HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/SAFAR/1441H
daidai da 11/OCTOBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
AMFANAR
DA MUTANE YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI
(نفع البرايا من خير السجايا)
Shehin
Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu Alkasim
–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AMFANAR DA MUTANE, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Ya ku Musulmai …
Amfanar da Mutane yana cikin mafi alherin sifofi,
MAFIL ALHERIN RANAKUN MUTUM SHINE YININ DA YA AMFANAR
KUMA AIKATA ALKHAIRI SHINE MAFI WANZUWAR ABINDA YA AIKATA
Kuma Mutum mai yawan amfanarwa mai yawaita taimako shine: Wanda ya
amfanar da Mutane da dukiyarsa, da kuma matsayinsa, da iliminsa, da dabi'unsa,
da kyautatawarsa, kuma wanda alherinsa yake da gwabi, kyautarsa dayawa, mai
amfani cikin aikinsa, mai faffadar tukunya, tafin hannunsa kamar girgije ne,
yana dawwama akan sada zumunci da kyauta da sadakoki, kuma yana tallafawa
gajiyayye, yana falala ga mai nemanta, kuma yana kokarin tsamar da mai neman
agajinsa mai neman taimakonsa, kuma yana ilmantar da jahili mai neman shiryawa,
kuma yana jin-kan maraya, kuma yana kokarin share hawayen mai bakin ciki, kuma
yana hulda da Mutane, cikin so da kauna, da kyautatawa, da tausasawa.
MUTANE SUNA CACIRINDO A KOFAR GIDANSA
AI DADDADAR MASHAYA, YANA DA YAWAN CUNKOSO
TSUNTSU YANA SAUKA A WURIN DA KWAYA TAKE A WATSE
KUMA ANA MAMAYE GIDAJEN MASU KARAMCI DA KYAUTA
Annabin Allah Isah –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Kuma ya sanya ni
mai albarka a duk inda na kasance" [Maryam: 31].
Malaman tafsiri suka ce, wato
Allah ya sanya ni na zama mai yawan amfanarwa, a duk inda na fiskanta, mai
biyan bukatu, mai karantar da alkhairi, mai umurni da kyakkyawa, mai hani ga
mummuna, mai albarka da nau'oin albarkoki.
Kuma Mutumin da yafi
amfanar da halittu gaba daya shine Annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- "Yana masa nauyi abinda yake wahalar da ku,
mai kwadayi ne akanku, kuma ga muminai Mai yawan tausasawa ne Mai jin kai"
[Maryam: 128].
BAN TABA GANI, KO NA JI LABARIN WANI A CIKIN MUTANE
GABA DAYA, KAMAR ANNABI MUHAMMADU BA
Kuma duk wanda ya kafa kansa domin amfanar da Mutane sai ya rayu a
gaba-gaba ana girmama shi, kuma fiska abar mutuntawa,
YABONSA DA DADI A BAKUNAN MUTANE
KUMA YABONSA YANA KASANCEWA A KOWANE WURI
Matsayinsa zai rika daukaka, kuma ambaton zai yi dadi
DA ZAKA RIKA BAYARWA A LOKACIN DA AKE ROKONKA
SAI RANKA TA ZAMA MAI BAYARWA, KUMA KOWANE MASOYI YA KAUNACE KA
Ana cewa, Cikar hankali, da kyakkyawar ambato basu cika haduwa ba.
Wani kuma ya ce: Hana kyauta, munana zato ne ga abin bauta.
DUKIYAR DA TA GADAR WA MA'ABUTARTA SAMUN YABO BATA TOZARTA BA
SAI DAI DUKIYAR MAROWACI ITACE TAKE TOZARTA
Daga cikin Mutane akwai wanda babu abin tatsa ga hantsarsa, kuma ba a
kwadayin samun amfanarwarsa,
MUTUM, MATUKAR ZAMANSA DA DAI, BAI YI FA'IDA BA
TO GIRGIJE NE WANDA RANA TA TARE, BAI ZUBO DA RUWA BA, KUMA BAI YI TAFIYA
BA
Wasu daga cikin Mutane, namijin dabino ne; basu da abin tsinka, kuma bashi
da inuwa, saidai wanda zai yi kansa
Sai ka kasance, ga halittun Allah mai yawan amfanarwa, mai amsa wa
mabukata, kuma ka mikar da hannunka domin bada alkhairi, ka mika tafinka.
An ruwaito daga Abu-hurairata –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherinku daga mafi
sharrinku ba? Sai Wani Mutum ya ce: E, ka bamu labari Ya Ma'aikin Allah, sai ya
ce: Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa, ake aminta daga sharrinsa,
kuma mafi sharrinku shine wanda ba a fatan samun alherinsa, kuma ba a amintuwa
daga sharrinsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi dan Umar –رضي الله عنهما- daga Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Mafi soyuwan Mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar da Mutane. Kuma
mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da daukaka shine farin ciki wanda ka
shigar da shi zuciyar Musulmi, ko ya yaye masa bakin ciki, ko ya biya masa
bashi, ko ka kawar masa da wata yunwa, kuma wallahi na yi tafiya tare da
dan'uwana Musulmi cikin bukatarsa, yafi soyuwa a wurina fiye da na yi i'itikafi
a wannan masallacin, wato Masallacin Madina- na tsawon wata guda", Dabaraniy ya ruwaito shi a mu'ujamul Ausad ya ruwaito shi
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairata -رضي الله عنه- lallai shi ya
ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya kwaranye wa Musulmi wani bakin ciki daga bakin cikin Duniya, Allah
zai kwaranye masa bakin ciki daga bakin cikin ranar kiyama. Kuma idan Mutum ya
saukaka wa wanda yake cikin wahala, to Allah zai saukaka masa a Duniya da
Lahira. Kuma idan Mutum ya rufa asirin Musulmi a Duniya, Allah zai rufa
asirinsa a Duniya da Lahira, Allah yana taimakon bawa matukar Bawan yana
taimakon dan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Nawai ya ce: "A cikin wannan
hadisin, akwai falalar biya wa Musulmai bukatu, da amfanar da su da abinda ya
saukaka, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko shawari a cikin wata maslaha, ko
nasiha, da makamancin haka".
BIYA BUKATA GWARGWADON IKO,
KUMA KA ZAMA MAI YAYEWA DAN'UWANKA BAKIN CIKI
LALLAI MAFI ALHERIN KWANAKIN MUTUM
SHINE YININ DA YA BIYA WA WASU BUKATU
Ya kai Bawan Allah!!!
Ka bayar da kyauta, kuma ka amsa wa Mutumin da yake cikin yanayi, kuma kada
ka raina abin hannunka da zaka yi kyauta da shi, kuma kada ka ga karacin
hidimar da zaka gabatar da ita, domin kananan ayyukan sharri, wanda ya aikata
su zai same su a halarce dalla-dalla, kuma koda gwargwadon zarra ne na
alkhairi, wanda ya aikata su zai same su a cike, a ajiye,
An ruwaito daga Abu Jaryin Alhujaimiy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon
Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Kada ka raina kyakkyawan abu; ka ki aikata shi, koda ka bada kyautar kulla
igiya ne, kuma koda ka diba daga gugarka zuwa ga kwaryar wanda ya nemi shayarwa
ne, kuma koda ka hadu da dan'uwanka Musulmi alhalin fiskarka tana shumfude
(murmushi) a gare shi, kuma koda ka debe kewa ga wanda yake cikinta ne da kanka,
ko kuma ka bayar da kyautar igiyar takalmi",
Ahmad da Abu-dawud da nasa'iy suka ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Jabir dan Abdullahi –رضي الله عنه- ya ce: Wata
kunama ta harbi wani daga cikinmu, alhalin muna zaune tare da Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai wani Mutum ya ce: Ya Ma'aikin Allah, shin ba zan masa
addu'ar rukiyya ba? Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Duk wanda ya samu damar ya amfanar da dan'uwansa to ya aikata", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, kada ka hana gararka, kuma kada ka rike falalarka, kada ka
killace alkhairinka, kuma kada ka yi rowa, kuma kada ka nuna kosawa, kada ka
nuna takura ga mai rokon da talauci ya bukatar da shi zuwa ga roko, ka bashi
koda kadan ne, ko ka mayar da shi da kyakkyawiyar magana, kuma kada ka yi
kokarin hada masa zafin talauci da kaskancin dake cikin roko da kausasa harshe
da jafa'i.
Kuma alkawarin tallafin mai karamci cika wa ne (ba ajalan ba), Shi kuma
alkawarin marowaci jinkiri ne, da lalubo uzuri. Kuma bada uzuri da laffuza masu
kyau shi yafi alkhairi fiye da jinkirtarwa mai tsawo. Kuma idan ka yi nufin
bada ni'ima to ka kyautata, idan kuma bukatar ba za ta samu ba, to ka fito da
bayani a fili.
An ruwaito daga Abdullahi dan Amru –رضي الله عنهما- ya ce: Manzon
Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Lallai Allah a wurin wasu Mutane, yana da ni'imomin da ya tabbatar da su a
wurinsu –ma'ana: ya dawwamar musu da su- matukar dai suna cikin bukatun
Musulmai; basu kosa daga gare su ba. To amma idan suka kosa daga biya musu
bukatu, sai Allah ya dauke ni'imomin zuwa ga wasunsu"Dabaraniy,
a cikin mu'ujamul kabir ya ruwaito shi.
KA KYAUTATA MATUKAR AKWAI DAMA DA IKO
DOMIN DAMAR, BA DOLE TA DAWWAMA GA MUTUM BA
Ina fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi
gafararsa, lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi Mai yawan
gafara.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Ya ku Musulmai…
Mustahabbi ne, yin ceto (shafa'a)
a cikin al'amuran alheri (wato sanya baki domin biya ma wani bukata), saboda
yin hakan, wani amfani ne da Mutumin da ya aikata hakan zai amfanar da wanda ya
nemi ceton dominsa.
Kuma idan Mutum ya yi ceto
mai kyau, wanda yake fatan ya amfanar da halittu, da kuma biyan bukatun Mutane,
to hakika ya yi kyauta mai gwabi, kuma zai samu yabon Mutane.
An ruwaito daga Abu-Musal
Ash'ariy –رضي
الله عنه- ya ce: Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ya kasance, idan wani mai bukata ya zo masa, sai ya fiskanci
abokan zamansa, sai ya ce: "Ku yi ceto; sai a baku
lada, Allah kuma zai hukunta abinda ya so ta harshen ManzonSa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
KA TAIMAKE SHI KODA DA MATSAYINKA NE, WANDA YA ZO MAKA DA WATA BUKATA
SABODA, KYAUTA DA MATSAYI, YAFI YIN KYAUTAR DUKIYA
Imamus Shafi'iy –رحمه الله تعالى- ya ce: "sanya baki domin yin ceto, shine a madadin
zakka a cikin mutunci".
AN FARLANTA MINI FITAR DA ZAKKAR ABINDA HANUNA YA MALLAKA
AMMA BADA ZAKKAR MATSAYINA KUMA SHINE, NA YI TAIMAKO, KUMA NA YI CETO
DON HAKA, IDA KA MALLAKI ABU, TO KA YI KYAUTA,
IDAN KUMA BAKA SAMU IKO BA, TO KA YI IYA KOKARINKA WAJEN GANIN KA AMFANAR
Kuma duk wanda ya yi ceto, domin a kai ga wata da'a, ko don samun sauki
cikin abu mai wahala, ko janyo alheri, ko domin tunkude wani sharri, ko domin
sulhu tsakanin masu husuma biyu, ko ya yi ceto domin wanda ake nema masa hakkin
ya kai zuwa ga wani hakki nasa, duk wanda ya aikata haka, yana da rabo daga alherin
ceton da ya yi da kuma ladanta.
Wanda kuma ya yi ceto, domin lalata wani hakki, ko domin tabbatar da wata
barna, ko domin tabbatar da zalunci, ko ya yi domin a gabatar da Mutumin da bai
cancanta ba, akan wanda ya cancanta, ko kuma domin a baiwa wanda bashi da
kwarewa, a kuma dakushe mai kwarewa, ko don bada aiki ga wanda aka nema masa
ceto, a kuma haramta wanda ya fishi cancanta, wanda ya aikata hakan, to lallai
yana da zunubin wannan ceto, mummuna, na zalunci da ya aikata.
Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Wanda ya yi ceto, mai kyau, zai samu rabo daga gare shi. Wanda kuma ya yi
ceto mummuna, to zai samu rabo daga cikinsa"
[Nisa'i: 85].
Kuma karbar kyauta, sakamakon amfanar Mutane da matsayinka da kuma saboda
ceto, yana tozarta ladan ceton, kuma yana tafiyar da falalarta, don haka, kada
ka yi gaggawar karbar ladan cetonka, kuma ka ajiye shi a matsayin guzurin domin
lahirarka.
Abdullahi dan Mas'ud –رضي الله عنه– ya ce: "Duk wanda ya yi ceto, domin a dawo da wani hakki, ko domin ya dauke wani
zalunci, sai aka masa kyauta, ya karba, to wannan haramun ne".
Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah Albahiliy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon
Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi wani ceto ga dan'uwansa, sai aka dauko kyauta aka bashi akanta,
to lallai hakika ya fada cikin wata kofa daga cikin kofofin riba", Ahmad da Abu-dawud sun ruwaito, saidai akwai magana akan
ingancinsa, Amma wasu Maluman sun ce hadisi ne hasan.
SAI KU YI SALATI DA SALLAMA, GA MUHAMMADU MAI SHIRYAR DA HALITTU GABA DAYA
DOMIN IDAN MUTUM YA MASA SALATI GUDA DAYA, ALLAH ZAI NINKA MASA DA WANNAN
HAR GUDA GOMA
…
No comments:
Post a Comment