HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
HARE-HARE
A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS
(الأحداث في البقيق والخريص)
Shehin
Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh AsSubaitiy
–Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HARE-HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye a bayan kasa ne, na
manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowar dukiya masu yawa, a karkashin kulawar
Mutane, domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda
ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga
arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].
Kuma dukkan umurni
da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin tabbatar da
ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma domin umurni da hani
a shari'a suna komawa ne ga/ Kiyaye
manufofin shari'ar, a cikin halittu. Kuma wadannan manufofin dole babu makawa, sai
an basu kulawa, gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka
rasa su, to maslahohin Duniya ba za su tabbatu ba.
Musulunci ya rataya mafi
tsananin azaba, akan kawo barna a ban kasa; kuma duk wanda ya yi barna a bayan
kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci
ne.
Matsala zata iya samun
Mutane saboda makircin makirai, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi,
wannan kuma domin Allah ya jarrabi Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin
munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewar su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi
akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan
asalin tushensu. Kuma hakikanin
al'ummomi yana bayyana ne a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin
ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna
girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma (bayan
ibtila'i) sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa,
himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa
karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiya ko gudanar rayuwa, a'a
al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai hare-hare masu
radadi da suka auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijrah da
Kharis, kuma suka yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa na wannan al'ummar,
aiki ne abin kyama, Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma
ba za su samu muradinsu na barna ba, kuma da falalar Allah, sannan da fadakar shugabannin
wannan kasa, da azamar jami'an tsaronta da masu gadin iyakoki, hare-haren za su
koma da asara mabayyaniya.
Kuma idan masu barna da
'yan rushe-rushe suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi
ta'addanci, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin
amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasar da bunkasata ya cigaba.
Duk da wadannan hare-haren
kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara
basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa
aminci da zaman lafiya.
Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da
fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin neman a
tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta tun a farkon fari, ana mata
haka domin ita ce cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya -masu aikin wofi- su sani, lallai ba za su iya rushe tsaron
wannan kasar ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba,
domin kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana tsananin yakar ta'addanci; kuma
saboda alakokin 'ya'yanta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar
Allah ganuwa ce mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin
kiyayewarsa, sakamakon daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune
ginshikin hukuncinta, mabubbuga ga shari'arta, salo kuma ga rayuwarta, matabbatan
samun iko a cikinta, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shi zai sanya al'amarin
tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta karfinsa, kuma Mutane suna fatan ganin
bunkasarsa.
Danganta kai ga kasarka al'amari ne wanda a al'adance aka dasa shi a jikin
Mutane, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro ta daga danganta
kai ga addini, sai su tafi a tare, Kuma yaya Mutum ba zai kaunaci kasar da yake
rayuwa akanta ba, ya taso a kan turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da
tarihinta? Kuma yaya ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi
fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki domin dakatar da
masu ta'addanci a gare ta ba?
Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa al'amarin tsaronsu da
dukkan nau'ukansa, sai ya karfafa dangatakar 'yan kasar ta cikin gida, wanda
kuma hakan shine zai kare su, daga wanda yake son kunno fitintinu da
tashin-tashina a cikin kasarsu.
Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata, shine hanyar
samun nasara, da daukaka, kuma shine sinadarin samun karfi, da natsuwa da zaman
lafiya. kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawa suke raunata kulle-kullen
makirci, suke dauke abu mai cutarwa.
Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, ta
Saudiya, shine ginshikin amincin al'ummar Musulmai, saboda Saudiya ita ce zuciya
mai bugawa na al'ummar, kuma guzurin al'umma mai tunkuda. Kuma lallai munana wa
kasar nan munanawa ne ga zaman lafiyar daukacin Musulmai. Kuma gangar jikin
al'umma ba zai gushe yana cikin alheri ba, matukar zuciyarta tana bugawa, domin
alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani basu yankewa. Kuma
hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasar, da kare ta daga
makircin makiya da kaidin masu kaidi, abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi
ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumowa da
wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki
domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana
hidima ne ga makiyan Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku
komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako. Kuma duk yadda kiraye-kiraye
barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare ta ya yawaita, to lallai barna gininsa mai
girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta,
sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].
Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk
yadda masu kaidi suke kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci,
masu jiran ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai
wannan kasar mai kariya ga harami biyu, gininta yana nan da karfinsa, madaukaki,
wanda zai gagari makiya, Mai neman ya taba girman kasar zai kaskanta, mai adawa
da ita zai fadi ya wulakanta, wannan kuma babu makawa akansa, saboda Musulunci
shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta, kuma lallai daukakarta yana
karkashin bin addininta, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi- ya
ce: "Mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai
Allah ya daukaka mu da Musulunci".
Zarata akan iyakokinmu suna yin zaman dako (ribadi), suna kiyaye addini da
kasa, suna gwabzawa da makiyansu suna lankwame su, kuma basu girgiza, cikin
kudurinsu, suna masu karfi da azamarsu da zukatansu, domin yanke (katse) karshen
masu ta'addanci, da kakkabe ko buge makamansu na barna.
A nan, Muna jinjina ga gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke
bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar
ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasarmu, da wargaza tsare-tsarensu
tun a farkon fari. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan
mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sai su yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga
yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro"
[Kuraish: 3-4].
Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai
girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa
mai hikima,
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Mumini a lokacin tsanani da fitintinu, alakarsa da UbangijinSa tana kara
karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da MajibincinSa, yana neman fakewa a mafakarSa,
"Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi
mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa ga Allah, da nuna
masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da
yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta.
Kuma idan Musulmii ya
bayyana bukatarSa ga MajibincinSa, to ya hada bukatarsa da aiki da kuma
lazimtar addu'a, kuma lallai Allah ya yi alkawarin amsa addu'ar wanda ya roke
shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai
amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai
kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta
al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta
damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta
kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga
Allah, to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za
ta samu gurbi ba a zuciyarsa, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma
zuwa gare shi lamura suke tafiya.
Kuma Al'ummar Musulmai za
su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk
wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya
isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana hasashen
zuwa lokaci na gaba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu cewar
Allah zai cika alkawarinsa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah
mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya kaddara ga dukkan komai" [Dalak: 3].
No comments:
Post a Comment