HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/Sawwal/1439H
daidai da 22/Yuni/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
BADA KULAWA KAN LOKATAI,
DA RASHIN TOZARTA HAKKOKI DA WAJIBAI
Shehin Malami wato: Abdullahi
bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RIBATAR LOKACI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah muna
gode maSa, muna neman taimakonSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin
kayukanmu da munanan ayyukanmu, Wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da
shi, wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah.
Kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne, manzonSa.
Allah yay i dadin salati
a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai yawa.
Ya ku bayin Allah…
Ina muku wasici da ni
kaina, da bin dokokin Allah Mabuwayi da daukaka, domin ita ce wasiyyar Allah ga
halittar farko dana karshe, "Kuma hakika mun yi wasiyya ga
wadanda aka baiwa littafi a gabaninku, da ku, cewa ku bi Allah da takawa"
[Nisa'i: 131].
Ya ku taron Musulmai…
Ku yi takawar Allah
Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma zantukanku su rika
tabbatar da ayyukanku, domin hakikanin rayuwar Mutum shine abinda ya aiwatar da
shi cikin biyayyar Allah. Kuma mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa,
kuma ya yi aiki saboda abinda ke zuwa bayan mutuwa. Gajiyayye kuma, Wanda ya
biye wa son zuciyarsa, sai kuma ya kwallafa wa Allah buri.
Idan (dama ta zo maka), isarka
ta busa, to ka ribace ta
Domin kowane abu yana da
lokacin natsawa.
Kuma kada ka gafala, ga barin
aikin kyautatawa a cikinsa
domin baka san lokacin da
damarka zata yanke ba
Ya ku bayin Allah
Lallai kun yi bankwana da
watan azumi, wato lokacin falala da da'a da samun gafara, saidai bamu san
wanene aka karbi ayyukansa a cikinmu ba, balle mu masa barka, wanene kuma aka
mayar da nasa, balle mu masa ta'aziya, Allah ya karbi ayyukanku na da'a, kuma
ya gafarta zunubanku, kuma ya ninninka muku lada.
Sannan ku daidaitu akan
addinin Allah, ku yi aiki domin karin kusanci zuwa gare shi, saboda tabbatuwa
akan da'a yana daga alamomin karbuwar aiki, kuma bawa bai kusanci Allah da
komai ba, wanda yafi soyuwa a gare shi fiye da wanda ya farlanta shi akansa,
kuma bawa ba zai gushe ba, yana kusantar Allah da nafilfili face Allah ya so,
shi. Kuma duk wanda ya kusanci Allah da kamar taki daya, to Allah zai kusance
shi da kamar zira'i, kuma wanda ya kusance shi da kamar zira'i, to Allah zai
kusance shi da kamar tsawon hannu biyu. Wanda ya je wa Allah yana tafiya, to
Allah zai je masa yana sauri.
Sai ku kiyaye farillai,
kuma kada ku kaurace wa Alkur'ani, kuma ku rika kwadayin sallolin dare, da
azumin yini, saboda an ruwaito daga Sufyan bn Abdullahi As-Sakafiy, ya ce: Na
ce wa Manzon Allah, Ka gaya min wata magana a cikin Musulunci wanda ba zan
tambayi wani a bayanka ba? Ya ce: "Ka ce: Na yi imani da Allah sannan ka daidaitu".
Kuma lallai yana daga
shiriyar Annabinku, azumtar yini shida a cikin watan Shawwal, saboda an ruwaito
daga Abu-Ayyub Al'ansariy –Allah ya kara yarda a gare shi- lallai shi ya bada
hadisi cewa, lallai Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Wanda ya yi azumin watan
Ramadana, sa'annan ya biyar musu da guda shida a cikin watan Shawwal, to ya
kasance kamar azumin shekara".
Ma'anar wannan shine:
Yayin da kyakkyawa aiki ana ninnika shi da kwatankwacinsa goma, to azumtar
watan Ramadana zai kasance kamar azumtar watanni guda goma ne, shi kuma azumtar
kwanaki shida na Shawwal kamar azumtar watanni biyu, wannan kuma shine daidai
da azumtar kwanakin shekara gaba daya.
Ya ku taron Musulmai…
Lokaci kamar dukiya ne,
kowanne daga cikinsu wajibi ne ayi kwadayin kiyaye shi, da tattali wajen
sarrafa shi da gudanar da lamarinsa.
Kuma idan dukiya za a iya
tattara ta, a taskance ta, tare da bunkasa ta, to lallai lokaci lamarinsa ba haka
ya ke ba; saboda kowace lahaza da dakika idan ta tafi, to ba za ta dawo gare ka
ba, har abada, koda ka kashe dukkan abinda ke bayan kasa gaba daya.
To, idan ya kasance
zamani an kaddara masa wani lokaci ayyananne, kuma iyakantacce, wanda ba zai
yiwu a gabato da shi ba, ko a jinkirta shi, sai kimarsa -wato lokaci- ta
kasance cikin kyautata amfani da shi = to ya wajaba ga kowane Mutum ya kiyaye
lokacinsa, ya yi amfani da shi ta hanyar da ta fi kyau, kuma kada ya yi sakaci
akan wani abu daga cikinsa; kadan ne ko mai yawa.
Kuma domin Mutum ya
kiyaye lokacin, dole ne ya san a ina yake tafiyar da lokacin? Da kuma yadda
yake gudanar da shi?
Sai ku saurara!
Lallai mafi girman abinda
aka tafiyar da lokaci a cikinsa, kuma mafi daukakansu shine, cikin yin biyayya
ga Allah Mabuwayi da daukaka.
Kuma duk zamanin ko lokaci,
wanda ka tafiyar da shi cikin wannan biyayyar to baza ka taba nadama a gare shi
ba, har abada.
Ya ku bayin Allah…
Rayuwa 'yar kadan ce, zamani
kuma gajere ne, kuma duk abinda ya shige ya shige, duk kuma abinda zai zo to
mai zuwa ne. kuma rayuwa gaba dayanta lokacin yin biyayya ga Allah ne, kuma
babu wata dama ta yin sakaci a cikinta, kuma dukkan rayuwa lokaci ne na
jarabtar bayi, don haka babu damar kakkautawa ko jira. Kuma da wannan rayuwar
gajeriya Mutum ka iya sayan tabbata madawwamiya a cikin Aljannoni, da wanzuwa
wanda ba zai yanke ba, a cikin wani zamani.
Ta daya fiskar kuma,
lallai duk wanda ya yi sakaci a rayuwarsa, to lallai zai auka cikin halaka da
hasara.
Don haka, Ya dace mai
hankali ya san kimar rayuwarsa, kuma ya yi dubi ga ransa cikin lamarinsa, sai
ya ribaci abinda ba zai yiwu a risko shi ba, wanda kuma sau dayawa cikin
tozarta shi ne, halakar bawa take.
Ya ku taron Musulmai…
Lallai lokacin hutu na bazara
da kuke rayuwa a cikinsa wata dama ce ta hutar da jiki, da kuma kokarin sauke
wasu hakkoki da yin abinda ya kubuce, da yin guzuri domin lokacin da ake
fiskanta na kusa da na nesa. Saboda ba ana bada hutu ba ne, domin a wofintar da
hakkoki na wajibai, da tozarta su, da dulmuya cikin sha'awowi, da kakkara dorin
doriyar aiyuka, da nauyaya kafadu da laftun ayyuka ko kakkara su a rayuwa.
Sai ku ji tsoron Allah a
lamarin iyalanku da 'ya'yanku, kuma ku tarbiyantar da su akan kwadayin kiyaye
lokaci, da amfani da shi cikin abubuwa masu amfani, na ilimi da aiki, ta fiskar
neman halal, ko aikin da'a da bautar Ma'abucin girma, wannan kuma ita ce
tarbiyyar Mazaje.
Kuma lallai tarbiyyar matasa
akan tuntsurar da lokuta da damammaki, ya kan koyar da su tozarta hakkoki da
wajibai, da gazawa wajen daukar amanoni da nauyin al'umma, kuma yana koyar da
su dabi'ar ko-oho, da kasa fiskantar matakan rayuwa.
Shi kuma faraga da rashin
aikin yi zai kai yara ga aukawa cikin hatsarin fitintinu, da soye-soyen zuciya,
da karkata, da bala'oi.
Ya ku bayin Allah…
Lallai ne Allah zai muku
tambaya kan lokutanku na rayuwa; da cewa, ga aikata me, kuka tafiyar da su?
Saboda an ruwaito daga Abu-Barzatah Al'aslamiy –Allah ya kara yarda a gare shi-
ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Duga-dugan bawa a ranar
Alkiyama ba za su gushe ba, face an tambaye shi kan abubuwa guda hudu; sai an
tambaye shi kan rayuwarsa akan me ya salwantar da ita, da iliminsa; me ya
aikata da shi, da dukiyarsa ta yaya ya same ta, kuma ga me ya ciyar da ita, da
tambaya kan jikinsa a me ya tsufar da shi?".
Kuma idan Mutum ya iso
wurin hisabi, sannan ya kafu tsaye akan kafofinsa babu takalmi, kuma babu
tufafi, (a gaba ga Ubangijinsa) babu shamaki, yana jiran a tambaye shi, kuma
yana shirin bada amsa = Sai aka tambaye shi kan rayuwarsa a me ya tafiyar da
ita? Da samartakarsa a me ya salwantar da ita?
Wayyo Allah! Me yafi
wannan lamari girma, kuma me yafi wannan musiba tsanani?
Wajibi ne kowanne daga
cikinmu ya tambayi kansa, idan aka jefo masa wannan tambayar, me zai darsu a
zuciyarsa?
Kuma wane aiki ya tanada
tsawon samartakarsa, da kuma rayuwarsa? Kuma me ya shirya don ya zama amsa?
Sai ku yi tanadin amsa
–Ya ku bayin Allah- ga wannan tambayar, kuma amsar ta zama daidai.
Allah ya sanya mu da ku, "daga cikin wadanda suke jin zance,
sai su bi mafi kyansa, domin wadannan sune wadanda Allah ya shiryar, kuma
wadannan sune ma'abuta hankali" [Zumar: 18].
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah,
kuma ya isar,
Salati da sallama su kara
tabbata ga bayinSa wadanda ya zaba.
Ya ku bayin Allah…
Lallai mai hankali ba zai
yarda ya tozarta dakikon numfashinsa ba, alhalin rayuwarsa tana raguwa, ya
tozarta su wuce kara zube, ba a cikin lamarin Duniya ko lamarin lahirarsa ba.
Kuma lallai samun lokaci
da faraga ni'ima ce, idan aka kyautata moransa, azaba ce kuma idan aka tozarta
aiki da shi, saboda an ruwaito daga Abdullahi bn Abbas –Allah ya kara yarda a
gare su- ya ce: Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ni'imomi guda biyu an rinjayi
Mutane dayawa akansu; sune lafiya da samun lokaci".
Don haka, almubazzarantar
da lokatai, bugun hanci ne da tawaya cikin addini, kuma rauni ne da wauta cikin
hankula, wanda aka jarrabi Mutane dayawa da aikata shi;
Sai ku ji tsoron Allah
akan rayukanku da abin kiyonku, kuma ku ribaci damammaki, kuma ku yi kwadayin
riko da su, domin an ruwaito daga Abdullahi bn Abbas –Allah ya kara yarda a
gare su- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya fada wa wani
Mutum alhalin yana masa wa'azi: "Ka ribaci abu biyar gabanin abubuwa biyar;
samartakarka gabanin tsufanka, da lafiyarka gabanin cutarka, da wadacinka
gabanin talaucinka, da faragarka gabanin shagaltuwarka, da rayuwarka gabanin
mutuwarka".
Ya ku masu yin tarbiyya…
Lallai ne babu wani kunci
cikin moriyar jin dadi, da shakatawa, da debe kewa, da neman sararawa, matukar
babu ketare iyaka, ko aikata abin ki a cikinsa, ko tozarta hakkoki da wajibai,
domin hakan yana cikin jin dadi da abubuwa na halal, kuma a cikin hakan akwai
sake jaddada karfin jiki, da nashadantar da rai. Saidai kuma ba tare da an
tuntsurar ko an yi almubazzarancin lokuta masu tsada ba, kuma ba tare da an
tsananta cikin wasa ko an zurfafa cikin gafala ba, domin al'ummar musulunci
tana da matsanancin bukatar karfi da lokutan 'ya'yanta, sai ku tsakaita, kuma
ku kwatanta.
Bayan haka, Ya ku taron
Musulmai…
Lallai abinda ke aukuwa
tsakanin Musulmai na sabani da gujewa-juna, da fadace-fadace, da soke-soke,
yana daga cikin manyan ababen bakin ciki, da musibu masu daga hankali, da
fitintinu mafiya tsanani, da manyan ababen da suke janyo wa zukata bacin rai.
Kuma lallai tsayar da
lamarin zuban jinin Musulmai, da kiyaye mutuncinsu da dukiyoyinsu, yana daga
cikin manya-manyan manufofin Musulunci, da tabbatattun abubuwa a cikin addini
mikakke, kuma wannan shine lafiyayyun hankali suke hukuntawa.
Kuma lallai Duniyar
Musulmai ta zura ido, tana fatan samun zaman lafiya tsakanin 'yan'uwanmu na
kasar Afganistan, kuma tana maraba da samun sulhu a tsakaninsu, bayan abinda ya
sauka akansu na bone da yakuka suka haifar, da kuma fadace-fadace, da rabuwar
kai da jayayya, wanda a cikinsu yara da mata suka dandani kudarsu. Har wadanda
basu ji, ko suka gani ba, suke ta neman taimakon Majibinci Madaukaki.
Taki ba komai ba ne, sai
abinda kuka sani, kuma kuka dandana
Kuma shi a wurinku, ba
labari ba ne na gaibu
Ya ku 'yan'uwa Mutanen
Afganistan…
Yin sulhu alheri ne, sai
ku ji tsoron Allah, ku yi sulhu, ku yi afuwa ku yi yafiya, "Lallai
Muminai 'yan'uwa ne; sai ku yi sulhu tsakanin 'yan'uwanku"
[Hujurat: 10].
"kuma wanda
ya yi hakuri, kuma ya gafarta, lallai wannan yana daga manyan lamura"
[Shura: 43].
Don haka, kyale wasu
maslahohin, domin tsayar da zuban jinin Musulmai yana da falala mai girma, kuma
maslaha ce babba, kuma karfin hali ne da gwarzantaka wanda ya kai makura.
Sai ku tsayar da shekar
da jinin jama'arku da al'ummarku, kuma ku yi sulhu abinda ke tsakaninku, kuma
ku taimaki junanku akan biyayyar Allah da takawa, kuma kada ku taimaki wani
akan sabo da ketare iyaka.
Allah ya hade abinda ya
wargaje a tsakaninku, ya daidaita kalmarku, ya kawo sulhu a tsakaninku, ya
daidaita tsakanin zukatanku, kuma ya kashe wutar fitina da zafin kai, wanda da
ta kunnu a kasarku.
No comments:
Post a Comment