HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/SAFAR/1441H
daidai da 4/OCTOBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULMUHSIN BN MUHAMMADU ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YARDAR
ALLAH TA'ALAH
(رضا الله)
Shehin
Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu Alkasim
–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YARDAR ALLAH, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a Musulunci da
igiya mai karfi.
Ya ku Musulmai …
Sunayen Allah sune mafiya kyawu, SifofinSa kuma masu girma. Kuma a cikin dukkan hakan Allah yana da sifa
madaukakiya. Kuma imani da su rukuni ne na Tauhidi. Kuma da hakan aiki yake
zama ingantacce.
Kuma YANA DAGA SIFOFIN ALLAH WADANDA SUKA ZO CIKIN ALKUR'ANI DA SUNNAH;
SIFAR YARDA (الرضا); Domin Allah Ta'alah yana fushi kuma yana yarda, kuma duka
biyun ba kamar na wani daga cikin Halittu ba ne. Kuma akan tabbatar da wannan
sifar, Sahabbai da Tabi'ai da magabatan Al'umma suka shude.
Kuma domin neman yardar Allah ne, AnnabawanSa da Waliyyai, da BayinSa;
Salihai suka zage damtse (suka yi fadi-tashi), Allah Ta'alah ya ce: "Kuma daga cikin
Mutane akwai wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah, Kuma
Allah Mai tausayi ne ga Bayi" [Bakara: 207].
Kuma annabi Isma'ilu –عليه السلام- Allah ya yabe shi a
cikin littafinSa da cewa, ya yi babban rabo da samun yardarSa, ya ce: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi;
lallai shi ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi *
Kuma ya kasance yana umurtar Iyalansa da salla da zaka, kuma ya kasance yardajje
a wurin UbangijinSa" [Maryam: 54-55].
Kuma annabi Musa –عليه السلام- UbangijinSa ya masa alkawarin
ganawa a gefen dutsen Dur, sai ya yi gaggawa zuwa gare shi, domin kwadayin
samun yardarSa, Allah ya ce: "Kuma menene
ya gaggautar da kai ga barin Mutanenka, Ya Musa? * Ya ce: Sune wadancan ga su a
bayana (za su iso), kuma na yi gaggawa zuwa gare ka ne, domin ka yarda" [Daha: 83-84].
Kuma annabi Sulaiman –عليه السلام- ya roki UbangijinSa, da cewar ya
cusa masa aikata abinda zai yardar da shi, ya ce: "Ya Ubangina! Ka cusa mini in gode wa ni'imarka wanda ka ni'imta ta a gare
ni, da kuma ga iyayena biyu, kuma in aikata aiki na kwarai wanda ka yarda da
shi" [Naml: 19].
Kuma annabi Zakariyya –عليه الصلام- ya kirayi UbangijinSa, da ya
azurta shi da yaro wanda ya yarda da shi, a inda ya ce: "Kuma ka sanya shi yardajje, Ya Ubangiji"
[Maryam: 6].
Kuma Allah ya sifanta annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- da
sahabbansa, da kyautata aiki, suna masu neman yardar Allah, Allah Ta'alah ya
ce: "Muhammadu Manzon Allah ne, kuma wadannan da
suke tare da shi, masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana
ganinsu suna ruku'u da sujjada, suna neman falala daga Allah da yardarSa" [Fat-h: 29].
Kuma domin neman yardar Allah ne, Muhajirawa suka kaura suka bar garinsu,
Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Da kuma, ga Matalauta masu hijira, wadanda aka fitar daga gidajensu da
dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah, da kuma yarda" [Hashr: 8].
Kuma Mumini yana tawassuli da yardar Allah domin ya tsare shi daga fushinSa,
kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- yake neman
tsari da hakan a cikin fadinsa: "Ya Allah lallai
ni ina neman tsari da yardarka, daga fushinka",
Muslim ya ruwaito.
Kuma kyan aiki da karbuwarsa suna rataya akan tsarkake niyya ga Allah, ta
hanyar neman yardarSa, Allah Ta'alah ya ce: "Babu alheri cikin yawancin ganawarsu, sai ga wanda ya yi umurni da wata
sadaka, ko wani alheri, ko kuwa sulhu a tsakanin Mutane, Kuma idan Mutum ya
aikata hakan, yana neman yardar Allah, to lallai za mu bashi lada mai girma" [Nisa'i: 114].
Kuma ciyarwa karbabbiya mai albarka, itace wanda sahibinta ya nemi yardar
Allah da ita, Allah ya ce: "Kuma sifar wadanda
suke ciyar da dukiyoyinsu domin neman yardar Allah, da tabbatarwa daga kansu,
kamar misalin lambu ne a wuri mai jigawa, wanda mamakon ruwa ya samu, sai lambun
ya bayar da amfaninsa ninki biyu. To idan ba ruwa mai yawa ne ya same shi ba,
sai yayyafi (ya isar masa), Kuma Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne" [Bakara: 265].
Kuma Allah ya girmama alfarmar Mahajjata da masu umrah, wadanda suke neman
yardarSa, a inda yake fadi: "Ya ku wadanda
suka yi imani, kada ku keta alfarmar wuraren yin bauta wa Allah, da kuma watanni
masu alfarma, da hadaya, da ratayar rakumar hadaya, da Masu nufin daki mai
alfarma suna neman falala daga Ubangijinsu da yarda"
[Ma'ida: 2].
Musulmi yana lazimtar neman yardar Allah a halin tafiye-tafiyensa da
zamansa a gida, da halin farin cikin da bakin ciki, da dukkan halinsa gaba daya,
domin a halin bulaguro ya kan bude tafiyarsa da rokon Allah, cewa ya saukake
masa dukkan abinda zai yardar da shi, sai ya ce: "Ya Allah, lallai muna rokonka a cikin bulaguronmu wannan, ayyukan biyayya
da takawa, da kuma aikin da zaka yarda",
Muslim ya ruwaito.
Kuma idan musiba ta sauko wa Musulmi, babu abinda zai kasance masa face
abinda zai yardar da Allah, Ibrahim; 'Dan Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu, sai Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai ido yana yin hawaye, zuciya kuma tana yin bakin ciki, saidai ba za
mu fadi wani abu ba, face abinda Ubangiji zai yarda da shi, Kuma lallai mu
dangane da rabuwa da kai –Ya Ibrahim- tabbas masu bakin ciki ne", Bukhariy ya ruwaito.
Yana daga RAHAMAR ALLAH DA KARRAMAWARSA Yadda ya shar'anta wa BayinSa
addinin da yarje musu shi, Allah Ta'alah ya ce: "A yau, na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imata akanku, kuma
na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku"
[Ma'ida: 3].
Kuma cikin aiki da addinin Musulunci abubuwan da suke hukunta yardar Allah
suke; domin imani da Allah shine sababin jin dadin Duniya da Lahira, kuma yana
gadar wa Bawa samun yardar MajibincinSa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi imani, kuma suka yi ayyukan kwarai, wadannan sune
mafifita alherin halittu * sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shine gidajen
Aljannar zama, koramu suna gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta
har abada. Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi. Wannan sakamako ne ga
wanda ya ji tsoron UbangijinSa" [Bayyinah: 7-8].
Kuma duk wanda ya yi imani kuma ya aikata kyakkyawan aiki, to lallai ya bi
hanyar samun yardar Ubangiji, Allah Ta'alah ya ce: "Idan kuka kafirce to lallai Allah wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda
da kafirci ga bayinSa, kuma idan kuka gode yana yarda da godiyar a gare ku" [Zumar: 7].
Tauhidi shine kadaita Allah da bauta, kuma shine mafi girman aiki a wurin
Allah, Kuma Allah ya yarje wa BayinSa; cewa: Su bauta masa; kada su hada shi da
komai, kuma su yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada su rarraba, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah yana
yarje muku abu uku, kuma yana kiye muku abu uku; yana yarje muku; ku bauta masa
kada ku hada shi da komai, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada ku
rarraba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma wanda ya tabbatar da Tauhidi sai Allah ya yarda da shi, Allah Ta'alah
ya ce: "Wadannan Allah ya rubuta imani a cikin
zukatansu, kuma ya karfafa su da wani ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su
gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a
cikinsu, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi"
[Mujadala: 22].
Kuma idan Mutum ya taimaki addinin Allah, sai Allah ya karfafe shi, kuma ya
yarda da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne hakika, Allah ya yarda da Muminan nan, a lokacin da suke maka mubaya'a
a karkashin bishiya, domin ya san abinda ke zukatansu, sai ya saukar da natsuwa
a kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci" [Fat-h: 18].
Kuma gaskiya shine tushen imani, kuma shine yake nuna samuwarsa,
kuma da gaskiya Bawa yake amfana a Duniyarsa da lahirarsa, Allah Ta'alah ya ce:
"Wannan shine yinin da gaskiyar masu gaskiya
take amfanarsu, suna da gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu,
suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da
shi, Wannan ne rabo mai girma" [Ma'ida: 119].
Godiya ita ce dabaibayi ga
ni'imomi, kuma da ita ni'imomin suke karuwa suke dawwama. Kuma yana daga cikin
manyan sakayyarta: yadda Allah yake yarda ga Masu godiya, cikin hadisin Mutane
uku daga Banu-Isra'ila; wato kuturu da mai kora da makaho, ya ce: "Sai Mala'ika ya zo wurin Makaho, ya ce: Ni Mutum ne, miskini, matafiyin da
dabara ta kare masa a tafiyarsa; don haka; bani da guzuri yau, sai a wurin
Allah, sannan a wurinka; Ina rokonka da wanda ya dawo maka da ganinka (Allah)
ka bani akuya daya, da zan yi guzuri da ita a cikin bulagurona, sai ya ce:
Hakika na kasane makaho, sai Allah ya dawo mini da ganina, kuma matalauci, sai
ya wadatar da ni; don haka; ka dauki abinda kake so, ina rantsuwa da Allah, ba
zan musa maka akan dukiyar da ka dauke ta don Allah ba, a yau. Sai ya ce: Rike
dukiyarka, domin jarrabar ku aka yi; kuma lallai hakika Allah ya yarda da kai,
kuma ya yi fushi ga abokanka biyu", Bukhariy da
Muslim suka ruwaito shi.
Bawa ba zai wadatu ga barin ci
da sha ba, Kuma yana daga falalar Allah, yadda Allahn yake ciyar da BawanSa ya
shayar da shi, Kuma idan Bawan ya yi godiya ga Ubangiji akan haka, sai Allah ya
yarda da shi, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Allah yana
yarda ga Bawa; ya ci abin ci, sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha,
sai ya gode masa akansa", Muslim ya ruwaito.
Duniya a
kewaye take da bala'i da gurbatattun lamura, Kuma Idan Mutum ya yi hakuri akan
bala'ointa sai ya rabauta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai girman sakamako ya kan zama gwargwadon girman bala'i, kuma lallai
Allah Ta'alah idan ya so Mutane sai ya jarrabe su; wanda ya yarda yana da yarda,
wanda kuma ya yi fushi, yana da fushi", Tirmiziy ya
ruwaito shi.
Harshe, mabudin alheri ne da
sharri; kuma da fadin kalma mai dadi Mutum zai riski yardar MahaliccinSa,
Annabi –عليه
الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Bawa ya kan fadi kalma cikin yardar Allah Ta'alah, bai dauke ta a bakin
komai ba, sai Allah ya daga darajojinsa da ita",
Bukhariy ya ruwaito.
Kamar yadda Allah yake son
tsarkin zuciya, to lallai yana yarda da tsarki na zahiri, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Aswaki tsarki ne ga
baki, kuma abin yarda ne ga Ubangiji", Tirmiziy ya
ruwaito shi.
Kuma idan kiyama ta tsayu,
dukiya ko 'ya'ya ba za su yi amfani ba, sai ga wanda ya je wa Allah da zuciya
lafiyayya, kuma babu mai yin ceto, face bayan izinin Allah, da yardarSa ga Mai
ceton, Allah Ta'alah ya ce: "A wannan ranar,
ceto baya yin amfani, face wanda Allah ya masa izini, kuma ya yarda da zancensa", [Daha: 109].
Kuma ceton ba zai amfanar ba,
face wadanda Allah ya yarda da su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma basu yin ceton, face ga wadanda ya yarda",
[Anbiya'i: 28].
Kuma a cikin Aljanna ana yin
ni'ima ga Muminai da abinda ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, kuma
bai taba darsuwa ga zuciyar wani Mutum ba, Kuma yana cikin manyan ni'imomin da
suka fi girma, yardar Ubangijinsu a gare su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah ya yi wa'adi ga Muminai maza da muminai mata, da gidajen
Aljannah, wadanda koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a
cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar zama, Kuma yarda
daga Allah ita ce mafi girma, Wannan shine babban rabo"
[Tauba: 72].
Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah zai ce wa
ma'abuta Aljannah: Ya Ma'abuta Aljanna! Sai su ce: Mun amsa maka –Ya
Ubangijinmu-, kuma dukkan alheri suna hannayenka, Sai ya ce: Shin kun yarda? Sai
su ce: Me zai sa ba za mu yarda ba, Ya Ubangiji, alhalin ka bamu abinda baka
bayar da shi ga wani daga cikin Halittunka ba? Sai ya ce: Shin ba
zan baku abinda yafi muku hakan ba? Sai su ce: Ya Ubangiji: Wane abu ne yafi
hakan girma? Sai ya ce: Zan saukar muku da yardata akanku; ba zan yi fushi da
ku a bayansa ba har abada" [Bukhariy da Muslim suka ruwaito].
BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI
Samun rabo gaba dayansa,
yana cikin riko da addini, kuma shine yake janyo yardar Allah, kuma idan Mutum ya
lazimci abinda yake yardar da Allah, Sai Allah ya yarda da shi, kuma ya yardar
da shi. Kuma idan Bawa ya nemi yardar UbangijinSa kuma ya fifita ta akan duk
abin da ba ita ba, to lallai Allah zai yarda da shi, kuma ya sa Mutane su yarda
da shi.
Kuma wanda ya nemi yardar
Mutane da fushin Allah, sai Allah ya yi fushi da shi, kuma ya sanya Mutane su
yi fushi da shi.
A'UZU BILLAHI MINAS
SHAIDANIR RAJIM
"Shin wanda ya bibiyi
yardar Allah, zai zamo kamar wanda ya komo da fushin Allah! Kuma makomarsa Jahannama
ce, kuma tir da ita a matsayin makoma" [Ali-imrana: 162].
Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai
girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa
mai hikima, ,,,
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;
Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai
girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi dadin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnunkuwa.
Ya ku Musulmai…
Wanda Allah ya yarda da shi,
sai ya karrama shi da ni'imomi, a cikin Aljannah, Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka kyautata,
suna da Aljanna da kari" [Yunus: 26].
Karin kuma shine: Dubi zuwa ga fiskar Allah Mai
karamci, kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya fassara
ayar da hakan, kuma idan Muminai suka yi dubi ga fiskar Ubangijinsu, to hakan
yafi soyuwa a wurinsu akan komai, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Idan Ma'abuta Aljannan suka shiga Aljannah, Sai Allah Tabaraka wa Ta'alah ya
ce: Kuna son wani abu na kara muku? Sai su ce: Ashe baka haskaka fiskarmu ba?
Ashe baka shigar da mu Aljannah, kuma ka tsamar da mu daga fadawa Wuta ba? Sai
ya yaye shamaki. Ba a baiwa 'yan Aljanna wani abu da yafi soyuwa a gare su fiye
da kallon fiskar Ubangijinsu ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan Muminai suka yi dubi ga fiskar Allah Mai karamci, sai su kara
kyawu da kwar jini, Allah Ta'alah ya ce: "Wasu fiskoki a wannan ranar masu annuri ne * zuwa ga Ubangijinsu masu dubi
ne" [Kiyama: 22-23].
Alhasan –رحمه الله– ya ce: "Sun kalli Ubangijinsu, sai suka samu annuri da haskenSa".
Sannan ku sani
Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa…
No comments:
Post a Comment