HUDUBAR IDIN AZUMI
DAGA
MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 01/SHAWWAL/1439H
Daidai da 15 /YUNIYO / 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN
ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD,
ALLAHU AKBAR KABIRAN,
WALHAMDU LILLAHI KASIRAN,
WA SUBNAHALLAHI BUKRATAN WA
ASILAH
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da
kuma a bayyane (a lokacin ganawa).
Ya ku musulmai …
Ya ku musulmai,,,;
YANA DAGA CIKIN SIFOFIN
ALLAH TA'ALAH, GODIYA DA KYAUTA, Kuma cikin falalarSa Allah Subhanahu ke dandana
wa masu biyayya a gare shi, wasu fa'idodi daga cikin fa'idodin bautar da suka
yi masa, tun a gidan Duniya, domin gaskiyar alkawarinsa na cewa zai basu
sakayya a cikin Aljannonin ni'ima ta tabbatu a gare su.
Kuma a cikin watan
Ramadhana Musulmai sun samu bushin iskar rahama kuma sun dandani rauhaniyya
daga Ubangijin Talikai; ta fiskar ratayar zukatansu da Allah, da buduwar
kirazansu, da garautakar zukatansu, domin bayi su iya lazimtar biyayyar
UbangijinSu, a sauran shekarun rayuwarsu, domin samun ni'ima da kasantuwa a
cikinta shine tukewar abinda rayuka ke bukata. Kuma da ni'imar zukata ke samun
walwala da farin ciki. Kuma halittu gaba dayansu kowa yana fafutikar neman
sa'ida ne; da kwadayinsu da ayyukansu.
Ita kuma ni'ima cikakka,
lallai tana kasancewa ne cikin riko da addinin Musulunci, ta fiskar saninsa da
aiki da shi. Saboda ma'abuta musulunci suna cikin ni'ima madawwamiya a
rayuwarsu ta Duniya da Barzahu da kuma Lahira, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai masu da'a ga
Allah, tabbas suna cikin ni'ima", [Infidaar: 13].
Saboda A DUNIYA Allah
ya buda kirazansu da musulunci, kamar yadda yake cewa: "Wanda Allah ya nufi
ya shiryar da shi, sai ya buda kirjinsa domin Musulunci" [An'am: 125]. Kuma
da Musuluncin Mutane ke samu rayuwarsu da haskensu, Allah Ta'alah ya ce: "Shin wanda ya
kasance matacce, sa'annan muka rayar da shi, kuma muka sanya masa wani haske,
wanda ke tafiya da shi, yana zama daidai da mutumin da misalinsa yana cikin
duffai, kuma ba zai taba fit aba daga gare su?" [An'am: 122].
Kuma Allah ya rubuta musu
samun rahama a Duniya da Lahira, kamar yadda yake cewa: "Kuma wadannan,
Allah zai musu rahama",
[Taubah: 71].
Kuma Allah Ta'alah ya kan
jiyar da Musulmai dadi, kuma gaggauta musu da sakamakonsu a Duniya da Lahira;
don haka suke samun sakayya tun a nan Duniya, kuma lallai abinda ya tanadar
musu shine mafi alkhairi da girma, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma ga wadanda
suka kyautata a cikin wannan duniyar suna da sakamako mai kyau, kuma hakika
Lahira ce mafi alheri",
[Nahl: 30].
Kuma MAFI GIRMAN
NI'IMOMIN ALLAH GA BAYINSA a wannan Duniyar Shine yadda ya sanya musu son
wannan addinin, kuma ya kawata shi a cikin zukatansu, kuma ya dandana musu
zakin da'a a gare shi, Sai zukatansu da badinunsu suka ci-kwalliya da kudurtar
ginshikan addini da lamuransa tabbatattu, Zahirinsu kuma suka dau ado, da yin
aiki da umarnin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Sai dai Allah ya
soyar da imani a gare ku, kuma ya kawata shi a cikin zukatanku", [Hujurat: 7].
Don haka, Fiskantar
Ubangiji (ta hanyar bauta) da mayar da lamura gare shi, da yarda da shi,
sakayya ne na gaggawa, kuma Aljanna ce halartacciya.
Kuma YIN IMANI DA ALLAH
DA KUMA MANZONSA shine abinda ya dunkule samun sa'ida, kuma asali ga
jin-dadi. Kuma imanin a cikin zuciya yana da wani irin zaki da dadi, wanda babu
abinda yake daidai da shi, Shehin Musulunci –Ibnu Taimiyyah Allah ya yi masa
rahama- ya ce: "A zuciya, babu abinda yafi zaki, kuma yafi dadi, yafi kasancewa mai
kyau da taushi da ni'ima, fiye da zakin imani, wanda ya ke kunsa: Bautar Allah,
da sonsa, da tsarkake addini a gare shi".
Kuma zakin imani a cikin
zuciya, alama ce da take nuna lallai Musulunci shine addinin gaskiya, Sarki
Hiraklu ya tambayi Abu-Sufyana, kan annabinmu Muhammadu –sallal Lahu alaihi wa
sallama- da lamarin gaskiyar annabcinsa, sai ya ce: "Sai na tambaye ka,
Shin wani daga cikin sahabbansa yana yin ridda ya fita daga Musulunci, saboda
fushi ga addininSa, bayan ya shiga cikinsa? Sai ka riya cewa, a'a, To haka
imani yake a lokacin da bushar zakinsa ta cakuda da zukata", Bukhariy da Muslim.
Domin muminai sun fi dukkan
mutane dadin rayuwa, kuma sun fi su samun ni'imar zukata, da fadin kiraza, da
farin cikin rayuka da zukata, Allah Ta'alah ya ce: "To, Lallai ne
masoyan Allah babu tsoro akansu, kuma ba za su kasance cikin bakin ciki ba *
sune wadanda suka yi imani, kuma suka kasance suna yin takawa", [Yunus: 62-63].
Kuma yana daga walwalarsu,
lallai aminci a cikin zuciya, da wajenta, yana hade da rayuwarsu, Allah Ta'alah
ya ce: "Wadanda suka yi imani, kuma bas u cakuda imaninsu da zalunci ba,
wadannan suna da aminci, kuma sune shiryayyu", [An'am: 82].
Kuma da imani ne, mutum zai
samu abinda ake kiransa "birru" gaba dayansa, wanda kuma shine abinda
mutum ke samu a cikin zuciyarsa na zaki da jin dadi da farin ciki, Allah
Ta'alah ya ce: "Bai zama addini ba, kawai, ku juyo da fiskokinku wajen gabas da
yamma, sai dai addini (cikakkensa) shi ne ga wanda yay i imani da Allah da
Ranar Lahira, da Mala'iku, da littatafai, da Annabawa…", [Bakara: 177].
Kuma a duniya babu wani jin
dadi da ni'imar da tafi girma akan wacce take cikin sanin AllahTa'alah da samun
ilimi akansa, kuma idan bawa ya san UbangijinSa sai ya so shi, kuma ya bauta
masa, kuma wannan shine Aljannar Duniya, kuma mafi kyan abinda ke cikin Duniyar.
Kuma babu wani abu wanda ya
kai TAUHIDIN ALLAH, yalwata kirji da sanya zuciya jin dadi, saboda a
cikin zuciya akwai wani gurbi wanda babu abinda ke cike shi, face ayyukan
fiskantar Allah, kuma idaniya bata samu sanyi, zuciya da rai basa samun natsuwa,
sai ta hanyar abin bautanta, wanda shine Allahn gaskiya subhanah.
Kuma ba a taba tunkude
tsanani, kuma a iya janyo ni'imomi ba, da abinda yafi tauhidi.
Kuma samun karshen farin
ciki ya kasancewa ne da Allah Ta'alah, Allah -subhanah- yana cewa: "Ka ce, da falalar
Allah, da rahamarSa, sais u yi farin ciki, domin shine mafi alheri daga abinda
suke tarawa"
[Yunus: 58].
Ibnul-kayyim –Allah yayi
masa rahama– ya ce: "Yin farin ciki da falalar Allah da rahamarsa, biye yake
da yin farin ciki da shi Allah -subhanah-, saboda mumini yana yin farin ciki da
UbangijinSa, sama da farin cikin wani mutum da abinda ke farin ciki da shi,
kuma zuciya ba za ta samu hakikanin imani ba, sai ta samu dandanon wannan farin
cikin, ta yadda jin dadinta zai bayyana a cikin zuciyarsa, haskenta kuma akan
fiskarta".
Kuma duk lokacin da sanin
bawa ga Ubangijinsa ya kara karfi, to sai sonsa ga Allah ya kara karfi.
Kuma bawa bashi da wani
farin ciki, ko jin-dadi, sai cikin son Allah, da kusantarsa da abinda yake so,
Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani sun fi matsanancin so ga Allah", [Bakara: 165].
An tambayi wani daga cikin
magabatan kwarai, kan abinda yafi dadi a cikin Duniya? sai ya ce: "Son Allah, da
saninSa, da ambatonSa".
Kuma BAUTAR ALLAH SHI
KADAI ita ce hikimar da ta sanya aka samar da halittu, kuma aka yi umurni.
Da ita ibadar ake ni'imta bayi, kuma ake karrama su.
Kuma babu abinda yafi
amfani ga bawa fiye da fiskantarsa ga Allah, da shagaltuwarsa da yin da'a a
gare shi, da fifita neman yardarsa.
SALLAH kuma ita ce, sanyi ga
idanun Musulmai, Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "An soyar mini daga
cikin abubuwan Duniya; tirare da mata, kuma an sanya sanyin idona a cikin
sallah"
Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma, yaya musulmi ba zai
ni'imtu da sallarsa ba, alhalin Allah yana ta bangaren mafiskantarsa idan ya
tashi sallah. Kuma mafi kusanyin yanayin bawa da UbangijinSa shine idan ya yi
sujada a cikin sallarsa. Kuma hakika mushirkai sun fada awani yaki tare da
musulmai: "Salla zata zo musu, wanda ita suka fi so, fiye da 'ya'yansu", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma duk lokacin da bawa ya
dandani zakin salla, to sai jawuwarsa gare ta yafi tsanani, aiki da ita kuma
yafi sauri.
Kuma ZAKKAH an gwama
ambatonta da sallah a cikin nassoshi.
Kuma duk wanda ya fitar da
zakka cikin dadin rai, to sai Allah ya dandana masa zakin imani da dandanonsa,
Ibnul-kayyim –Allah yay i masa rahama- ya ce: "Mai sadaka a duk
lokacin da ya bayar da wata sadaka, sai zuciyarsa ta samu natsuwa da hakan,
kirjinsa ya yi fadi da aikata hakan, sai farin cikinsa yay i karfi, jin dadinsa
ya kara girma, To da sadaka bata da wani fa'ida sai wannan ita kadai, to ya
dace musulmi ya yawaita sadaka, kuma ya rika gaggawan aikata ta".
AZUMI shi kuma yana da wani dadi,
ma'abutansa kuma suna da wani farin ciki, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa
sallama- ya ce: "Mai azumi yana da farin ciki biyu da zai yi su; farin ciki daya a
lokacin buda-bakinsa, da farin ciki a lokacin saduwarsa da UbangijinSa", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito.
HAJJI kuma rayuka suna haniniyar
sonsa, sais u shisshirya domin shi, kuma su ji dadin aikata shi, suna msau
gaggawan tafiya wuraren da ake aiwatar shi (Masha'ir, Arfa, Minah da
Muzdalifah), da kwadayin gushewar zunubansu, har su dawo kamar yadda aka haife
su.
Don haka, samun rabo gaba
dayansa yana cikin TSARKAKE RAYUKA, ta hanyar yin bauta, da kyawawan
halaye, Allah Ta'alah yake cewa: "Hakika wanda ya tsarkake ransa ya samu
babban rabo",
[Shams: 9].
Mai yin da'awa zuwa ga
Allah, zai samu babban rabo, kuma yay i linkaya cikin ni'ima da farin ciki,
Allah Ta'alah ya ce: "Wata jama'a daga cikinku ta kasance tana kira zuwa ga
alheri, kuma suna umurni da kyakkyawa, suna hani ga abin ki, kuma wadannan sune
masu samun babban rabo", [Ali-imrana: 104].
Kuma ilimi mai amfani yana
buda kirji yana kuma yalwata shi, kuma ba zai gushe da ma'abucinsa ba cikin
ni'ima da farin ciki, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai wadanda suke
jin tsoron Allah daga cikin bayinSa sune Malamai", [fadir: 28].
Shekhul Islam
Ibnu-taimiyyah –Allah yayi masa rahama- ya ce: "A duniya babu wata
ni'imar da ta yi kamantacciya da ni'imar lahira, face ni'imar imani da ta ilimi".
AMBATON ALLAH yana buda kirji, kuma
zuciya tana samun ni'ima da shi, kuma zikirin yafi sauran ayyukan da'a karancin
wahala, kuma ya fi su girman dadi, da yawaita sanya farin ciki da walwala, Allah
Ta'alah ya ce: "Wadanda suka yi imani, kuma zukatansu suka natsu da ambaton Allah,
kuma lallai da ambaton Allah zukata ke samun natsuwa", [Ra'ad: 28].
Shekhul Islam
Ibnu-taimiyyah –Allah yayi masa rahama- ya ce: "Mutum yana samu a
cikin zuciyarsa, da ambaton Allah, da ambaton yabonsa da ni'imominsa da
bautarsa, yana samun dadi, irin dadin da baya samu a cikin abinda ba su ba".
Kuma MAFI GIRMAN ZIKIRI shine
Alkur'ani Mai karamci, wato maganar Ubangijin talikai, shine shiriya da waraka,
da jin-kai ga muminai, kuma Kur'ani shine falalar Allah da rahamarsa wanda bayi
suke farin ciki da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wadanda muka
basu littafi, suna yin farin ciki da abinda muka saukar zuwa gare ka", [Ra'ad: 36].
Kuma idan mumini ya ji
ayoyin Allah ana tilawarsu sai ya cika da bushara da farin ciki, saboda abinda
ya ke samu a zuciyarsa na zaki da jin dadi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan aka
saukar da wata sura, to daga cikinsu akwai wadanda suke cewa, wane a cikinku,
wannan sura ta kara masa imani, to amma wadanda suka yi imani, sai ta kara musu
imani, kuma su suna yin bushara", [Tauba: 124].
Ibnul-kayyim –Allah yayi
masa rahama- ya ce: "Idan ka so, ka san abinda ke wurinka da abinda ke wurin
waninka na soyayyar Allah, to ka yi dubi kan son Alkur'ani wanda yake
zuciyarka, da yadda ka ke jin dadin sauraronsa".
Alkur'ani yana da halawar
da tafi ta zuma, Wani Mutum ya zo wurin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-
sai ya ce: "Lallai ne ni a cikin barci nayi mafarkin girgije mai inuwa, wanda
kuma mai da zuma suke digowa daga gare shi, Sai Abubakar ya ce Manzon Allah
–sallal Lahu alaihi wa sallama- ka kyale ni, na fassara mafarkin, sai ya ce: to
ka fassara, Sai ya ce: Amma wannan girgijen Musulunci ne, shi kuma abinda
digowa na mai da zuma to shine Alkur'ani ne halawarsa take digowa ", Bukhariy da Muslim.
"Misalin Mumini
wanda yake karanta Alkur'ani, kamar dan icen utrujja ne, kamshinsa mai dadi ne,
dandanonsa shima yana da dadi", Bukhariy da Muslim.
Kuma ga ma'abuta Alkur'ani
ne natsuwa da rahama take sassauka, kuma duk wanda ya karanta shi, sa'annan ya
yi aiki da abinda ke cikinsa to ba zai bace ba, kuma ba zai tabe ba.
Kuma MA'ABUTA BIYAYYA GA
ALLAH ba za su gushe ba suna cikin ni'ima, har zuwa lokacin da za su
rabautar da samun kololuwar jin dadinta a cikin Aljannar ni'ima. Kuma mafi
girman jin dadinsu a cikin Aljanna ganin Allah Subhanah, da jin maganarSa daga
gare shi. Kuma samun wannan shine fa'idar sanin Allah da yin bauta a gare shi,
a Duniya; Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Sai Allah ya yaye
shamaki (sais u ganshi), lallai ba a baiwa 'yan Aljanna komai ba, wanda yafi
soyuwa a gare su, fiye da yin dubi zuwa ga fiskar Ubangijinsu Mabuwayi da
daukaka",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ya kasance daga cikin
addu'ar Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kan ce: "Kuma ina rokonka
samun dadin da ke cikin dubi zuwa ga fiskarka, da kuma begen saduwa da kai", Nasa'iy ya ruwaito
shi.
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Wanda ya dandani zakin imani, to lallai ba zai taba koshi
daga gare shi ba, sai ya rika fiskantar ayyukan biyayya ga Allah, sai tasirinsu
kuma su rika bayyana a harshensa da gabbansa, sai kuma ransa ta rika mika wuya
ga Allah, sai ya tsira daga dukkan abinda ka iya lalata masa addininsa, sai
Allah ya rika kautar da hankalinsa daga aikata haramun; ta yadda ba zai waiwaya
zuwa gare su ba, kuma ba zai shagaltu da su ba, sai zuciyarsa ta samu garkuwa
daga hakan, Allah Ta'alah ya ce: "Saidai Allah ya soyar da imani a gare ku,
kuma ya kawata shi a cikin zukatanku, kuma ya kyamantar da kafirci da fasicci
da sabo zuwa gare ku, kuma wadannan su ne shiryayyu", [Hujurat: 7].
Ibnul-Rajab –Allah yayi
masa rahama- ya ce: "Idan zuciya ya samu zakin imani sai ya rika jin dacin
kafirci da fasicci da sabo, don haka annabi Yusuf –alaihis salam- yake cewa: YA
UBANGIJINA, KURKUKU SHINE YAFI SOYUWA A WURINA AKAN ABINDA SUKE KIRANA ZUWA
GARE SHI, KUMA IDAN BAKA KAUTAR DA KAIDINSU DAGA GARE NI BA, ZAN KARKATA ZUWA
GARE SU, SAI IN KASANCE DAGA JAHILAI".
Kuma duk lokacin da bawa ya
dandani zakin imani, ba zai rika jiran yabon mutane ba, kuma ba zai dena abu
ba, domin suna yin zargi.
Kuma ni'imar da take cikin
ayyukan biyayya tana gadar da tabbatuwa a cikin addini, kuma haka imani yake a
lokacin da zakinsa ya cakuda da zukata, babu wani da ke bakanta masa rai. Kuma duk
wanda ya dandani zakin ibada sai ya dawwama akanta, kuma aikin Annabi –sallal Lahu
alaihi wa sallama- ya kan dawwama masa, saboda ya kasance idan ya aikata wani
aiki sai ya tabbatu akansa. Kuma idan imani ya tabbatu a cikin wata zuciya, har
ta samu zakinsa, to sai ta so shi, kuma ta so tabbatuwa akansa da dawwamarsa,
da samun kari a cikinsa. Sai kuma ya rika kyamar rabuwa da shi, har ya zama yafi
tsananin kin ya rabu da shi fiye da kinsa kan a jefa shi cikin wuta.
Kuma lallai addini yana da
zaki da dandano; wanda samu dandanonsa, sai ya debe masa kewa daga Duniya da
abinda ke cikinta (na bala'oi), sai musibu su zama masu sauki a wurinsa, kamar
yadda masihirta suka gaya wa Fir'auna a lokacin da suka dandani zakin sujjada
da imani: "Lallai ne mu mun yi imani da Ubangijinmu domin ya gafarta mana
kura-kurenmu, da abinda ka tilasta mu akansa na sihiri, Kuma Allah shine mafi
alheri, kuma mafi wanzuwa", [Daha: 73].
Kuma suka ce masa: "Ka aikata abinda
kake iya hukuntawa, ai kana hukunci ne akan rayuwar Duniya kawai", [Daha: 72].
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD
Ni'imar imani da zakin biyayya gabanin samunsu ana shardanta
musu IKHLASI wato yin aiki domin Allah, domin babu wani bawan da zai samu zakin
ibada face ya nufi fiskar Allah da ita, domin da hakan ne kawai zai samu
hadewar zuciyarsa da yalwarta. Kuma da yin ikhlasi da nasiha, da lazimtar
jama'ar Musulmai ne ake samun salamar zuciya da budewarta, Annabi –sallal Lahu
alaihi wa sallama- ya ce: "Ababe uku zuciyar Musulmi ba ta yin kulli
akansu; tsarkake aiki ga Allah, da nasiha ga jagororin Musulmai, da lazimtar
jama'ar Musulmai",
Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma samun zakin imani yana
biye ne da cikar son bawa ga UbangijinSa, wannan kuma ta hanyar cike soyayyar
asalinta da reshenta, da kuma tunkude abinda ka iya kishiyantarta, Annabi –sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Abu uku, wanda suka kasance a tare da shi,
to lallai ya samu zakin imani da su, Ya kasance Allah da Manzonsa sune yafi so,
akan wadanda ba su ba, kuma ya so mutum ba komai ya sanya yake sons aba, face
domin Allah, kuma ya kyamanci komawa cikin kafirci bayan Allah ya tsamar da shi
daga gare shi, kamar yadda yake kyamar a jefa shi a cikin wuta", Bukhariy da Muslim.
Kuma bawa ba zai samu zakin
imani ba da kuma dadin biyayya, face ya kasance babban abinda ke sanya shi
farin ciki shine addininsa da bautarsa ga Allah, kuma sai ya tsananta mika wuya
ga UbangijinSa da annabinSa, saboda Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya
ce: "Ya samu dandanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, Musulunci
kukma addini, annabi Muhammadu kuma a matsayin manzo", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma ibadar rokon Allah,
da kyautata zato a gare shi sune mabudan kowane alheri, Allah a cikin
hadisin kudusiy yana cewa: "NI, ina wurin da bawana yay i zatona".
Kuma imani da KADDARAR
DA ALLAH KE HUKUNTAWA, yana kai ma'abucinsa ga jin dadi, kuma babu wani
bawan da zai samu zakin imani sai ta hanyar hakan, Ubadah bn As-Samit yake fada
wa dansa: "Lallai kai ba zakat aba samun dandanon hakikanin imani ba, har sai
ka san cewa lallai abinda ya same ka, ba zai taba kubce maka ba, kuma abinda ya
kubuce maka, lallai bai zama zai same ka ba", Abu-Dawud ya ruwaito shi.
Ibrahimul Harbiy –Allah yay
i masa rahama- ya ce: "Masu hankalin kowace al'umma sun yi ijma'i, cewa lallai
wanda bai tafi da imani da kaddara ba, to ba zai taba jin dadin rayuwarsa ba".
Kuma tambarin jin dadin
bawa shine, Idan Allah yay i masa ni'ima sai ya yi godiya, idan kuma aka
jarabce shi sai yay i hakuri, idan kuma bawa yay i zunubi sai ya nemi gafara.
Kuma yawaita nafilfili,
da neman taimako cikin hakuri da salla, suna bude wa bawa kofofin ni'imomi, Allah
Ta'alah a cikin hadisin kudusiy yana cewa: "Kuma bawana ba zai
gushe ba, yana kusantata da nafilfili, face na so shi", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma mafi alherin abinda ke
taimakon bawa wajen riskar ni'imomi shine yakar rai, da tursasa mata akan
ayyukan biyayya, Shekhul Islam Ibnu Taimayya –Allah ya masa rahama- ya ce: "Wanda ya ga cewa
lallai kirjinsa baya buduwa, kuma baya samun zakin imani, da kuma hasken
shiriya, sai ya yawaita tuba da neman gafara, sai kuma ya lazimci Karin kokarin
bauta, gwargwadon abinda ya sauwaka, saboda Allah yana cewa: KUMA WADANNAN DA
SUKA YI KOKARI GA NEMAN YARDARMU, LALLAI ZA MU SHIRYAR DA SU HANYOYINMU".
Kuma HANA RAI DAGA CIN
HARAM wani dadi ne ke biyo bayansa, da kuma samun tsira.
Kuma KALLON HARAMUN kibiya
ne daga cikin kibiyoyin Iblis, wanda ya bar kallon, saboda tsoron Allah sai
Allah ya sakanta masa da bashi imanin da zai rika jin zakinsa a cikin
zuciyarsa, Mujahid –Allah yay i masa rahama- ya ce: "Runtse gani daga ababen
da Allah ya haramta, yana gadar wa mutum son Allah".
BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Bayi ba za su taba samun ni'ima ba, kuma basu da farin ciki,
da walwala a Duniya, face ta hanyar sanin Allah da sonSa. Natsuwa kuma ana
samunta da ambatonSa. Farin ciki da walwala kuma a cikin da'a a gare shi, da
rigaggeniya cikin neman yardarSa.
A Lahira kuma basu da ni'ima sai sun makwabce shi a gidan
ni'ima, da kallon fiskarSa. Kuma wadannan sune Aljannoni guda biyu, wadanda
babu mai shiga ta biyun, face ya fara shiga ta farkon.
Kuma duk wanda bai ji zakin aiki ba a cikin zuciyarSa, to ya
tuhumi kansa da aikinsa, domin Ubangiji Mai yawan godiya ne.
Kuma abin mamakin ba yana
ga mutumin da bai samu dadin biyayya ba ne, Abin mamakin yana ga mutumin da ya
kai ga samun dadin biyayya, sa'annan sai ya bar ibadar, Ta yaya zai iya hakurin
barinta?
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Wanda ya aikata
aiki na kwarai, daga namiji ko mace, alhali yana mumini, to, hakika, za mu
rayar da shi rayuwa mai dadi, kuma hakika za mu sakanta masa ladansa da mafi kyawun
abinda suka kasance suke aikatawa", [Nahl: 97].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …
HUDUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA
LILLAHIL HAMD,
Yabo ya tabbata ga Allah kan
kyautatawarSa, kuma godiaya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; ina mai
girmama sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi dadin
salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai
ninninkuwa
Ya ku Musulmai…
A lokacin idi farin cikin Musulunci yana kara sabunta
a gare su, kuma ni'imomin Allah da baiwawwakinsa suna kara bayyana akansu,
Sai ku bayyanar da farin
ciki, kuma ku rika shigar da walwala da jin dadi ga wasunku, kuma ku kara
yalwata wa iyalanku cikin abinda aka halatta muku,
Kuma ku sanya farin cikinku
ga idi ta abuci, takawar Allah da tsoronSa,
Kuma ku gode wa Allah akan
abinda ya muku na baiwa,
Kuma ki nisanci sabonSa
bayan ficewan watan biyayya ga Allah
Kuma ku rika rokon Allah karbar
aiki, da yin dace cikin abinda ke zuwa muku, domin Ramadhana wata ne na alheri wanda
wasu lokutan alherin suna biyo bayansa,
Kuma Allah yana son bayinSa
su rika dawwamar da aiki, koda kadan ne,
Kuma duk wanda ya cika
azumin watan, sannan ya bi shi da azumi guda shida a watan Shawwal, to kamar ya
yi azumin kwanakin shekarar ne gaba dayansu.
Kuma idan idi ya dace da
ranar Juma'a kamar wannan yinin, to ya halatta ga wanda ya halarci sallar idi yay
i sallar juma'a, ko kuma ya yi sallar azahar, Saidai abinda yake da fifiko
shine yay i sallar juma'ar tare da sauran Musulmai.
>>>
Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da
sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana
yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani
akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu
tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment