HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله
عليه وسلم)
JUMA'A, 03/SHAWWAL/1437H
Daidai 08/JULY/2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALU AL-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
SE KUMA ME, BAYAN
SHUXEWAR WATAN AZUMI?
Shehin Malami wato: Husaini xan Abdul'aziz Alu
Al-Sheikh –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SE KUMA ME, BAYAN
SHUXEWAR WATAN AZUMI, Wanda a cikinta kuma ya tattauna, akan watan ramadana da
tunatarwa kan shuxewar yinin ramadana da dadarensa, da abinda suka qunsa a
cikinsu na aiyukanmu; na alherinsu da sharrinsu, da abinda ke wajaba akan
musulmi na biyar da kyakkyawan aiki bayan kyakkyawa, Sannan ya ambaci lamarin
tayar da boma-bomai da ya zama sababin zubar da jinane da kashe rayuka a qasar
Harami biyu, Yana mai faxakar da iyaye da Maluma da wayayyu da kafafen sadarwa
cewa su riqa koyar da samari suna faxakar da su kan shari'ar Allah (تعالى).
HUXUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah akan ni'imominsa da
ba a qididdige su.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah; shi kaxai ya ke ba shi da abokin tarayya, a lahira da duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu
bawansa ne kuma manzonsa, annabi zavavve, kuma bawa zavavve.
Ya Allah! ka yi daxin salati da sallama da
albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abuta gaskiya da tsoron Allah
( taqawa).
"Ya ku waxanda suka yi imani ku bi dokokin
Allah da taqawa, kuma ku faxi magana ta daidai * Zai gyara muku aiyukanku, kuma
ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi xa'a wa Allah da Manzonsa to
haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].
'Yan'uwan Musulunci
Mamakin saurin shuxewar kwanaki, da wucewar
watanni!
Shi mai hankalin da aka yi masa dacen taufiqi
shine ke riqan kwanaki da watanni a matsayin lokatan kusantar Allah majivinci –جل وعلا-, tare da kiyaye yin biyayya a gare shi, a
sirrance da a bayyane.
Kuma lallai abinda ya wajaba akan musulmi a
cikin wannan rayuwar shine: Ya yi qoqarin tabbatar da manufar samar da shi, a
tsawon rayuwarsa gabaxayanta; ta hanyar tsayuwa akan tauhidin Allah (جل وعلا), da bin dokokinsa, da biyayya wa Majivincinsa
(Allah); Saboda rayuwa gabaxayanta; Manufarta mafi girma itace, yin aiki da
umurnin Allah, da qoqarin tabbatar da bauta a gare shi (سبحانه), kamar yadda Allah (جل وعلا) ya ke cewa: "Ka ce: Lallai
sallata da yanke-yankena, da rayuwata, da mutuwata ga Allah ne Ubangijin
talikai * Bashi da abokin tarayya, kuma da aikata haka aka umurce ni, kuma nine
farkon musulmai" [An'aam: 162-163].
Da faxinsa (جل وعلا): "Kuma, ka bauta wa
Ubangijinka har mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana ambaton Allah a dukkan
lokutansa.
Ya
ku taron Musulmai!!
Idan Musulmi
ya tsayu a cikin watan ramadana don ya amfana da lokutansa, ta hanyar gaggawa
cikin aikata aiyukan alkhairi, da kusantar Ubangiji da sauran mustahabbai, To
wajibi ne akansa ya yi godiya wa Allah (جل وعلا)
akan haka, Sai kuma ya yi iya qoqarinsa a cikin shekararsa gabaxayanta, wajen
aikata dangogin xa'a, gwargwadon iko, saboda Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Aikin da Allah
ya fi so, shi ne wanda aka dawwama akansa, koda ya yi kaxan",
Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma
hanyoyin samun lada, da damammakin kwasar garavasar kyawawan aiyuka, a cikin
shari'ar rangwame da sauqi da rahama da falala (wato: shari'ar musulunci), suna
da matuqar yawa, kuma nau'i-nau'i ne, a cikin zantuka da aiyuka.
'Yan'uwan
Musulunci!!
Sha'anin
da yafi girma, Shi ne musulmi ya tsayu wajen aikata aiyuka na wajibi, da
nisantar munana; ababen kyama da shari'a ta yi hani akansu, Allah (تعالى) yana cewa: "Ka tsayu, kamar
yadda aka umurce ka, da waxanda suka tuba a tare da kai, kuma kada ka qetare
iyaka" [Hud: 112].
Kuma Manzonmu (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ka ce: Na
yi Imani da Allah, sa'annan ka tsayu".
Ya
ku bayin Allah!
Ku kiyaye
aiyunku kyawawa, kuma ku nisanci gurvata abinda Allah ya yi muku ni'imar aikata
su, saboda fallasasshen Mutum na haqiqa a madubi na shari'a, kamar yadda
nassoshi su ka nuna shi ne: Wanda zai gina aiyuka kyawawa manya-manya, sa'annan
sai ya rushe su, ta hanyar sakar wa gavvansa linzami cikin zaluntar halittun
Allah, da yin ta'addanci a gare su, cikin magana ko aiki.
Ya
ku taron Musulmai!
A
qarshe-qarshen watan azumi, a lokacin da musulmai su ke farin cikin qarisa
azumi da salloli ko tsayuwar dare, bayan kuma Allah ya yi wa Musulmai dacen
kammala tilawar maganar Allah Mai hikima, Masani: Sai kwatsam musulmai su ka
tashi da jin labarin aika-aikan kaiwar harin boma-boman da su ka zubar da jinni,
su ka kuma kashe rayuka, su ka tsoratar, har guda uku, a qasar harami biyu,
wanda a cikinsu su ka tara mafi girman ababen qi, Daga cikin laifuka kuma, su
ka qunshi mafi muninsu, Daga cikin kaba'irai kuma mafi girmansu, daga wata
qungiya, wanda ta karkace daga koyarwar wahayin alqur'ani da sunnah, sannan (qungiyar)
ta fice daga jama'ar musulmai, kuma ta haifar da ababen da su ka jawo varna mai
girma a qasashen musulmai, da kuma sharri mai yaxuwa, Wanda babu mai farin ciki
da aukuwar hakan sai maqiyan addini.
Shin
waxannan, ba za su ji tsoron damqar Mai girma Allah (maxaukaki da buwaya) ba?!
Shin ba za su yi taqawar Mabuwayi Mai gafara
ba?!
Ina su ke lokacin da Ubangijinsu zai tambaye
su, kan kashe rayukan mutanen da basu ji ba, basu gani ba?!
Menene kuma matsayansu dangane da
mahaliccinsu, alhalin suna yawo da varna mai faxi, ta hanyar razanar da
amintattu, masu bauta, da sallah, ta hanyar kashe marasa laifi, masu azumi,
musamman a kusa da masallacin ManzonSa amintacce, a cikin wata mai girma,
alhalin sauran mutane suna cikin salloli, da qanqan-da-kai ga Ubangijin
talikai!
Ku
saurara!
Ya
ku samari Musulmai!
Ku
tsaya, tsayawa ta tunani da hankalta, kuma ku xauki darasi daga munanan qarshe,
wacce aqidun waxanda su ka karkace daga jama'ar musulmai, su ke kai su, mutanen
da su ka halatta jinin masu bauta, masu azumi, da salloli, da i'itikafi (don
yin bauta) ga Ubanjinsu, suna masu sujjada da qanqan-da kai (a gare shi).
Ya
wanda aqida ta sanya shi zamewa daga (turbar) daidai, har ya kauce wa hanya ya
bar tafarkin gaskiya… Ka tuba zuwa ga Ubangijinka (جل وعلا) gabanin ka sadu da shi, Ka dawo zuwa ga
hanyar muminai kamar yadda Ubangijinka ya umurce ka da aikata hakan, kuma
Manzonka (صلى الله عليه وسلم) ya umurce ka da
aikata hakan, Ka komo izuwa ga kewayen jama'ar musulmai, saboda nassoshin
shari'a sun tsawatar maka, daga fanxarewa ga jama'a, kuma sun hane ka, kan raba
kai, da nisantar jama'a.
Kuma mafi girman hanya a tarihin al'ummar
musulmai, mafi girman hanyar da Shexanun aljanu ko na mutane su ke bi, don vata
kwakwale, kuma domin fitar da su daga shiriya miqaqqa, ita ce: Nisantar jama'ar
masu sallah, da shiriyar masu bauta, da turbar ko tafarkin muminai, "Kuma kada ku bi
hanyoyin shexan, lallai shi a gare ku, maqiyi ne bayyananne"
[Baqara: 168, da 208, da An'aam: 146].
Kuma Alqur'ani da sunna basu nusar da mu ba,
sai izuwa ga ababen da za su gyara halayenmu, Kuma a duk lokacin da mu ka yi
nisa da haka, sai varna mai faxi ta auku.
Ya
samarin musulunci!
Lallai
mafi girman takobi ko makamin da masu qiyayya da musulunci, kuma maqiya annabi
Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) su ke bi; domin kekketa
riga ko ganuwar addini, ko domin yaqar garurrukan musulmai: Mafi girman
makaminsu shi ne Ta hanyar qosar da sabbuban jawo rabuwar kai (a cikin al'ummah), da fitar
da samari daga jama'ar musulmai, da hujjojin da zahirinsu rahama ne, baxininsu
kuma azaba, wato: hujjar taimakon addini, da yin hidima wa lamuransa. Hakan
kuma baya kasancewa daga gare su sai bayan sun nesanta samari daga Maluma na
Allah, da jiga-jigan faqihai masu ilimi na tantancewa, da shugabanni masu neman
kawo gyara.
Kuma duk wanda ya karanta tarihi to hakan zai
bayyana masa qarara; Saboda (a tarihance) babu abinda ya sha gaban al'ummar
Annabi Muhammadu (S.A.W) wajen yin hidima ga addininta, da yaxa saqon
Annabinta, fiye da fitinar (khawarijawa) ta fanxarewa ga jama'ar musulmai,
wanda dukkan ma'abuta musulunci gabaxaya su ke tare da ita. Saboda idan akwai
irin waxannan fitintinun to ba za a iya hidima wa addini ba, kuma ba zai yiwu a
yi masa hidima ba, kuma ba za a iya tsayar da wata rayuwa managarciya ba.
Hasali ma fanxarewa jama'ar musulmai bai jawo komai ga musulunci da musulmai
ba, sai varna mai girma, ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da kuma sharri mai yaxuwa. wanda harshen
mai fasaha (a cikin huxuba) bai isa ya qididdige irin varnar ba, a wuri irin
wannan.
Ya ku Mutanen wannan qasa !
Lallai qasarku ana nufinta da sharri, cikin hidimarta
ga harami biyu, da kuma cikin abinda Allah ya yi mata na ni'imomi masu yawa,
sai ku haxa kanku akan alkhairi, ku nisanci rabuwar kai da dukkan nau'ukansa,
ku kiyaye daga aukawa cikin tarkon maqiya, da masu jiran ganin aukuwar sharri,
waxanda su ke yin fata a gare ku, da al'ummarku, da 'ya'yanku da jikokinku masu
zuwa, su ke muku fatan qarewa da halaka da rugujewa.
Lallai hanyoyin sadarwa wajibi ne akansu su
gyara tafiyarsu, kuma su zama an fiskantar da su domin kawo amincin al'ummai,
da kiyaye yara da jikoki.
Kuma wajibi ne akan dukkan musulmai su nisanci
makami mai illa, wanda raunin da ya ke yi yana zubar da jini, Shine: Jita-jita
masu mugun manufa, da qarerayi masu jijjiga mutane.
Wajibi ne ga ma'abuta garin harami biyu, su
zama jini da tsoka tare da jagororinsu, suna xauka daga malumansu na Allah,
waxanda aka yi musu shaida da zurfin ilimi da addini da tsantseni da hikima da
sanin jiya-da-yau.
Kuma wajibi ne akan kowa, ya rinjayar da
maslahohi na gabaxaya, akan na xaixaiku.
Kuma su yi ta faxi-tashi wajen hidima wa
qasarsu, da gaskiya da ikhlasi, suna masu neman lada da sakayya (a wurin
Allah), saboda kasancewarta qasar harami ne guda biyu da ta ke yin hidima wa
addini, kuma ta ke yin hidima wa musulmai gabaxaya, wajibi ne su yi qoqari
wajen haka, suna xaukar haka daga faxakarwar addininsu da manufofin shari'arsu.
Wajibi ne akan iyalai su riqa kula da
'ya'yansu samari, suna bibiyar halayensu, suna dubi cikin yanayinsu, kuma su
riqa sanya musu ido cikin ababen da su ke fiskanta, tare da komawa zuwa ga
Allah (جل وعلا) da yin addu'ar
cewa ya kiyaye 'ya'yansu daga kowace fitina da jarabawa da kuma aqida vatatta,
saboda yin addu'a daga iyaye biyu sababi ne mai girma na samun gyaruwa.
Ya malaman wannan al'ummar!
Himmatuwa da lamuran wannan al'ummar ya kasance
kuna sanya hikima a cikinsa da kaifin hankali, da kyautata duban mai zai-je ya
komo, kuma mu kiyayi kowace magana ko fatawar da samari za su iya fahimtarta ba
a gurbinta ba, ko su su xora ta ba a ingantaccen wajen xaukar ta ba. Wannan
kuma ba zai yiwu ba, sai idan ana lura da manufofin shari'a, waxanda maluman
musulunci su ka yi bayaninsu, tare da kyautata karatun fahimtar addini ta hanya
miqaqqa, wanda zai xauki samari izuwa ga aiki da hikima da bi sannu-sannu, da
tausasawa, da nisantar gaggawa.
Daga qarshe:
Kalmar godiya ce, ga jami'an tsaro a qasarmu,
da kuma shi mutum na farko mai kula da tsaro (wato shugaba), saboda suna kan
tozo na azama, da hasama, da kula da hidima wa musulmai, da kiyaye musu
amincinsu, da zaman lafiya, bayan Allah (جل وعلا);
da fatan Allah ya saka musu da mafi alkhairin sakamako.
kuma ya kiyaye su daga kowani mummuna.
Kuma ya karvi wanda ya mutu daga cikinsu cikin
shahidai.
kuma Allah ya warkar da kowani maras lafiya
mai rauni.
Ina faxar wannan maganar,
kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da
sauran musulmai daga kowani zunubi,
sai ku nemi gafararsa, lallai shi Mai gafara
ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU
Ina
godiya wa Ubangijina kuma ina yin yabo a gare shi.
Ya
ku Musulmai:
Yana daga falalar
Allah (جل وعلا) ga
al'umma: Abinda ya shar'anta a gare su, na aiyukan biyayya da xa'a; waxannan da
za su basu lada mai yawa, Saboda Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya faxa cewa: "Wanda yayi
azumin ramadana, sannan ya biyar da guda shida a watan shawwal, to kamar ya
azumci shekara ne".
Kuma
baya halatta –a xayan zancen maluma guda biyu da ya fi fitowa fili-, ga wanda
akwai ramukon azumi na wajibi akansa ya gabatar da azumi na mustahabbi; saboda
yin hakan ya saba wa qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi ingantattu.
Sai
ku kasance –Ya ku bayin Allah- kuna masu xaukar darasi daga watan azumi,
wanda zai kai ku izuwa ga falaloli masu girma, da halayya kyawawa. Kuna masu
siffantuwa da sifar kyauta a rayuwarku gabaxaya, da kuma kyautatawa da
jin qai a asirce da a bayyane.
Saboda al'ummar annabi Muhammadu al'umma ce da
ya wajaba ta rayu a duniya da halayya maxaukaka, da kyawawan ababe masu girma.
Kuma yin hakan, yana cikin MANUFOFIN ADDININMU DA MANYAN HADAFIN SHARI'AR
UBANGIJINMU na farlanta farillai, da wajabta wajibabbu.
Sannan
yana daga cikin aiyuka mafi girma: Yin salati da sallama ga annabi mai karimci,
Ya
Allah! Kayi salati da sallama da albarka ga annabinmu kuma shugabanmu,
masoyinmu Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Ya
Allah! Ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a
kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a
kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye musulmai a
kowani wuri,
Ya Allah! Ka kiyaye su da
kiyayewarka, da kulawarka da kariyarka,
Ya Allah! Ka yaye baqin cikinsu, ka
kawar da vacin ransu.
Ya
Allah! Ka yi maganin maqiya musulunci,
Ya Allah! Ka yi maganin maqiya
musulmai,
Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da
makircinsu, Ya Ma'abucin girma da karramawa,
Ya Allah! Ka vata tsare-tsarensu da
makircinsu, Ya Mabuwayi Ya Mai hikima.
Ya
Allah! Ka gafarta wa muminai maza da muminai mata, da musulmai maza da
musulmai mata, rayayyu daga cikinsu da matattu.
Ya
Allah! Ka datar da majivincin lamarinmu zuwa ga abinda ka ke so, kuma ka
yarda, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
Ya
Allah! Ka kiyaye qasarmu daga dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen
musulmai,
Ya Allah! Ka kiyaye qasarmu daga
dukkan mummuna da abin qi, da sauran qasashen musulmai, Ya Ma'abucin girma
da karramawa.
Ya
Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu,
Ya Allah! Ka kiyaye jami'an tsaronmu,
Ya Allah! Ka qarfafe su, ka datar da
su, ka tagaza musu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
Ya
Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu umrah,
Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu
umrah,
Ya Allah! Ka kiyaye mahajjata da masu
umrah, Ya Ma'abucin girma da karramawa.
Kuma ka mayar da su zuwa qasashensu cikin
lafiya da riba, Ya Rayayye, Ya Tsayayye.
Ya
Allah ka bamu mai kyau a duniya, A lahira ma mai kyau, Ka kare mu daga azabar
wuta".
Ya
Allah! Ka sanya mu cikin waxanda ka karvi azuminsu da sallolinsu,
kuma ka gafarta musu zunubansu, Ya Rayayye Ya tsayayye.
Ya
Allah! Ka samar wa musulmi wani lamari na shiriya, Ya Allah! Ka
samar wa musulmi gabaxaya wani lamari na shiriya, wanda za ka gyara halinsu da
shi, Ya rayayye Ya tsayayye.
Qarshen addu'armu shine: ALHAMDU
LILLAHI RABBIL ALAMINA.
No comments:
Post a Comment