HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 13 /ALMUHARRAM/1438H
daidai
da 14/OKTOBA/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
wanda ya shiryar da mu zuwa ga shari'a mai haske, wacce bayaninta shi ne
sauqaqawa, takenta kuma jin qai da tausasawa.
Ina shaidawa babu abun
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya,
shaidawar da sha'aninta ya yi girma a cikin zukatan masu tauhidi.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonSa; Allah ya turo
shi don ya kasance rahama ga halittu, da
addini miqaqqe, da kuma wata shari'a wacce ta bada kulawa ga mukallafai (wato
masu hankali daga mutane da aljanu), sai Manzon ya tafiyar da rayuwarsa cikin
kira da ita, kuma zuwa gare ta, yana xaukan hujjojinta na-yankan-shakku yana
bata kariya da su.
Salatin Allah da sallamarSa
su qara tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa.
Bayan haka;
Ya ku musulmai …
Ku kiyaye dokokin
Allah, saboda taqawar Allah ita ce
mafificin abinda aka aikata, Yin xa'a a gare shi kuma shi ne mafi girman
danganta ko nasaba; "Ya ku waxanda su ka yi imani ku kiyaye dokokin Allah
iyaka kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai", [Ali-imraan: 102].
Ya
ku musulmai …
Ku yi
godiya ga Allah, akan ni'imomi da kyautuka, kuma ku yi yabo a gare shi, akan
abin da ya tunkuxe muku, na azabobi da bala'oi.
Kuma ku xauki ibra ko darasi da waxannan da su ke kewaye da ku, saboda QASASHE NAWA NE aka samu rabuwar kan mutanensu,
shugabanci kuma ya wargaje, kwar-jini ko girmama hukunci ya faxi qasa, har ya
zama babu shugabaci, babu haxin kai, sai mutanen wannan qasar su ka kama yaqi
da junansu, haxin kansu ya tsattsage, zaman lafiyansu shi kuma ya wulaqanta.
Shi kuma
zaman lafiya, idan har ya samu koma-baya, sai lamarin rashin aminci ya yi
girma, dawo da amincin kuma ya yi wahala. Saboda fitina barci ta ke yi, babu
mai tayar da ita (daga barcinta) sai mai dauxa, kuma babu mai jawo ta face
mutum maha'inci, kuma babu mai sake ta (ga mutane) face mai yawan zalunci.
Ita fitina
(ko-yaushe) ana mata barbara ne har ta yi ciki: ta hanyar habaici (wato:
maganganun da ba na kai-tsaye ba), sai kuma ta haife, ko ta auku: da kalmomin
zaburarwa ko kwaxaitarwa.
Kuma
wace manufa ya ke fatan samu, Wanda ba shi da wata sana'a, sai kiran mutane su
fito zanga-zanga ko fito-na-fito, da muzaharori, da zaman dirshan, ko aikin tuntsurar
da gwamnatoci, ko fita daga xa'ar ma'abuta mulki da shugabanni ! ?
Bayan
kuma, abubuwan da su ka auku (a qasashe daban-daban) sun tabbatar cewa: FICEWA DAGA XA'AR MASU MULKI DA SHUGABANNI SHI NE GINSHIQIN SHARRI
DA FITINA DA BALA'I, saboda An ruwaito daga Usaid bn
Hudair (رضي الله عنه), ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Ku, a bayana, za ku
haxu da son kai (na shugabanni), Sai ku yi ta haquri, har ku haxu da ni, akan
tafki",
Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Imam An-Nawawiy –رحمه
الله تعالى-
ya ce: ((Kalmar
"asarah (الأَثَرَةُ)" tana nufin: Kevance kai da abubuwan duniya, da fifita
kansu da shi, Ma'ana: Ku ji maganan shugabanni, kuma ku yi biyayya a gare su,
koda sun keve kansu da kayan duniya, koda kuma ba su isar da haqqoqinku da su ke
wurinsu izuwa gare ku ba)).
Shekhul Islami Ibnu-Taimiyya (رحمه
الله تعالى)
shi kuma ya ce: ((Kaxan
ne, ake ficewa daga biyayyar shugaba mai iko, face ya
kasance abinda wannan aikin ke haifarwa na sharri, ya fi yawa, akan abinda
hakan ke haifarwa na alheri)).
Kuma Amru bn Al-aas (رضي
الله عنه)
yana faxa; cikin wasiyyar da ya yi wa xansa: ((YA KAI XANA! Samun shugaba adali
ya fi alkhairi a kan sauqar ruwa, da samun raquma. Shi kuma zama qarqashin shugaba
azzalumi maqetaci, ya fi alheri akan fitinar da za ta dawwama)).
FITINTINU suna gajiyar da masu kaifin kwakwalwa,
suna kunyata jahilai. Kuma idan yaqi ya kunnu, mutane kuma su ka kama
faxace-faxace, sai hankula su zame; su yi kure, duga-dugai kuma su goce, Tunani
ko hankula su kuma, sai su shiga ximuwa, Sai dai wanda ilimi da haquri su ka
qawata shi, sannan ya ji tsoron aukawa cikin zunubi da zalunci.
KUMA HIKIMAR HARSHE, DA TA TAKOBI suna kasancewa ne a cikin: Tsanaki,
wanda ke tunkuxe wauta, da kuma a cikin ilimi wanda ke kore jahilci, da cikin hankali
wanda ke kawar da mutum daga aukawa cikin fitina.
Hankulanku –Ya ku mutane-
kada ku nisance su
Kada kuma ku yanke
zumuncinku, da juya baya wa juna
Ya ku
Musulmai !!
Idan
sautuka su ka cakuxa, Husumomi kuma su ka tsananta, kiraye-kiraye kuma su ka
bayyana, Muzaharori da fito-na-fito su ka tsayu, to lallai farkon wanda ke
ribatar hakan, har ya haye tsakiyarta ya bayyana, Su ne: Maqiyan musulmai,
waxanda siyasarsu ta kafu a kan xaukar haqqoqin musulmai ba a bakin komai ba,
da halatta cin dukiyarsu da varna, da halaka garurrukansu, da rurrusa tattalin
arziqinsu, da kuma mamaye dukiyoyinsu, da yaxa zaman kara-zube a cikin
qasashensu, suna masu riqan abubuwan da su ka auku a matsayin hanyar bi, don tabbatar
da buqatunsu munana.
Shi kuma ADALCI ba za su zana iyakokinsa, da hukunce-hukuncensa, da
tsare-tsarensa ba: Qasashe 'yan mamaya azzalumai, waxanda su ka faxa cikin rami
mai zurfi, kuma qarfi ya ruxe su.
Haqiqanin rahama da adalci a cikin zukatan masu rahama, ba zai yi daidai da
riya hakan ba; wanda (a kullum) masu kisa waxanda su ka kakkafa kayukansu, a
matsayin masu yin wasici ga qasashen duniya, wai kuma sune masu kare haqqoqi,
da kiyaye aminci da zaman lafiya.
Kuma ta yaya zai kiyaye zaman
lafiya wanda ya shuka zanga-zangar fito-na-fito, ya kuma qarfafi juyin
juya-hali da tuntsurar da gwamnatoci, ya kuma kunna yaquka, da faxace-faxace,
ya taimaki maha'inta, A shekarun da kuma, su ka yaqi masarautun da su ka
kasance sun kai maqura wajen qarfi da wadaci da zaman lafiya?!
Haqiqa al'ummomin wannan zamani, da majalisar amincinsu sun xau alqawura, kan
kakkafa zaman lafiya, da tabbatar da aminci, sai dai kuma kamar sun yi alqawari
ne kan rurrushe zaman lafiya, ko kamar sun qulla cewa za su share shi (daga
doron qasa)!
Rattaba hannu don kawo zaman lafiya, bai zama komai ba, face zane a saman
takardu, da tawadar qarya akan fefofi, daga bishiyar cin amana da yaudara;
Sau nawa, aka rattaba hannun, don
kawo zaman lafiya, Wanda iskar siyasa sai ta yi wasa da ita, ta arewa da kudu
Idan har za ku rubuta wani
alqawari na kawo zaman lafiya, To ku sanya hawayen iyayen da aka kashe musu
'ya'ya; cakuxe da wannan tawadar
Ko kui yi zanen tsarin, da
jinanen waxanda aka kashe da zalunci,
Kuna masu tuna yini mai
tsananin firgici da su ka samu kansu a cikinsa
Sai ku qirqiro shi, wato:
adalci ga dukkan mutane,
Ba wurin kiyon da zai zama
yabanya ga masu qarfi kawai ba
Ya ku masu riya kiyaye zaman lafiya ! !
Haqiqa lamarin samun aminci da zaman lafiya ya
wulaqanta, qarqashin kwaxayin qasashe, sai zaman lafiya a qarqashin siyasosinku
ya zama burin da aka rasa, kuma qarya abar qi ko qyama.
Sai ku rage sautin fantamawar da ku ke juyi a cikinsa, domin kada ku tayar da
mafarkin mayunwata, da waxanda aka kora, ko aka qauratar daga garurrukansu !
Ku sake
rage sautin wargin da ku ke wasa a cikinsa, domin ka da ku yanke
mafarke-mafarken yaran da su ke ci-gaba da barci a qarqashin rusassun xakuna da
gidaje da asibitoci ! !
Shi kuma fiskantar gungun Ahlus Sunnah, a hukumominsu, da jagororinsu, da
manya-manyansu, da malumansu, da qarfinsu, da tattalin arziqinsu, da kuma aikin
qaqaba takunkumi, a garurrukan Sunnah, da qalubalantar masallatai da rurrusa majami'oin
juma'a, da lalata makarantun Ahlus Sunnah da boma-bomai, ana qirga shi a
matsayin ta'addacin da aka tsattsara, akan musulmai gabaxaya, kuma laifuka ne
na yaqi, kuma keta alfarmar haqqoqin 'yan adam musulmi ne a garurrukansu da
qasashensu.
Ya ku Musulmai
!!
Yayewar
musibu a tsakanin sahun musulmai alamominsa sun fara bayyana, Saidai kuma
cikinsu akwai yaguwa da fuji, da rarrabuwar kai a ra'ayoyi, da bin son zuciya,
da qungiyoyi, da jama'oi, kuma kowace qungiya daga cikinsu tana da wani
niyya da manufa, kuma kowace jama'a tana da mashaya (da take xaukar tsarin
tafiyarta), kuma kowace qungiya tana qanqanta sha'anin wata, kuma tana
aikin tsoratarwa daga gare ta. Babu kuma abinda mu ke iya ji sai sautin mai
tsoratarwa, mai kashedi, kuma babu abinda mu ke iya gani sai alamar mai
tsanantawa mai kaushin rai; Kowa takobinsa yana cinye kubensa; saboda kaifinsa,
kuma yana tsananta wa xan'uwansa musulmi; saboda tsananinsa.
Kuma
wanda ya kunna wutar savani, ya ke iza ta, ba zai iya tattara abinda ya rarraba
na lamarin wannan al'ummar ba, ko ya iya haxa kalmarta.
Haka kuma wanda ya ke kore mutane
daga addini, da tsanantawa, ko kaushin rai.
Haka mai alfasha wanda ke ta'addaci
ga mutane, da gangancin zaginsu.
Ko kuma maqiyin da ya ke shiga
tsakanin zukatan da su ke guje wa juna, da sahu masu qara nisantar juna.
Haka mutumin da ke yin shisshigi wa
ilimi, kana, ya ke kukkutsawa cikin fatawa ba tare da ilimi, ko bin abu da
tsanaki ba.
Haka wanda ya karkata da bin bidi'a
da tatsuniyoyi ko qare-rayi.
Lallai
yin savani, a fura'a da mas'alolin fiqihu ba sa hukunta gaba, ko rarrabar
kalma, ko tunkuxe lamarin haxin kai, kuma savanin ba ya hukunta bidi'antarwa,
ko fasiqantarwa, ko kafirta wanda ya sava wa (fahimtarka).
Kuma wajibi ne akan musulmi ya riqa kirdadon ko
neman gaskiya, sannan ya xauki abin da dalili daga Alqur'ani da Sunnah
su ka yi nuni akansa, koda kuwa ya sava wa mazhabarsa, da shehinsa ko
malaminsa.
Kuma baya halatta ya riqi savani a cikin waxannan mas'alolin a matsayin wata
hanya, ta yin jayayya, da faxa, da qaurace wa juna, da rabuwar kai; Saboda
magabatan kwarai (رضي
الله عنهم)
sun yi savani a mas'aloli masu yawan gaske, sai dai sashinsu bai kasance yana
inkari wa sashi a mas'aloli da za a iya ijtihadi a cikinsu ba, kuma zukatansu
sun kasance suna iya xaukar hakan; Imam As-Shafi'i yana cewa: ((Shin, ba zai yiwu mu kasance
'yan'uwan juna ba, koda kuwa ba mu yi ittifaqi a mas'ala ba ! !)).
Kuma dukkan zance, ko aikin da ya sava wa Sunnah ko ijma'i, to wajibi ne a yi
inkarinsa. Kuma kowani zance a cikin mas'alar da babu Sunnah ko ijma'i a kanta,
kuma ijtihadi na iya samun gurbi a cikinta, to ba a yin inkari ga wanda ya yi
aiki, da ita, mujtahidi ne malami, ko kuma muqallidi mabiyi.
Kuma baya halatta a bada fatawa da abinda ya sava wa nassin Qur'ani ko Sunnah,
kuma zancen mujtahidi a irin wannan ya kan zama yasasshe, kuma haramun ne a yi
taqlidi da mujtahidi idan ya yi fatawa da abinda ya sava wa nassoshi na
shari'a, kuma haramun ne ayi masa taqlidi; saboda cikin yin taqlidi ga
mujtahidi a irin wannan, akwai gabatar da maganarsa, akan maganar mai shari'a
(Allah da ManzonSa), kuma yin hakan haramun ne.
Kuma
baya cikin hankali da hikima a ruro wutar husumomi a tsakanin mazhabobin
Sunnah, alhalin maqiyan Sunnah suna yagan jikin wannan al'ummar da haqoransu,
tare da qarfafawar kai-tsaye da na bayan fage daga qasashe azzalumai, Allah
mabuwayi da xaukaka yana cewa: "Kuma kada ku yi jayayya, sai ku raunata, sai qarfinku ya tafi" [Anfal: 46].
Domin yin jayayya yana haifar da
rauni da shanyewar vangare, da samun rinjaye daga maqiyi.
An ruwaito daga Amru bn Shu'aibin,
daga Babansa, daga Kakansa, ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
ya ce: "Musulmai
jininsu yana daidaita, kuma wanda ya fi qaranta a cikinsu yana iya qulla
alkawarinsu, kuma Su hanu xaya ne ga wanda ba su ba", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya yi sallah irin tamu, ya
kuma fiskanci alqiblarmu, ya ci abin yankarmu, to wannan shi ne musulmi,
wannan, da alqawarin Allah da alqawarin Manzonsa su ke a kansa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Amma ita
kuma AQIDA To lallai haqiqa sahabbai sun yi
ittifaqi akanta, kuma babu wani savani da ya auku a tsakaninsu a cikinta, ko
jayayya.
Kuma dukkansu sun haxu wajen
tabbatar da abinda littafin Allah ya zo da shi, da sunnar Manzo.
Kuma sahabbai (رضوان
الله عليهم)
sun kasance suna tsawatarwa kan yin bauta da bidi'oi da kuma qirqirarrun
lamuran da Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم)
bai shar'anta su ba.
KUMA
YANA DAGA CIKIN BIDI'OI QIRQIRARRU: Wanda wajibi ne a tsawatar akansu: Bidi'ar xawafin qaburbura, da
yin yanka don kabari, da yin bakance wa qabari, da neman agajin ma'abutan
qabari, da kuma bidi'ar wuce iyaka cikin waliyyai da salihai, ta hanyar sunkuyo
da qanqan-da-kai, da yin ruku'i, da sujjada a gare su, da neman tabarruki (albarka)
da yawunsu da jikinsu.
Kuma
qiyasin tabarruki da jikinsu, da lamarin yin tabarruki da mai sonmu abin so;
annabi Muhammadu (صلى
الله عليه وسلم)
a lokacin yana raye, wannan qiyasin varna ne, ta kowace fiska; saboda, Da wani
hankalin ne kuma, ko wani dalilin, za a yi qiyasin wani malami ko waliyyi, duk
yadda ibadarsa ta kai, a yi qiyasinsa da shugaban mutane; Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ? !
KUMA
YANA DAGA CIKIN WAXANNAN BIDI'OIN: Bidi'ar yin rawa, da tsalle-tsalle, da karkaxa jiki, da
kewayawa, da motsawa ta kowani sashe, a lokacin yin zikiri (wato: lokacin
zikirin Allah), a cikin masallatai, da wajensu. Da wasu wannan, daga cikin
bidi'oi, wanda wasu musulmai ke aukawa cikinsu, saboda jahilci, da taqlidanci.
Kuma dukkan
wannan, suna daga abinda ya wajaba ayi inkarinsa, Sai dai, dole ya zama cikin
hikima da wa'azi mai kyau, da zancen da maslahohi za su tabbatu da shi,
dangogin varna kuma, a tunkuxe su da shi.
Kuma duk
wanda ya auka cikin bidi'a ko varna, to wajibi ne akansa ya dawo daga
rakiyarsu, saboda komowa izuwa ga gaskiya shi ya fi alheri akan dawwama cikin
varna.
Kuma
babu abin da zai tattara kan mutane face littafin alqur'ani da Sunnah, a bisa
fahimtar magabatan al'umma.
Kuma
zance ba zai dace ba, sai tare da aiki.
Kuma
zance da aiki ba za su dace ba, sai da niyyah.
Haka
zance da aiki da niyya ba za su dace ba, face sun yi muwafaqa da Sunnah.
Ya
Allah! Ka nuna
mana shiriyarmu, kuma ka kare mu daga sharrin kayukanku, kuma ina neman gafarar
Allah, sai ku nemi gafararSa; lallai ne shi ya kasance ga Masu komawa
gare shi Mai yawan gafara ne.
HUXUBA TA BIYU
Yabo na Allah ne; wanda ya bada mafaka ga wanda ya nemi fakewa
ga tausasawarSa.
Kuma ina shaidawa babu abun
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Ya warkar
–cikin ni'imarSa- wanda ya xebe tsammani waraka daga cutukansa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa; Wanda ya bi Shi
haqiqa ya shiryu, wanda kuma ya sava masa ya kasance cikin ruxu da vata da
halaka.
Allah
yayi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, salatin da
ke wanzuwa, da sallaman da ta ke maimaituwa tana bibiya.
Bayana
haka:
Ya ku
Musulmai!!
Ku
bi dokokinAllah da taqawa, kuma ku yi masa biyayya, kada ku sava masa, "Ya ku waxanda su ka yi imani ku bi
dokokin Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Tauba: 119].
Ya ku Musulmai!!
Ku
kiyaye bibiyar dayawa daga waxanda suka xaga sauti, ko su ka fito, ta hanyoyin
sada zuminci na zamani, waxanda wautarsu da muninsu su ka bayyana daga
rubuce-rubucensu, da bidiyoyin da su ke yaxawa, saboda sau dayawa su kan yaxa
sharri da varna, kuma su kan watsa qarya da abin qyama, kuma su kan faxi wauta
da abin qi, Sai dai wanda Allah ya yi rahama a gare su, kuma su kaxan ne.
Kuma lallai waxannan hanyoyin sun wayi gari filin sukuwar kowani marashin
ilimin da bai mallaki komai ba, waxanda neman shahara ta ke jansu, qoqarin
fitowa ko bayyana ya ke burge su, Wanda (sau dayawa) yawan masu bibiyansa ke
ruxar da su, har su ke zaton cewa, babu wanda zai iya shan gabansa, ko babu wanda
zai iya tsayawa a matsayarsu.
Kuma –wallahi- Mutum ya zama wanda
ya ke sitirce, ta yadda idan bai halarci wuri ba, ba za a nemi shi ba, faqiri,
voyayye, wanda ake rufe masa qofofi, shi ya fi alheri a gare shi, a kan ya
kasance shahararre da aikin varna, wanda ya sanu da mummunan aiki.
Ya ku 'yan jarida, da masu xago
sauti !!
Ku bada kariya ga addininku, ku bada kariya ga qasarku;
masarautar larabawa ta Saudiyya, kuma ku sanya alqaluman rubutunku cikin abinda
zai qarfafi zaman lafiyanku, ya dawwamar da amincinku, ya kiyaye haxin kanku. Kuma
ku nisanci duk abinda zai shuka fitina, da rashin tsari, ya kuma yi allura ga
qasqantattun mutane ko wawaye.
Kuma ku
nemi tabbaci da bin diddigi cikin duk abinda ku ke rubutawa, ko ku ke faxa.
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad Mai shiryarwa, Mai ceton mutane gabaxaya;
saboda idan Mutum ya yi masa salati
xaya, to Allah ta'alah zai yi masa guda goma,
Ya Allah ka yi salati da sallama ga
bawanka kuma manzonka Muhammadu,
Kuma ya Allah ka
yarda da dukkan iyalan Annabi da sahabbai,
Ka haxa da mu, Ya Mai karimci,
Ya Mai yawan baiwa,
Ya Allah ka xaukaka musulunci da
musulmai,
Kuma ka qasqantar da shirka
da mushirkai,
Kuma ka halaka maqiya
wannan addinin,
Ka sanya wannan qasa ta
zama cikin aminci da zaman lafiya da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah ka datar da shugabanmu
kuma jagoranmu izuwa ga abinda ka ke so, kuma ka yarda,
Ka kama qeyarsa izuwa
biyayyarka da aikin taqawa
Ya Allah ka datar da xaukacin masu
jagorantar lamuran musulmai izuwa ga yin hukunci da shari'arka,
da bin sunnar annabinka
Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), Ya Ubangijin
halittu.
Ya Allah ka zama mai taimakon garin
Halab da Shaam,
Ya Allah ka tausaya wa rauninsu,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka yaqi wanda ya yaqe su,
Ya Allah ka saukar da azaba da
qasqanci da fushinka ga wanda ya rushe gidajensu akansu,
Ya Allah ka kashe su da makaminsu,
ka qona su da wutar da su
ka fura,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka tseratar da waxanda ake
ta raunana su daga cikin musulmai, a kowani wuri, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kawo aminci a
iyakokinmu,
ka kare rundunoninmu,
ka taimake su akan
maqiyanka kuma maqiyansu,
Ya Ubangijin halittu.
Ya Allah ka karvi matattunsu cikin
shahidai,
ka warkar da wanda aka yi
masa rauni daga cikinsu,
Ya Mai amsa addu'a.
Ya Allah ka sanya addu'anmu ya zama
karvavve,
Sautinmu kuma abun xagawa,
Ya Mai karimci, Ya Mai
girma, Ya Mai jin qai.
No comments:
Post a Comment