Masu warware Musulunci
(النواقض العشرة)
Bismillahir-Rahmanir-Rahim!
Ka sani! Lallai abubuwan da suke warware
Musulunci goma ne:
1) Shirka cikin bautar Allah Madaukaki. Allah Ta'alah yana
cewa:
“Lallai ne Allah ba
ya gafarta ayi shirka da shi, kuma yana gafarta koma bayan haka, ga wanda yake
so” (Nisa, 116.)
Kuma ya ce:
“Lallai, wanda ya
yi shirka da Allah, to lallai Allah ya haramta masa Aljanna, kuma makomarsa
Wuta ce, kuma azzalumai basu da masu taimakawa” (Ma'ida, 72.)
Daga cikin shirka
akwai: Yin yanka ga wanda ba Allah ba, kamar mai yin yanka ga Aljani ko ga
kabari.
2) Wanda ya riki tsani tsakaninsa da tsakanin
Allah; yana rokonsu yana
neman ceto daga gare su, yana dogaro akansu, ya kafirta, da ijma'i.
3) Wanda bai kafirta mushirkai ba, ko
ya yi shakka kan
kafircinsu, ko yake inganta addininsu da suke tafiya akai, ya kafirta.
4) Wanda ya kudurta cewa lallai shiriyar waninsa
–sallal Lahu alaihi wa sallama- wai tafi ta
Annabi kamala, ko kuma hukuncin wanin Annabi yafi kyau akan hukuncin Annabi, kamar wadanda
suke fifita hukuncin 'Dagutai akan hukuncinsa, to wannan kafiri ne.
5) Wanda ya kyamaci wani abu, daga cikin
abubuwan da Manzon Allah –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya zo da su, koda ya yi aiki da shi, to ya kafirta.
6) Wanda ya yi izgili da wani abu na addinin Manzon Allah, ko
ladan Allah, ko ukubarsa, ya kafirta, Dalili kuma shine fadinsa Madaukaki:
“Ka ce: Shin da
Allah da kuma ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuke izgili * kada ku kawo wani
uzuri, hakika kun kafirta bayan imaninku'” (Tauba, 65-66)
7) Sihiri. Daga cikinsa akwai: sihirin juya
masoya, dana kulla su, Duk wanda ya aikata shi, ko ya yarda da shi, ya kafirta,
Dalili akan haka shine fadinsa Madaukaki:
“Kuma basu ilmantar
da wani Mutum, face sun ce: Mu jarrabawa ce kawai, saboda haka kada ka kafirta” (Bakara, 102).
8) Agazawa Mushirkai da basu taimako akan
Musulmai. Dalili akansa shine
fadinsa Madaukaki:
“Wanda ya jibince
su daga gare ku, to, lallai ne shi yana daga gare su, Lallai Allah ba ya
shiryar da Mutane azzalumai” (Ma'ida, 51).
9) Wanda ya kudurta cewa, lallai wasu Mutane
ya halatta musu su fice daga shari'ar annabi Muhammadu –sallal
Lahu alaihi wa sallama-. Kamar yadda bawan
Allah Khadir ya fita daga tsarin shari'ar annabi Musa –sallal Lahu alaihi wa
sallama-, to shi mai wannan kudurin ya kafirta.
10) Bijire wa addinin Allah Ta'alah. Ta yadda zai
kasance baya koyansa kuma baya aiki da shi, Dalili kuma shine fadinsa Madaukaki:
“Babu wanda yafi
zalunci, bisa ga wanda aka tunatar da ayoyin Ubangijinsa, sa'annan ya bijire
daga barinsu, Lallai Mu masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi” (Sajada, 22)
Ba
banbanci cikin wadannan ababe masu warware Musulunci, tsakanin mai wargi da mai
yi da gaske, da wanda yake tsorace, saidai wanda aka tilasta. Kuma dukkansu
suna da girman hatsari, kuma suna yawaita aukuwa; don haka ya dace Musulmi ya
kiyaye su, kuma ya ji tsoronsu ga kansa. Muna neman tsarin Allah daga ababen da
suke hukunta fushinsa da ukubarsa mai radadi.
Allah ya
yi dadin salati ga fiyayyen halittarsa; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa,
da sallamar amintarwa.
No comments:
Post a Comment