2018/03/01

hudubar 14 Jumadal Akhirah 1439 صلاح البدير daidai da 2 Maris 2018








HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
 JUMA'A, 14/JUMADAL AKHIRAH/1439H
Daidai da 2/MARIS/2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA




بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ku ji tsoron Allah; saboda tsoronsa shine daukaka a duniya, kuma samun tsira a lahira,

Kuma mutum ana ambatonsa, da ababe masu kyau, a bayan mutuwarsa,
Sai ka daukaka ginin ambatonka, ta hanyar aikata kyakkyawa
والمرأُ يُذكَرُ بالجمائل بعدَه   ### فارفعْ لذكرك بالجميل بناءَ
Kuma lallai, ka sani, za a sake ambatonka, a karo na-gaba
Sai ace, Wane ya kyauta, ko ace, Wane, ya munana
واعلم بأنك سوف تُذكَر مرةً  ### فيقال: أحسَنَ، أو يقال: أساءَ
Sai ka yi dabaibayi –Ya kai bawan Allah- ga harshenka, idan ba wa'azi zai yi, ko hikima zai furta, ko nasiha gamammiya, ko kalma daddada ba.

YA KU MUSULMAI!
Hakika shari'ar Allah ta zo da akidar tsakaitawa, da saukakawa, da sassautawa, da bada sauki, da fadadawa, da rangwame, da dauke kunci ga Mutane da Aljani. Allah Ta'alah ya ce: "ALLAHU KUMA, BAI SANYA MUKU KUNCI, A CIKIN ADDINI BA" [Hajj: 87].
Kuma Allah Madaukaki ya ce: "ALLAH YANA NUFIN YA YI SAUKI AKANKU, KUMA AN HALITTA MUTUM YANA MAI RAUNI" [Nisa'i: 77]. Wato, ya muku rangwame cikin shari'oinsa, da umarce-umarcensa, da haninsa, da cikin abinda ke kaddara muku. "KUMA AN HALITTA MUTUM YANA MAI RAUNI", Wannan ya sanya, sassautawar ta dace da shi, saboda rauninsa, a karan-kansa, da raunin azamarsa da himmarsa.
        Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah –رضي الله عنه- daga Annabi –صلى الله عليه وسلم-, yana cewa: "Lallai addini yana da sauki, kuma babu mai tsanantawa a lamarin addini, face ya gallabe shi, Sai ku kwatanta daidai; ku kokarta, kuma albishirinku, kuma ku nemi taimako da ibadar safiya, da ta maraice, da wata a cikin duhun dare".
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai ku, al'umma ce, da aka nufe ta da sauki". A cikin wata riwayar kuma: "Lallai mafi alherin addininku shine mafi saukinsa". Ahmad ya ruwaito su.
Kuma an ruwaito daga Anas bn Malik –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku sassauta; kada ku tsananta, kuma ku natsu, kada ku kore mutane", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Kuma ya zo cikin abinda Bukhariy da Muslim suka ruwaito, Lallai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce, wa Mu'azu da Abu-Musa –رضي الله عنهما-, a lokacin da ya aike su, garin Yaman: "Ku yi, albishir; kada ku kore mutane, kuma ku saukaka; kada ku tsananta, ku hada kai; kada ku yi sabani".
Kuma ya zo, a littatafan sunan da masanid, lallai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "An turo ni da mikakken addini, mai sauki".
Yana daga ka'idodin shari'armu, Saukakawa
Cikin dukkan lamarin da tsanani ya shiga cikinsa
ومن قواعد شرعنا التيسير   ### في كل أمر نابه تعسير

Ba manufar saukakawa a cikin addini, ita ce, nemo, ko bibiyar saukakawar mazhabobin fikihu, da na zantukan maluma, don zabo maganar da tafi sauki daga cikinsu ba, A'a, Manufar ita ce, aiki da sauki irin na shari'a, a cikin lamuran da dalilai na shari'a su ka zo da saukakawa a cikinsu, kamar ga ma'abuta uzurori; misalign maras lafiya, da matafiyi, da karamin yaro, da wanin haka, na daga rangwantawa da saukakawa, a cikin farillai da wajibai; domin an ruwaito daga Abu-Hamza, ya ce: Na tambayi Abdullahi bn Abbas –رضي الله عنه- kan azumi a halin tafiya, sai ya ce: "Sauki da wahala, sai ka yi riko da saukakawar Allah".
Kuma an ruwaito daga Katadah, dangane da fadin Allah Ta'alah: -Allah yana nufin ya saukaka muku, baya nufin tsanani a gare ku- [Bakara: 185]. Sai ku yi nufi wa kanku, irin abinda Allah ya nufe ku da shi".
Kuma an ruwaito daga Ya'alah bn Umayyah, ya ce: Nace: wa Umar bn Alkhaddab: FadinSa: -Babu kunci akanku, ku yi kasarun sallah, idan kuka ji tsoron Kafirai za su fitine ku- [Nisa'i: 101] To, yanzu mutane suna cikin aminci (me yasa ake yin kasaru)? Sai ya ce, Nima nayi irin mamakin da ka yi, Sai na tambayi Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- akan haka, Sai ya ce: Sadaka ce, Allah ya ku, sai ku karbi sadakar Allah", Muslim ya ruwaito.
Wadannan ma'anoni ne masu girma, masu kyau, tabbatattu, a cikin shari'a, wanda basu nufin (mutum) ya kagi karya ya jingina wa Allah, ko mai fatawa ya riki tsakaitawar shari'a (الوسطية) da saukinta a matsayin abin dogaro, wajen yin zance akan shari'ar ba tare da ilimi ba, ko bada fatawa da abinda ya dace da son zuciya, ko bibiyar fatawowin masu rangwantawa, ba tare da hujjojin addini ba.
Azzahabiy –رحمه الله- ya ce: "Duk wanda ya harhada saukakawan mazhabobi, da kura-kuran da malamai mujtahidai suka auka, to addininsa, ya sakwarkwace".
Kuma Ibnu-Hazmin –رحمه الله- ya ce: "Akwai mutanen da sakwarkwacewan addini, da karancin tsoron Allah a wurinsu, suka kwashe su zuwa ga tattaro ko bin duk abinda ya dace da son zukatansu, daga zantukan masu magana; wadannan suna dauko ko yin aiki ne da duk abinda suka samu na sassautawar maluma, kuma basu neman abinda nassi daga Allah Ta'alah, da ManzonSa –صلى الله عليه وسلم- suka hukunta".
Kuma Imam Ahmad ya ce: "Da mutum zai yi aiki da kowace maganar rangwantawan, da ya samu, to da ya zama fasiki".
An ruwaito daga Alhasan, ya ce: "Na rantse da wanda babu abin bautawa da gaskiya face Shi, Sunnah tana tsakanin mai wuce iyaka da mai gajartawa; sai ku yi hakurin riko da ita –Allah ya muku rahama-, domin Ahlus-Sunnah sun kasance sune mafi karanci a baya, Kuma sune suka fi karanci cikin abinda zai zo. Kuma sune wadanda basu tafi tare da masu folewa cikin folewarsu ba, kuma basu tafi tare da 'yan bidi'a cikin bidi'arsu ba, sai suka hakurtar da kansu akan sunnah, har zuwa haduwa da Ubangijinsu, To, kuma ku kasance kamar haka –Insha Allahu-".
Kuma Aliyu –رضي الله عنه- ya ce: "Lallai malami na hakika, shine wanda baya sanya mutane debe tsammanin rahamar Ubangijinsu, kuma baya sanya su amintuwa daga azabar Allah, kuma baya musu rangwame cikin sabon Allah, kuma baya kyale Kur'ani zuwa ga waninsa. Kuma babu alheri cikin ibadar da babu ilimi a cikinta, kuma babu alheri cikin ilimin da babu zurfin fahimta tare da shi".

        Yana daga IBTALA'I, Yadda wasu mutane ke gaggawar kakkafa kayukansu a matsayin masu bada fatawa, alhalin dayansu a tsakanin maluma, bako ne, wanda ba a sanshi da ilimi ba, domin bashi da wani makami ko rabo na ilimin da zai yi fatawa.
Abinda ke kara rudar da irin wadannan shine, tambayoyin da jahilai ke gabatar musu, da kuma yadda wadanda suka gaza su a jahilci ke gaggawan zuwa daukar fatawarsu.
Imamu Malik –رحمه الله- yana cewa: "Wani mutum ya bani labari, cewa lallai shi, ya shiga wurin Rabiy'ah bn Abdurrahman, sai ya same shi yana yin kuka, sai ya ce masa: Me ya sanya ka kuka? Wata musiba ce, ta sauko maka? Sai ya ce: A'a, saboda an yi fatawa ga wadanda basu da ilimi, kuma lamari mai girma ya bayyana a cikin musulunci. Sai kuma ya ce: Lallai sashen wadanda suke yin fatawa a nan, sune suka fi cancantar zaman gidan kurkuku, fiye da barayi".
        Kuma duk lokacin da, mutanen da suka jahilci manufofin shari'a, wadanda basu fahimci yadda ake samo hukunce-hukuncenta ba, masu kiri-fadi kan ma'anoninta da zato, masu kutse a cikin ilimi; wadanda basu samu tabbatuwa cikin ilima ba, masu kutsawa ga mazatar cakudar mas'aloli ba tare da sun mallaki abin tantancewa ba, masu tsunduma ga aikin fatawa, ba tare da ilimi ko tanadi ko shiri ba, = to sai a canja addini a karkatar da shi a jirkita shi, kuma sai a ketare iyakar shari'a kuma a mata rauni, daga nan sai a yada bakin fatawoyi cikin al'umma, da yasassun maganganu, wadanda suke fitowa daga mutanen da basu da gogewa wadanda suke rushe musulunci, suke kawo masa koma-baya, suke kawo balbalin bala'i da fitina, Sai kuma a fitini masu raunin hankula da ilimi da addini, sai gaskiya ta bayyana cikin rigar barna, barna kuma a rigar gaskiya.  
       
Kuma yana daga kiren karya ga Allah, ko yin karya ga shari'arsa da bayinsa, abinda wadanda suke neman samun ababen duniya na gaggawa, kuma mai gushewa, suke aikata shi na saurin bada fatawa ba tare da ilimi ba, da laka wa Allah Ta'alah magana ba tare da hujja ba, da bada fatawa gwargwadon sha'awa, da bada amsar wata fatawar ga wata fatawar, da riko da maganganun masu sassauci masu saba wa dalili ingantacce, da nemo bakin maganganu (شواذ) fandararru, wadanda madogararsu dalilai ne da aka soke aiki da su, ko masu rauni, Wadanda barnar da ke cikinsu masu yawa, da tasirinsu mummuna masu girma, ga musulunci da ma'abutansa, basu buya ga wanda ke da basira koda karama ce, irin maganganun da babu mai fadinsu, sai wanda ya wofintar da zuciyarsa daga girmama Allah da tsoronsa, wanda aka rayar da zuciyarsa da son duniya, da neman samun gindin zama da kusanci ga wasu halittun, ba Mahalicci ba.
Wani daga cikin magabata yana cewa: "Mutumin da yafi dukkan mutane tabewa shine wanda ya sayar da lahirarsa da duniyarsa, wanda kuma yafi shi tabewa shine wanda ya sayar da lahirarsa da duniyar waninsa".
Ku saurara!
Irin wadannan mutanen, su rika tuna ranar tunzuri da faduwa, wanda gabbai da bangarorin jiki a cikinsa ke bada shaida, sai a bayyanar da abinda ke cikin kiraza, a kuma tone abinda ke cikin kaburbura, To a wannan yinin ne, masu yaudara za su san cewa lallai su suna yaudarar kayukansu ne, kuma sun yi wasa ne, da addininsu, "Kuma ba ga kowa suke makirci ba, face ga rayukansu, saidai basu san da haka ba" [An'am: 123].
"Domin su dauki dakon zunubansu cikakku, a ranar kiyama, da kuma zunuban wadanda suka batar da su, ba tare da ilimi ba, Kuma abinda suke dauka na zunubai ya munana" [Nahl: 25].
Mutane ne, wadanda a babin ilimi karatunsu ya zama kadan, kuma nazarinsu da bincikensu ya karanta, suke dimuwa, suke bayyanar da ababen da suke cin karo da shari'a mai haske, kuma suke magana da suna ko yawun musulunci, suke fadan abinda musuluncin ya barranta daga gare shi.

Kuma Suhnun bn Sa'id –رحمه الله- ya yi gaskiya a inda yake fadin cewa: "Wanda yafi mutane gaba-gadin bada fatawa, shine ya fi su karancin ilimi, saboda mutum ya kan iya babi daya na ilimi, sai ya yi zaton gaskiya dukkanta lallai tana cikin babin"  
Ibnu-Wahab yake cewa: "Naji Malik yana cewa: Gaggawan bayar da fatawa, nau'i ne na jahilci da wauta".
Kuma Malik –رحمه الله- ya ce, "Ban fara bayar da fatawa ba, sai da maluma saba'in suka ban shaidar cewa ni, na cancanci hakan".
Kuma Abdurrahman bn Mahdiy yace: "Mun kasance, a wurin imam Malik, sai wani mutum ya zo masa, ya ce, Ya Abu-Abdillahi! Na zo wurinka daga kimanin tafiyar watanni shida, kuma mutanen garina sun dora min alhakin na maka wasu tambayoyi , Sai mutumin ya masa wata tambaya, sai Malik ya ce: BAN SAN AMSARTA BA, Sai mutumin ya dimauta! Sannan ya ce, me zan fada wa mutanen garina, idan na koma wurinsu? Sai ya ce, ka ce musu: Malik ya ce: BAN SAN AMSAR BA".
Marwaziy ya ce: "Na ji Abu-Abdillahi yana cewa: Lallai mutum ya ji tsoron Allah, kuma ya yi dubi kan abinda yake fadi da abinda yake magana da shi, saboda lallai za a masa tambaya".
Wani daga cikin magabata ya ce: "Dayanku ya ji tsoron ya rika cewa: Allah ya halatta kaza, ko ya haramta kaza, domin kada Allah ya ce: Ka yi karya, ban halatta kaza ba, ban haramta kaza ba".
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku ce, domin abinda harsunanku ke siffantawa da karya, wannan halas ne, kuma wannan haramun ne, domin ku kirkira karya ga Allah, lallai ne wadanda suke kirkira karya ga Allah ba za su ci nasara ba * Jin dadi ne kadan, kuma suna da wata azaba mai radadi" [Nahl: 116-117].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce abin sani kawai, Ubangijina ya hana abubuwan alfasha; na bayyane daga cikinsu, da wanda ya buya, da zunubi, da zalunci, ba da wani hakki ba, kuma ya haramta ku yi shirki da Allah, ga abinda bai saukar da wani dalili ba gare shi, kuma ya haramta ku fadi abinda baku sani ba gare shi" [A'araf: 33].

        Ina fadan abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa; lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamari gare shi, Mai yawan gafara ne.


HUDUBA TA BIYU
       
        Ya ku musulmai
Addinin Allah tsakaitawa ne, tsakanin wanda ke ketare iyaka a cikinsa, da mai gajartawa.
Kuma da guluwwi, da jafa'i, da sakaci da wuce iyaka, cutuka ne guda biyu masu matukar muni, kuma turbobi ne karkatattu, kuma hanyoyi ne na bata, kuma binsu ficewa ne daga mikakken addini, da shiriya mai girma, da tafarki mikakke.
Sai ku kiyayi aukawa cikin guluwwi da jafa'i, kuma ku kiyayi bin wadancan hanyoyin, ko bin soye-soyen zukata.
Allah Mabuwayi cikin daukakansa ya ce: "Kuma lallai wannan tafarkina ne mikakke, sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyin da za su raba ku daga bin hanyata" [An'am: 153].
        An ruwaito daga Abdullahi bn Mas'ud – ya ce: "Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya yi mana zane, sa'annan ya ce, Wannan shine tafarkin Allah, sa'annan sai ya zana wasu zanen ta dama da hagunsa, sa'annan ya ce, Wadannan kuma hanyoyin bata ne mabanbanta, kuma akan kowanne daga cikinsu akwai shedanin da ke kiran halittu zuwa gare ta, sa'annan sai ya karanta: KUMA LALLAI WANNAN TAFARKINA NE MIKAKKE, SAI KU BI SHI, KUMA KADA KU BI WASU HANYOYI DA ZA SU RABA KU DAGA BIN HANYATA", Ahmad da Tirmiziy da Ibnu Majah.
        Kuma wani mutum ya tambayi Abdullahi bn Mas'ud –رضي الله عنه- cewa: Menene tafarki madaidaici? Sai ya ce: Annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- ya rasu; ya barmu a karshen doronsa, kuma gefensa dayan yana cikin Aljannah, kuma ta dama da shi akwai dokin ingarma, ta hagu akwai ingarma, sai kuma wasu mazaje da suke yin da'awah ga wanda ya shige ta wurinsu, kuma duk wanda ya dauka daga wadannan dawakin, sai su kai shi ga wuta, wanda kuma ya yi riko da doron wannan tafarkin sai ya kai shi ga shiga Aljannah. Sa'annan sai Abdullahi bn Mas'ud ya karanta ayar da ta gabata.
        Kuma an ruwaito daga Annawwas bn Sam'ana --, daga Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Allah ya buga misali ga TAFARKI MADAIDAICI, kuma ta gefen wannan tafarkin biyu akwai katangu, wanda a jikinsu akwai kofofin da aka bubbude, a jikin kofofin kuma akwai labulan da aka shumfudo su, a bakin kofar wannan tafarkin akwai mai yin da'awa yana kira, cewa: Ya ku mutane, ku shiga wannan tafarkin gabadaya, kada ku karkace, akwai wani mai da'awar kuma a saman wannan tafarkin shima yana kira, kuma idan wani ya nemi ya bude wani abu na wadancan kofofin, sai ya ce, Kaitonka, kada ka bude wannan kofar, domin idan ka bude to za ka kutsa cikinsa. WANNAN TAFARKIN SHINE MUSULUNCI. Su kuma KATANGUN DOKOKIN ALLAH, KOFOFIN DA AKA BUBBUDE KUMA ABABEN DA ALLAH YA HARAMTA, MAI YIN DA'AWA KUMA TA KAN TAFARKIN SHINE LITTAFIN ALLAH, Shi kuma MAI YIN KIRA TA SAMAN TAFARKIN SHINE MAI WA'AZI GA ALLAH DA KE CIKIN ZUCIYAR KOWANE MUSULMI".
        An ruwaito daga Abu-Sa'alabah Alkhushaniy –رضي الله عنه-, daga Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, lallai ya ce: "Lallai ne Allah ya farlanta farillai, kada ku tozarta su, kuma ya kafa iyakoki; kada ku ketare su, kuma ya haramta abubuwa; kada ku kekketa alfarmarsu, kuma ya yi shiru kan wasu abubuwa domin rahama a gare ku; ba domin mantuwa ba; to kada ku nemi binciko su", Addarakudniy ya ruwaito shi, kuma Annawawiy ya ce, hadisi ne hasan.

        Sai ku yi salati da sallama, ga Muhammadu Mai shiryarwa, Mai ceton mutane gaba daya,
Saboda idan ka yi masa salati guda daya, to sai Allah ya maka salati guda goma da shi



2018/02/17

GUGUWA DA KURA A GARIN MADINA DA KEWAYE

ALLAH MAJI ROKON BA*
Wadanda suke garin Madina da kewayenta, da masu bibiyan labarunta, Lallai sun san cewa,
A satin da ya kare, Kura mai shiga hancin mutane da idanu, da takura musu ko hana su walwala, ta addabi mutanen wannan yanki na duniya, yadda har lamarin ya sanya shugabanni daukar matakin rufe makarantun jihar Madina gabadayansu, kanana da manya (na cikin gari da kewaye) a ranakun talata da alamis, kula da lafiyan dalibai, kuma hukuma ta shelanta haka ne a ranakun litinin da laraba, bayan ofishin da ke bincike kan sararin samaniya da hasashen yanayi ya sanar da ita sakamakon bincikensa na cewa, suna hasashen za a samu yanayi na kura a kwanakin da na ambata, Nan take kuma, hukuma ta bada umarnin a yayata dokarta na rufe makarantun gabadaya, lura da lafiyan 'yan kasa.
Mutane kuma, suka kara bada kulawa game da shigi-da-fici, da kai-komon iyalansu, domin nisantar da su abinda zai zama kalu-bale ga lafiyansu, musamman kananan yara.
Kamar yadda suka dukufa wajen yin addu'oi, suna masu rokon Allah, ya fitar da su daga wannan yanayi cikin koshin lafiya, Suka kara da rokon Allah Ta'alah ya saukar da ruwan sama, a wannan yanki, domin ya kwantar da wannan kurar, gari yayi dadi, yanayi kuma ya kara sanyi,
Ko a cikin hudubobin juma'a anyi addu'oin rokon ruwa, musamman a masallacin Manzon Allah SAW (babban matattarar jama'a)
Kuma da yake Allah shine Mai amsa addu'ar bayi, sai gashi, Mutanen garin Madina, sun wayi-gari cikin ruwan sama, wanda ya dadada yanayi, ya kawo karin nashadi cikin sanyin safiya, ga kuma karin gajimaren da ya mamaye sararin samaniya, wanda ake zaton sake samun wani ruwan; a koda-yaushe.
*Ababen lura*
1- Allah ya kan jarrabi bayinsa da abinda yaga dama, a lokacin da ya so.
2- Abinda ya auku a satin da ya gabata, na kura, da yadda ta haifar da rufe makarantu a ranakun talata da alamis a cikin sati guda, tarihin Madina ba zai manta da shi ba, don ko ni ina wannan gari tun 2003 Amma ba a taba rufe makarantu har sau biyu a cikin mako daya da wannan sababin ba.
3- Jin-kan Allah ga BayinSa, da yadda yake tausaya musu, ta yadda yake dauke musu bala'oi, idan suka koma gare shi.
4- Komawar bayi ga Allah shi kadai, domin neman yaye bala'oi, da yawaita addu'oi.
5- Damuwar hukumomi ga 'yan kasa, da yadda suke fatan nesanta su, daga dukkan abinda ake zaton zai iya cutar da su.
6- Damuwar iyaye ga 'ya'yansu, da yadda ya kamata su rika yi a lokutan saukar ruwa ko kura, da sauran duk abinda akwai barazana a cikinsu.
7- Kowane ofishin hukuma -kamar ofishin kula da yanayi da sararin samaniya, da bincike kan abinda ake hasashen zuwansa na ruwan sama, ko kura, ko hazo, da sanyi da zafi da sauransu- akwai alhakin da ya rataya akansa, Kuma wajibi ne irin wadannan ofisoshi da hukumomi, su tsayu wajen sauke nauyin da aka dora musu.
8- Da sauran darrusa da izina da daidaikun mutane ko hukumomi da kungiyoyi zasu iya dauka, daga irin wannan kissa.
Allah ne Mafi sani.
17/Feb/2018

Hudubar Masallacin Annabi (S.A.W), A Takaice كن في الدنيا كأنك غريب أو عابر سبيل

Hudubar Masallacin Annabi (S.A.W), A Takaice
30/Jumaadal-Ula/1439H
Limamin Masallacin Annabi, kuma Mai huduba; wato As-Sheikh Husain bn Abdul'aziz Alus-Sheikh ya yi hudubarsa, akan maudu'in *KA KASANCE A DUNIYA KAMAR BAKO, KO KAMAR MAI TSALLAKE HANYA*
➡ Mai yin dubi da idanun basira, ga halin wasu Mutane a yau, zai ga yadda suka rungumi duniya suka makalkale mata, tunaninsu gaba daya ya rataya akan yadda za su samu duniyar, karshen burinsu kuma, yin aiki domin tattara duniya, har aka wayi-gari akan abin duniya suke kulla soyayya, akanta suke adawa, kuma akanta suke yarda akanta suke kiyayya.
➡ Lallai Mumini yana more duniyarsa, irin jin-dadin da ba zai cutar da addini ko lahirarsa ba, Wannan ma'anar kuma, itace daya daga cikin tafsirai biyu da aka yi wa fadinSa Madaukaki: *KUMA KADA KA MANTA DA RABONKA NA DUNIYA*.
➡ Wanda ya sanya lahira da yin aiki domin ita, suka zama babban tunani ko damuwarsa, Allah zai isar masa ga damuwoyin duniyarsa.
Wanda kuma duniya ta mamaye zuciyarsa, kuma ta kasance damuwarsa, sai ya rayu yana bautar duniya, cikin tarin damuwoyi, mai dinbin matsaloli, wanda baya wadatuwa da mai yawa, balle abu kadan ya jiyar da shi dadi.
➡ Musulmi; tambarinsa, a rayuwar duniya shine, FadinSa Madaukaki:
*KA CE: JIN DADIN DUNIYA 'DAN KADAN NE*; Alokacin ne kuma, zai riki duniyarsa a matsayin wurin da zai shuka lahirarsa, ta yadda ba zai rinjayar da duniya akan lahira ba, kuma ba zai fifita sha'awarsa ko son zuciya akan lahirarsa ba.
➡ Duk wanda duniyarsa ta kautar da shi daga neman lahirarsa; ya biye wa sha'awarsa; a wuraren da ta saba wa shari'ar UbangijinSa, ya auka cikin babbar asara, kuma ya tsunduma cikin rashin rabo mai girma.
➡ A wannan zamanin, ababen rudin duniya sun kame zukatan dayawa daga cikin mutane, kuma rayukan Musulmai dadama suna ta kokarin fafutikar neman kayan dadin duniya da sha'awowinta; Sai ya wajaba ga Musulmi ya yi tsayuwar hisabi, domin tantance tabbatattun ababe, da kokarin gano karshen lamura.
*Sako* / Daga Ofishin Fassara Na Masallacin Annabi (S.A.W).

2018/02/14

hudubar 30 jumadal ula 1439h daidai da 16 Fabarairu 2018M حسين آل الشيخ









HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
 JUMA'A, 30/JUMADAL ULA/1439H
Daidai da 16/FEBRAIRU/2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA




بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata Allah wanda yake cewa: "KAWAI DAI, KUNA FIFITA RAYUWAR DUNIYA NE, ALHALI LAHIRA ITACE MAFI ALHERI, KUMA MAFI WANZUWA" [A'alah: 16-17].
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Madaukakin da yafi daukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne, manzonSa, Annabi, zababbe.
Ya Allah ka yi salati da sallama, da albarka, a gare shi, da iyalansa da sahabansa; masu biyayya da takawa.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ina muku wasiyya, da ni kaina da bin dokokin Allah, Mabuwayi da daukaka "KUMA KU YI GUZURI; AMMA MAFI ALHERIN GUZURI SHINE TSORON ALLAH" [Bakara: 198].

Ya ku Musulmai
MAI YIN DUBI DA IDANUN BASIRA, GA HALIN DA SASHEN MUTANE A YAU KE KANSA, zai ga yadda suka rungumi duniya suka malkale mata da karfi; son zukatansu ya rataya ga yadda za su sam duniyar, karshen burinsu kuma, yin aiki ko bin dukkan hanyoyin tara ta; har suka wayi-gari basu da wata manufa face ita; akan duniya suke kulla soyayya, akanta suke yin kiyayya, akanta suke yarda, akanta suke ki, har maganar wani ya tabbatu akansu:
ومن البلاء، وللبلاء علامةٌ    أن لا يُرى لك عن هواك نُزوع
Ma'ana:
Yana daga cikin bala'i, kuma bala'in yana da alama
A ganka baka ficewa daga biyewa son zuciyarka.

Kuma lallai Muminin da aka masa taufiki, ya kan rinjayar da lahirarsa, akan lamarin duniyarsa, kuma mumini yana gudanar da rayuwarsa ne kamar yadda Ubangijinsa ya tsara masa, a cikin fadinSa: "Kuma ka nema –daga abinda Allah ya baka- ka nemi gidan lahira, kuma kada ka manta rabonka na duniya, ka kyautata, kamar yadda Allah ya kyautata maka" [Kasas: 77].
Don haka Mumini yana bin hanyoyi, kuma yana aiki -iya kokarinsa- wajen neman arzikinsa, yana kokarin raya kasa, da abinda zai yardar da Allah Mabuwayi da daukaka.

Kuma yana more duniyarsa, irin jin-dadin da ba zai cutar da addini ko lahirarsa ba, kuma wannan ma'anar ita ce, 'dayan tafsiri biyu da aka yi wa fadinSa Madaukaki:
(ولا تنس نصيبك من الدنيا).
Wato, "Kada ka manta rabonka na duniya".

        Kuma Allah (سبحانه) ya ce:
(ربنا آتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقنا عذاب النار).
Wato, "Ya Ubangijinmu, ka bamu mai kyau a duniya, a lahira mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar wuta" [Bakara: 201].
        Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Sai wannan addu'ar ta game dukkan alherin duniya, kuma ta tunkude dukkan sharri; domin mai kyau a duniya ya kunshi dukkan abin duniyan da ake nema; ta bangaren lafiya, da gida mai fadi, da kyakkyawar mace, da arziki mai yawa da fadi, da ilimi mai amfani, da aiki nagari, da abin hawa lafiyayye, da yabo mai kyau".

        'Yan'uwana musulmai!
        Lallai wanda ya sanya lahira da yin aiki dominta suka zama tunani ko babbar damuwarsa, to, sai Allah ya isar masa ga damuwoyin duniyarsa.
        Wanda kuma duniya ta mamaye zuciyarsa, kuma ta kasance damuwarsa, sai ya rayu yana bawan da duniya ta yi wa dabaibayi, cikin dinbin matsaloli, da dogon buri, wanda baya wadatuwa da mai yawa, balle kuma abu kadan ya sanya shi walwala ko jin dadi; Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda lahira ta zama damuwarsa, sai Allah ya sanya wadacinsa a cikin zuciyarsa, ya kuma tattara hankalinsa (wuri guda), sai duniya ta zo masa, alhalin tana kaskantacciya. Wanda kuma duniya ta zama damuwarsa, sai Allah ya sanya talaucinsa a tsakanin idanunsa biyu, ya wargaza masa abinda ya tara, kuma ba zai samu duniyar ba, sai gwargwadon yadda aka kaddara masa", Ahmad ya ruwaito shi, da Tirmiziy da Ibnu-Majah.
Irakiy yace: Isnadinsa mai kyau ne, kuma Maluma dayawa sun inganta shi.

Musulmi tambarinsa a rayuwar duniya, shine fadinSa Madaukaki: "Ka ce: Dadin duniya dan kadan ne", a lokacin ne, zai riki rayuwarsa ta duniya a matsayin wurin shukan lahirarsa, ta yadda ba zai rinjayar da duniya akan lahira ba, kuma ba zai fifita sha'awarsa ko son zuciya akan lahira ba, yana mai amsa wa fadin UbangijinSa: "Ka ce: Dadin duniya kadan ne, kuma lahira rayuwarta shine mafi alheri ga wanda ya yi takawa, kuma ba a zaluntarku koda sililin hancin gurtsun dabino" [Nisa'i: 77].
        "Kuma dukkan wancan ba komai ba, face jin dadin duniya kawai, kuma lahira a wurin Ubangijinka, ta masu takawa ce" [Zukhruf: 35].

Sai ka kiyaye Ya kai musulmi; daga ruduwa da wannan duniyar, ka kiyayi gafala da bin sha'awa da son zuciya, Allah (Ta'alah) ya ce: "Ya ku mutane lallai ne alkawarin Allah gaskiya ne, don haka, kada rayuwar duniya, ta rude ku, kuma kada shedan ya rudar da ku, ga barin Allah" [Fadir: 5].

Ya ku bayin Allah!
Duk wanda duniya ta rudar ko ta kautar da shi daga neman lahirarsa, sai ya biye wa sha'awarsa, a wuraren da ta saba wa shari'ar UbangijinSa, to ya auka cikin babbar hasara, kuma ya dulmuyi cikin rashin rabo ko tabewa mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada dukiyoyinku da 'ya'yanku su shagaltar da ku, daga ambaton Allah, duk wanda ya aikata haka, to lallai wadannan sune suka yi hasara" [Munafikuna: 9].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Sai masu mayewa a bayansu suka maye, suka tozarta salla, kuma suka bi sha'awowinsu, to da sannu za su hadu da wani kwarin azaba mai sharri" [Maryam: 59].
"Kuma rayuwa ba komai ba ce, face jin dadin rudi" [Ali-imrana: 185].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai bautar dinari ya halaka, mai bautar dirhami ya halaka, mai bautar tufafi ya halaka, kuma ya samu koma baya (tunda ya bar bautar Allah, ya kama bautar halittu), kuma ana masa addu'ar idan kaya ta soke shi, kada ya samu damar cire ta".  Ma'anar hadisin: Shine lallai ya tabe, yayi rashin rabo, ya auka cikin wulakanci da bala'i.

Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alkur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban Manzanni, da maganganunsa mikakku.
Sai ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah, sannan ku kiyayi dukkan abinda zai kautar da ku daga samun yardarm Allah, Madaukaki, Allah Ta'alah ya ce: "KAWAI DAI, KUNA FIFITA RAYUWAR DUNIYA NE, ALHALI LAHIRA ITACE MAFI ALHERI, KUMA MAFI WANZUWA" [A'alah: 16-17].
Allah ya yi min albarka ni da ku, cikin Alkur'ani Mai girma.
Ina fadar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa; saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin kai.


HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah, yabo maiyawa, mai dadi, mai albarka, kamar yadda Ubangijinmu yake so, kuma ya yarda.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yak e bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonsa.
Ya Allah, ka yi dadin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa.
        Bayan haka!
        Ya ku musulmai
A wannan zamanin ababen rudin duniya sun samu gindin zama a cikin zukatan dayawa daga cikin mutane, kuma rayukan dayawa daga cikin musulmai sun zaku wajen leko kayan dadin duniya da ababen sha'awarta,Sai ya wajaba ga Musulmi ya yi tsayuwar hisabi, domin tunani ko tantance tabbatattun ababe, da kokarin hango karshen lamura, Allah Ta'alah yana cewa: "Dukiya da 'diya sune kawar rayuwar duniya, kuma ayyukan kwarai masu wanzuwa, sun fi zama alheri a wurin Ubangijinka, ga lada, kuma sun fi alheri ga buri" [Kahf: 46].
        Kuma ya zo cikin hadisi "Me ya hada ni, da duniya, lallai misalina da misalin duniya, kamar mahayi ne wanda ya yi barci a karkashin wata bishiya, a wani yini mai zafi, sa'annan ya tashi ya barta", Ahmad da Tirmiziy suka ruwaito shi.
        Sai ku saurari wasiyyar Annabi –صلى الله عليه وسلم- sauraron amsawa da yin aiki da ita, An ruwaito daga Abdullahi bn Umar –رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kama kafadata, sa'annan ya ce: "Ka kasance, a duniya kamar wani bako, ko mai tsallake hanya". Sai Abdullahi dan Umar ya kasance, yana cewa: "Idan ka yi yammaci, to kada ka jira zuwan safiya, idan kuma ka wayi-gari, to kada ka jira zuwan yammaci, kuma ka yi amfani da lafiyarka gabanin zuwan cutarka, da kuma rayuwarka domin mutuwarka", Bukhariy ya ruwaito shi.


        Bayin  Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku wadanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
………………….



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...