HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 15/SHAWWAL/1439H
Daidai da 29 /YUNIYO / 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN
ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TSARKAKE RAYUKA DA
KOKARIN GYARA SU
تزكية النفوس وإصلاحها
Shehin Malami wato:
Abdulmuhsin bn Muhammadu bn Abdurrahman Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya
yi hudubar juma'a mai taken: TSARKAKE RAYUKA DA KOKARIN GYARA SU, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da
kuma a bayyane (a lokacin ganawa).
Ya ku musulmai …
GYARUWAN HALITTU DA TSAYUWAR
LAMURANSU, YANA
CIKIN BAIWA HALITTU HAKKOKINSU, kuma wannan shine adalcin da Sammai da Kassai
suka tsayu da shi, kuma
akansa Duniya da Lahira suka tsayu.
Kuma kowace Rai, tana da
wani hakki akan sahibinta, wanda za a tambaye ta akansa, a ranar sakamako,
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kuma lallai Ranka
tana da hakki akanka",
Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma mafi girma daga cikin
hakkokin Rai, shine tsarkake ta.
Kuma da haka ake kiyaye ta
daga lalacewa da hallaka, saboda Rayuka an dabi'antar da su akan halaye ababen
zargi, wannan ya sanya suke yawaita umurni da mummuna, kamar yadda Allah
Ta'alah ya ce: "Lallai ne Rai, hakika mai yawan umurni ne da mummunan aiki ne", [Yusuf: 53].
Kuma tana da sharri, wanda
ake neman tsarin Allah daga gare shi, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ina neman tsarinka daga sharrin raina", Ahmad ya ruwaito
shi.
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana fada a farkon hudubarsa, cewa:
"Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu", Tirmiziy ya ruwaito
shi.
Don haka, babu makawa dole
sai an nemi gyaruwansu.
Kuma Allah yana son hakan
ga bayinSa, Allah Ta'alah ya ce: "Allah baya nufin ya sanya wani kunci
akanku, saidai yana nufin ya tsarkake ku –zahirinku da badininku-", [Ma'ida: 6].
Kuma SABODA GIRMAN
LAMARIN TSARKAKE RAYUKA, SAI HAKAN YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN MAFUFOFIN TURO
MANZANNI,
Saboda ga annabi Ibrahim da
Isma'ila –عليهما السلام- a lokacin da suka
kasance suna rokon Allah, akan ya turo wani Manzo daga cikinsu domin ya
tsarkake su, a inda suke cewa: "Kuma Ya Ubangijinmu! Ka aiko da wani manzo
a cikinsu, yana karanta musu ayoyinka, kuma yana karanta musu littafi da
hikima, kuma yana tsarkake su", [Bakara: 129].
Kuma annabi Musa, Allah ya
tura shi zuwa ga Fir'auna sai ya ce masa: "Ka tafi zuwa ga
Fir'auna lallai shi ya yi dagawa * sai ka ce: shin ko za ka so ka tsarkaka?", [Nazi'at: 17-18].
Kuma Allah ya turo
Annabinmu Muhammadu –صلى
الله عليه وسلم- domin ya tsarkake bayi, Allah Ta'alah ya ce: "Shine wanda ya aiko
a cikin ummiyawa (marasa rubutu da karatu) wani Manzo daga cikinsu, yana
karanta musu ayoyinSa, kuma yana tsarkake su, kuma yana koyar da su littafi da
hikima",
[Jumu'ah: 2].
Kuma da hakan Allah ya yi
babbar falala ga bayinSa muminai, a inda ya ce: "Kuma hakika, Allah ya yi babbar baiwa ga
muminai, yayin da a cikinsu ya aika Manzo daga ainihinsu, yana karanta ayoyinSa
a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su littafi da hikima", [Ali-imrana: 164].
Mai yin da'awa zuwa ga
Allah ba zai kawar da fiskarsa ga wani mutum ba, koda kuwa bashi da wani
matsayi, saboda kwadayin tsarkakarsu da shiriyarsu, Allah ya ce: "Ya daure fiska kuma
ya juya baya * saboda makaho ya je masa * to me ya sanar da kai, la'alla
watakila shine zai tsarkaka", [Abasa: 1-3].
Kuma samun rabo gaba
dayansa, lallai yana cikin tsarkake Rai,
Tabewa kuma da yin hasara suna
cikin kishiyan haka, kuma akan wannan ne Allah Ta'alah ya yi rantsuwa da mafi
tsawon rantsuwa a cikin littafinSa, sa'annan ya ce: "Lallai ne wanda ya
tsarkake Rai ya samu babban rabo * Wanda kuma ya turbude ta da laifi, ya tabe", [Laili: 9-10].
Katadah da waninsa suka ce:
"Lallai ya samu babban rabo, wanda ya tsarkake Ransa da 'da'a ga
Allah, da kuma ayyuka nagari".
Kuma wannan shine manzanci
gaba daya suka hadu akansa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne wanda ya
tsarkaka (da imani) ya samu babban rabo * kuma ya ambaci sunan UbangijinSa,
sa'annan ya yi sallah * kuma lallai kuna zabin rayuwa ta kusa (Duniya) * alhali
Lahira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa *
lallai wannan yana cikin littafan farko * wato, littafan Ibrahima da
Musa"
[A'alah: 14-19].
Kuma yana daga sifofin
Muminai, tsarkake rayukansu, Allah Ta'alah ya ce: "Sune wadanda, ga
tsarkaka masu aikatawa ne", [Muminuna: 4].
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "shine zakkar tsarkake
rayuka, da kuma zakkar dukiya, kuma Mumini kamili, shine wanda yake aiki da
wannan, kuma yake aiki da wancan".
Kuma duk wanda Ransa ta
tsarkaka, to hakika Allah ya masa babban baiwa, kuma ya karrama shi, Allah Ta'alah
ya ce: "Ba domin falalar Allah akanku ba, da rahamarSa, babu wani Mutum daga
cikinku da zai tsarkaka har abada" [Nur: 21].
Kuma Aljannah a Lahira,
sakamako ne na Wanda ya gyara kansa, Allah Ta'alah ya ce: "kuma amma wanda ya
ji tsoron tsayuwa a gaba ga UbangijinSa, kuma ya kange kansa daga son rai * to
lallai Aljannah ita ce makoma", [Nazi'at: 40-41].
Kuma darajoji madaukaka a
cikin Aljannah shine sakamakon wanda ya tsarkake ransa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya je
masa yana mai imani, alhali ya aikata aikin kwarai, to lallai wadannan suna da
darajoji madaukaka * a gidajen Aljannar zama, koguna suna gudana daga
karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, kuma wannan shine sakamakon wanda ya
tsarkaku",
[Daha: 75-76].
Kuma yin aiki
domin tabbatar da wannan baiwar wajibi ne, akan dukkan bayi, wannan kuma ta
hanyar aiki da umurnin Allah, da nisantar haninsa, domin babbar manufa cikin
umurni da hani –bayan tabbatar da bauta ga Allah- shine tsarkake rayuka da
gyaran su.
Kuma lallai yana daga manyan
manufofi, a cikin shari'a: Kiyaye rayuka, kuma kaiwa makura wajen kiyaye
su, shine aiki domin tsarkake su.
Kuma mafi girman ababen da
rayuka suke tsarkaka da su, shine TAUHIDIN ALLAH, ta hanyar yin bauta a
gare shi; shi kadai, bashi da abokin tarayya, kuma lallai babu wani tsarkaka ga
rayuka, sai ta hanyar tauhidi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma bone ya
tabbata ga masu yin shirka * wadanda basu zowa tsarkaka, kuma su a game da
Lahira su kafirai ne",
[Fussilat: 6-7].
Shekhul-Islam IbnuTaimiyyah
–رحمه الله- ya ce: "shine tauhidi da
imani, wanda rai ke tsarkaka da su, saboda yana kunsar kore bauta ga wanda ba
Allah ba, daga cikin zuciya, da tabbatar da cancantar bauta ga Allah daga cikin
zuciya, wanda shine hakikanin LA ILAHA ILLAL LAHU, kuma wannan shine ginshiki
na ababen da suke tsarkake Rai".
Kuma SALLAH tsarki ne ga Rai, kuma tsarkaka ga Bawa,
Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne sallah tana hana alfasha da munkari", [Ankabut: 45].
Kuma tana gyara
ma'abutanta; sai ta tafiyar musu da kura-kurai, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku bani labari, da za
a samu wani kogi a kofar dayanku, sai yake yin wanka a cikinsa kullum sau
biyar, shin wani abu na dattinsa zai wanzu? Sai suka ce, a'a! babu wani abu na
dattinsa da zai saura, sai ya ce: to wannan shine misalin salloli guda biyar;
Allah yana share kura-kurai da su", Bukhariy da Muslim.
Kuma da ZAKKAH rayuka
suke tatuwa kuma suke tsarkaka, Allah Ta'alah ya ce: "Ka karbi sadaka
daga dukiyarsu, kana mai tsarkake su, kuma kana mai tabbatar da kirkinsu da ita", [Tauba: 103].
Kuma tsira daga fadawa Wuta
shine sakamakon wanda ya tsarkake Ransa, Allah S.W.T ya ce: "Kuma da sannu za a
nisantar da mafi takawa daga fadawa cikinta * wanda yake bayar da dukiyarsa,
yana neman tsarkaka",
[Laili: 17-18].
Kuma AZUMI kariya ne
daga cutukan rayuka da sharrace-sharracensu, kuma fidiya ga ma'abutansa
daga ayyukan alfasha, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka
yi imani an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga wadanda suke
gabaninku, la'alla zaku samu takawa", [Bakara: 183].
Kuma a lokacin HAJJI
rayuka suna tsarkaka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya yi
niyyar hajji a cikinsu, to babu kwarkwasa, kuma babu fasikci, kuma babu jayayya
a cikin hajji",
[Bakara: 197].
Kuma wanda ya samu karbuwa daga cikin Mahajjata zai koma yana
tsarkakakken Rai, kamar ranar da Mahaifiyarsa ta haife shi, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "wanda ya yi hajji
domin Allah, bai yi kwarkwasa ba, kuma bai yi fasikci ba, zai koma kamar ranar
da Mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim.
Kuma ADDU'A ibada ce mai girma, kuma da ita ce, bawa ke
samun abin nemansa, kuma Allah S.W.T
a hannunSa gyaruwan zukata suke da tsarkinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai Allah ne ke
tsarkake wanda ya ga dama", [Nisa'i: 49].
Kuma daga cikin addu'oin
Annabi –صلى الله عليه وسلم- fadinsa "Ya Allah! Ka baiwa
raina takawarta, ka tsarkake ta, domin kai ne mafi alherin wanda zai tsarkake
ta",
Muslim.
Kuma yawaita AMBATON ALLAH cikinsa akwai yalwatar
zuciya, da tsarkin Rai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai da ambaton
Allah zukata suke natsuwa", [Ra'ad: 28].
Kuma duk wanda ya shagaltu
da ALKUR'ANI yana tilawarsa, yana tadabburin ma'anoninsa, yana aiki da
shi, yana koyansa yana koyar da shi, sai Ransa ta gyaru, kuma ta mika wuya zuwa
ga Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ya ku Mutane! Hakika wa'azi ya zo muku daga
Ubangijinku, da warakar abinda ke cikin kiraza, da shiriya da rahama ga Muminai", [Yunus: 57].
Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: "Alkur'ani shine
magani cikakke, daga dukkan cutukan zuciya da jiki, da cutukan Duniya da Lahira".
Kuma ILIMI mai amfani
yana tsarkake ma'abutansa, kuma shi ilimin shine ke nuna musu hanyar samun
tsarkakan Rai, Allah Ta'alah ya ce: "Shin, wanda yake mai tawali'u sa'oin
dare, yana mai sujada, kuma yana mai tsayuwa ga sallah, yana tsoron Lahira,
kuma yana fatan rahamar UbangijinSa, (wannan yana zama daidai da waninsa?), Ka
ce: shin wadanda suka sani suna daidaita da wadanda ba su sani ba? Kawai
wadanda suke tunani sune masu hankali!", [Zumar: 9].
Kuma ilimi ba zai gushe
yana tare da ma'abucinsa ba, har sai ya kai kololuwar tsarkaka, sai ya kasance
daga ma'abuta ibadar tsoron Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai Malamai ne ke
tsoron Allah, daga cikin bayinSa", [Fadir: 28].
Kuma KARANTA TARIHIN Maluma
da gwaraza yana zaburar da Rayuka, su yi koyi da su, da kokarin shiga
tawagarsu, kuma duk wanda ya yi nazari cikin tarihin magabatanmu, sai sakacinsa
ya bayyana a gare shi.
Kuma da gyaruwar zuciya ne,
da tsarkakarta gyaruwan zahirin bawa da badininsa suke, kuma duk wanda ya yi
gwagwarmaya da Ransa, to sai ya rabauta da samun makasudinsa.
Kuma dawwamar da KIYAYAR
ALLAH, yana mayar da ma'abutansa kamilai, sai su riski matakan bayi masu
kyautata ibada.
Kuma tsarkakar Rai, yana
rataya ne akan yin hisabi a gare ta, saboda Rai bata tsarkakuwa kuma bata
gyaruwa sai idan ana mata hisabi, kuma da aikata hakan bawa zai iya tsinkayar
aibobin Ransa, sai kuma ya yi aiki tukuru wajen gyara su.
Kuma RUNTSE IDANU yana daga
abinda Rai ke tsarkaka da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce wa Mumianai
su rika runtse sashen ganinsu, kuma su kiyaye farjojinsu, Wannan shine mafi
tsarki a gare su",
[Nur: 30].
Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ya ku taron samari!
Wanda ya samu iko daga cikinku ya yi aure, domin aure yafi runtse idanu, kuma
yafi katange farji, Wanda kuma bai samu ba, sai ya yi azumi, domin shi a
wurinsa kamar fidiya ne", Bukhariy da Muslimsuka ruwaito shi.
Kuma katange Rai daga yawaita kalle-kalle da yawar magana
yana daga sabbuban tsarkinta, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: "kuma mafi yawan sabo, lallai suna haifuwa
ne daga yawar magana da yawaita kalle-kalle, kuma sune kofofin da suka fi fadi
daga cikin kofofin da Shedan ke shigowa, saboda wadannan gabban ba su cika
kosawa ba".
Kuma "Aboki yana kan
addinin abokinsa ne, sai dayanku ya yi dubi, cewa da wa yake abota", kuma lallai samun
abota ta gari taimako ne mafi alheri kan isa ga lamura madaukaka, saboda idan
ya gafala, sai abokansa su tuna masa, idan kuma ya tuna sai su taimake shi.
Kuma cikin ZIYARTAR MAKABARTA,
da TUNA MUTUWA, rayuwar zukata da daidaituwarsu suke.
Ita kuma TUBA tana
tsarkake bawa, kuma tana wanke shi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku tuba zuwa
ga Allah, ya ku Muminai, tsammanin ku samu babban rabo", [Nur: 31].
"Kuma lallai bawa idan ya aikata laifi, sai a diga masa wani
digo baki a jikin zuciyarsa, idan kuma ya bar laifin, ya nemi gafara, ya tuba,
sai a kankare masa shi", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Shekhul Islam
Ibnu-taimiyyah –رحمه
الله-
ya ce: "Rai da ayyuka, ba su tsarkaka, sai an gusar musu da abinda ke
warware alheri daga jikinsu, kuma Mutum ba zai kasance mai tsarkaka ba, face ya
bar sharri, don haka, TAZKIYYAH, duk da cewa asalinsa shine bunkasa, da albarka,
da karuwar alkhairi, to lallai tana kasancewa ne, idan aka gusar da sharri,
wannan ya sanya mai tsarkaka dole ya hada wannan, da kuma wannan".
BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Asalin da ke bayanin yadda ake samun tsarkakar RAI shine
littafin Allah, da sunnar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, ta hanyar yin biyayya ga Allah, da bin shiriyar Annabi –صلى الله عليه وسلم-.
Kuma wannan shine hanyar
Allah, da addininSa, da kuma turbarSa mikakkiya.
Kuma da haka ake samun
tsarkin Rayuka da gyaruwansu, da rabautar halittu da daukakansu.
A UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR
RAJIM:
"Kuma wanda ya nemi
tsarkaka, to lallai yana tsarkaka ne domin kansa", [Fadir: 18].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. …
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa, kuma godiya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; ina mai
girmama sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi dadin
salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai
ninninkuwa
Ya ku Musulmai…
Canzuwar halayen bayi; ta fiskar gyaruwansu da baci, da
wadaci da tsanani, da aminci da tsoro, yana ratayuwa ne da canjuwan abinda ke
cikin Rayukansu, Allah Ta'alah ya ce :
"Lallai Allah baya canza abinda yake ga Mutane, sai sun canja abinda
yake ga zukatansu",
[Ra'ad: 11].
Kuma duk abinda ke samun bayi tushensa daga kayukansu ne,
Allah Ta'alah ya ce: "Shin, a lokacin da wata masifa ta same ku, alhali kuwa
kun samar da biyunta, sai ku ke cewa: Daga ina wannan ya ke? ka ce: daga wurin
kayukanku ne",
[Ali-imrana: 165].
Kuma duk wanda ya gyara zuciyarsa sai Allah ya gyara masa
zahirinsa.
Kuma duk wanda ya gyara tsakaninsa da tsakanin Allah, sai
Allah ya gyara masa tsakaninsa da tsakanin Mutane.
Kuma duk wanda ya yi aiki domin Lahirarsa, sai Allah ya isar
masa a lamarin Duniyarsa.
Mumini mai yawan tsoro ne a zuci, saboda yana hada
tsakanin kyautata aiki da tsoro, sai yake kokarin gyara kansa da tsarkake Ransa,
amma kuma baya neman a yabe shi da aikata hakan, Allah Ta'alah ya ce: "saboda haka, kada
ku tsarkake kanku, shine mafi sani ga wanda ya yi takawa ", [Najm: 32].
>>>
Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da
sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana
yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani
akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu
tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.