Sifar Umrah da hajji
Sheikh Ibn
Usaimin –Allah ya yi masa rahama- ya ce:
Idan kuka iso mikati, sai ku yi wanka,
ku sanya turare a jikinku, kamar kai, gemu, sannan ku yi harama da umrah, da
nufin yin tamattu'i ku tafi zuwa garin Makkah kuna yin LABBAIKAL LAHUMMA
LABBAIK…. Idan Kuka isa daki mai alfarma, ku yi dawafi sau bakwai, a
matsayin dawafin umrah. Kuma ku sani, gaba dayan Masallacin wuri ne na dawafi;
kusa ne da dakin Ka'aban ko nesa, saidai kusantar ka'aban shine yafi falala;
matukar ba za ka cutu da cunkoso ba. Amma idan akwai cunkoso, to ka tafi nesa
da dakin, al'amarin yana da fadi, Wa lilLahil hamd. Idan kuka kammala dawafi,
to ku yi raka'oi biyu a bayan makamu Ibrahima –AS-, ko ta kusa da shi,
idan an samu damar hakan, idan kuma ba a samu ba, to koda nesa ne da shi, kawai
dai Makamu Ibrahima ya kasance a tsakaninku da tsakanin ka'abah. Sai ku fita
zuwa ga sa'ayin umrah a tsakanin Safah da Marwah, ku fara da dutsen Safah, idan
kuka kammala zagaye bakwai, sai ku rage gashin kanku ta dukkan kan, domin rage
shi ta gefe daya baya wadatarwa, kuma kada ku rudu da aikin Mutane dayawa
Idan ranar takwas ga watan zulhijjah
ta zo, sai ku yi wanka, ku sanya turare, ku yi harama da hajji, daga
masaukanku. Ku fita zuwa ga Minah, ku yi sallar azahar, La'asar, Magriba,
Isha'i, da asuba. Kuna masu kasaru, ba tare da kun hade salloli biyu ba;
saboda Annabinku ﷺ ya kasance yana yin kasarun salloli a Minah da Makkah,
amma baya hada su. Idan rana ta fudo a ranarArafah,
sai ku tafi, kuna yin Talbiyyah cikin kankan da-kai ga Allah, zuwa ga filin
Arafah. Sai ku hade sallolin Azahar da La'asar a Arafah
a lokacin azahar (jam'u takdim), kuma raka'oi bibbiyu ga kowacce.
Sannan ku shagaltu da
addu'a da marairaice wa Allah, kuma ku yi kwadayin kasancewa cikin tsarki (da
alwala), ku fiskanci alkibla, koda dutsen Arafah ya kasance ta bayanku; domin
abinda aka shar'anta shine fiskantar alkiblah, kuma ku kula sosai da iyakokin Arafah
da alamominta, sai ku kasance a cikinta, domin Mahajjata dayawa suna tsayawa ba
a cikinta ba, kuma duk wanda bai samu Arafah ba, to bashi da hajji, saboda
fadin Annabinmu ﷺ: "Hajji shine Arafah".
Kuma matukar ka tsaya a farfajiyar Arafah, ta gabas ne ko ta yamma, ko ta
kudunta ko ta arewa, to hakan ya yi, in banda Badanul wadiy (Wadiy
Uranah); saboda fadin Annabi ﷺ: "Na tsaya a nan, kuma Arafah dukkanta wurin
tsayuwa ne".
Idan rana ta fadi,
kuka tabbatar ta fadin, sai ku tafi zuwa ga Muzdalifah kuna masu Talbiyah
da kankan da-kai ga Allah. Kuma ku lazimci natsuwa, gwargwadon iko, kamar yadda
Annabinku ﷺ ya umurce ku da aikata hakan, saboda ya fito daga Arafah
alhalin yana jan linzamin rakumarsa baya, har kanta yana kokarin taba jikin
tudun sirdi, alhalin yana fada da hannunsa mai karamci: "Ya ku Mutane!
Abi a hankali, a tafi a natse".
Idan kuka iso
farfajiyar Muzdalifah, ku yi sallar Magriba da Isha'i, sai
ku yi barci har asubah. Kuma Annabi ﷺ bai yi rangwame ga wani ya bar Muzdalifa ba, sai ga
Mutane masu rauni; su kam ya musu rangwamen su tafi a karshen dare. Idan kuka
yi sallar asuba, sai ku fiskanci alkiblah, kuna masu
kabbara da gode masa, da yin addu'oi, har haske ya bayyana sosai, sai ku tafi
gabanin fudowar rana, zuwa minah. Sannan ku tsinci
duwatsu guda bakwai, ku tafi zuwa ga Babbar Jamrah wanda itace ta
karshe, ta bangaren Makkah, Sai ku jefe ta, bayan fudowar rana, da
duwatsu guda bakwai, kuna masu yin kabbara Allahu Akbar tare da kowane
dutse, kuna masu kankan da-kai a gare shi, kuna girmama shi. Kuma ku sani
lallai makasudin jifan shine girmama Allah, da tsayar da ambatonsa. Kuma wajibi
ne dutsen ya fada cikin kewayen, amma ba sharadi ba ne, ya bugi ginshikin.
Idan kuka gama jifan
duwatsun, sai ku yanka hadaya, kuma bata isarwa ga al'amarin hadaya; sai dabbar
da take isarwa ga layya, kuma babu laifi ka wakilta wani ya yanka maka. Sannan
bayan kun yi yanka, sai ku aske gashinku, kuma wajibi ne ku aske dukkan gashin,
kuma baya halatta ku aske sashensa ku bar sashe. Mace kuma zata rage gashinta ta
kowace kusurwa daga kanta gwargwadon kan 'yar yatsa.
Bayan haka, kun yi
abinda ake kiransa tahallulul Awwal, sai ku sanya tufafinku, ku yanke
farcenku, ku sanya turarenku, amma ba za ku sadu da matanku ba. Sa'annan sai ku
sauka gabanin sallar azahar zuwa cikin Makkah domin yin dawafin hajji,
kuma ku yi sa'ayi tsakanin Safah da Marwah. Sa'annan ku koma Minah. Kuma da
yin dawafi, da aikata sa'ayi, tare da jifan Shedan da aski, to kun samu abinda
ake kiransa: Tahallulus Saniy, kuma komai ya halatta a gare ku, har kwanciya da
Matanku.
Ya ku Mutane! Lallai Mahajjaci a ranar idi yana aikata ayyuka ne guda hudu: Jifan
jamrah, sa'annan yanka, sa'annan aski, sa'annan dawafi da sa'ayi. Wannan kuma
shine jearanta ayyukan, wanda yafi falala. Saidai idan mutum ya gabatar da wani
akan wani, sai kuka yi aski gabanin yanka ga misali, to babu komai. Kuma da za
ku jinkirta dawafi da sa'ayi, har sai kun dawo garin Makkah daga Minah, to
babu komai. Kuma da za ku jinkirta yanka zuwa ranar goma sha uku, sai ku yi shi
a garin Makkah, babu komai, musamman idan akwai bukatar hakan, da maslaha. Ku
kwana daren goma sha daya 11 a Minah. Idan Rana ta yi zawali
(lokacin azahar) sai ku yi jifa jamraat guda uku, ku fara da jamrah ta farko,
sa'annan ta biyu, sannan ta karshe; wato akabah, kowane daya da tsakuwa guda
bakwai, za ku rika yin kabbara (Allahu Akbar), tare da kowace tsakuwa.
Lokacin jifa, a ranar idi, ga mai iko (lafiyayye), daga fudowar Rana ne, Mai
rauni kuma tun daga karshen dare ne. Karshen lokacin kuma zuwa faduwar rana.
Lokacinsa kuma a sauran kwanakin (bayan idi), daga zawali ne, zuwa faduwar
Rana. Amma baya halatta a yi jifan gabanin zawali. Kuma ya halatta ayi jifan a
cikin dare, idan akwai cunkoso mai tsanani, a cikin yini. Wanda ba zai iya jifa
ba, ko saboda kasancewarsa karami, ko tsufa, ko cuta, to yana da damar ya
wakilta wanda zai masa jifan. Kuma babu laifi, wakilin ya yi jifa wa kansa, da
wanda yake wakilta a tsayuwa daya, saidai zai fara jifa ga kansa. . Idan kuka
yi jifan ranar sha biyu 12, to lallai hajji ya kare, Kuma kuna da zabi
kan dawowa Makkah, ko kuma ku sake kwana a Minah zuwa yini na 13domin
ku sake jifan, bayan Azahar ga wuraren jifan guda uku; Wannan kuma shine
yafi, saboda shine aikin Annabi ﷺ.
Idan kuka so ku bar
garin Makkah, Sai ku yi Dawafin bankwana. Saidai babu dawafin
ga Mai haila da kuma mai jinin haihuwa (nifasi), kuma ba shar'anta musu zuwa
jikin kofar Masallaci da tsayuwa a wurinsa ba .
No comments:
Post a Comment