HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله
عليه وسلم
JUMA'A, 30/JUMADAL
ULA/1439H
Daidai da 16/FEBRAIRU/2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI DAN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata Allah wanda yake cewa: "KAWAI DAI, KUNA
FIFITA RAYUWAR DUNIYA NE, ALHALI LAHIRA ITACE MAFI ALHERI, KUMA MAFI WANZUWA" [A'alah:
16-17].
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Madaukakin da yafi daukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu
bawanSa ne, manzonSa, Annabi, zababbe.
Ya Allah ka yi salati da sallama, da albarka,
a gare shi, da iyalansa da sahabansa; masu biyayya da takawa.
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Ina muku wasiyya, da ni kaina da bin dokokin
Allah, Mabuwayi da daukaka "KUMA KU YI GUZURI; AMMA MAFI ALHERIN
GUZURI SHINE TSORON ALLAH" [Bakara: 198].
Ya ku Musulmai
MAI YIN DUBI DA IDANUN BASIRA, GA HALIN DA
SASHEN MUTANE A YAU KE KANSA, zai ga yadda suka rungumi duniya suka malkale
mata da karfi; son zukatansu ya rataya ga yadda za su sam duniyar, karshen burinsu
kuma, yin aiki ko bin dukkan hanyoyin tara ta; har suka wayi-gari basu da wata
manufa face ita; akan duniya suke kulla soyayya, akanta suke yin kiyayya,
akanta suke yarda, akanta suke ki, har maganar wani ya tabbatu akansu:
ومن البلاء، وللبلاء علامةٌ
أن لا يُرى لك عن هواك نُزوع
Ma'ana:
Yana daga cikin bala'i, kuma
bala'in yana da alama
A ganka baka ficewa daga biyewa son zuciyarka.
Kuma lallai Muminin da aka masa taufiki, ya kan
rinjayar da lahirarsa, akan lamarin duniyarsa, kuma mumini yana gudanar da
rayuwarsa ne kamar yadda Ubangijinsa ya tsara masa, a cikin fadinSa: "Kuma ka nema –daga
abinda Allah ya baka- ka nemi gidan lahira, kuma kada ka manta rabonka na
duniya, ka kyautata, kamar yadda Allah ya kyautata maka" [Kasas:
77].
Don haka Mumini yana bin hanyoyi, kuma yana aiki
-iya kokarinsa- wajen neman arzikinsa, yana kokarin raya kasa, da abinda zai
yardar da Allah Mabuwayi da daukaka.
Kuma yana more duniyarsa, irin jin-dadin da ba
zai cutar da addini ko lahirarsa ba, kuma wannan ma'anar ita ce, 'dayan tafsiri
biyu da aka yi wa fadinSa Madaukaki:
(ولا تنس نصيبك
من الدنيا).
Wato, "Kada ka manta rabonka na duniya".
Kuma
Allah (سبحانه) ya
ce:
(ربنا آتنا في
الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقنا عذاب النار).
Wato, "Ya Ubangijinmu, ka bamu mai kyau a
duniya, a lahira mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar wuta" [Bakara:
201].
Ibnu-kasir
–رحمه الله- ya ce: "Sai
wannan addu'ar ta game dukkan alherin duniya, kuma ta tunkude dukkan sharri;
domin mai kyau a duniya ya kunshi dukkan abin duniyan da ake nema; ta
bangaren lafiya, da gida mai fadi, da kyakkyawar mace, da arziki mai yawa da
fadi, da ilimi mai amfani, da aiki nagari, da abin hawa lafiyayye, da yabo mai
kyau".
'Yan'uwana
musulmai!
Lallai
wanda ya sanya lahira da yin aiki dominta suka zama tunani ko babbar damuwarsa,
to, sai Allah ya isar masa ga damuwoyin duniyarsa.
Wanda
kuma duniya ta mamaye zuciyarsa, kuma ta kasance damuwarsa, sai ya rayu yana
bawan da duniya ta yi wa dabaibayi, cikin dinbin matsaloli, da dogon buri,
wanda baya wadatuwa da mai yawa, balle kuma abu kadan ya sanya shi walwala ko
jin dadi; Annabi –صلى
الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda lahira ta
zama damuwarsa, sai Allah ya sanya wadacinsa a cikin zuciyarsa, ya kuma tattara
hankalinsa (wuri guda), sai duniya ta zo masa, alhalin tana kaskantacciya.
Wanda kuma duniya ta zama damuwarsa, sai Allah ya sanya talaucinsa a tsakanin
idanunsa biyu, ya wargaza masa abinda ya tara, kuma ba zai samu duniyar ba, sai
gwargwadon yadda aka kaddara masa", Ahmad ya ruwaito shi, da
Tirmiziy da Ibnu-Majah.
Irakiy yace: Isnadinsa mai kyau ne, kuma
Maluma dayawa sun inganta shi.
Musulmi tambarinsa a rayuwar duniya, shine
fadinSa Madaukaki: "Ka ce: Dadin duniya dan kadan ne", a
lokacin ne, zai riki rayuwarsa ta duniya a matsayin wurin shukan lahirarsa, ta
yadda ba zai rinjayar da duniya akan lahira ba, kuma ba zai fifita sha'awarsa
ko son zuciya akan lahira ba, yana mai amsa wa fadin UbangijinSa: "Ka ce: Dadin duniya
kadan ne, kuma lahira rayuwarta shine mafi alheri ga wanda ya yi takawa, kuma
ba a zaluntarku koda sililin hancin gurtsun dabino" [Nisa'i:
77].
"Kuma dukkan wancan
ba komai ba, face jin dadin duniya kawai, kuma lahira a wurin Ubangijinka, ta
masu takawa ce" [Zukhruf: 35].
Sai ka kiyaye Ya kai musulmi; daga ruduwa
da wannan duniyar, ka kiyayi gafala da bin sha'awa da son zuciya, Allah
(Ta'alah) ya ce: "Ya ku mutane lallai ne alkawarin Allah gaskiya ne, don
haka, kada rayuwar duniya, ta rude ku, kuma kada shedan ya rudar da ku, ga
barin Allah" [Fadir: 5].
Ya ku bayin Allah!
Duk wanda duniya ta rudar ko ta kautar da shi
daga neman lahirarsa, sai ya biye wa sha'awarsa, a wuraren da ta saba wa
shari'ar UbangijinSa, to ya auka cikin babbar hasara, kuma ya dulmuyi cikin rashin
rabo ko tabewa mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda
suka yi imani, kada dukiyoyinku da 'ya'yanku su shagaltar da ku, daga ambaton
Allah, duk wanda ya aikata haka, to lallai wadannan sune suka yi hasara"
[Munafikuna: 9].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Sai masu mayewa a
bayansu suka maye, suka tozarta salla, kuma suka bi sha'awowinsu, to da sannu
za su hadu da wani kwarin azaba mai sharri" [Maryam: 59].
"Kuma rayuwa ba komai ba ce, face jin
dadin rudi" [Ali-imrana: 185].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai bautar dinari
ya halaka, mai bautar dirhami ya halaka, mai bautar tufafi ya halaka, kuma ya
samu koma baya (tunda ya bar bautar Allah, ya kama bautar halittu), kuma ana masa
addu'ar idan kaya ta soke shi, kada ya samu damar cire ta". Ma'anar hadisin: Shine lallai ya tabe, yayi
rashin rabo, ya auka cikin wulakanci da bala'i.
Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alkur'ani
mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa na ayoyi, da
tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban Manzanni, da
maganganunsa mikakku.
Sai ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah,
sannan ku kiyayi dukkan abinda zai kautar da ku daga samun yardarm Allah,
Madaukaki, Allah Ta'alah ya ce: "KAWAI DAI, KUNA FIFITA RAYUWAR DUNIYA NE,
ALHALI LAHIRA ITACE MAFI ALHERI, KUMA MAFI WANZUWA" [A'alah:
16-17].
Allah ya yi min albarka ni da ku, cikin
Alkur'ani Mai girma.
Ina fadar maganata wannan, kuma ina neman
gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa;
saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin kai.
HUDUBA TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah, yabo maiyawa, mai dadi, mai albarka, kamar yadda
Ubangijinmu yake so, kuma ya yarda.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah; shi kadai yak e bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu
bawansa ne, kuma manzonsa.
Ya Allah, ka yi dadin salati da sallama a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa.
Bayan
haka!
Ya
ku musulmai
A wannan
zamanin ababen rudin duniya sun samu gindin zama a cikin zukatan dayawa daga
cikin mutane, kuma rayukan dayawa daga cikin musulmai sun zaku wajen leko kayan
dadin duniya da ababen sha'awarta,Sai ya wajaba ga Musulmi ya yi tsayuwar
hisabi, domin tunani ko tantance tabbatattun ababe, da kokarin hango karshen
lamura, Allah Ta'alah yana cewa: "Dukiya da 'diya sune kawar rayuwar duniya,
kuma ayyukan kwarai masu wanzuwa, sun fi zama alheri a wurin Ubangijinka, ga
lada, kuma sun fi alheri ga buri" [Kahf: 46].
Kuma
ya zo cikin hadisi "Me ya hada ni, da duniya, lallai misalina da misalin
duniya, kamar mahayi ne wanda ya yi barci a karkashin wata bishiya, a wani yini
mai zafi, sa'annan ya tashi ya barta", Ahmad da Tirmiziy suka
ruwaito shi.
Sai
ku saurari wasiyyar Annabi –صلى
الله عليه وسلم- sauraron amsawa da yin aiki da ita, An
ruwaito daga Abdullahi bn Umar –رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kama kafadata,
sa'annan ya ce: "Ka kasance, a duniya kamar wani bako, ko mai tsallake hanya".
Sai Abdullahi dan Umar ya kasance, yana cewa: "Idan ka yi
yammaci, to kada ka jira zuwan safiya, idan kuma ka wayi-gari, to kada ka jira
zuwan yammaci, kuma ka yi amfani da lafiyarka gabanin zuwan cutarka, da kuma
rayuwarka domin mutuwarka", Bukhariy ya ruwaito shi.
Bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku
wadanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
"Lallai Allah yana yin umurni
da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha
da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
………………….
No comments:
Post a Comment