FALALAN
AZUMTAR GOMA GA WATAN MUHARRAM (YININ ASHURA)
فضل صيام 10 محرم –يوم عاشوراء-
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم
الله الرحمن الرحيم
YININ ASHURA
Shi ne yinin da a
cikinsa Allah ya tseratar da annabi Musa (عليه السلام) da mutanensa, ya kuma dulmuyar da Fir'auna da rundunarsa.
Kuma haqiqa
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
ya azumci wannan yinin; domin nuna soyayya da kuma 'yan'uwantaka ga annabi
Musa, da kuma godiya ga Allah (تعالى)
a kan yaye musiba, da kuma nasarar da ya bayar.
Kuma haqiqa ya zo
cikin hadisinsa mai girma, cewa:
«صِيَامُ يَوْمِ عَاشُورَاءَ،
أَحْتَسِبُ عَلَى اللهِ أَنْ يُكَفِّرَ السَّنَةَ الَّتِي قَبْلَهُ»
Ma'ana: "Azumtar yinin Ashura, ina kyautata zato
wa Allah cewa; zai kankare zunubin shekarar da ta gabace shi".
Kamar yadda
mustahabbi ne a azumci yinin tara (9) tare da yinin goman (10), domin savawa
Yahudawa da Nasara.
Abun qi ne, a
wannan yinin: Abinda wasu 'yan bidi'a su ke aikatawa, na riqon ranar Ashura a
matsayin lokacin bikin nuna baqin ciki, da shewa, da kuma azabtar da kayukansu,
ta hanyar marin kai, da sassara jiki (taxbir), saboda an kashe Husain bn Aliyu; domin nuna
vacin ranmu akan kashe Husain (رضي الله عنه)
zai kasance ne ta hanyar
YIN HAQURI KAN WANNAN MUSIBAR
DA KUMA NEMAN LADA
TARE DA YARDA DA
ABINDA ALLAH YA HUKUNTA
Ba wai da irin
waxannan aiyukan ba.
Ashura yana sake tayar
da fata a cikin zukata, kuma yinin ya kan
qarfafa rai, kan kusantowar nasara, ko yaye baqin ciki, da kuma jin cewa Allah
zai tsamar da masoyansa da bayinsa muminai, ya kuma halaka azzalumai, koda
bayan wani lokaci ne. kamar yadda ya tseratar da annabi Musa (عليه السلام), kuma ya dulmuyar da Fir'auna.
No comments:
Post a Comment