TSAWATARWA
GA MAZA KAN TSAWAITA TUFAFI
(التحذير من إسبال الرجال)
Na
Shehun Malami Muhammadu dan Salih Al-usaimin
Allah
ya yi masa rahama
Tarjamar: Abubakar Hamza
Sake tufafi nau’i biyu ne:
NA FARKO: Ya kasance da
takama da alfahari, Wannan yana daga cikin zunibin kaba’irai, kuma ukubarsa
tana da girma, domin ya zo a cikin Bukhariy da Muslim, daga hadisin Abdullahi
bn Umar, lallai Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda yaja tufafinsa da takama, Allah
ba zai yi dubi gare shi ba, ranar kiyama". Kuma an
ruwaito daga Abu-Zarrin Algifariy (R.A), lallai Annabi (S.A.W ) ya ce: “Mutane
uku, Allah ba zai yi magana da su ba ranar kiyama, kuma ba zai yi dubi a gare
su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi Ya
ce: Sai Annabi ya maimata hakan sau uku, Abu-Zarrin ya ce: Sun tabe sun yi
hasara Ya Ma’aikin Allah! Su wanene Ya Manzon Allah (S.A.W)?
Ya ce: Mai sake tufafinsa, da mai yin gori, da
mai tallata kayansa da rantsuwar karya”. Wannan nau’in shine sake
tufafin da ya hadu da takama (da girman kai), Kuma a cikinsa akwai narkon nan; na
azaba mai tsanani; wanda kuma shine fadin: Allah ba zai yi dubi ga mai aikata
shi ba, kuma ba zai yi magana da shi ba, kuma ba zai tsarkake shi a ranar
kiyama ba, kuma yana da azaba mai radadi.
Wannan gamewar
da ta zo a cikin hadisin Abu-Zarrin (R.A) an kebance ta, da abinda ya zo a cikin
hadisin Abdullahi bn Umar (R.A), sai narkon da ya zo a cikinsa ya kasance ga
wanda ya aikata hakan (wato, take tufafinsa) cikin takama (da girman kai)
kawai; saboda aikin da kuma horon iri daya ne, a cikin hadisan biyu.
NAU’I NA BIYU NA
TSAWAITA TUFAFI: Shi
ne ya take su bada takama ko girman kai ba, Wannan kuma haramun ne, kuma ana
tsoron ya kasance cikin laifukan kaba’irai, saboda Annabi (S.A.W) ya fadi narkon Wuta akansa, domin ya zo a
cikin Sahihul Bukhariy, daga Abu-Hurairah (R.A), lallai Annabi (S.A.W) ya ce: "Abinda
ya zama kasa da idanun sawu biyu, na tufafi, to yana cikin Wuta".
Shi wannan hadisin ba zai kasance an kebance hukuncinsa
da hadisin Abdullahi dan Umar ba (wato, ba za a ce, azabar ta takaita ne ga
wanda ya take tufafinsa da takama kadai ba); saboda ukubar da ta zo a cikin
hadisan biyu ta banbanta da juna. Da kuma saboda hadisin Abu-Sa’id Alkhudriy
(R.A) wanda ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya
ce: “Tufafin Mumini zuwa rabin kwabri ne, Babu
laifi ko ya ce: Babu matsala akan abinda
ya kasance a tsakanin kwabrinsa da tsakanin idanun sawu biyu. Amma abinda ya
kasance kasa da idanun sawu toyana cikin Wuta, Kuma wanda ya ja tufafinsa da
takama (alfahari) Allah ba zai yi dubi gare shi ba", Malikya
ruwaito shi, da Abu-Dawud, da Nasa’iy da Ibnu-Majah,da Ibnu-Hibbana a cikin
sahihinsa.
Sai Annabi (S.A.W) ya
banbance tsakanin wanda ya ja tufafinsa da takama (da girman kai), da Mutumin
da tufafinsa sukakasance a kasa da idanun sawunsa biyu (ba tare da takamaba, ya
bayyana narkon azabar kowanne daga cikinsu).
Saidai Mutumin da ya kasance tufafinsa yana zamewa ko
zobewa ya rufe masaidanun sawunsa biyu,ba tare da nufi ba, alhalin yna bin
tufafin nasa yana daga shi, to wannan babulaifi akansa, domin a hadisin
Abdullahi da Umar da ya gabata, lallai Abubakar (R.A) ya ce: "Ya Manzon Allah! Lallai daya daga cunar tufafina yana
zamewa,saidai idan ina binsa, (ina dago shi), Sai Annabi (S.AW) ya ce: "Kai
bakakasance daga cikin masu aikata hakan da takama (girman kai ba)"([1]).
No comments:
Post a Comment