HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 01/Sawwal/1439H
daidai da 15/Yuni/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
BANKWANA DA WATAN AZUMI
Shehin Malami wato: Abdulbariy
bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: BANKWANA DA WATAN AZUMI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
akan abinda ya kaddara a cikin watan Ramadhana na alkhairi, kuma ya yi baiwa.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, ya yi
albisir ga muminai da samun gafara, kuma ya kwaranye bakin ciki.
Kuma ina shaidawa lallai
shugabanmu kuma annabi Muhammadu bawansa ne, manzonsa, ya kasance mai gaggawan
aikata ayyukan samun kusanci.
Allah ya yi salati a gare
shi, da iyalansa da sahabbansa, wadanda suka kai ga kololuwar daraja da
martabobi.
Bayan haka:
Ina muku wasici da kaina,
da bin dokokin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda
suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar jin tsoronSa, kuma kada ku mutu face
kuna Musulmai" [Ali-imran: 102].
Musulmi na yin bankwana
da watan Ramadhana, wanda dararensa suka kasance masu zaki, Yininsa kuma suke
kasancewa cikin taushi, numfasawarsa kuma suke da kyautayi.
Dararen ramadhana sun yi
kaura, yininsa kuma sun juya baya, saidai kyansa yana wanzuwa a cikin rayuka,
tasirinsa kuma a cikin zukata, girmansa kuma akan kasar da duga-dugan masu
azumi suka tafi akansu.
Idan muka yi tunani cikin
ma'anonin surar ALAM NASHRAH, Wanda ayoyinta suka yi Magana da Manzon Allah
–sallal Lahu alaihi wa sallama-, za mu samu cewa, suna sifanta mana mafi girmar
fa'idar da ya kamaci Musulmi ya fita da su a lokacin ficewar watan Ramadhana,
da irin salon rayuwar da ya dace Musulmi ya tafi akansa bayan ficewar watan,
Allah Ta'alah ya ce:
(ألم نشرح لك صدرك ...)
Ma'ana: "Ashe bamu buda maka zuciyarka
ba? * kuma muka tafiyar maka da nauyin laifinka * wanda ya nauyaya bayanka *
kuma muka daukaka maka ambatonka * to lallai ne tare da tsananin nan akwai wani
sauki * kuma lallai ne tsananin nan akwai wani sauki * saboda haka idan ka kare
ibada sai ka kafu kana rokon Allah * kuma zuwa ga Ubangijinka shi kadai ka nuna
kwadayi" [Sharh: 1-8].
Fadinsa "Ashe bamu buda maka zuciyarka
ba?" [1], a cikinta Allah ya yi babbar baiwa ga Annabinsa da
ni'imar da tana cikin mafi girman ni'imomi, wacce ita ce: Ni'imar buda zuciya, wanda
kuma tana daga cikin alamomin karbuwar ayyukan Ramadhana, kuma duk wanda ya
samu ni'imar buda zuciya, to lallai ya samu wani haske mai girma daga wurin
Ubangijinsa, wanda zai rika haskaka masa rayuwarsa, yana bubbude masa kafofin
cin nasara.
Wani dacen ne, yafi
matsanancin girma, fiye da Allah ya yi baiwar zuciya budaddiya ga bawansa,
bayan ma'abucin zuciyar ya dandani zakin imani a cikin watan Ramadhana? Kuma
ma'anonin alkur'ani suka haskaka zuciyarsa??
Kuma duk wanda ya ji
dadin abu da zakinsa, kuma ya dandana shi, to ba zai iya hakurin jure masa ba,
wannan kuma saboda rai ta kan dandana ababe, sai ta zabi abu ta kwallafa masa
so, don haka; idan ta dandana, sai ta so shi.
Kuma duk lokacin da
Musulmi yafi yawan tsarkake aiki (wato, ikhlasi) da yawaita ibadodin karin
kusanci ga Allah, sai zuciyar tafi yawan farin-ciki da natsuwa, kuma wannan
shine ya sanya kake samun mumini da'iman a ko-yaushe cikin halin budewar zuciya
da farin ciki, sawa'un ya kasance cikin wata ni'ima ce, ko a cikin jarabawar
rayuwa, domin halinsa ba zai taba ficewa daga dayan lamura biyu ba; ko dai
cikin godiya, ko kuma cikin hakuri, Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- yana
cewa: "Mamakin lamarin mumini, lallai lamarinsa gaba dayansa alheri ne,
kuma hakan bag a kowa yake ba, sai ga mumini, idan lamarin farin cikin ya same
shi, sai ya yi godiya ga Allah, sai hakan ya zama alkhairi a gare shi. Idan
kuma cuta ce ta same shi sai ya yi hakuri, sai hakan ya kasance alheri a gare
shi".
Kuma akwai matukar
banbanci tsakanin budaddiyar zuciya mai yalwar fadi, wanda take yin rayuwarta
cikin farin ciki, da kyakkyawan fata, da kuma zuciya rufaffiya mai kunci, wanda
rayuwarta ke jujjuyawa cikin wahala da damuwa.
(ووضعنا عنك وزرك)
"Kuma muka tafiyar maka da
nauyin laifinka" [2]. Lallai yana daga cikin alamomin karbuwar Ramadhana, da
Allah Ubangiji ke yin baiwa da ita ga bayinSa; salihai; dauke zunubansu, da
share munanansu da kura-kuransu. Kuma Mutum duk lokacin da ya zama sako-sako;
bashi da zunubai dayawa, to yafi kusantar samun sa'ida.
(الذي أنقض ظهرك)
"Wanda ya nauyaya bayanka"
[3]. Kuma lallai zunubai da ayyukan sabo, nauyinsu ga mutum yana da girma, kuma
dabaibayin da suke yi ga gabbai mai karfi ne, saboda suna gadar masa da cutuka
da rashin lafiya, domin cutukan jiki suna kasancewa ne sakamakon rashin lafiya,
su kuma cutukan zukata sakamakon zunubai.
Kuma kamar yadda jikin
mutum baya jin dadin abinci idan bashi da lafiya, to haka nan zuciya bata samun
zaki ko dadin ibadodi matukar ta cakuda da zunubai.
Kuma lallai yana cikin
mafi nauyin zunubai a wuyan Mutum, irin zunuban da Mutum ke cutar da wasu
mutane da su, kamar giba da annamimanci da karya da zalunci.
Kuma hakika Alkur'ani ya
sifanta nauyin zunubai da nauyin da yayi kusan karya bayan Mutum, sai Allah ya
ce:
(الذي أنقض ظهرك)
Ma'ana: "Wanda ya nauyaya bayanka"
[3].
(ورفعنا لك ذكرك)
"Kuma muka daukaka maka
ambatonka" [4]. Allah ya daukaka matsayin AnnabinSa –sallal Lahu
alaihi wa sallama-, kuma ya daukaka ambatonsa; har ya zama ba a ambaton Allah,
face an ambaci Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- a tare da shi. Haka
yake a cikin kiran salla, da ikamar salla, da hudubobi.
Kuma Annabi –sallal Lahu
alaihi wa sallama- a cikin zukatan al'ummarSa yana da mafi girman soyayya da
girmamawa da darajantawa, irin matsayin da waninsa in ba Allah ba, bashi da
ita.
Kuma mutanen da gabbansu
suka samu tawali'u, kuma zukatansu suka natsu da Alkur'ani, harshensu kuma ya
yi ta furta zikiri da ambaton Allah, da addu'oi da hailala da godiya ga Allah,
a cikin yinin Ramadhana da dararensa, to Allah lallai zai daukaka darajojinsu,
kuma zai basu matsayi mai girma a Duniya da Lahira. Kuma wannan shine ma'aunin
samun banbanci da fifiko a tsakanin mutane, Umar bn Alkhaddab –Allah ya kara
yarda a gare shi- yana cewa: Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Lallai Allah yana daukaka
wanda ya so, da wannan Kur'anin, kuma yana dankwafar da darajar wadanda ya so,
da wannan Kur'anin".
Kuma An ruwaito, daga
Abdullahi bn Amrin, ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Za a gaya wa ma'abucin haddar
Alkur'ani: Ka karanta, sai ka hau darajoji, kuma ka kyautata karatunsa kamar
yadda kake kyautata shi a Duniya, saboda matsayin yana nan ne, a karshen ayar
da ka karanta ta".
Allah ya yi mini albarka
NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina
neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani
zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai
rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
irin yabon masu godiya,
kuma ina shaidawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, majibincin
masu hakuri.
Kuma na shaida lallai
shugabanmu kuma annabinmu Muhammdu bawansa ne manzonsa, shugaban masu takawa.
Allah ya yi salati a gare
shi da iyalansa da sahabbansa gaba daya.
"saboda haka idan ka kare
ibada sai ka kafu kana rokon Allah" [Sharh: 7]. Haka
nan, wajibi ne bawa ya kasance mai dogewa da cigaba da yin da'a wa Allah, tabbatacce
akan shari'arSa, tsayayye akan addininSa, domin rayuwar Musulmi gaba dayanta,
lokaci ne na yin aiki da samar da kusanci zuwa ga Allah. Don haka, idan ka kare
yin ibadar salla, sai ka nuna kwadayinka ga Ubangijinka ta hanyar addu'a, kuma
ka kafu akan hakan.
Haka idan k agama lamarin
Duniyarka, to sai ka kafu cikin ibadar Ubangijinka, wannan kuma domin rayuwar
Musulmi ibada tana lazimtarta matukar rayuwar bata kare ba.
Saboda mumini bashi da
lokacin daukar hutun ibada, a'a, kawai yak an ciru ne daga wannan nau'in na
biyayya zuwa wancan.
Kuma babu lokacin da yafi
kyau fiye da wanda kayi watsi da shagalin Duniya a cikinsa da kuma damuwowinta
ka yi wurgi da su a can bayan-bayanka, domin kebanta da Ubangijinka, kana mai
yin bauta a gare shi. "saboda haka idan ka kare ibada sai ka kafu kana
rokon Allah * kuma zuwa ga Ubangijinka shi kadai ka nuna kwadayi"
[Sharh: 7-8].
Wadannan ayoyin, kira ne
da babbar murya, kuma fadakarwa ne, kan: Yin aiki cikin kwazo, tare da amfana
da lokaci, gabanin yin nadama.
Kuma abin koyin Musulmi
wajen gaggawar aikata nau'ukan da'a, da kuma dawwama akansu, shine Annabin
rahama –صلى الله
عليه وسلم-, saboda ya kasance yana yin sallolin
dare, har kafofinsa suyi ta kumbura.
Kuma lallai yana cikin
rashin rabo, mutum ya koma bayan kwasar ganimar da aka yi a cikin watan azumi,
ya koma yana mai hasara. Ko ya tozarta ribar da Allah ya yi masa taufikin
tarawa a cikin watan alkhairori, Allah Ta'alah yana cewa: "Sai ka yi tasbihi kana gode
wa Ubangijinka, kuma ka kasance cikin masu sujada * Kuma ka yi ta bauta ga
Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka" [98-99].
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka
yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu.
No comments:
Post a Comment