SHIRYA MAMACI DA
YI MASA SALLAH DA KUMA BUNNE SHI.
Ga bayanin mas'alolin filla-filla kamar haka:
Na farko: An
so a rika lakkanawa mai mutuwa kalmar La
ila illal Lahu; saboda fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
gare Shi: "ku lakkanawa mamatanku kalmar la ilaha illalLahu".
Abinda aka
nufa da mamata a nan su ne: wadanda alamun mutuwa suka bayyana tare da su.
Na biyu: Idan
aka tabbatar da mutuwarsa sai a rufe idanunsa, a daure gemunsa, kamar yadda
sunna ta zo da shi.
Na uku: Wajibi
ne a yi wanka ga Musulmin da ya mutu, matukar ba shahidin da ya mutu a wurin
yaki ba ne, saboda shahidin yaki ba a yi
masa wanka, ba a yi masa sallah, haka ake rufe shi a cikin kayansa, saboda
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi bai wanke wadanda suka yi
shahada a yakin uhudu ba, haka bai yi musu sallah ba.
Na hudu: Sifar
wankar gawa:
Za a suturce
wa mamaci al'aurarsa, sannan a daga shi kadan, sai a tatse cikinsa a hankali,
sai wanda zai yi masa wankan ya daura kyalle ko makamancisa a hannunsa, sai ya
masa tsarki da shi, daga nan sai ya masa al'walar sallah, sannan ya wanke masa
kansa da gemunsa da ruwa da kuma magarya, ko makamancinta, sannan sai ya wanke
bangaren damarsa, sannan sai bangaren hagu. Zai masa hakan har sau uku, a
kowanne wanka zai bi da hannunsa ta cikinsa yana dan dannawa kadan-kadan, idan
wani abu ya fito ya wanke shi. Sai kuma ya toshe duburarsa da auduga ko
makamacinta, idan abin bai dena fitowa ba, sai ya toshe da tabon kasa, ko kuma
ayi amfani da hanyoyin likitanci na zamani kamar sanya gam, ko plaster ko makamancinsa.
Sannan ya sake
masa alwala. Idan aka masa wanka sau uku, sai bai fita ba, to sai a kara adadin
zuwa biyar ko bakwai. Sa'annan a tsane shi da tawul. Sannan a shafa masa turare
a hamatarsa da matsematsinsa da makamantansu, da kuma guraben sujaddarsa. Da za
a shafe gaba dayan jikin mamacin da turare to hakan shi ne yafi. Kuma an so a
kunna turaren wuta a gaba dayan likafaninsa. Idan gashin bakinsa ko faratansa
sun yi tsawo dayawa sai a rage su, idan kuma aka bar su haka shima babu laifi.
Ba zai taje masa kai ba, ko ya aske masa mara ko ya yi masa kaciya ba, domin
babu dalilin da ya yi nuni akan hakan. Mace kuma za a yi mata kitso ne (yawo)
guda uku daga goshinta su yi bayanta.
Na biyar:
Sanya wa mamaci Likkafani:
Abinda aka fi
so shi ne: a yi likkafani wa mamaci namiji acikin tufafi guda uku farare, ba
tare da anyi masa Riga ko Rawani ba; kamar yadda aka yi wa Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a
saka shi a cikinsu shigarwa. Idan kuma aka masa likkafani da Riga da Izari da Mayafi; to babu laifi.
Mace kuma ana
sanyata a cikin Likkafani biyar: Riga,
da Zani, da dan kwali, sai kuma Mayafai biyu.
Yaro, ana masa
likkafani cikin tufafi daya zuwa uku. Karamar yarinya kuma, cikin riga daya
mayafai biyu.
Likkafani daya
wadatacce wanda zai rufe jiki gaba daya; shi ne wajibi ga mace ko namiji.
Amma idan
mamacin ya dauki harama da umrah ko hajji sai ya rasu; to za a yi masa wanka ne
da ruwa da magarya, sannan a lullube shi a cikin ihramansa ko wasunsu, baza a
rufe kansa ko fuskarsa ba, ba za a sanya masa turare ba; domin za a tashe shi
ranar alkiyama yana yin Talbiyya (wato yana cewa: labbaikallLahumma labbaik),
kamar yadda haidisi ingantacce ya zo daga Annabi Muhammadu tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi.
Amma idan
maniyyaciya ce, -wato- mace ce, to za a shirya ta ne kamar ba maniyyaciya ba,
sai dai itama ba za a sanya mata turare ba, baza a rufe fuskarta da nikabi ba,
ba za a sanya mata safar hannu ba, za a rufe fuskarta da hannayenta da
likkafaninta ne kadai, kamar yadda bayanin ya gabata, a sifar yadda ake sanya
wa Mace likkafani.
Na shida:
Wanda ya fi kowa cancantar wanke mamaci namiji, da kuma yi masa sallah da rufe
shi, shi ne wanda mamacin ya yi wasici da shi, sannan sai mahaifi, sai kaka,
haka za a yi ta duba wanda ya fi kusa da shi a cikin magadansa.
Wadda kuwa
tafi cancantar wanke Mace ita ce wadda ta yi wasici da ita, sa'annan sai
mahaifiyarta, sai kakarta, sannan wadda ta fi kusanci da ita a cikin mata.
Kowanne daya
daga cikin ma'aurata zai iya wanke dan'uwansa, (wato miji ya wanke matarsa, ko
ita ta wanke shi); domin sayyidina Abubakar Assidik matarsa (Asma'u bnt Umais)
ce ta wanke shi. Shi kuma sayidina Aliyu shine ya wanke matarsa –wato, Fatima,
Allah ya kara yarda a gare ta.
Na bakwai:
Sifar sallar gawa: za a yi kabbara hudu ne, a kabbara ta farko ana karanta
Fatiha, idan aka kara da gajeriyar sura ko aya daya ko biyu ya yi kyau, saboda
ingantaccen hadisin da ya zo daga Abdullahi dan Abbas a kan hakan. A kabbara ta
biyu kuma sai a yi salati ga Annabi Muhammadu kamar yadda ake yi a Tahiya
(salatin ibrahimiyya). Sai ayi kabbara ta uku, a ita ne ake yin addu'a kamar
haka:
"Ya Allah Ka gafarta wa wadanda suke raye aciknmu da matattunmu, da
wadanda suke nan da wadanda basu nan, da manyanmu da kanananmu, Mazanmu da
Matanmu. Ya Allah wanda ka rayar da shi a cikinmu to Ka rayar da shi akan
tafarkin musulumci, wanda kuwa Ka karbi rayuwarsa to Ka karbe ta akan Imani. Ya
Allah Ka gafarta masa Ka ji kansa, Ka ba shi lafiya Ka yi masa rangwame, Ka
kyautata masaukinsa, Ka yalwata mashigarsa, Ka wanke shi da Ruwa da kankara da
kuma Raba, Ka tsarka ke shi daga kurakurensa kamar yadda ake tsaftace farin
tufafi daga kazanta, Ka canza masa gida mafi alheri daga gidansa, da iyali
mafiya alheri daga nasa, Ka shigar da shi Aljannah, ka tsare shi daga azabar
kabari da azabar wuta, ka yalwata masa kabarinsa Ka haskaka masa shi, ya Allah
kada Ka haramta mana ladansa, kada kuma Ka batar da mu a bayansa.
Sannan sai ya
yi kabbara ta hudu, ya yi sallama daya bayanta a hannun dama. Kuma anso a daga
hannaye a kowacce kabbara.
Idan kuma
gawar mace ce sai a yi anfani da lamirin mata, a ce: ya Allah Ka gafarta mata
….har zuwa karshe), idan kuma Mutum sama da daya ne sai a ce: (Ya Allah Ka gafarta
musu….. har zuwa karshe).
Idan gawar
yaro ce, sai a ce: (Ya Allah ka sanya shi ya zama marigayi kuma taska ga
iyayensa, kuma mai ceto abin amsawa. Ya Allah! Ka nauyaya ma'auninsu da shi, Ka
girmama ladansu da shi, Ka riskar da shi ga mummunai magabata nagari, Ka sanya
shi karkashin rainon Annabi Ibrahim tsira da aminci su tabbata a gare shi, Ka
kare shi daga azabar jahimu da rahamarka.
Sunnah -a yayin sallah- ita
ce: limamin ya tsaya daura da kan mamaci Namiji, Mace kuma a tsakiyarta, idan
kuma mamatan sun hada da Maza da Mata, to namiji zai zamto yana bin liman ne
–wato daga liman sai gawar Namiji-, ita kuma Mace tana bin alkibla. idan kuma a
kwai gawar yara sai Namiji babba ya zanto shi ne kusa da liman, sai karamin
yaro, sai babbar Mace, sai karamar yarinya. Kai na karamin yaron zai zamto a
saitin kan gawar babban Mutum, tsakiyar babbar Mace kuma a saitin kawukansu.
Haka nan karamar yarinya kanta zai zamto a setin kan babbar Mace, itama zai
zamto a tsakiyarta tana dai-dai da kan Namiji;
Su kuma sauran
Masallata za su zamto gaba dayansu a bayan liman, saidai wanda bai samu wuri
a bayan liman ba, sai ya tsaya kusa da
shi a hannunsa na dama.
Na takwas:
Sifar bunne mamaci: Abinda aka shar'anta shi ne zurfafa kabari gwargwadon yadda
zai kai kwankwason Mutum, sannan Lahadu din ya zama a bangaren alkibla –za a
tona shi-, kuma za a saka Mamacin ne ta bangaren damarsa, sai a warware kullin
likafanin, ba janye zaren za a yi ba, kuma ba za a bude fuskarsa ba; Namiji ne
ko Mace, daga nan sai a sanya tubala a daure shi da kwababbiyar laka; domin
kada kasa ta shiga cikin kabarin. Idan kuma ba a sami Tubali ba sai ayi amfani
da katanga/kasko, ko duwatsu, ko itace wanda zai iya hana kasa shiga cikin
kabarin, sannan sai a tura turbaya a kai. An so yayin saka gawar a kabarinta a
ce: Bismillah wa ala millati Rasulillah. Kuma za a daga kabarin gwargwado taqi
daya, in an sami dama sai a dora dan dutse a kai, sai kuma a yayyafa ruwa a
samansa.
Abin da aka
shar'anta wa wadanda suka raka gawa shi ne: mikewa tsaye a makarbarta bayan
rufe mamacin don su yi masa addu’a, saboda Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare Shi ya kasance yana mikewa tsaye ne idan aka gama rufe gawa
sannan ya ce: "ku nema wa dan'uwanku gafara, ku roka masa tabbatuwa, domin
a halin yanzu za a masa tambayoyi".
Na tara: Shari'a
ta yarda ga wanda bai samu damar yi masa sallah ba ya yi masa bayan rufe shi da
kimanin wata daya kawai, domin Annabi SAW ya aikata hakan,. Amma idan aka haura
wata daya to bai halatta ayi sallah a makabarta ba, saboda rashin dalilin dake
nuni cewa Annabi SAW ya aikata hakan bayan wata daya da rufe gawa.
Na goma:
Haramun ne wadanda aka yiwa mutuwa su yi wa Mutane abinci, saboda hadisin Jarir
dan Abdullahi Albajaliy -Allah ya yarda da shi- ya ce: (Mun kasance muna kirga taruwa
a gidan wanda dan'uwansu ya rasu, da kuma yin abinci bayan rufe gawa daga cikin
kururuwar Mutuwa).
Amma su yi
abinci don su ci, ko su baiwa bakinsu babu laifi. Kuma an shar'anta wa yan'uwa
da makwabta su yi musu abinci, saboda lokacin da labarin kashe Ja'afar dan Abi
Talib ya zowa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi sai
ya umurci iyalansa da su shirya abinci ga mutanen gidan Ja'afar, ya ce: “Hakika
abinda zai shagaltar da su ya same su”.
Babu laifi
idan yan'uwan mamaci suka kira makwabtansu ko wasu domin cin abincin da aka
kawo musu kyautarsa. Kuma wannan bashi da wani kayyadajjen lokaci a iyakar
saninmu da shari'a.
Na sha daya:
Bai halatta Mace ta yi takabar sama da kwana uku ga wani mamaci ba, face ga
Mijinta, shi kam wajibi ne ta yi masa takabar wata hudu da kwana goma, sai in
ya barta da ciki, sai takabar ta zama zuwa haihuwarta, saboda zuwan ingantattun
hadisai daga Annabi Muhammadu SAW akan hakan.
Namiji kuwa
haramun ne ya yi takaba ga wani mamaci dan'uwansa ne ko ba dan'uwansa ba.
Na sha biyu:
An shar'anta wa Maza ziyartar makabartai, lokaci bayan lokaci; domin yiwa
mamatan addu'a, da nema musu rahama, da kuma tuna mutuwa da abinda zai zo bayan
mutuwar, saboda fadin Manzon Allah: "Ku rika ziyartar makabartai; domin
suna tunatar da ku Lahira".
Kuma Manzo
Allah ya kasance yana koya wa sahabbansa addu'ar ziyartar makabartai kamar
haka: "Amincin Allah ya tabbata a gare ku, Ya ku ma'abuta wannan gida daga
Muminai da Musulmai, mu ma za mu riske ku in Allah Ya yarda, Allah ya ba mu
lafiya mu da ku. Allah ya gafarta wa wadanda suka rigaye mu da jimawa da
mutuwa, har da wadanda basu jima ba".
Mata kuma basu
yin ziyarar makabartai saboda Manzon Allah ya la'anci mata masu yawan ziyartar
makabarta, kuma saboda tsoron fitina da gajen hakuri idan suka yi ziyarar.
Haka nan baya
halatta ga Mata su raka gawa zuwa makabarta ba, saboda Annabi ya hana su, amma
yi wa mamaci sallah a cikin masallaci ko a waje halal ne ga maza da mata.
Wannan shi ne karshen abin
da ya sauwaka.
Tsira da
aminci su kara tabbata ga Annabinmu (Muhammad) da mutan gidansa da sahabbansa.
No comments:
Post a Comment