Hudubar Masallacin Annabi (S.A.W), A Takaice
30/Jumaadal-Ula/1439H
Limamin Masallacin Annabi, kuma Mai huduba; wato As-Sheikh Husain bn Abdul'aziz Alus-Sheikh ya yi hudubarsa, akan maudu'in *KA KASANCE A DUNIYA KAMAR BAKO, KO KAMAR MAI TSALLAKE HANYA*
➡ Mai yin dubi da idanun basira, ga halin wasu Mutane a yau, zai ga yadda suka rungumi duniya suka makalkale mata, tunaninsu gaba daya ya rataya akan yadda za su samu duniyar, karshen burinsu kuma, yin aiki domin tattara duniya, har aka wayi-gari akan abin duniya suke kulla soyayya, akanta suke adawa, kuma akanta suke yarda akanta suke kiyayya.
➡ Lallai Mumini yana more duniyarsa, irin jin-dadin da ba zai cutar da addini ko lahirarsa ba, Wannan ma'anar kuma, itace daya daga cikin tafsirai biyu da aka yi wa fadinSa Madaukaki: *KUMA KADA KA MANTA DA RABONKA NA DUNIYA*.
➡ Wanda ya sanya lahira da yin aiki domin ita, suka zama babban tunani ko damuwarsa, Allah zai isar masa ga damuwoyin duniyarsa.
Wanda kuma duniya ta mamaye zuciyarsa, kuma ta kasance damuwarsa, sai ya rayu yana bautar duniya, cikin tarin damuwoyi, mai dinbin matsaloli, wanda baya wadatuwa da mai yawa, balle abu kadan ya jiyar da shi dadi.

➡ Musulmi; tambarinsa, a rayuwar duniya shine, FadinSa Madaukaki:
*KA CE: JIN DADIN DUNIYA 'DAN KADAN NE*; Alokacin ne kuma, zai riki duniyarsa a matsayin wurin da zai shuka lahirarsa, ta yadda ba zai rinjayar da duniya akan lahira ba, kuma ba zai fifita sha'awarsa ko son zuciya akan lahirarsa ba.

➡ Duk wanda duniyarsa ta kautar da shi daga neman lahirarsa; ya biye wa sha'awarsa; a wuraren da ta saba wa shari'ar UbangijinSa, ya auka cikin babbar asara, kuma ya tsunduma cikin rashin rabo mai girma.
➡ A wannan zamanin, ababen rudin duniya sun kame zukatan dayawa daga cikin mutane, kuma rayukan Musulmai dadama suna ta kokarin fafutikar neman kayan dadin duniya da sha'awowinta; Sai ya wajaba ga Musulmi ya yi tsayuwar hisabi, domin tantance tabbatattun ababe, da kokarin gano karshen lamura.
*Sako* / Daga Ofishin Fassara Na Masallacin Annabi (S.A.W).
No comments:
Post a Comment