FARIN CIKIN IDI
(فرحة العيد)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Lallai yana daga misalan RAHAMAR
ALLAH MADAUKAKI cikin shari'arSa da tausasawarSa ga bayinSa; yadda Allah ya shar'anta musu, bayan lokatan
biyayya na musamman, ya shar'anta musu wasu kwanaki domin watayawa da farin
ciki da kuma yalwatawa; saboda an ruwaito daga Anas –رضي الله عنه- ya ce:
"قدم رسول الله صلى الله عليه وسلم
المدينة، ولهم يومان يلعبون فيهما فقال: ما هذان اليومان؟ قالوا: كنا نلعب فيهما
في الجاهلية، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إنّ الله قد أبدلكم بهما خيرًا
منهما، يوم الأضحى ويوم الفطر"، أخرجه أبو داود والنسائي وصححه
الألباني.
Ma'ana: "Manzon allah –sallal Lahu
alaihi wa sallama- ya iso garin Madina, alhalin mutanen garin suna da wasu
kwanaki biyu, wadanda suke yin wasa a cikinsu, sai ya ce: Menene wadannan yinin
biyu? Sai suka ce: Mun kasance a zamanin Jahiliyya muna yin wasa a cikinsu, Sai
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Lallai
Allah ya muku canjin kwanaki biyu wadanda suka fi su alkhairi; wato ranar idin
layya, da idin azumi", Abu-dawud da Nasa'iy suka ruwaito shi,
kuma Albaniy ya inganta shi.
Don haka, Yana daga cikin muhimman AYYUKAN RANAR IDI DA LADUBANSA; Kokarin
shigar da farin ciki da annashuwa ga rai, da iyalai, da makusanta, da sauran
Musulmai; A'isha –Allah ya kara yarda a gare ta- alhalin tana sifanta wani yini
daga cikin kwanakin idi, a lokacin rayuwar Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa
sallama-:
"وكان يوم عيد يلعب السودان
بالدرق والحراب، فإما سألت النبي صلى الله عليه وسلم، وإما قال: تشتهين تنظرين؟
فقلت: نعم فأقامني وراءه خدي على خده وهو يقول: دونكم يا بني أرفدة" متفق عليه.
Ma'ana: "Kuma ranar idi bakaken mutane
sun kasance suna yin wasa da silken fata, da kayan harbi, ko dai na tambayi
Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-, ko kuma ya ce: Kina sha'awar ki ga ni
ne? sai na ce: E, to sai ya tsayar da ni ta bayansa; har kumatuna yana taba
kumatunsa, alhalin yana cewa: KU CIGABA DA WANNAN WASAN YA KU HABASHAWA!",
Bukhariy da Muslim.
Kuma Sahabbai sun kasance idan suka hadu a lokacin idi, sashen ya kan ce
ga sashe:
تقبل
الله منا ومنك
Ma'ana: Allah ya karba mana (ayyuka), kai ma ya karba maka.
Kuma an shar'anta yin kabbarori, tun bayan faduwar ranar daren idi, har
zuwa lokacin da za a yi sallar idi,
"ولتكملوا العدة ولتكبروا الله على ما هداكم ولعلكم تشكرون"
[البقرة:
185].
"Kuma domin ku cika kidaya, kuma
domin ku yi kabbarori ga Allah, akan abinda ya yi na shiryar da ku, kuma
la'alla za ku yi godiya", [Bakara: 185].
Sifar kabbarorin kuma shine
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
LA ILAHA ILLAL LAHU
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
WA LILLAHIL HAMDU
No comments:
Post a Comment