HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/SAFAR/1441H
daidai da 4/OCTOBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULMUHSIN BN MUHAMMADU ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YARDAR
ALLAH TA'ALAH
(رضا الله)
Shehin
Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu Alkasim
–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YARDAR ALLAH, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a Musulunci da
igiya mai karfi.
Ya ku Musulmai …
Sunayen Allah sune mafiya kyau, SifofinSa kuma madaukaka ne. Kuma Allah a cikin dukkan hakan yana da sifa
madaukakiya. Kuma imani da su rukuni ne na Tauhidi. Kuma da haka aiki yake zama
ingantacce.
Kuma YANA DAGA SIFOFIN ALLAH WANDA ALKUR'ANI DA SUNNA SUKA AMBATA; SIFAR
YARDA (الرضا); Domin Allah Ta'alah yana
yin fushi kuma yana yarda, ba kuma kamar na wani daga cikin halittu ba. Kuma
akan tabbatar da wannan sifar, Sahabbai da Tabi'ai suka shude, da kuma sauran
jagororin Musulmai.
Kuma domin neman yardar Allah ne, AnnabawanSa da WaliyyanSa da Bayin
Allah; Salihai suka zage damtse (suke ta fadi-tashi), Allah Ta'alah ya ce: "Kuma daga cikin
Mutane akwai wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah, Kuma Allah
Mai tausayi ne ga Bayi" [Bakara: 207].
Kuma annabi Isma'ilu –عليه السلام- Allah ya yabe shi a
cikin littafinSa da cewa, ya samu rabauta da yardarSa, a inda ya ce: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi;
lallai shi ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi *
Kuma ya kasance yana umurtar Iyalansa da salla da zaka, kuma ya kasance
yardajje a wurin UbangijinSa" [Maryam: 54-55].
Kuma annabi Musa –عليه السلام- UbangijinSa ya masa alkawarin
ganawa a gefen dutsen Dur, sai ya yi gaggawa zuwa gare shi, domin kwadayin
samun yardarsa, Allah ya ce: "Kuma menene
ya gaggautar da kai ga barin Mutanenka, Ya Musa? * Ya ce: Sune wadannan ga su a
bayana (za su iso), kuma na yi gaggawa zuwa gare ka ne, domin ka yarda" [Daha: 83-84].
Kuma annabi Sulaiman –عليه السلام- ya roki UbangijinSa, ya masa
ilhamar aikata abinda zai yardar da shi, a inda ya ce: "Ya Ubangina! Ka cusa mini inj gode wa ni'imarka wanda ka ni'imta ta a gare
ni, da kuma ga iyayena biyu, kuma in aikata aiki na kwarai wanda kake yarda da
shi" [Naml: 19].
Kuma annabi Zakariyya –عليه الصلام- ya kira UbangijinSa, da ya
azurta shi da yaro wanda ya yarda da shi, a inda ya ce: "Kuma ka sanya shi yardajje, Ya Ubangiji"
[Maryam: 6].
Kuma Allah ya sifanta annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- da
sahabbansa, da kyautata aiki, suna masu neman yardar Allah, Allah Ta'alah ya
ce: "Muhammadu Manzon Allah ne, kuma wadannan da
suke tare da shi, masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana
ganinsu suna ruku'u suna sujjada, suna neman falala daga Allah da yardarSa" [Fat-h: 29].
Kuma domin neman yardar Allah ne, Muhajirawa suka kaura suka bar garinsu,
Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Da kuma, ga Matalauta masu hijira, wadanda aka fitar daga gidajensu da
dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda" [Hashr: 8].
Mumini yana neman tsari da yardar Allah daga fushinsa, kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya nemi hakan a cikin fadinsa: "Ya Allah lallai ni ina tsari da yardarka daga fushinka", Muslim ya ruwaito.
Kuma kyan aiki da karbuwarsa ya rataya ne akan tsarkake niyya ga Allah, ta
hanyar neman yardarSa, Allah Ta'alah ya ce: "Babu alheri cikin yawa-yawan ganawansu, sai ga wanda ya yi umurni da wata
sadaka, ko wani alheri, ko kuwa sulhu a tsakanin Mutane, Kuma wanda ya aikata
haka, yana mai neman yardar Allah, to lallai za mu bashi lada mai girma" [Nisa'i: 114].
Kuma ciyarwa karbabbiya mai albarka, itace wanda sahibinta ya nemi yardar
Allah, Allah ya ce: "Kuma sifar wadanda
suke ciyar da dukiyoyinsu domin neman yardar Allah, da tabbatuwa daga kansu,
kamar misalin lambu ne a jigawa, wanda wabilin hadiri ya samu, sai ya bayar da
amfaninsasa ninki biyu. To idan kuma wabili bai same ta ba, sai yayyafi (ya
isar mata), Kuma Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne" [Bakara: 265].
Kuma Allah ya girmama alfarmar Mahajjata da masu umrah, wadanda suke neman
yardarSa, a cikin fadinSa: "Ya ku wadanda suka yi
imani, kada ku keta alfarmar wuraren bautar Allah, da kuma wata mai alfarma, da
hadaya, da ratayar rakumar hadaya, da Masu nifin daki mai alfarma suna neman
falala daga Ubangijinsu da yarda" [Ma'ida: 2].
Musulmi yana lazimtar neman yardar Allah a halin tafiye-tafiyensa da
zamansa na gida, da farin cikinsa da bakin cikinsa, da dukkan halinsa, domin a
halin tafiya ya kan bude bulaguronsa ne da rokon Allah ya saukake masa dukkan
abinda zai yardar da shi, sai ya ce: "Ya Allah, lallai muna rokonka a cikin bulaguronmu wannan, biyayyarka da
takawa, da kuma irin aikin da zaka yarda",
Muslim ya ruwaito.
Kuma idan musiba ta sauko masa, to babu abinda ya ke kasancewa ga Musulmi,
sai abinda zai yardar da Allah, Ibrahim; Dan Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu, sai Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai ido yana yin hawaye, zuciya kuma tana yin bakin ciki, saidai ba za
mu fadi komai ba, face abinda Ubangijinmu zai yarda, Kuma lallai mu dangane da
rabuwa da kai –Ya Ibrahim- tabbas masu bakin ciki ne",
Bukhariy ya ruwaito.
Yana daga RAHAMAR ALLAH DA KARRAMAWARSA Yadda ya shar'anta wa BayinSa
addinin da yarje musu shi, Allah Ta'alah ya ce: "A yau, na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imata akanku, kuma na
yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku"
[Ma'ida: 3].
Kuma cikin aiki da addinin Musulunci ake samun abinda yake hukunta yardar
Allah; domin imani da Allah shine sababin sa'idar Duniya da Lahira, kuma yana
gadar wa Bawa samun yardar MajibincinSa, Allah ta'alah ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukn kwarai, wadannan
sune mafifita alherin halittu * sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shine gidajen
Aljannar zama, koramu suna gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta
har abada. Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi. Wannan sakamako ne ga
wanda ya ji tsoron UbangijinSa" [Bayyinah: 7-8].
Kuma duk wanda ya yi imani kuma ya aikata kakkawan aiki, to lallai ya bi
hanyar godiya, da samun yarda, Allah Ta'alah ya ce: "Idan kuka butulce to lallai Allah wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda
da kafirci ga bayinSa, kuma idan kun gode zai yarda da godiyar a gare ku" [Zumar: 7].
Kuma Tauhidi shine kadaita Allah da bauta, Kuma Allah ya yarje wa Bayinsa
da su rika bauta masa; ba tare da sun hada shi da komai ba, kuma su yi riko da
igiyar Allah gaba dayansu; kada su rarraba, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah ya yarje
muku abu uku, kuma yana kiye muku abu uku; yana yarje muku ku bauta masa kada
ku hada shi da komai, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada ku
rarraba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma inanin Bawa baya daidaita, sai da son muminai da kin kafirai, kuma duk
wanda ya yi haka, sai Allah ya saka masa, kuma ya yarda da shi, Allah Ta'alah
ya ce: "Kuma ba za ka samu Mutanen da suka yi imani da
Allah da ranar karshe, suna soyayya da wanda ya saba wa Allah da manzonSa ba,
koda sun kasance Iyayensu ne, ko 'ya'yansu, ko yan'uwansu, ko danginsu,
Wadannan Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma ya karfafa su da wani
ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su gidajen Aljannar da koramu suke
gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su, kuma
suma sun yarda da shi" [Mujadala: 22].
Kuma duk wanda ya taimaki addinin Allah, Allah sai ya karfafe shi, kuma ya
yarda da shi, Allah Ta'alah: "Lallai ne
hakika, Allah ya yarda da Muminan nan, a lokacin da suke maka mubaya'a a
karkashin bishiya, domin ya san abinda ke zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a
kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci"
[Fat-h: 18].
Kuma gaskiya shine tushen imani, kuma shine yake nuna samuwarsa, kuma da
shi Bawa yake amfana a Duniyarsa da lahirarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Wannan shine yinin da gaskiyar masu gaskiya take amfanarsu, suna da gidajen
Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har
abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi, Wannan ne rabo mai girma" [Ma'ida: 119].
Kuma cikin zikirin Allah akwai gyaruwar zukata, da samun yardar Masanin
abinda yake fake, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherin ayyukanku, kuma wanda Mamallakinku
yafi yarda da shi, kuma wanda yafi daga muku darajarku, kuma yafi alheri a gare
ku fiye da bayar da zinari da azurfa, da kuma jihadi; wato ku hadu da makiyanku,
ku sare wuyansu suma su sare wuyanku? Sai suka ce: Menene haka Ya Ma'aikin
Allah? Sai ya ce: Ambaton Allah", Ibnu-Majah ya ruwaito.
Godiya ita ce dabaibayi ga
ni'imomi, kuma da ita ni'imomin suke karuwa suke dawwama. Kuma yana daga cikin
manyan sakayyar godiya: yardar Allah ga Ma'abutansa, cikin hadisin Mutane uku
daga Banu-Isra'ila; wato kuturu da mai kora da makaho, ya ce: "Sai Mala'ika ya zo wurin Makaho, ya ce: Ni mutum ne, miskini, matafiyin da
dabara ta kare masa a tafiyarsa; don haka bani da guzuri yau, sai a wurin
Allah, sannan a wurinka; Ina rokonka da wanda ya dawo maka da ganinka (Allah)
ka bani akuya daya, da zany i guzuri da ita a cikin bulagurona, sai ya ce:
Hakika na kasane makaho, sai Allah ya dawo mini da ganina, kuma matalauci, sai
ya wadatar da ni; don haka; ka dauki abinda kake so, ina rantsuwa da Allah, ba zan
musa maka akan wani abin da ka dauke shi don Allah ba a yau. Sai ya ce: Rike
dukiyarka, domin jarrabar ku aka yi; kuma lallai hakika Allah ya yarda da kai,
kuma yay i fushi ga abokanka biyu", Bukhariy da Muslim.
Yana daga falalar Allah, yadda Allahn yake ciyar da BawanSa ya
shayar da shi, Kuma idan Bawa ya yi godiya ga Ubangiji akan haka, Allah sai ya
yarda da shi, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Allah yana yarda ga
Bawa; ya ci abin ci, sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha, sai ya
gode masa akansa",
Muslim ya ruwaito.
Kuma Duniya a kewaye take da bala'i da
gurbatattun lamura, Wanda ya yi hakuri akan bala'ointa sai ya rabauta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai girman
sakamako ya kan zama gwargwadon girman bala'i, kuma lallai Allah Ta'alah idan
ya so Mutane sai ya jarrabe su; wanda ya yarda yana da yarda, wanda kuma ya yi fushi
to yana da fushi",
Tirmiziy ya ruwaito shi.
Harshe mabudin alheri ne da sharri; kuma da kalma mai dadi Mutum
zai riski yardar MahaliccinSa, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Bawa ya kan
fadi kalma cikin yardar Allah Ta'alah, bai dauke ta da girma ba, sai Allah ya
daga darajojinsa da ita", Bukhariy ya ruwaito.
Mutanen da suka fi cancantar kyautata musu da biyayya sune
iyaye biyu, kuma a cikin yardarsu ake samun yardar Allah, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Yardar Ubangiji
tana cikin yardar mahaifi, kuma fushin Ubangiji yana cikin mahaifi", Tirmiziy ya ruwaito.
Kamar yadda Allah yake son tsarkin zuciya, to lallai yana son
tsarki na zahiri, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Aswaki tsarki ne ga
baki, kuma abin yarda ne ga Ubangiji", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma idan kiyama ta tsayu, dukiya ko 'ya'ya ba za su wani amfani
ba, sai ga wanda ya je wa Allah da zuciya lafiyayya, kuma babu mai yin ceto,
face da izinin Allah, da yardarSa ga wanda zai yi ceton, Allah Ta'alah ya ce: "A wannan ranar,
ceto baya yin amfani, face wanda Allah ya masa izini, kuma ya yarda da zancensa", [Daha: 109].
Kuma baya amfani, face ga wadanda Allah ya yarda da su, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma basu yin ceto, face ga wanda ya yarda", [Anbiya'i: 28].
Kuma a cikin Aljanna ana yin ni'ima ga muminai da abinda idanu
basu gani ba, kunne bai ji ba, kuma bait aba darsuwa ga zuciyar wani mutum ba,
Kuma yana cikin madaukakan ni'imomi da suka fi girma, yardar Ubangijinsu a gare
su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yay i wa'adi ga muminai maza da
muminai mata, da gidajen Aljannah, wadanda koramu suke gudana a karkashinsu,
suna masu dawwama a cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar
zama, Kuma yarda daga Allah ita ce mafi girma, Wannan shine babban rabo" [Tauba: 72].
Annabi –عليه الصلاة والسلام- y ace: "Lallai Allah zai ce
wa ma'abuta Aljannah: Ya Ma'abuta Aljanna! Sai su ce: Mun amsa maka –Ya Ubangijinmu-,
kuma dukkan alheri suna hannayenka, Sai ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Me
yasa ba za mu yarda ba, Ya Ubangiji, alhalin ka bamu abinda baka bayar da wani
daga cikin halittunka ba? Sai ya ce: Shin ba zan baku abinda yafi muku hakan ba?
Sai su ce: Ya Ubangiji: Wane abu ne yafi hakan falala? Sai ya ce: Zan saukar
muku da yardata akanku; ba zan yi fushi da ku a bayansa ba har abada" [Bukhariy da Muslim].
BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI
Samun rabo gaba dayansa,
yana cikin riko da addini, kuma duk wanda ya lazimci abinda yake yardar da
Allah, Allah sai ya yarda da shi kuma ya yardar da shi. Kuma idan Bawa ya nemi yardar
UbangijinSa kuma ya fifita shi akan dukkan abinda ba shi ba, to lallai Allah
zai yarda da shi, kuma ya sa Mutane su yarda da shi.
Kuma wanda ya nemi yardar Mutane
da fusata Allah, sai Allah yay i fushi da shi, kuma ya sanya Mutane su yi fushi
da shi.
A UZU BILLAHI MINAS
SHAIDANIR RAJIM
"Shin wanda ya
bibiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya komo da fushin Allah! Kuma makomarsa
jahannama ce, kuma tir da ita a matsayin makoma" [Ali-imrana: 162].
Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai
girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa
mai hikima,
,,,
,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;
Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai
girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi dadin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnunkuwa.
Ya ku Musulmai…
Wanda Allah ya yarda da
shi, to sai ya karrama shi da mafifiyar ni'ima, a cikin Aljannah, Allah Ta'alah
ya ce: "Wasu fiskoki a
wannan ranar masu annuri ne * zuwa ga Ubangijinsu masu kallo ne" [Kiyama: 22-23].
Alhasan –رحمه الله– ya ce: "Sun kalli Ubangijinsu, sai suka haskaka da haskensa".
Kuma dubi zuwa ga fiskar Allah mai karamci, shine karin da Allah ya yi
alkawari ga BayinSa; masu kyautatawa, Allah ya ce: "Wadanda suka kyautata suna da Aljanna da kari"
[Yunus: 26].
Annabi –عليه الصلاة
والسلام- ya ce: "Idan Ma'abuta Aljannan suka shiga Aljannah, Sai Allah Tabaraka wa Ta'alah ya
ce: Kuna son wani abu na kara muku? Sai su ce: Ashe baka haskaka fiskarmu ba?
Ashe baka shigar da mu Aljannah, kuma ka tsamar da mu daga wuta ba? Sai ya yaye
shamaki. Ba a baiwa 'yan Aljanna wani abu da yafi soyuwa a gare su fiye da
kallon fiskar Ubangijinsu ba", Muslim ya ruwaito shi.
Sannan ku sani
Lallai Allah ya umurce ku
da yin salati da sallama ga AnnabinSa…
No comments:
Post a Comment