2016/11/09

GYARAN ZUKATA DA AIYUKA

الحديث الثاني: إصلاح القلوب والأعمال
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، قَال:
قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّم:
إِنَّ اللَّهَ لا يَنْظُرُ إِلَى صُوَرِكُمْ وَأَمْوَالِكُمْ، وَلَكِنْ يَنْظُرُ إِلَى قُلُوبِكُمْ وَأَعْمَالِكُمْ.
أخرجه مسلم [2564].

HADISI NA BIYU: GYARAN ZUKATA DA AIYUKA
An ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:
Lallai ne Allah baya dubi zuwa ga surar jikinku da dukiyoyinku, Saidai yana yin dubi ne izuwa ga zukatanku, da aiyukanku.
Muslim [2564] ya ruwaito shi.
FA'IDODI DAGA HADISIN
1-  Lallai karvar aiyuka da bada lada akansu yana rataye ne da tsarkin zuciya, da kuma kyawun aiki.
2-  Wajabcin kula da zuciya, da tsarkake ta daga dukkan sifar da Allah Mabuwayi da xaukaka yak e qi, kamar shirka da riya, …
3-  Hadisin: Allah yana yin dubi ne kawai, ga zukatan bayi da aiyukansu, qarin bayani ne ga faxin Allah ta'alah: "Lallai waxanda su ka fi girma a wurin Allah, daga cikinku su ne waxanda su ka fi taqawa" [Hujuraat: 13].

4-   Qirar jikin bawa, ko dukiyarsa ba su ne, Allah ke dubawa ba, kasancewar Allah shi ke daidaita halitta, kuma shi ke bayarwa.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...