisi daga Sa’id dan Abul Hasan, ya ce: Wani Mutum ya zo ga Ibnu-Abbas sai ya ce: Ni Mutum ne da nake daukar irin wadannan fotunan; ka min fatawa akansu? Sai ya ce: Matso kusa da ni, sai ya kusance shi, har ya sanya hannunsa akan kansa, sannan ya ce: "Dukkan mai yin foto yana cikin Wuta, za a sanya masa dangane da kowane foton da ya dauka, za a sanya mata rai, ta rika azabtar da shia cikin Jahannama". Sai ya ce: Idan babu makawa sai ka yi, to ka yi foton bishiyoyi, da abinda bashi da rai.
Shi kuma Bukhariy ya ruwaito fadinsa: Idan babu makawa sai ka yi, ne a karshen hadisin da ya gabata kafin wannan, da irin lafazin da Muslim ya ambato shi.
Kuma wadannan hadisan da abinda ya zo da ma’anarsu, suna yin nuni a zahiri, kan haramcin daukan foton duk wani abu mai rai. Kuma sun nuna cewa aikata hakan yana daga manyan zunuban da aka ambaci narkon Wuta akansu.
Kuma lallai sun game, duk nau’ukan foto, sawa’un foto ne mai inuwa, ko maras inuwa, kuma sawa’un foton a jikin Katanga ko labule ko riga ko madubi ko littafi ko a wanin haka yake.
Kuma babu banbanci a cikin haka, tsakanin foto masu jiki, da irin wadanda akazana su a jikin labule ko littafi ko makamancin haka, ko tsakanin fotunan ‘yan Adam da wasunsu; na daya daga halittu masu rai, ko tsakanin tsakanin fotunan masu mulki da malamai ko wasunsu, ballamarin haramcin foton masu mulki da maluma da sauran Mutanen da ake girmamawa shi yafi tsanani; domin an fi fitinuwa da wadannan. Kuma kakkafa fotunansu a majalisosinsu da makamancin haka, da girmama su yana cikin mafi girmar hanyoyin shirka, da yin bauta ga wanin Allah, kamar yadda hakan ya auku ga Mutanen annabi Nuhu.
Salatin Allah ya kara tabbata ga Annabinmu; Muhammadu, da iyalansa, da kuma amincinsa([1]). Amin.  


([1])MAJMU’U FATAWA IBNU-BAAZ, (4/ 210), a takaice.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...