HUƊUBAR
MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه
وسلم)
JUMA'A, 12/SAFAR/1441H
daidai da 11/OCTOBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUƊUBA
SHEIKH DR. SALAH BN
MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
AMFANAR DA HALITTU
YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI
(نفع البرايا من خير السجايا)
Shehin Malami wato: Salah ɗan
Muhammadu Albudair –Allah ya kiyaye shi-
ya yi huɗubar juma'a
mai taken: AMFANAR DA HALITTU YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI, wanda kuma a
cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUƊUBAR
FARKO
Ya
ku Musulmai …
Amfanar da
Halittu yana cikin mafi alherin sifofi,
MAFI ALHERIN RANAKUN MUTUM SHINE YININ DA
YA AMFANAR
AIKATA ALHERI KUMA SHINE MAFI WANZUWAR
ABINDA YA AIKATA
Kuma Mai yawan
amfanarwa mai taimako shine: Wanda ya amfanar da Mutane da dukiyarsa, da
matsayinsa, da iliminsa, da ɗabi'unsa, da
kyautatawarsa, Mai gwaɓin alheri, mai kyauta dayawa, mai amfani cikin
aikinsa. mai faffaɗar tukunya, tafinsa kamar girgije, yana dawwama akan
sada zumunci da kyauta da sadaƙoƙi, yana tallafawa gajiyayye, yana falala ga mai neman
falala, yana tsamar da mai neman agaji da taimako, yana ilmantar da jahilin
dake neman shiryarwa, yana jin-ƙan maraya,
yana share hawayen mai baƙin ciki, yana hulɗa
da Mutane, cikin so, da kyautatawa, da taushi
MUTANE SUNA CINCIRINDO A ƘOFAR GIDANSA
DADDAƊAR
MASHAYA, TANA DA YAWAN CUNKOSO
TSUNTSU YANA SAUKA A WURIN DA KWAYA TAKE
WATSUWA
KUMA ANA KAI-KOMO A GIDAJEN MASU KARAMCI
Annabin Allah
Isah –عليه
الصلاة والسلام- ya ce: "Kuma ya
sanya ni mai albarka a duk inda na kasance" [Maryam: 31].
Malaman
tafsiri suka ce, wato Allah ya sanya ni Na zama mai yawan amfanarwa, a duk inda
na fiskanta, mai biyan buƙatu, mai karantar da alkhairi, mai umurni da
kyakkyawa, mai hani ga mummuna, mai albarka da nau'oin albarkoki.
Kuma Mutumin
da yafi dukkan halitta amfanar da halittu shine Annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- " … abinda ke wahalar da ku yana masa nauyi, Mai kwaɗayi ne akanku, kuma ga muminai Mai tausayi
ne Mai jin ƙai" [Taubah: 128].
BAN TAƁA
GANI, KO NA JI LABARIN WANI A CIKIN MUTANE
GABA DAYANSU, KAMAR ANNABI MUHAMMADU BA
Kuma duk wanda
ya kafa kansa domin amfanar da Mutane, sai ya rayu a gaba-gaba ana girmama shi,
fiskarsa abar mutuntawa,
YABONSA DA DAƊI A BAKUNAN MUTANE
KUMA YABON YA KASANCE A KOWANE WURI
Matsayinsa zai ɗaukaka, ambatonsa kuma ya yi daɗi
DA ZAKA RIƘA BAYARWA A LOKACIN DA AKE ROƘONKA
SAI RANKA TA KOYI BAYARWAR, KUMA KOWANE
MASOYI YA JI DAƊINKA
Ana cewa, Cikar
hankali, da kyakkyawan ambato basu cika haɗuwa
ga Mutum ɗaya ba.
Wani kuma ya ce: Hana kyauta, munana zato
ne ga Allah abin bauta.
BATA TOZARTA BA, DUKIYAR DA TA GADAR WA
MA'ABUTANTA SAMUN YABO
SAIDAI DUKIYAR MAROWACI ITACE, TA TOZARTA
Wasu Mutane babu
abin tatsa ga hantsarsu, kuma ba a kwaɗayin
samun amfaninsu,
MUTUM, MATUƘAR ZAMANSA BAI AMFANAR BA
TO GIRGIJE NE WANDA RANA TA TARE, BAI
ZUBO DA RUWA BA, KUMA BAI TAFI BA
Wasu Mutane
namijin dabino ne; babu abin tsinka daga gare su, kuma basu da inuwa, sai idan
kai nasu ne.
Sai ka
kasance, ga halittun Allah mai yawan amfanarwa, mai amsa wa mabuƙata, kuma ka miƙar
da tafin hannunka domin bada alheri miƙarwa.
An ruwaito daga Abu-hurairata –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya
ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherinku
daga mafi sharrinku ba? Sai Wani Mutum ya ce: E, ka bamu labarin Ya Ma'aikin
Allah, sai ya ce: Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa, ake aminta
daga sharrinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba a fatan alherinsa, kuma ba a
aminta daga sharrinsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito.
Kuma an
ruwaito daga Abdullahi ɗan Umar
–رضي الله عنهما- daga Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Mafi
soyuwan Mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar da Mutane. Kuma mafi
soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da ɗaukaka shine farin cikin da ka shigar da shi
zuciyar Musulmi, ko ya yaye masa baƙin ciki, ko ya biya masa bashi, ko ka kawar
masa da yunwa, kuma wallahi na yi tafiya tare da ɗan'uwana Musulmi cikin buƙatarsa, yafi soyuwa a wurina fiye da na yi
i'itikafi a wannan Masallacin, wato Masallacin Madina- na tsawon wata guda", Ɗabaraniy
ya ruwaito shi a mu'ujamul Ausad.
Kuma an ruwaito
daga Abu-hurairata
-رضي الله عنه- lallai shi ya ce: Manzon
Allah –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya kwaranye wa Musulmi wani baƙin cikin Duniya, Allah zai kwaranye masa baƙin cikin yinin ƙiyama. Kuma wanda ya sauƙaƙa wa Mutumin da yake cikin wahala, to Allah
zai sauƙaƙa masa a Duniya da Lahira. Kuma wanda ya
rufa asirin Musulmi a Duniya, Allah zai rufa asirinsa a Duniya da Lahira, Allah
yana taimakon Bawa matuƙar Bawan yana taimakon ɗan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Nawawiy ya ce:
"A cikin hadisin, akwai falalar biya wa Musulmai buƙatu, da amfanar da su da abinda ya sauƙaƙa, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko shawari a cikin wata maslaha, ko
nasiha, da makamancin haka".
KA BIYA BUƘATU GWARGWADON IKO,
KUMA KA KASANCE MAI YAYE BAƘIN CIKI GA ƊAN'UWANKA
DOMIN MAFI ALHERIN KWANAKIN MUTUM SHINE
YININ DA YA BIYA WA WADANSU BUƘATU
Ya kai
Bawan Allah!!!
Ka bayar da
kyauta, ka riƙa amsa wa wanda yake cikin baƙin ciki, kuma kada ka raina abin da zaka yi kyauta da
shi, kada ka ga karancin hidimar da zaka gabatar, domin ƙananan ayyukan sharri, mai aikata su zai same su a
halarce dalla-dalla. haka kwayar zarra na alheri, wanda ya aikata ta zai same
ta a cike, a ajiye.
An ruwaito
daga Abu Jaryin Alhujaimiy
–رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kada ka raina
kyakkyawan abu; ka ki aikata shi, koda ka bada kyautar kulla igiya ne, kuma
koda ka ɗiba daga
gugarka zuwa ga kwaryar wanda ya nemi shayarwa ne, kuma koda ka haɗu da ɗan'uwanka Musulmi alhalin fiskarka tana
shumfuɗe (kana
murmushi) a gare shi, kuma koda ka ɗebe kewa ga wanda ke cikinta ne da kanka, ko
kuma ka bayar da kyautar igiyar takalmi",
Ahmad da Abu-dawud da Nasa'iy suka ruwaito shi.
Kuma an
ruwaito daga Jabir ɗan Abdullahi
–رضي الله عنه- ya ce: Wata kunama ta
harbi wani daga cikinmu, alhalin muna zaune tare da Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai
wani Mutum ya ce: Ya Ma'aikin Allah, shin ba zan masa addu'ar ruƙiyya ba? Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya
ce: "Duk wanda ya samu damar ya amfanar da ɗan'uwansa to ya aikata", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, kada
ka hana kyautarka, kada ka riƙe falalarka,
kada ka killace alherinka, kada ka yi rowa, kada ka nuna ƙosawa, kada ka nuna takura ga mai roƙon da talauci ya buƙatar
da shi ga roƙo, ka bashi koda kaɗan
ne, ko ka mayar da shi da kyakkyawiyar magana, kada ka haɗa masa zafin talauci da ƙasƙancin dake cikin roƙo
da kausasa harshe da jafa'i.
Kuma alƙawarin tallafin karimi faɗa ne da cikawa.
Shi kuma Marowaci
alƙawarinsa jinkiri ne, da lalubo uzuri.
Kuma bada
uzuri da laffuza masu kyawu shi yafi alheri fiye da jinkirtarwa mai tsawo.
Idan ka yi
nufin ni'ima to ka zartar, idan kuma buƙatar
ba za ta samu ba, to ka yi bayani a fili.
An ruwaito
daga Abdullahi ɗan Amru
–رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Allah,
a wurin wasu Mutane, yana da ni'imomin da ya tabbatar da su a wurinsu –wato: ya
dawwamar musu da su- matuƙar suna cikin buƙatun Musulmai; basu ƙosa daga gare su ba. To amma idan suka ƙosa daga biya musu buƙatu, sai Allah ya ɗauke ni'imomin zuwa ga wasunsu", Ɗabaraniy,
a cikin mu'ujamul kabir ya ruwaito shi.
KA KYAUTATA MATUƘAR AKWAI DAMA DA IKO
DOMIN DAMAR, BA DOLE TA DAWWAMA GA MUTUM
BA
Ina faɗar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai
ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi
Mai yawan gafara.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUƊUBA
TA BIYU
Ya
ku Musulmai…
Mustahabbi ne,
yin ceto (ko sanya baki domin biya ma wani buƙata) a cikin al'amuran alheri, saboda amfanarwa ne ga Mutumin da aka
nemi ceton dominsa.
Kuma idan
Mutum ya yi ceto mai kyau, wanda yake fatan amfanarwa ga halittu, da biyan buƙatun Mutane, to lallai ya yi kyauta mai gwaɓi, kuma zai samu yabon Mutane.
An ruwaito
daga Abu-Musal Ash'ariy
–رضي الله عنه- ya ce: Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ya kasance, idan wani
mai buƙata ya zo
masa, sai ya fiskanci abokan zamansa, ya ce: "Ku yi ceto; zaku samu lada,
Allah kuma zai hukunta abinda ya so ta harshen ManzonSa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
KA TAIMAKE SHI, KO DA MATSAYINKA NE,
WANDA YA ZO MAKA DA WATA BUƘATA
DOMIN, KYAUTA DA MATSAYI, TAFI KYAUTAR
DUKIYA
Imamus
Shafi'iy
–رحمه الله تعالى- ya ce: "sanya baki domin yin ceto, shine zakkar mutunci".
AN FARLANTA MINI FITAR DA ZAKKAR ABINDA
HANUNA YA MALLAKA
SHI KUMA BADA ZAKKAR MATSAYINA SHINE, NA
YI TAIMAKO, KUMA NA YI CETO
DON HAKA, IDAN KA MALLAKI ABU, TO KA YI
KYAUTA,
IDAN KUMA BAKA SAMU IKO BA, TO KA YI IYA ƘOƘARINKA WAJEN
GANIN KA AMFANAR
Wanda ya yi
ceto, domin a kai ga wata ɗa'a, ko don
samun sauƙi cikin abu mai wahala, ko janyo alheri, ko domin
tunkuɗe wani sharri, ko domin sulhu tsakanin masu husuma
biyu, ko domin kaiwar wanda ake masa ceton ga haƙƙinsa, to lallai, yana da rabo daga alherin ceton, da kuma ladanta.
Wanda kuma ya
yi ceto, don a lalata wani haƙƙi, ko domin
tabbatar da ɓarna, ko domin tabbatar da zalunci, ko domin a fifita
wanda bai cancanta ba, akan wanda ya cancanta, ko domin a baiwa wanda bashi da
kwarewa, a kuma daƙushe mai kwarewar, ko don bada aiki ga wanda aka nema
masa ceto, a haramta shi ga wanda ya
fishi cancanta, to lallai yana da zunubin wannan ceto, mummuna, na zalunci.
Allah Mabuwayi
da ɗaukaka ya ce: "Wanda
ya yi ceto, ceto mai kyau, zai samu rabo daga gare shi. Wanda kuma ya yi ceto
ceto mummuna, to zai samu rabo daga cikinsa" [Nisa'i: 85].
Kuma karɓar kyauta, sakamakon amfanar da wani da matsayinka ko
saboda ceto, yana tozarta ladan ceton, kuma yana tafiyar da falalarta, don
haka, kada ka yi gaggawar ladan cetonka, kuma ka bar ladan a matsayin guzurin
Lahirarka.
Abdullahi ɗan Mas'ud
–رضي الله عنه– ya ce: "Duk wanda ya yi ceto, domin a dawo da wani haƙƙi, ko domin ya ɗauke wani zalunci, sai aka masa kyauta, ya
karɓa, to wannan
suhut ne (haramun)".
Kuma an
ruwaito daga Abu-Umamah Albahiliy
–رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi
ceto ga ɗan'uwansa,
sai aka ɗauko kyauta
aka bashi akanta, to lallai haƙiƙa ya faɗa ta wata ƙofa daga ƙofofin riba", Ahmad da Abu-dawud suka ruwaito shi, saidai
akwai magana akan ingancinsa, Amma wasu Maluman sun ce hadisi ne hasan.
SAI KU YI SALATI DA SALLAMA, GA MUHAMMADU
MAI SHIRYAR DA HALITTU GABA ƊAYA
DOMIN IDAN MUTUM YA MASA SALATI GUDA ƊAYA, ALLAH ZAI NINKA MASA DA WANNAN HAR GUDA GOMA …
No comments:
Post a Comment