2016/10/27

HUdUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم, 27 Muharram1438H daidai da 28 Oktoba2016M ta DR. ABDULBARIY AS-SUBAITIY











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27 /Muharram/1438H
daidai da 28/ Oktoba/ 2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
MAXAUKAKIYAR HIMMA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: MAXAUKAKIYAR HIMMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan xaukaka himma, da wajabcin samar da ita a cikin musulmai, musamman a wannan lokaci, yana yin ishara ga abinda ke aukuwa a cikin faya-fayen bidiyo dayawa, na watsa ko yaxa bidiyoyi marasa qima, waxanda ba su da wani amfani, sai ma cutarwa, yana mai bayyana cewa lallai akan kafafen sadarwa, da samari, da 'yan'mata, da wassunsu daga cikin vangarorin al'umma, rawar takata, da wasu aiyuka, waxanda suka dace da matsayinsu a cikin al'umma, wajen yaqar waxannan ababen marasa qima.

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah, yabo ya tabbata ga Allah wanda ya kare zukatanmu daga vata, da kuma kafofin shigowar ababe marasa qima, Ina yabo a gare shi -سبحانه- kuma ina gode masa, akan dukkan alheri da falala, da kuma qari.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, wanda ya cike rayuka da imani, da kuma jin daxi.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, jagora abin misalicikin hukunci da jagoranci.
Allah ya qara salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, waxanda su ka jagoranci wannan al'ummar da kyakkyawan jagoranci.

Bayan haka:

            Ina yin wasiyya a gare ku, da kaina da tsoron Allah, Allah maxaukaki yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-imrana: 102].

Musulunci yana renon mutum musulmi da hukuncinsa da hukunce-hukuncensa da halayyarsa da laddubansa akan SIFANTUWA DA MAXAUKAKIYAR HIMMA, DA BADA MUHIMMANCI GA ABABE MAXAUKAKA, waxanda za su sanya rayuwar musulmi ta yi ta xaukaka, manufofinsa kuma su yi ta qara tabbatuwa, aiyukansa kuma, su yi ta ginuwa suna bada fa'ida, domin mutuntakarsa ta yi fice, ya kuma xaga kai daga, yasassun lamura, da qananansu marasa qima, ya kuma fiskanci aiki tuquru, da buri maxaukaki, wanda zai bunqasa shekarunsa, ta hanyar gina su, da aiyuka, da sadaukarwa. Waxannan sifofin basa canzawa don an samu canjin zamani da lokatai, kuma musulmi baya kaucewa daga aikata irinsu, duk yadda aka samu canje-canjen hanyoyi, ko banbancin fasahar zamani, Umar bn Abdul'aziz (رحمه الله) ya ce: "Lallai ne Ni ina da wata rai, mai tsananin bege da himma, ban tava samun wani abu ba face na yi sha'awar abinda ya fi shi alheri, Na yi sha'awar zama Gwamna, a yayin da na same shi, sai na yi sha'war na zama khalifa, a  yayin da na samu khalifa kuma sai na yi sha'awar samun abinda ya fi shi alkhairi; wato aljannah, kuma ina fatan zan same ta".

            Musulunci ya tsarkake xabi'ar musulmi daga kukkutsawa cikin qananan lamura marasa qima da amfani, ko aukawa cikin tavon varna, izuwa ga neman cimma manufofi masu girman xaukaka, da isa ga ababe masu muhimmancin daraja, da qulla rai ko rayuwar musulmi da yin bauta ga Allah (سبحانه وتعالى) wanda hakan shi ne mafi girman matsayi, kuma babbar manufa, kuma shi ya ke haskaka hanya, aiyuka kuma a jikinsa su ke rataya, kuma shi ne tushen abubuwa masu muhimmanci.

             Varna da bin qananan lamura marasa qima, su kan kautar da mutum daga manya-manyan lamura, kuma suna kashe ruhin aiki ko raunata shi, har ya zama ba za a yi fatan samun wani amfani ba, ko a aminta daga wata cuta (daga mai irin wannan hali).

            Zukatan da suka abauce, suna sauka daga aiyuka ko manufofinsu maxaukaka, sai su sanya lokutansu gabaxayansa ya zama a wargi, mafi yawan kwanakinsu kuma, ya kasance aikin kara-zube, haka kuma suna tozarta aikinsu na wajibi (dole), sai matsayinsu ya zagwanye, rayuwarsu kuma ta wayi gari a wofi, da aiyuka marasa qima.

            Himmomi suna yankwanewa, a lokacin da su ke dulmuya cikin lamura marasa qima, sai su xauki vangarori iri-iri daban-daban, kamar: QOQARIN TABBATAR DA LABARIN YASASSUN ABUBUWA MARASA QIMA,  DA JANYO ABABE MUNANA, KO WAUTA, A CIKIN WASU SHIRYE-SHIRYE (na radio ko talabijin) WULAQANTATTU, DA QOQARIN YAXA SU, TA HANYOYIN GANAWA NA AL'UMMAH (facebook), don neman suna, ko samun shaharar da ba ta asali ba, da qoqarin wasafta abubuwan da ke aukuwa marasa qima, masu cutarwar da ba sa amfanarwa, kuma masu jawo varna, wanda ba sa kawo amfani ba, sannan kuma suna munanta kama, ko tarihin mai aikata su, tare da kwaye tsiraicinsa, a lokacin da ke bayyana cikin wata tufa ko yanayi mummuna, ko ya ke wata magana ta alfasha, ko wani aiki mai aibi, ko cikin wani yanayin da zai sanya masu hankali a cikin al'umma su raina shi, masu mutunci kuma su ji qyamarsa.
A cikin hakan kuma, akwai munana wa addininsa, da qasarsa, da al'ummarsa.

            Dogewa cikin yasassun lamura, irin waxannan, ya kan sanya tsatsa cikin halayya, da tawaya cikin hankali, kuma yana nuni kan jahiltar abinda ake ce wa RAYUWA, da rashin zurfin tunani, da samun koma-baya cikin sani da wayewa. Kamar yadda ya ke kashe kyakkyawan nufi, ya ke raunata lamarin bunqasa. Kuma lallai ba zai vuya wa mai hankali ba, abin da hakan zai jawo, na varna a zamantakewa, da rayuwarsa da iyali.

            Duk wanda ya sauko, da tunaninsa zuwa ga lamura marasa qima  ko amfani, to sai ya girmama bin son zuciya, ya kuma yi sakaci, ko sako-sako da abubuwan da Allah ya haramta, Sai zuciyarsa ta yi dauxa da aikata savo, azamarsa ta yankwane, saboda aikata zunubai, fixirarsa ta addini kuma ta samu koma-baya.
Kuma ba zai vuya ga mai hankali ba cewa, lallai sababin da ya sanya wannan al'ummar samun kanta cikin qasqanci, har ta wulaqanta, a wurin Allah da halittunsa shi ne: Keta abubuwan da Allah ya haramta, Allah (تعالى) yana cewa: "Haka, Kuma duk wanda ya girmama haramiyar Allah, to shi ne mafifici a gare shi a wurin UbangijinSa" [Hajj: 30].

Miqa-wuya ga qananan lamuran marasa qima ko amfani, da abubuwan varna, na kaiwa zuwa ga/ rashin kulawar mutum ga mutane, da kuma baiyanar da aikin savo, wanda ke kashe xabi'ar kunya, wannan kuma shine abinda ManzonAllah (صلى الله عليه وسلم) ya tsawatar akansa, a cikin faxinsa: "Dukkan al'ummata za a musu afuwa, in banda masu bayyanar da laifi, kuma yana daga cikin bayyanar da laifi: Mutum ya aikata wani aiki cikin dare, sai ya wayi gari alhalin Allah ya rufa masa asiri, ya riqa cewa: ya kai wane: ai jiya da dare, na aikata kaza da kaza; shi ya kwana Ubangijinsa yana rufa masa asiri, sai ga shi ya wayi gari yana yaye sitirar da Allah ya yi masa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Allah (سبحانه وتعالى) Mai rufa asirin bawa ne, a ranar qiyama, kuma zai sanya sitirarsa ga wanda ya aikata laifi, matuqar dai bai bayyanar da shi ba, Manzon Allah (صلى الله9 عليه وسلم) yana cewa: "Lallai Allah zai kusantar da mumini, sai ya xora masa lulluvinsa, ya suturce shi, sannan ya ce: Shin ka san zunubi kaza? Shin ka san zunubi kaza, Sai ya ce: E, Ubangijina! Har sai ya sanya shi, ya tabbatar da zunubansa, ya kuma gani a cikin ransa cewa, ya halaka, Sai ya ce: Na rufa maka asiri akansu a duniya, kuma Ni zan gafarta maka su, a yau. Sai a bashi littafin kyawawan aiyukansa", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

Himmatuwa da abubuwa marasa qima, da bibiyar mutane marasa amfani: Zai sanya mu, mu samar da wassu taurari daga cikinsu, waxanda za su riqa fitowa a gaba-gaba a cikin lamura, alhalin su qazantattu ne ababen qyama, kuma za mu riqa tunkuxa su, don samun shahara, da tallen da mu ke yi wa aiyukansu munana, da fina-finansu qasqantattu, kuma hakan zai kai, a buxa musu fili domin vata jama'a, da rusa halayya, da kawar da mutane daga bunqasa a fagagen aiyukan nasara da bunqasa.
Abinda kuma ya fi xaci ko muni, Shine Ruxuwar waxannan mutane marasa qima ko amfani, da shahararsu, sai su baqanta wasu mas'aloli da basa fahimtar su, da kuma ilimin da basu mallaki mafarinsa ba; har a samu masu fitowa gaba-gaba suna fatawa cikin hukunce-hukuncen shari'a da addini cikin jahilci, da son zuciya, sai kuma a samu matar da ta fito ta ke nuna qarancin muhimmanci sanya hijabi, kuma ta ke izgili da shi, A samu wani na uku, yana izgili da karantarwar musulunci da hukunce-hukuncensa, wani na huxu kuma, yana cakalar mutuncin shugabanni, Na biyar kuma, a samu yana aibanta maluma da masu da'awa da xaliban ilimi. A zamanin da ana cewa: Idan ruwa ya fita daga cikin gora, to sai iska ta cika shi.

            Wanda ke bibiyar abubuwa marasa qima, da mutane marasa amfani: Ya kan cika yininsa da jayayya, imaninsa kuma da tawaya, azamarsa kuma da rauni, da kuma xabi'arsa ta hanyar yaxa jita-jita, sai kuma ya cutar da al'ummarsa da yaxa qare-rayi, da kawo koma-baya cikin zaman lafiya. Kuma sau nawa ne, waxannan qananan lamura marasa qima su ka haifar da rabuwar da babu haxin kai bayanta, da gaba ko adawar da bata warkewa!

            Son shahara ko neman suna cuta ne a cikin zuciya voyayya, kuma idan ya bunqasa a cikin tunanin mutum sai ya iza shi zuwa ga jin halaccin bin kowace hanya, sai ya sanya shi tsallaka kowace qima, ya kuma sanya masa wata yana a cikin zuciyarsa, ta yadda ba zai ga makamar alkhairi da hasken gaskiya, da ita ba, don haka ne, shari'a ta tsawatar daga son shahara, ko bayyana da neman suna, wanda rayuka da suke fama da cutar riya, mai rushe aiyuka, a ma'aunin shari'a su ke fama da shi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda ya sanya tufar neman shahara ko suna, Allah zai tufatar da shi ranar qiyama da tufar qasqanci", Ibnu-Majah.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka ce: Lallai ne sallata da yanke-yankena, da rayuwata da mutuwata, ga Allah ne Ubangijin talikai * Bashi da abokin tarayya" [An'am: 162-163].

            Bayan wani lokaci, wanda ya shagaltu da ababe marasa qima zai falka, bayan kuma waxanda suka ci nasarar rayuwa sun wuce shi, kuma masu yin abu babu wargi sun xaukaka sun barshi (a qasa), To, a wannan lokacin ne kuma zai ciza yatsun nadama, a lokacin da zai ga kansa cikin barci mai nauyi, da kawalwalniya mai yaudara, (saboda bai canza ba) yana nan a wurinsa na da, bayan jahilcinsa ya yasar da shi, kuma himmarsa qasqantatta ta rumbuxar da shi, lokacin gyara kuma ya wuce, kwata-kwata kuma babu damar aiki da nadama!

            Shi musulmi, ma'abucin wani saqo ne, a cikin rayuwa, yana yin nesa da kansa daga faxawa tavon lamura marasa qima da varna, da himmarsa maxaukakiya, da kuma bada lokaci cikin abinda Allah zai  yardar da shi, kuma ya amfanar da addininsa da qasarsa, da al'ummarsa, da ilimi mai amfani, da kuma aiki managarci.

            Wasiyyoyin musulunci masu gamewar ma'ana sun zo, waxanda su ke kare al'umma daga tasirin munanan xabi'u, da su ke cin karo da ginshiqan da halayya su ka ginu akansu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:  "Lallai Allah, Mai karimci ne, yana son kyauta, da maxaukakan halaye, kuma yana qin qasqantattu daga cikinsu", Alhakim ya ruwaito shi a cikin Mustadrak xinsa.
             
            Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah; yabon da bashi da iyaka.
            Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yak e bashi da abokin tarayya, kuma bamu da Ubangiji; idan bashi ba.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, manzonsa, kuma zavavvensa.
            Allah ya yi qarin salati akansa da iyalansa dasahabbansa da waxanda su ka shiryu da shiriyarsa.

            Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah iyakar jin tsoronsa, kuma ku kiyaye shi a cikin sirri da gannawa.

Su iyalai sune kariya mai qarfi ta farko wajen yaqi da yadda 'ya'ya ke bada muhimmanci  ga lamura marasa qima, ta hanyar siffantuwa da sifa mai kyau, da kasancewa abin koyi nagari, da samar da wuraren bada tarbiyya ko horo domin gina himmomi, da zana manufofin xaukaka zuwa ga samun ababen xaukakar.

Su ma kafafen sadarwa, su cika da aiyukan da ba za a yi sakaci da su ba,  wajen tottoshe wurare ko mavuvvugar ababen da basu da qima, da hana fitowar mutane marasa qima ko amfani, tare da tottoshe kafofin da su ke shigowa.
Kuma hanyar da ta fi bayyana a fili wajen aikata haka; ita ce: Aiki da tabbatattun mas'alolin aqida, da gino sifa maxaukakiya.

Kuma samarinmu masu albarka suna da rawar takawa, wajen bunne lamura marasa qima, ta hanyar, qin yaxa su, ko tallata su, ko sauraren sharewarsu.

Amma ita kuma, budurwa musulma, to kunyarta shi ne tushen izzarta da kyanta; Saboda qyale kafofin ababe marasa qima magangarar rugujewar halayya ce mai hatsari, kuma sharri ne mai yaxuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kunya da Imani an gwama su a tare, kuma idan aka xage xayansu to an xauke xayan", Alhakim a cikin Mustadrak ya ruwaito shi.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku sassauta magana; domin kada wanda a cikin zuciyarsa akwai cuta, ya kwaxaitu" [Ahzab: 32].

            Kuma musulmi zai kare kansa ne daga yasassun lamura marasa qima ko amfani, da kuma varna, ta hanyar dawwamar da tunanin haxuwa da Allah, wanda hakan zai bashi kariya mai qarfi daga duk ganin da ya qaru akan na buqata, da jin da ya wuce wanda ake buqata, da maganar da ta wuce wanda ake buqata, da hulxar da ta wuce wacce ake buqata.

            Kamar yadda dawwamar da jin cewa Allah yana ganin bawa, ya kan sanya shi, ya rataya da neman matsayin da ke wurin Allah, wanda ya fi girman xaukaka akan neman suna ko son samun shahara da bayyana.

            Kuma ma'aunin gidan lahira ba shi ne ma'aunin duniya ba, Allah (تعالى) ya ce: "Idan mai aukuwa ta auku * Babu wata rai mai qaryatawa ga aukuwarta * Mai qasaqntarwa ce, mai xaukakawa" [Waqi'ah: 1-3].

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.      
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman a garin Halab, da Shaam, da Mausil, da Iraqi, da Filasxinu, da kowani wuri ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
Ya Allah! Lallai su, masu jin yunwa ne ka ciyar da su, basu da takalma ka basu, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su ka taimake su,
Ya Allah! Duk wanda ya nufe su da mummuna to ka sanya kaidinsa a qirjinsa, kuma ka sanya rugujewarsu cikin tsare-tsarensu, Ya Mai amsa addu'a
Ya Allah ka rarraba kan maqiyansu, kuma ka wargaza haxuwarsu, ka sanya mummuna ya juyo akansu, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah Wanda ya saukar da littafi, wandas ke gudanar da gajimare, Mai ruguza qungiyoyi, ka ruguza maqiya musulmai, kuma ka taimake musulmai akansu, Ya Ubangijin talika, Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu, wanda shine qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce rayuwarmu ta ke cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda zuwa gare ta ake mayar da mu, kuma ka sanya rayuwa ta zamo qari a gare mu daga kowani alkhairi, kuma ka sanya mutuwa ta zama hutu a gare mu daga aikata kowani sharri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla musu akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu,
            Ya Allah! Ka sanya mu mu zama masu ambatonta, masu gode maka, masu tsoro a gare ka, masu yin kuka a gare ka, masu mayar da lamari,
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, kuma ka tabbatar da hujjarmu, ka daidaita harsunanmu, kuma ka cire dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da canzawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan fushinka.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada waraka ga marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, kuma ka sa mu cika da alheri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara sha'aninmu dukkansa, kuma kada ka dogarar da mu zuwa ga kayukanmu, daidai da kyaftawar ido,
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka kyakkyawan cikawa, da kuma afuwa kan abinda ya gabata, ko ya kasance
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana daga albarkokinka, da rahamarka, da falalarka, da arziqinka
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka –ya Allah- saboda kai ne Allah, wanda babu abin bauta sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma mu ne faqirai, Ya Allah ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama.
Ya Allah!, shayarwa ta rahama, ba na azaba, ko bala'i, ko rusau, ko nitsewa ba
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
            Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...