2018/06/21

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) JUMA'A, 8 Sawwal 1439H LIMAMI SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/Sawwal/1439H
daidai da 22/Yuni/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
RIBATAR LOKACI
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RIBATAR LOKACI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah muna gode maSa, muna neman taimakonSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da munanan ayyukanmu, Wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne, manzonSa.
Allah ya turo shi da gaskiya, yana mai gargadi da bushara, gabanin zuwan Alkiyama.
Wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa to hakika shiryatu, wanda kuma ya saba masa, to lallai bai cutar da Allah da komai ba; bai cutar da kowa ba, sai kansa.

Bayan haka:
Lallai mafi alherin zance shine littafin Allah, kuma lallai mafi alherin shiriya ita ce shiriyar annabi Muhammadu –sallal Lahu alaihi wa sallama-, kuma mafiya sharrin lamura sune kirkirarru daga cikinsu, kuma kowace bidi'a bata ce, kowace bata kuma tana cikin Wuta.

Ya ku bayin Allah…
Ina muku wasici da ni kaina, da bin dokokin Allah Mabuwayi da daukaka, domin ita ce wasiyyar Allah ga halittar farko dana karshe, "Kuma hakika mun yi wasiyya ga wadanda aka baiwa littafi a gabaninku, da ku, cewa ku bi Allah da takawa" [Nisa'i: 131].

Ya ku taron Musulmai…
Ku yi takawar Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma zantukanku su rika tabbatar da ayyukanku, domin hakikanin rayuwar Mutum shine abinda ya aiwatar da shi cikin biyayyar Allah. Kuma mai hankali shine wanda ya yi hisabi ga kansa, kuma ya yi aiki saboda abinda ke zuwa bayan mutuwa. Gajiyayye kuma, Wanda ya biye wa son zuciyarsa, sai kuma ya kwallafa wa Allah buri.

Idan (dama ta zo maka), isarka ta busa, to ka ribace ta
Domin kowane abu yana da lokacin natsawa.

Kuma kada ka gafala, ga barin aikin kyautatawa a cikinsa
domin baka san lokacin da damarka zata yanke ba 

Ya ku bayin Allah
Lallai kun yi bankwana da watan azumi, wato lokacin falala da da'a da samun gafara, saidai bamu san wanene aka karbi ayyukansa a cikinmu ba, balle mu masa barka, wanene kuma aka mayar da nasa, balle mu masa ta'aziya, Allah ya karbi ayyukanku na da'a, kuma ya gafarta zunubanku, kuma ya ninninka muku lada, An ruwaito daga Abu-hurairah –Allah ya kara yarda a gare shi-, lallai Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya kasance yana cewa: "Salloli guda biyar, da juma'a zuwa juma'a, da Ramadana zuwa Ramadana, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne, matukar ya nisancilaifukan  kaba'irai".

Ya ku bayin Allah…
Sai ku daidaitu akan addinin Allah, ku yi aiki domin karin kusanci zuwa gare shi, saboda tabbatuwa akan da'a yana daga alamomin karbuwar aiki, kuma bawa bai kusanci Allah da komai ba, wanda yafi soyuwa a gare shi fiye da wanda ya farlanta shi akansa, kuma bawa ba zai gushe ba, yana kusantar Allah da nafilfili face Allah ya so, shi. Kuma duk wanda ya kusanci Allah da kamar taki daya, to Allah zai kusance shi da kamar zira'i, kuma wanda ya kusance shi da kamar zira'i, to Allah zai kusance shi da kamar tsawon hannu biyu. Wanda ya je wa Allah yana tafiya, to Allah zai je masa yana sauri.
Sai ku kiyaye farillai, kuma kada ku kaurace wa Alkur'ani, kuma ku rika kwadayin sallolin dare, da azumin yini, saboda an ruwaito daga Sufyan bn Abdullahi As-Sakafiy, ya ce: Na ce wa Manzon Allah, Ka gaya min wata magana a cikin Musulunci wanda ba zan tambayi wani a bayanka ba? Ya ce: "Ka ce: Na yi imani da Allah sannan ka daidaitu".

Ya ku taron Musulmai…
Lokaci kamar dukiya ne, kowanne daga cikinsu wajibi ne ayi kwadayin kiyaye shi, da tattali wajen sarrafa shi da gudanar da lamarinsa.
Kuma idan dukiya za a iya tattara ta, a taskance ta, tare da bunkasa ta, to lallai lokaci lamarinsa ba haka ya ke ba; saboda kowace lahaza da dakika idan ta tafi, to ba za ta dawo gare ka ba, har abada, koda ka kashe dukkan abinda ke bayan kasa gaba daya.
To, idan ya kasance zamani an kaddara masa wani lokaci ayyananne, kuma iyakantacce, wanda ba zai yiwu a gabato da shi ba, ko a jinkirta shi, sai kimarsa -wato lokaci- ta kasance cikin kyautata amfani da shi = to ya wajaba ga kowane Mutum ya kiyaye lokacinsa, ya yi amfani da shi ta hanyar da ta fi kyau, kuma kada ya yi sakaci akan wani abu daga cikinsa; kadan ne ko mai yawa.
Kuma domin Mutum ya kiyaye lokacin, dole ne ya san a ina yake tafiyar da lokacin? Da kuma yadda yake gudanar da shi?
Sai ku saurara!
Lallai mafi girman abinda aka tafiyar da lokaci a cikinsa, kuma mafi daukakansu shine, cikin yin biyayya ga Allah Mabuwayi da daukaka.
Kuma duk zamanin ko lokaci, wanda ka tafiyar da shi cikin wannan biyayyar to baza ka taba nadama a gare shi ba, har abada.

Ya ku bayin Allah…
Rayuwa 'yar kadan ce, zamani kuma gajere ne, kuma duk abinda ya shige ya shige, duk kuma abinda zai zo to mai zuwa ne. kuma rayuwa gaba dayanta lokacin yin biyayya ga Allah ne, kuma babu wata dama ta yin sakaci a cikinta, kuma dukkan rayuwa lokaci ne na jarabtar bayi, don haka babu damar kakkautawa ko jira. Kuma da wannan rayuwar gajeriya Mutum ka iya sayan tabbata madawwamiya a cikin Aljannoni, da wanzuwa wanda ba zai yanke ba, a cikin wani zamani.
Ta daya fiskar kuma, lallai duk wanda ya yi sakaci a rayuwarsa, to lallai zai auka cikin halaka da hasara.
Don haka, Ya dace mai hankali ya san kimar rayuwarsa, kuma ya yi dubi ga ransa cikin lamarinsa, sai ya ribaci abinda ba zai yiwu a risko shi ba, wanda kuma sau dayawa cikin tozarta shi ne, halakar bawa take.

Ya ku taron Musulmai…
Lallai lokacin hutu na bazara da kuke rayuwa cikinsa wata dama ce ta hutar da jiki, da kuma kokarin sauke wasu hakkoki da yin abinda ya kubuce, da yin guzuri domin lokacin da ake fiskanta na kusa da na nesa. Saboda ba ana bada hutu ba ne, domin a wofintar da hakkoki na wajibai, da tozarta su, da dulmuya cikin sha'awowi, da kakkara dorin doriyar aiyuka, da nauyaya kafadu da laftun ayyuka ko kakkara su a rayuwa.
Sai ku ji tsoron Allah a lamarin iyalanku da 'ya'yanku, kuma ku tarbiyantar da su akan kwadayin kiyaye lokaci, da amfani da shi cikin abubuwa masu amfani, na ilimi da aiki, ta fiskar neman halal, ko aikin da'a da bautar Ma'abucin girma, wannan kuma ita ce tarbiyyar Mazaje.

Kuma lallai tarbiyyar matasa akan tuntsurar da lokuta da damammaki, yana koyar da su ne tozarta hakkoki da wajibai, da kasa daukar amanoni da nauyin al'umma, kuma yana koyar da su dabi'ar ko-oho, da kasa fiskantar matakan rayuwa.
Shi kuma faraga da rashin aikin yi zai kai yara ga aukawa cikin hatsarin fitintinu, da soye-soyen zuciya, da karkata, da bala'oi.

Ya ku bayin Allah…
Lallai ne Allah zai muku tambaya kan lokutanku na rayuwa; da cewa, ga aikata me, kuka tafiyar da su? Saboda an ruwaito daga Abu-Barzatah Al'aslamiy –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Duga-dugan bawa a ranar Alkiyama ba za su gushe ba, face an tambaye shi kan abubuwa guda hudu; sai an tambaye shi kan rayuwarsa akan me ya salwantar da ita, da iliminsa; me ya aikata da shi, da dukiyarsa ta yaya ya same ta, kuma ga me ya ciyar da ita, da tambaya kan jikinsa a me ya tsufar da shi?".

Kuma idan Mutum ya iso wurin hisabi, sannan ya kafu tsaye akan kafofinsa babu takalmi, kuma babu tufafi, (a gaba ga Ubangijinsa) babu shamaki, yana jiran a tambaye shi, kuma yana shirin bada amsa = Sai aka tambaye shi kan rayuwarsa a me ya tafiyar da ita? Da samartakarsa a me ya salwantar da ita?
Wayyo Allah! Me yafi wannan lamari girma, kuma me yafi wannan musiba tsanani?

Wajibi ne kowanne daga cikinmu ya tambayi kansa, idan aka jefo masa wannan tambayar, me zai darsu a zuciyarsa?
Kuma wane aiki ya tanada tsawon samartakarsa, da kuma rayuwarsa? Kuma me ya shirya don ya zama amsa?

Sai ku yi tanadin amsa –Ya ku bayin Allah- ga wannan tambayar, kuma amsar ta zama daidai.

Allah ya sanya mu da ku, "daga cikin wadanda suke jin zance, sai su bi mafi kyansa, domin wadannan sune wadanda Allah ya shiryar, kuma wadannan sune ma'abuta hankali" [Zumar: 18].

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Masanin ababen da suke fake na gaibu, Mai yawan gafarar zunubai, Mai yaye bacin rai da bakin ciki, muna yin yabo a gare shi, irin yabon da ya dace da girman matsayinsa, da mulkinsa mai girma, kuma yake zama sakayya ga yawaitar ni'imominSa.
Salati da sallama su kara tabbata ga fiyayyen AnnabawanSa, da iyalansa da sahabbansa da majibintansa.

Ya ku bayin Allah…
Lallai mai hankali ba zai yarda ya tozarta dakikon numfashinsa ba, alhalin rayuwarsa tana raguwa, ya tozarta su wuce kara zube, ba a cikin lamarin Duniya ko lamarin lahirarsa ba.
Kuma lallai samun lokaci da faraga ni'ima ce, idan aka kyautata moransa, azaba ce kuma idan aka tozarta aiki da shi, saboda an ruwaito daga Abdullahi bn Abbas –Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ni'imomi guda biyu an rinjayi Mutane dayawa akansu; sune lafiya da samun lokaci".
Don haka, almubazzarantar da lokatai, bugun hanci ne da tawaya cikin addini, kuma rauni ne da wauta cikin hankali, wanda aka jarrabi Mutane dayawa akansa;
Sai ku ji tsoron Allah akan rayukanku da abin kiyonku, kuma ku ribaci damammaki, kuma ku yi kwadayin riko da su, domin an ruwaito daga Abdullahi bn Abbas –Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya fada wa wani Mutum alhalin yana masa wa'azi: "Ka ribaci abu biyar gabanin abubuwa biyar; samartakarka gabanin tsufanka, da lafiyarka gabanin cutarka, da wadacinka gabanin talaucinka, da faragarka gabanin shagaltuwarka, da rayuwarka gabanin mutuwarka".

Ya ku masu yin tarbiyya…
Lallai ne babu wani kunci cikin moriyar jin dadi, da shakatawa, da debe kewa, da neman sararawa, matukar babu ketare iyaka, ko aikata abin ki a cikinsa, ko tozarta hakkoki da wajibai, domin hakan yana cikin jin dadi da abubuwa na halal, kuma a cikin hakan akwai sake jaddada karfin jiki, da nashadantar da rai. Saidai kuma ba tare da an tuntsurar ko an yi almubazzarancin lokuta masu tsada ba, kuma ba tare da an tsananta cikin wasa ko an zurfafa cikin gafala ba, domin al'ummar musulunci tana da matsanancin bukatar karfi da lokutan 'ya'yanta, sai ku tsakaita, kuma ku kwatanta.

Ya ku taron Musulmai…
Lallai yana daga shiriyar Annabinku, azumtar yini shida a cikin watan Shawwal, saboda an ruwaito daga Abu-Ayyub Al'ansariy –Allah ya kara yarda a gare shi- lallai shi ya bada hadisi cewa, lallai Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Wanda ya yi azumin watan Ramadana, sa'annan ya biyar musu da guda shida a cikin watan Shawwal, to ya kasance kamar azumin shekara".
Ma'anar wannan shine: Yayin da kyakkyawa aiki ana ninnika shi da kwatankwacinsa goma, to azumtar watan Ramadana zai kasance kamar azumtar watanni guda goma ne, shi kuma azumtar kwanaki shida na Shawwal kamar azumtar watanni biyu, wannan kuma shine daidai da azumtar kwanakin shekara gaba daya.

 Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...