ALLAH MAJI ROKON BA*
Wadanda suke garin Madina da kewayenta, da masu bibiyan labarunta, Lallai sun san cewa,
A satin da ya kare, Kura mai shiga hancin mutane da idanu, da takura musu ko hana su walwala, ta addabi mutanen wannan yanki na duniya, yadda har lamarin ya sanya shugabanni daukar matakin rufe makarantun jihar Madina gabadayansu, kanana da manya (na cikin gari da kewaye) a ranakun talata da alamis, kula da lafiyan dalibai, kuma hukuma ta shelanta haka ne a ranakun litinin da laraba, bayan ofishin da ke bincike kan sararin samaniya da hasashen yanayi ya sanar da ita sakamakon bincikensa na cewa, suna hasashen za a samu yanayi na kura a kwanakin da na ambata, Nan take kuma, hukuma ta bada umarnin a yayata dokarta na rufe makarantun gabadaya, lura da lafiyan 'yan kasa.

Mutane kuma, suka kara bada kulawa game da shigi-da-fici, da kai-komon iyalansu, domin nisantar da su abinda zai zama kalu-bale ga lafiyansu, musamman kananan yara.
Kamar yadda suka dukufa wajen yin addu'oi, suna masu rokon Allah, ya fitar da su daga wannan yanayi cikin koshin lafiya, Suka kara da rokon Allah Ta'alah ya saukar da ruwan sama, a wannan yanki, domin ya kwantar da wannan kurar, gari yayi dadi, yanayi kuma ya kara sanyi,
Ko a cikin hudubobin juma'a anyi addu'oin rokon ruwa, musamman a masallacin Manzon Allah SAW (babban matattarar jama'a)

Kuma da yake Allah shine Mai amsa addu'ar bayi, sai gashi, Mutanen garin Madina, sun wayi-gari cikin ruwan sama, wanda ya dadada yanayi, ya kawo karin nashadi cikin sanyin safiya, ga kuma karin gajimaren da ya mamaye sararin samaniya, wanda ake zaton sake samun wani ruwan; a koda-yaushe.
*Ababen lura*
1- Allah ya kan jarrabi bayinsa da abinda yaga dama, a lokacin da ya so.
2- Abinda ya auku a satin da ya gabata, na kura, da yadda ta haifar da rufe makarantu a ranakun talata da alamis a cikin sati guda, tarihin Madina ba zai manta da shi ba, don ko ni ina wannan gari tun 2003 Amma ba a taba rufe makarantu har sau biyu a cikin mako daya da wannan sababin ba.
3- Jin-kan Allah ga BayinSa, da yadda yake tausaya musu, ta yadda yake dauke musu bala'oi, idan suka koma gare shi.
4- Komawar bayi ga Allah shi kadai, domin neman yaye bala'oi, da yawaita addu'oi.
5- Damuwar hukumomi ga 'yan kasa, da yadda suke fatan nesanta su, daga dukkan abinda ake zaton zai iya cutar da su.
6- Damuwar iyaye ga 'ya'yansu, da yadda ya kamata su rika yi a lokutan saukar ruwa ko kura, da sauran duk abinda akwai barazana a cikinsu.
7- Kowane ofishin hukuma -kamar ofishin kula da yanayi da sararin samaniya, da bincike kan abinda ake hasashen zuwansa na ruwan sama, ko kura, ko hazo, da sanyi da zafi da sauransu- akwai alhakin da ya rataya akansa, Kuma wajibi ne irin wadannan ofisoshi da hukumomi, su tsayu wajen sauke nauyin da aka dora musu.
8- Da sauran darrusa da izina da daidaikun mutane ko hukumomi da kungiyoyi zasu iya dauka, daga irin wannan kissa.
Allah ne Mafi sani.
17/Feb/2018
17/Feb/2018
No comments:
Post a Comment