HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 23/Ramadhana/1439H
daidai da 08/Yuni/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YIN HISABI GA RAI A CIKIN
WATAN RAMADHANA, DA NI'IMAR ALKUR'ANI
Shehin Malami wato: Aliyu bn
Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YIN HISABI GA RAI A CIKIN
WATAN RAMADHANA, DA NI'IMAR ALKUR'ANI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke
tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo na
Allah ne; Ubangijin kasa da sammai, Ma'abucin ni'imomi da albarkoki,
Ayyukan
da'a basu amfanar da shi, kuma munana basu cutar da shi, kawai suna amfanar ko
su cutar da wanda ya aikata su ne, saboda Allah Wadatacce ne baya bukatar
halittu,
Ina yin
yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa wadanda muke sani, da
wadanda bamu sani ba, saboda yabo da godiya nasa ne a cikin dukkan halaye
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da
abokin tarayya, Yana da sunaye mafiya kyau, da mafi girman sifofi.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, wanda ake karfafarsa
da hujjoji da kuma mu'ujizozi.
Ya Allah ka yi dadin
salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da IyalanSa da
SahabbanSa masu gaggawar aikata alkhairori
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah Mabuwayi
da daukaka ta hanyar ayyukan da suke yardarm da shi, da nisantar fushinSa da
sabonSa, saboda babu mai samu rabo sai masu takawa. Kuma babu mai yin hasara face
mujirimai.
Ya ku musulmai …
Yin hisabi ga Rai, da
kokarin yin ayyukan da'a, da neman kara kyawawan ayyuka, da kiyaye abinda Allah
ya taimaki bawanSa ya masa taufikin dace; na daga ayyuka nagari, da nisantar
lamuran da suke bata ayyukan da'oi = sune hakikanin samun rabo da tsira a cikin
wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwa; Allah Ta'alah ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwar
gaban UbangijinSa, sai ya kange ransa daga son Rai * to lallai Aljannah ita ce
makoma" [40-41].
Kuma Allah Mabuwayi da
daukaka ya ce dangane da ma'abuta Aljanna: "Sai sashensu ya fiskanci
sashe suna tambayar juna * suka ce: Lallai mu, mun kasance a gabanin wannan (a
Duniya), a cikin iyalanmu munan jin tsoro * Sai Allah yay i mana kyauta falala,
kuma ya tsare mu daga azabar iskar zafi" [Dur: 25-27].
Kuma Allah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani ku
yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa, kuma kada ku bata ayyukanku"
[Muhammadu: 33].
Ibnu-kasir –Allah ya yi
masa rahama- yake fada dangane da tafsirin fadinSa Allah Ta'alah: "Kuma Rai ta yi dubi kan
abinda ta aikata don gobe" [Hashr: 18], Ma'ana: Ku yi hisabi ga
rayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku yi dubi kan abinda kuka yi tanadi ga
kayukanku na kyawawan ayyuka, domin ranar da za a dawo da ku, kuma a bijiro da
ku ga Ubangijinku. maganarsa ta kare.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya
ce: : "Mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa, sannan ya yi aiki
domin abinda zai kasance a bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya biye wa
son zuciyarsa; sai yake ta kwallafa buri ga Allah".
Kamar yadda TABEWA DA
HASARAR RAYUWA YAKE CIKIN BIN SOYE-SOYEN ZUCIYA, DA AIKATA HARAMUN, DA BARIN
AYYUKAN DA'A, KO AUKAWA CIKIN ABABEN DA SUKE RUGUZA KYAWAWAN AYYUKA, kuma
lallai, ya ishi mutum sharri, ya rika aikata abunda zai tauye masa ladansa!
Ya ku Musulmai…
Lallai kuna ganin saurin
tafiyan darare da yini, da yadda shekaru suke ta wucewa, Kuma lallai duk yinin
da ya shude, to lallai ya tafi da abinda aka yi a cikinsa; ba zai dawo ba.
Kuma rayuwa gaba dayanta
ba komai b ace, face wasu darare da yini, sai ajalin bawa ya sauka a gare shi,
aikinsa ya yanke, sai kuma ya samu yakini akan yadda guri ya rude shi.
Kuma hakika mafi yawan
kwanakin watan alkhairori (na Ramadana) sun shige, Sai wasu darare da yini
madaukaka a cikin watan suka saura, da awoyi masu daraja; Don haka:
Duk wanda ya kyautata
ayyuka, to yayi godiya ga Allahn da ya taimake shi, ya masa dace a cikinsu, sai
kuma ya kiyaye ayyukansa daga abubuwan suke bata su, ko kuma rage musu lada, da
aukawa a cikin ukubobi, sai kuma bi aikin kyautatawa da aikin da yafi shi kyau,
Allah Ta'alah ya ce: "Ba komai ba ne sakamakon kyautatawa, face
kyautatawa" [Arrahman: 60].
Wanda shi kuma ya kasance
ya yi sakaci, to sai ya zage damtse wajen kara kokari, ya zabura wajen aiki da
nau'ukan ibadodi da dangogin da'oi, domin ya tottoshe abinda yay i na sakaci;
saboda ayyuka suna kara samun tagomashi ne da abinda aka cike su, daren
Lailatul kadari kuma har yanzu ana fatan dacewa da ita, su kuma zunubai da
rahamar Allah Mabuwayi da daukaka da gafararSa, da hakurinSa da karramawarSa da
yafiyarSa ababen gogewa ne. kuma ya zo cikin hadisi cewa: : "Wanda ya yi tsayuwar daren
Lailatul kadari (yana salla) cikin imani da neman lada, to an gafarta masa
abinda ya gabata daga zunubansa", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah –رضي الله عنه-.
Allah Ta'alah ya ce: : "Daren Lailatul kadari tafi
alheri fiye da watanni dubu" [kadr: 3]. Maluman tafsiri suka ce:
Ma'ana yin bauta a cikinta yafi falala akan bautar watanni dubu; wadanda babu
Lailatul kadari a cikinsu; Abu-Mus'ab; wato Ahmad bn Abubakar Azzuhuriy yace:
Malik ya bamu labara, cewa: lallai labara ya same shi, cewa lallai
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- an nuna masa shekarun mutanen da suka
rigaye shi, sai ya yi kamar ya raina shekarun al'ummarsa, saboda tsoron ba za
su iya aikin da wasunsu suka yi ba; sakamakon tsawon shekarunsu, Amma sai Allah
ya bashi daren lailatul kadari, wanda yafi watanni dubu alkhairi.
Kuma yana daga cikin
hikimomin Allah masu kololuwan girma, da rahamarSa mai fadi, da falarSa mai
yalwa da girma, Yadda ya farlanta azumin watan Ramadhana ga al'ummar Musulmai,
wato, watan da aka saukar da Alkur'ani Mai girma a cikinsa.
Shi kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya
sunnanta mana yin salloli a cikin dararen watan, kuma ya kwadaitar akan hakan,
a inda ya ce: : "Wanda yayi salloli da tsayuwan dararen watan Ramadhana, an gafarta
masa abinda ya gabata dagab zunubansa", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah.
Kuma Alkur'ani da sunnah,
sun kwadaitar akan nau'ukan ayyukan biyayya ga Allah gaba dayansu, a cikin
wannan wata mai albarka, ta hanyar farlanta azumtarsa, da kwadaitarwa kan yin
salloli a cikin darensa, da kwadaitarwa kan aikata alkhairori, n agodiya wa
Allah Ta'alah akan ni'imar saukar Alkur'ani mai girma, wanda Allah ya saukar da
shi, domin ya zama jin-kai ga talikai, saboda Kur'ani shine mafi girman ni'ima
kuma baiwar da tafi daukaka, wanda ruhi ke rayuwa da shi, saboda shine farkon
ni'imar da aka yi ga ruhi ga al'ummar Musulunci, bayansa kuma sai ni'imar
imani, saboda duk mutumin da Allah Ta'alah ya masa ni'imar imani daga cikin
wannan al'ummar, to hakika an hada masa ni'ima ta farko mai gamewa, wanda shine
Alkur'ani mai girma, da ni'ima ta farko wanda ta kebanta da shi, wanda kuma
shine ni'imar imani.
Kuma yana cikin hakkokin
ni'imar Kur'ani mai girma, da kuma hakkin ni'imar imani, Yin godiya ga Allah
Mabuwayi da daukaka
Kuma su; azumi da salloli
ko tsayuwar dararen Ramadhana, da nau'ukan da'oi, godiya ne ga Allah Ta'alah akan ni'imominSa, kuma ayyukan samun
kusanci ne zuwa gare shi.
Su ni'imomi hakkinsu da
abinda suke wajabtawa, shine ayi godiya ga Allah; ta hanyar aiki da zance, da
nuna soyayya ga Mai bada ni'imomi (wato, Allah) Mabuwayi da daukaka, Allah
Ta'alah yana cewa: "Lallai ne mu, mun yi maka
kyauta mai yawa" [kausar: 1]. Abinda ake nufi da "kausar" shine
alheri mai fadi mai albarka, wanda baya yankewa, wanda kuma daga cikinsa akwai
tafkin alkausara.
Sai Allah –a cikin wannan
surar- ya shiryar da ManzonSa annabi Muhammadu zuwa ga tsayuwa da hakkin Allah
Ta'alah, ta hanyar yin salla da makamancinta daga cikin ibadodi, domin ya
kyautata wa kansa, kuma hakika Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya cika dukkan
matakan bauta ta hanyar bada hakkokinsu, kuma ya tsayu da haka cikakken
tsayawa. Sa'annan sai Allah ya shiryar da AnnabinSa –صلى الله عليه وسلم-
zuwa ga kyautata wa halittu, ta hanyar ciyarwa da gamammen amfanarwa. Kuma
hakika Annabinmu ya yi aiki da hakan.
Wannan misali ne na
godiyar Annabinmu –صلى الله عليه وسلم- akan ni'imomi.
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma, ga Allah ne kadai zaka yi bauta, kuma ka kasance daga masu
godiya" [Zumar: 66]. Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- yake cewa A'isha
–Allah ya kara yarda a gare ta-, a lokacin da take cewa, Ka ke yin salloli har
kafofinka suke kumbura? Alhalin Allah ya gafarta maka abinda ya gabata daga
zunubanka da abinda ya jinkirta?? "Shin ba zan kasance, Bawa mai godiya ba",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Ku aikata godiya –Ya ku diyan dawuda-, kuma kadan ne mai godiya daga
cikin bayina" [Saba'i: 13].
Kuma Allah Ta'alah yake
fada dangane da annabi Musa –عليه الصلاة والسلام-: "Ka riko da abinda ba baka,
kuma ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
Kuma a lokacin da Allah
ya ambaci ni'imominSa da ya yi wa Maryama –عليها السلام- sai ya ce: "Ya Maryamu! Ki yi
Kankan-da-kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi ruku'i tare da masu
ruku'i" [Ali-imrana: 43].
Kuma Allah yake fada
dangane da sahabbai –Allah ya kara yarda a gare su-: "Kana ganinsu suna masu
ruku'I, masu sujada, suna neman falala daga Allah, da yardarSa. Alamarsu tana a
cikin fuskokinsu na guraben sujada" [Fat-h: 29].
Don haka,
ibadodi a cikin watan Ramadhana suna daga godiyar Allah akan ni'imar saukar da
Alkur'ani mai girma.
Kuma Kur'ani mai karamci
yana da karfin tasiri ga ruhi, a cikin watan Ramadhana, domin yana shiryar da
ruhi zuwa ga dukkan alkhairi, kuma ya tsawatar da ita daga aikata kowane
sharri; domin a yayin da rai mai umarni da aikata munana take zama ta yi rauni
saboda azumin da take yi, to sai ruhi kuma ya samu abincinsa a cikin Alkur'ani,
sai ya gyaru.
Sai ka jarraba kanka da
kanka –Ya kai Musulmi- shin ka tuba zuwa ga Allah a cikin watan Ramadhana?
Shin a cikin watan
Ramadhana, ka yi aiki domin abinda zai kasance a bayan mutuwa?
Shin ka mayar da ababen
da ka zalunta ga ma'abutansu, gabanin zuwan lokacin hisabi?
Shin ka kame sharrinka,
ga barin halittu?
Shin ka kyautata wa
halittu?
Shin ka sadar da
zumuncinka?
Shin ka yi biyayya ga
iyayenka?
Shin ka yi umarni da
kyakkyawan aiki, ka yi hani kan mummuna?
Shin ka dena cin riba, da
dukiyoyin haramun?
Shin ka yi kokarin koyi
da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- da sahabbanSa –Allah ya kara yarda a gare
su-, da da wadanda suka bi su, da kyautatawa, cikin tsarkin ruhi, da mikakkun
dabi'u, da karuwar imani, da karfin yakini, da ma'anoni madaukaka wadanda suka
yi dacen samunsu a cikin watan Ramadhana?
Ka karanta littafinka –Ya
kai Musulmi- tun a nan duniya, gabanin a lahira ce maka: "Ka karanta littafinka, domin
a yau, Ranka ta isa ta zama mai hisabi akanka", [Isra'i: 14].
Alkur'ani mai girma shine
babbar ni'imar da Allah ya saukar da ita a cikin watan Ramadhana.
Kuma lallai babu abinda
zai gyara halin da musulmai suke ciki face Alkur'ani da sunnah. Kuma da masu
hikimar Duniya za su hadu gaba dayansu, daga farkonsu har na karshensu,da
rayayyunsu da matattunsu, domin warware matsala daya daga cikin matsalolin
duniya, to lallai da ba za su samu hanyar hakan ba, sai ta hanyar Alkur'ani mai
girma.
Ka dubi MAS'ALAR AKIDA
KAN ALLAH TA'ALAH DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA DA AYYUKANSA, DA HAKKINSA DA YAKE
DA SU AKAN BAYINSA; Kay i dubi, akidu nawa ne a wannan mas'alar? Za ka samu
ba za su iya kididdiguwa ko kirguwa ba?
Kuma gaskiya a cikin
wannan mas'alar tana cikin abinda Alkur'ani mai karamci.
Kuma matsalar TATTALIN
ARZIKI a Duniya itama ta gagari masu hikima, kuma gaskiya a cikinta shine
abinda Kur'ani da sunnah suka fada akanta.
Wasu wadanda ba musulmai
ba, sun amfana da shari'ar musulunci a cikin irin wannan lamari, a cikin wasu
kofofin.
Kuma ba zai yiwu mutane
gaba dayansu su kasance musulmai ba. Sai dai kuma wajibi ne akan musulmai suyi
riko da Alkur'ani da sunnah, har idan sauran mutane suka ga abin koyi mai kyau,
daga kowane musulmi, to sais u amfana da su, koda kuwa cikin lamuransu na
duniya ne.
Kuma dukkan diyan-Adamu
masu kuskure ne, saidai mafiya alherin masu kuskure sune masu tuba.
Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai ne wannan Alkur'anin
yana shiryarwa zuwa hanyar da tafi mikewa, kuma yana yin albishir ga muminai
wadanda suke aikata ayyuka kwarai, cewa: Lallai ne suna da lada mai girma"
[Isra'i:9].
Allah ya yi mini albarka
NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina
neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani
zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai
rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina
gode masa,
Kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai
matsanancin karfi,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, amintacce,
Ya Allah ka yi dadin
salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da
sahabbansa gaba daya.
Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah
Ta'alah, kuma ku nemi kusanci da shi da aikata abinda ya yi umarni, da kuma
nisantar abinda ya yi hani kuma ya tsawatar, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai hakika wanda ya
tsarkaka (da imani) ya samu babban rabo * Kuma ya ambaci sunan UbangijinSa,
sa'annan ya yi salla" [A'alah: 14-15].
An ruwaito daga Umar bn
Abdul'aziz, lallai shi ya kasance yana umartar Mutane do su fitar da zakkar
fidr, sai ya karanta wannan ayar.
Kuma zakkar fidda-kai
wajibi ce akan kowane musulmi, saboda an ruwaito daga Abu-Sa'id –رضي الله عنه- ya
ce: "Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya farlanta zakkar
fidira, sa'in alkama, ko sa'in sha'ir, ko sa'i na dabino, ko sa'i na cukui, ko
sa'i na zabib; wato busasshen inabi".
Kuma gwargwadon sa'iy
shine kilo uku in banda 'dan kadan, sai dai bayar da kilo uku shine yafi
tsantseni (da fita daga sabani).
Kuma yana wadatarwa a
fitar daga abincin mutanen gari.
Kuma ana bayar da ita ga
karami dabba, da namiji da mace.
Kuma ya halatta a fitar
da ita gabanin idi da yini daya, ko biyu.
Kuma ta kan kasance
tsarkaka ne, ga mai azumi daga wargi, kuma tana zama toshiya ga abinda aka samu
na sakaci.
Kuma duk wanda ya bayar
da ita gabanin fitarsa ga salla, to hakan yana cikin lokacinta.
Wanda kuma ya bayar da
bayan idar da sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki.
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka
yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu.
No comments:
Post a Comment